Showing 204001 words to 207000 words out of 218311 words

Chapter 69 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

akan Mamy taji ta tsani matar sosai. Haka family ɗin Darma suke akwai kishin nasu. Akan ɗan uwansu komai zasu iya maka suna son juna. Yanzu ma darajar su Babban Yaya dake a wajen taci Nuwaira ta gaisheta. RK ma dai ya gaisheta dan shi akwai iya taku, yanda Mamy ta iya fuska biyu shima baka isa sanin shike ƙullama Mamyn tsiyataku ta ƙarƙashin ƙasa ba. Suma su Maanal su Yaya Fawzan duk sun mata Barka da fitowa. Tadai danne duk tana amsawa fuska a sauƙaƙe. A haka Abah da Oum suka sakko daga sama suna dariya. Daka gansu kasan baibaye suke da kwanciyar hankali da farin ciki, ga tarin ƙaunar junansu da bata ɓoyuwa a cikin idanunsu kida a gaban ƴayansu ne. Abu mai nauyi ya tsayama Mamy a maƙoshi, haka dai ta danne sa da ƙyar Hari Abah ya zauna Oum kuma ta zauna a kusa da ita tana gaisheta fuskarta da fara'a. Dannewa tai ta amsa, Saheeba ma da tunda ta shigo babu wanda ya kulata ta gaida Oum da Abah........✍️










