Showing 216001 words to 218311 words out of 218311 words

Chapter 73 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

yaja fasali cike da takaici, sannan yace, “Fawzan kafa san halin yarinyar nan bata da hankali, cewa ta tuba na tabbatar ba har zuciyarta bane ba akwai dai abinda take ƙullawa”.
“Wlhy babu abinda nake ƙullawa Daddyn Naufal, dan ALLAH ka yafe min, ALLAH zan gyara yanzu...”
“Karma ki gyara, dan wlhy zaɓi biyu ne dake yanzu a gidan nan. Kodai kibi shawarar Fawzan ki zauna lafiya, ko kuma ƙofa a buɗe take na barin gidan gaba ɗaya. Shawara ta rage ga mai shiga rijiya....”
Ya miƙe abinsa yama fice a sashen. Nasiha sosai Yaya Fawzan ya sake mata sannan ya fito shima. Yana fita babu jimawa Mamanta ta shigo. Zama tai kusa da Saheeban. Ta ɗago da sauri tana kallonta da mamaki. Murmushi Nana tai mata da faɗin, “Ai naji duk abinda kuka tattauna ina bayan window ɗinku. Ina son ki bisu a hakan kawai, dan na fahimci dole ne mu sake sabon taku musamman akan uwarsu (Mamy😆). Dole ne mu ajiyeta a gefe muyi abinda ya dace. Na gaji da wannan tafiyar hawainiyar, ki kwantar da hankalinki komai zai zama labari, daga ke har Nuratu sai kunyi dariya. Dan haka ki jawo ƴar uwarki ta dawo nan ta zauna tare dake, tunda aikin maƙaryatan malaman nan yaƙi ci yaƙi cinyewa sai mu koma kissa, dama can Hajiya Turai ta sani wannan biye-biyen banzar da babu riba. Yanzu kam wasan ɗan gaske za'a buga. Fatana dai Nuratu ta shigo gidan ki samu abokiyar gwagwarmaya.”
“Mama niko da zaki yarda da an haƙura da abubuwan nan. Wlhy da kike ganin Mamy jarumar kanta ce. Kuma a ɗan zaman nan nawa sashenta fahimci abubuwa da yawa a kanta. Kanta kawai ta sani wlhy, sannan amfani kawai take damu dan ganin ƴayanta sun dawo tafin hannunta. Ki duba fa kiga maganar kishiyar nan ko'a jikinta, sai ma hankalinta data maida akan wani abu daban da ban fahimta ba.”
“Na fahimci komai Saheeba, shiyyasa nake son muma mu canja salo, dan munyi sake na jingina da alfarmarta tun farko. Dan ya kamata ace tun bayan shigowarki gidan nan mun raba aiki da ita, amma yanzu ma bamu makara ba. Itama Nuratu zan zauna da ita, ku kwantar da hankaliku ku canja taku. Ku koma musu yanda suke so ta haka ne za'a buga wasa ɗan gaske. Dan a yanzu gaɓar wasan ƙarshe ake mai nasara ya ɗauki kofi. Ina fatan ke da Nuratu kune zaku ɗauki wannan kofin koda tsiya ko da tsiya-tsiya. Ku barta taje can tai nata wasan da kishiyar tata, kai ku koma yima Fateeman hidima a yanzu, ku maida ita uwa kuma a gidan nan, duk wani rashin arziƙi da take sakaku kuna mata a baya yanzu ku daina shi. Zata gane cewa mu gatanta ne, sannan da bazarmu take duk rawa, bamune mukeyi da tata ba. Sai ta biya diyyar marin da tai miki tas”........✍️


Tofa Mamy, kin raini mayakanki zasu dawo yaki dake yanzu 🥺








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣7️⃣




______________




.....Sosai Saheeba taji daɗin bayanin Mamanta. Ta kuma gamsu. Tana wucewa ta tashi ta hau gyara inda su Babban Yaya sukaci abinci, tana bin sashen da kallo dan yasha gyara sosai kam alamar amarya kawai yake jira. Hawaye ne suka zubo mata masu zafi, haka tasa hannu ta sharesu ta wuce bedroom dan gyara kanta. Dan yau bazatai sakaci ba mijinta take buƙatar kasancewa da shi, wata guda ai ba wasa ba.....