*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣0️⃣




______________




.....Sai a lokacin Nibras ta shigo, duk tayi wani wujiga-wujiga itama ta rame. Itama dai ta gaida kowa sannan ta nema waje ta zauna. Aba ya fara da gyaran murya dan haka kowa ya sake nutsuwa ya bashi hankalinsa. Yay musu sallama da addu'a, kafin ya fara da faɗin,
“Na tara ku anan ne domin dalilai guda biyu. Na farko nasiha a garemu baki ɗaya. Musamman akan zamantakewar gidan nan da nake ganin tana neman canja salo daga bigiren da muka ginosa na shekaru zuwa yanzu. Hakan baya min daɗi. Muɗin ahali ɗaya ne, da su da aka haifa a gidan, da ku da suka auro a wajena a yanzu duk matsayinku ɗaya ne, domin duk ƴaƴa kuke a wajenmu. Ita rayuwar aure ibada ce, daga ɓangaren mace har na namiji duk wanda ya samu raunin sauke hakkin ɗan uwansa akan ganganci UBANGIJI bazai barshi ba. Sannan kuma masu haihuwa ne, wataran zaku aurar da naku ƴaƴan ko mazan su auro muku. Dan haka ina nasiha a gareku da komai ma a ajiyeshi hakanan ya isa. Mu haɗu mu zauna lafiya da junanmu kamar yanda muka saba. Karna sake jin ko ganin wani yazo daga waje ya tada min tarzoma a gida akan abinda bai shafesa ba. Idan ba hakaba kuma zan ɗauki mataki.”
A nutse suka shiga bashi haƙuri, tare da neman afuwa. Aba ya cigaba da faɗin, “Abu na biyu hidimar biki dake tunkaro mu. Kowa dai yasan an ɗaurama Fawzan aure a cikin hidimar bikin nan na Ajwaad, bata tare bane saboda exam da take yi kuma Alhamdullah ta kammala. Dan haka zamu fara shirye-shiryen tarewarta nan da kwana goma. Sai dai ba ita kaɗai bace, dan wani alkairin ya sake shigo mana. Shima Fadeel zai ƙara auren......”
Wani irin kallon Abah Mamy da Saheeba sukai. Cikin rawar murya Saheeba ta ce, “Abah! Fadeel kuma?”.
Wani banzan kallo Babban Yaya ya jefa mata na ki shiga hankalinki. Abah kuwa sai yay murmushi. A nutsensa ya ce, “Tabbas Fadeel Saheeba, domin ALLAH ya bamu dama mu maza muyi mace daga ɗaya har zuwa huɗu. Sai dai ba hakan na nufin ku da muka fara ajiyewa zamu wulaƙanta ku ba, ko kuma mun ƙara ne dan mu wulaƙantaku. Sam ba haka bane ba, shi ƙarin aure da son mace fiye da ɗaya a jininmu mu maza yake”.
Ƙasa-ƙasa Maanal ta kalla AA, sai akai sa'a shima kallonta yake. Ganin yanda idanunta suka cika da ƙwalla sai ya shiga girgiza mata kai, tare da yi mata alamar shi dai banda shi. Ba AA da Maanal kawai ba Nuwaira nacan ta tsare RK da ido itama fuska kicin-kicin. Shima dai lallashi yake da ido dan Abah na neman ɓallo ruwa da wannan jawabi gaskiya. Duk abinda suke Abah na lure da su, dan hankalinsa nakan kowa. Sai abimma ya bashi dariya. Amma dai ya danne baiyi ba. Cigaba yay da faɗin, “Amma hakan ba yana nufin kowane namiji nada wannan ra'ayin ba. Wani ƙaddara ce take sakawa ya ƙara, wani auren dole ma ake masa da tsiya-tsiya....” kallonsa Oum tai dan tasan da ita yake kuma yanzu, aiko shima kallon nata yake, ya saki wani guntun murmushi ya ɗauke kansa. Mamy kam wani irin dukanta kalaman Abah ɗin sukayi, suka kuma shiga yimata kai-kawo a zuciyarta da tai nauyi sakamakon ambata zancen auren Fadeel. Oho Abah ya cigaba da maganarsa. “Wasu kuma sakacin matan dake gidan ne ke sakasu son su ƙara ɗin, wani kuma shi dama ra'ayinsa kenan. Kai wani jin daɗin ƙyautatawar da ake masa ma zata iya sakashi ya ƙaro dan farin cikinsa ya ƙaru. To koma dai miye sai mu zama masu tsarkake zukatanmu a komai na rayuwa. Ku dukanku shaida ne kun taso kunga iyayenku su biyu ne, kuma babu wanda zaice ga wata rana tazo suna sa'insa a tsakaninsu, ko cin mutuncin juna, ko wani abu makamancin hakan. Ina son kuyi koyi da su, domin mu haɗu mu gudu tare mu tsira tare. Hakan zai sakamu a farin ciki baki ɗaya, dan gaskiya bana son halin banza. Nayi tunanin a saka musu gini suma, sai dai guri ya ƙure mana gaskiya, dan haka kuyi haƙuri zaku fara zama a tare waje guda zuwa bayan babbar salla za'a sanya aikin nasu suma tunda muna da filin yin hakan. Akwai auren Maimoon itama da Ameer, dan haka sai mu fara shirye-shiryen dukkan abinda ya dace. Ina sake gargaɗin kowa da bana son kowane irin tashin hankali a gidan nan, mu mutunta kammu ayi taro lafiya a tashi kamar yanda aka saba. Idan ba haka ba, duk ta inda wani abu ya ɓullo to lallai Zan hukunta ko wanene da hukunci mai tsauri. ALLAH yay muku albarka. Ya bamu zaman lafiya baki ɗaya. Kuje abinku. Amma Saheeba da Nibras su zauna zanyi magana da su. Kaima Rafeeq zauna”....


_________★

Nasihar Abah ta saka kowa nutsuwa a zahiri. A bayan fage kam Mamy da Saheeba a birkice suke. Dan tunda ta koma sashenta bedroom ta shige ta kulle kanta. Bala'i ne fal a cikinta, sai dai shakkar sakamakon yinsa ya hanata fitarwa. Fin minti talatin ta gama yanke shawarar zuwa yau dai ga Abah, amma kafin haka zata fara da Fadeel ne.
Babban Yaya na tsaye a compound shi da AA da Fawzan suna magana kiran Mamy ya shigo masa. Koda yaga itace bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga. Sai dai tunda ya ambaci sunanta AA da Fawzan suka maida hankalinsu kansa sosai. Koda ya sauke wayar daga kunnensa dan umarnin zuwa kawai ta bashi ta yanke baice ma ƙannen nasa komai ba sai “Ina zuwa”.
Da kallo duk suka bishi, sai kuma Fawzan ya kalla AA. “Da alama shima Babban Yaya Mamy bata son ƙara auren nan nashi”.
Murmushin basarwa AA yayi, tare da faɗin, “Kai ko Yaya taya zata so ama ƴarta kishiya”.
“Amma tana son aima ƴar wasu tunda tana son kai ka auri Nuratu. Ni nayi mamaki ma yau da bata kawo batun Nuratun ba”.
“Maybe tayi shirun ne dan na Babban Yaya ya bata mamaki, tunda koda alama shi ba taɓa nunawa yay zai ƙara ba. Lokaci guda abin ya taso”.
“Hakane kuma”.


★Babban Yaya yakai zaune yana kallon Mamy da mamakin ganin yanda ranta ke a matuƙar ɓace. Cikin kasa iya shanyewa ya ce, “Mamy lafiya kuwa?”.
Bata amsa masa ba, sai ma tambaya ta jeho masa a fusace. “Fadeel wace yarinya ce zaka aura?”
Kai tsaye babu wani kwana-kwana ya ce, “Ameerah ce”.
“Ameerah! Wacece hakan?”.
Ɗan jimm yay na mamaki, sai kuma ya ce, “Wai Mamy lafiya kuwa?”.
“Tambayarka nai wacce?”.
Sai da ya furzar da iska sannan yace, “Ƙanwar Ameer nan makwaftanmu ƴar Momy Shuwa”.
“To baka isa ba! Ba kuma zai yiwu ba!”.
Murmushi ya saki a karo na farko. Cikin girgiza kai ya ce, “Mamy dan mi bazai yiwu ba? Saboda Saheeba kike tunani ko ƴan uwanki. Mamy bazan ɓoye miki ba na gaji da halin Saheeba. Na miki iya biyya akan zama da yarinyar nan mara tarbiyya, nayi haƙuri nayi kawaici, sai dai anzo gaɓar da komai zai iya faruwa. Dan zaɓi biyu ne. Kodai ta zauna da wadda zan auro, ko kuma na saita mata hanya. Amma bazan iya haƙurin ƙin ƙara aure ba. To mima ya rage iyaye har sun shiga hatta sadaki an bada. Mamy farin cikin Saheeba yafi nawa muhimmanci ne a wajenki? Nayi haƙuri na rasa Shahidah, ALLAH ne shaida kuma har gobe ina son yarinyar nan, na auri Saheeba, tsahon shekaru bana jin daɗin zama da ita, ban taɓa zuwa na miki ƙorafi ba duk wani banzan halinta na shanye ma cikina. Yanzu kuma naga wadda zata bani salama da kwanciyar hankali saboda kar ran wata banza Saheeba ya ɓaci sai na haƙura Mamy. Oum ta bani goyon baya, Abah ya bani goyon baya, miyyasa ke bazaki bani ba? Dan tana ɗiyar ƴar uwarki?. Gaskiya kimin afuwa babu abinda zai hanani auren nan sai dai idan na mutu ne kafin kwanakin”.
Daga haka yay shiru ransa a matuƙar ɓace. Ai mutuwar tsaye Mamy tai tana kallonsa. To ashe gwara-gwara Fawzan ma. Tana ganin AA yafi Fawzan, to ashe Fawzan ma mai biyayya ne. Dan gaba ɗaya ma Fadeel yau ya juye mata ne kamar Abah. Wlhy saima taji ta rasa abinda zatace masa. Sai wani irin tsuma da jikinta ke mata. Zuciyarta kam zafi take mata, gashi tai nauyi a cikin ƙirjinta...
Dai-dai nan Saheeba ta shigo tana sharar hawaye. Ganin Babban Yaya zaune sai ta tsaya tana kallonsa kukan na sake kufce mata. Ƙasa takai durƙushe, tana ƙara fashewa da kuka ta ce, “Dan ALLAH na tuba Daddyn Naufal, dan ALLAH kada kamin kishiya, wlhy na rantse maka zan canja, duk abinda kake ganin inayi baka so zan daina shi. Dama bayin kaina bane Mamy da Mama ke sakani yinsu. Amma wlhy bazan sake biye musu ba....”
Da wani irin sauri Mamy ta kalla Saheeba, har taune harshe take wajen faɗin, “Saheeba! Wace banzar magana ce wannan. Nice ma zan sakaki ki masa halin rashin arziƙi?”.
Babu ko ɗar Saheeba ta ce, “Wlhy kece Mamy, ke da Mama kune ke tsara komai kuce nayi saboda na ƙwato muku shi daga hannun O......”
Ai wani irin tassss!!! Kake jin Mamy ta saukewa Saheeba mari. Zata ƙara magana ta sake ɗauketa da wani marin na biyu. Sannan ta ce, “Wawuya kawai, kin haukace ne? Kodan mijinki zai aure sai hankalinki yabar jikinki har ki kasa tauna maganar dake fitowa daga bakinki. To idan kin manta bara na tuna miki nice na haifi Fadeel har kika aura shashasha”.
Tsam Babban Yaya da mamaki ya kashe ya miƙe. Raɓasu yay ya fice abinsa zuciyarsa na matuƙar jinjina al'amarin Mamyn da Saheeba. Mizai saka Mamyn harzuƙa haka dan Saheeba tace sune suke sakata yin abu. Sannan a ina za'a ƙwatoshi kuma? To shi koma dai minene su suka sani, aure dai kam in sha ALLAHU babu fashi sai yayi. Ita kuma ya rage nata ta gyara ko ta cigaba da yin abinda tai niyya shima zai fara yin wanda yay niyya kuwa. Dan yanzu ya ɗauki ɗammarar saitata a layi. Abinda ya ɗauka a baya ko kwatarsa bazai ɗauka a yanzu ba daga garetan............✍️