________★


Da safe ainahin rikicewa Maanal tayi da ganin Ammie. Dan AA shiru yay yaƙi gaya mata koda ta dawo daga massallaci ya ganta a kitchen. Sanin yau duk abincin da za'aci a gidan kawoshi za'ai yace mi takeyi a kitchen da sassafen nan. Batare data kallesa ba ta ce, “Abah nake haɗama abinci, nasan yau Oum ko tunawa da shi bazatai ba”.
A hankali AA ya lumshe ido ya sake buɗewa a kanta, sai kuma ya saki murmushi mai sanyi da takowa a hankali ya tungumeta. Yanzun kam kallonsa tayi, sai kuma ta saka yatsunta biyu a goshinsa. Ƙasa-ƙasa tace, “Shagwaɓan na miye kuma? Lafiyan ka dai ƙalau Besty. Ko barcin bai isheka ba?”.
Murmushi ya sake saki da jinjina lamarin Bestyn tasa, ji yanda take masa abu like wani ɗan yaronta. Hakan na sakashi nishaɗi da jinsa dai-dai da shekarunta, harma ya dinga tuna baya yana jinsu kamar a wancan lokacin.
Maanal da taji shiru baice komai ba cikin kunensa tace, “Bestie girki fa nake yi, ba kuma mu kaɗai bane ba a sashen nan wani zai iya shigowa cikin ƴammatan nan”.
Ƙin sakin nata yay ya kuma ƙi magana, sai da ya mula dan kansa sannan. Kanta ta ɗan girgiza, tare da juyawa ta cigaba da aikinta. Sake matsowa kusa da ita yay ciki-ciki yace, “Mizan tayaki?”.
“Na hutar da kai jeka kwanta, nima saura kaɗan na kammala”. Kansa kawai ya jinjina mata ya juya ya fita dan da gaske barcin yake ji kuwa. Jiya ya gaji da wannan zuwa Zarian, ya dawo kuma ya cinye daren a aiki. Itama bata wani jimaba ta kammala komai, ta shirya na Abah a basket ta shirya na AA a tray ta haura da shi sama. A dining ta shirya masa shi duk da abincin yafi ƙarfin cin mutum ɗaya ma. Koda ta shiga bedroom barci ta samu AA ɗin nayi, sai ta wuce bathroom kawai, dan ita koda kuɗi kuma akace tayi barcin yanzu bazata iya ba. Wanka tai bayan ta gyara bayin, ta fito tai shiri cikin atamfa lass da akaima wani shegen ɗinkin ƴan gayu daya zauna mata ɗas a jiki. Cikin nan a lafe babu alamar akwai wani abu tare da ita. (Koda yake hasashen Mamy ne dama ai🤣🤙) Tai ɗaurinta mara hayaniya tasa turare ta yafa mayafi kamar ka saceta ka gudu. Gaban gadon taje ta shafa kan AA dake barci ta masa kiss sannan ta ɗauka wayarsa tama kanta hoto biyu ta ajiye masa kusa da shi ta fita.
Sai yanzu da take fitowa ne take jin motsin su Maimoon na tashi, batabi takansu ba ta ɗauka breakfast ɗin Abah ta fice. Da yaya Fawzan suka haɗu shima zaije sashen Abah ɗin. Cikin tsokanar daya saba mata suka gaisa, ya kalla basket ɗin da faɗin, “Wannan kayan daɗin fa Lilly?”.
Ɓoye basket ɗin tai gefe da faɗin, “Yaya F na Abah ne ba cinsa zakai ba kuma”. Dariya yay dai-dai suna shiga, tare da faɗin, “Lilly ki dinga min biyayya nine second Abanki a gidan nan fa ke da Mijinki tam”.
“Wa kai ɗin, tab Babban Yaya dai. Kaida kake damumu da tsokala”.
Murmushi Abah dake jiyo drama ɗin tasu tun kan su shigo ya saki, a ransa yana ƙara jin ƙaunar yarinyar. Dan sam shi baya ɗaukar Maanal matsayin suruka, ƴa yake kallonta kamar sauran sojojinsa uku. Ansha tambayarsa yaransa nawa yace huɗu.... Shigowarsu ta katse masa tunani, ya ajiye littafin hannunsa yana kallonsu, su duka inda yake suka nufi, Fauzan ya zauna yana gaisheshi, Maanal ta ajiye basket ɗin itama ta zauna ƙasa kusa da ƙafafunsa tana gaishesa. Cike da kulawa ya amsa musu su dukan, kafin ya maida hankalinsa ga Maanal ya ce, “Auta har kin tashi kinyi girki da safen nan?”.
Fuskar Maanal da murmushi ta ce, “Abah kasan yau Oum ba tamu take ba, kar'a barka da yunwa shiyyasa”. Murmushi Abah ya saki, Yaya Fawzan kuwa ya ce, “To nima dai ALLAH ya kaimu randa Anum zata girma ta fara min irin wannan tattalin da ƴaƴa kema iyaye.”
Abah na dariya yace, “To amin, amma duk jealous ɗinka ni aka fara yimawa Fawzan”.
Dariya sosai Fawzan yake yi, Manaal ma na murmushi, suna cikin haka sai ga Babban Yaya da RK sun shigo, gaishesu Maanal tayi suma. Sun zauna ana ɗan taɓa hira ta miƙe domin zuwa gaishe da dasu Oum. Albarka Abah ya saka mata sosai su Babban Yaya na tayashi da Amin. Tana fita suka dasa hirar ƙyawawan halinta. Tare da taya Autansu dacewa da samun mace ta gari. Suma sunama kansu fatan ALLAH yasa amarensu su kasance kamar Maanal ɗin.


Manaal kam sashen Oum ta wuce kai tsaye. Sai da ta fara shiga ta gaida su Umma dake bedrooms ɗin ƙasa sunata faman tsokanarta irin na kakanni wanda ke matsayin iyaye na kareta. Suma dai kowa ya kalla Maanal ɗin sai ya ambaci Masha ALLAH. Dan ba ƙaramin ƙyau tayi ba a sati biyar kacal. Masu idon gane ciki da wuri kam irin su Mah-mah tuni sun fahimci Maanal ɗin ta harbu kam. Sai dai ai fatan kuma ALLAH ya inganta.
Rashin ganin Oum a ƙasa yasa ta haura sama. Sai da ta fara leƙa ɗakunan da su Aunty Rufaidah suke taga duk barci suke ta rufo musu ƙofar a hankali dan kar ta tashesu, tana shiga ɗakin Oum taci karo da Ammie. Yanda Maanal tai zuru tana kallon Ammie ya bama Oum dariya, dan su biyu ne kawai a ɗakin. Oum ta taɓata da faɗin, “Baby yaya dai?”.
Manaal ta ce, “Oum mamakin duniya ne ya isheni, yanzu ni Ammie zatazo gidan nan ta kwana ta tashi bata nuna ta san da zamana ba, dan ALLAH ya za'a kira wanan abun, sallamawa ko mantawa?”.
Ba ƙaramar dariya ta bama Ammie da Oum ba, amma sai Ammie ta fiske. Oum dake gimtse dariya ganin Maanal ta fara hawaye tace, “Gaskiya ƙanwata baki kyauta ba, ki kwana ki hantse yarinyata bata san kina gidan nan ba, to faɗa mana, kin sallama mu ne ko kin manta da mu?”.
Ammie dake murmushi ta ce, “Aunty ai ni nama manta anan gidan take zaune. Kuma ni ai ba wajenta nazo ba.”
Kuka Maanal ta fashe da shi. Zata juya ta fita Oum ta riƙota tana faɗin, “Ƙyaleta kinji Baby, so take dama ta kunnaki. Indai zata manta da ɗiyata nima kuwa zata manta da ni kenan”.
Dariya Ammie tayi kawai, dan kallo ɗaya tama Manaal ɗin ta fahimci halin da take ciki. Shagwaɓa, saurin kuka shine salon da take fara fahimtar ta samu ciki. Dan duk rashin mutuncin Babu a farkon samun cikinta kasa gane kanta yake. Birkice masa take sosai, abu kaɗan ta hau taita masa masifa, duk kuma abinda zasuyi faɗa tasan hanyar takaloshi, haka ma cikin su Waleed tayi, dan Daddy lokacin data samu cikin Hameed abinda ta dinga masa sai da yace ko aljanu gareta. Sai daga baya data samu cikin Waleed sai ya fahimta cikine ke sata wannan riginar...
Rungumeta da Maanal tayi ya katse mata tunaninta. Ta kalleta tana murmushi, sai kuma ta shafa bayanta cike da lallashi ta ce, “Kefa shagwaɓar ki tayi yawa Auta, yanzu miye abin kuka to anan?”.
“Ammie bakin daina soma ba”. Ta ƙara faɗa cikin kuka bil haƙƙi. Abin sai ma ya ƙara bama Ammie dariya ƙwarai da gaske. Amma ta danne dan tasan irin wannan yanayin sarai. Cikin sake kwantar da murya da lallashi ta ce, “Ni na isa na daina son Auta ta, Babyn Oum ɗinta. Yi haƙuri sanda muka iso ance kina barci shiyyasa nace abarki sai kin tashi. Harfa tsaraba nayo miki”.
Tashi Maanal tai tana dariya ga hawaye kuma. Ta zauna da ƙyau tana faɗin, “Shike nan na haƙura”. Sai kuma ta sake rungume Ammie ta ce, “I really miss you Ammie.”
Cikin kunne Ammie ta raɗa mata, “I miss you too Autar Ammie”.
Maanal ta ƙara ƙanƙame Ammie tana dariyar farin ciki. Kafin ta sake tashi da ƙyau ta zauna ta gaisheta da tambayarta su Waleed da Aunty Sakeena da su Nene?.
“Kowa yana nan lafiya. Su Hameed anjima zasu zo da Daddynku wajen ɗaurin auren Yayanku. Sakeena ana biki dangin babansu shiyyasa basu zo ba har su Nene.”
“ALLAH ya sanya alkairi. Didi Amaal bataje Zaria ba?”.
“Bataje ba surukarta jiya aka kai asibiti, amma da sauƙi itama yau zasu taho da mijin, nasan ma yanzu sun taso”.
Addu'a Maanal taima mara lafiyar, sai kuma suka fara hirar yaushe gamo. A haka Oum data fita tun ɗazun saboda masu kawo abinci da suka kirata sun iso ta dawo ɗauke da abincin data shiryoma Ammie. Sannu Ammie tai mata. Oum ta zauna tana faɗin,........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login