😂😂Hajiya Mamy yada haka kuma. Marin surukai fa baida ƙyau gaskiya🤣.








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣1️⃣




______________




.....A wannan dare dai Mamy bata iya ta tunkari Abah ba, dan Babban Yaya da Saheeba sun fusata ta. Sai washe gari da safe suna shigowa daga massallaci tai dakonsa. Dan suna fita dama ta fito a nata sashen sai ga Oum ta fita daga sashen Abah ɗin dan dama ita haka take yi. Sai kawai tai wuff ta shige ita bayan ta gama zagin Oum da tsine mata a zuciya. Anan falon Aban tai sallar asuba. Ta cigaba da zaman tsammanin dawowarsa har suka shigo.
Koda Abah ya shigo ya ganta ɗauke kansa yay tamkar bai gantan ba. Sai taji gaba ɗaya ta sake rikicewa. Amma haka ta daure tace masa ina kwana. Idan bangon ɗakin ta tanka shima ya tanka. Jikinta na ƴar tsuma ta tari gabansa, muryarta na rawa tana kallonsa da idannunta da suka kaɗe ta ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka saurareni ko sau ɗaya ne. Wlhy-wlhy ba abinda kake tunani bane ranar zan gaya maka gaskiyar komai, Fadeel ne......”
“Kinji nace miki ina buƙatar sanin miya faru ne?”. Abah ya katseta babu alamar hayaniya a muryarsa.
“Kayi haƙuri dan girman ALLAH. Zan maka bayani koda bakace kana buƙatar ji ba ko hakan zai sa ka sassauta min. Wlhy a duniyar nan fushinka shine mafi ƙololuwar tashin hankalina fiye da komai kaima ka sani”.
“Ni a suwa da fushina zai zama ƙololuwar tashin hankalinki Kamila. Idan ma shi ɗinne kwantar da hankalinki baki da matsala dani. Duk abinda kike tunanin dai-dai ne ƙofa a buɗe take kiyi abinki.” ya ƙare maganar da raɓata zai wuce. Da sauri ta riƙo hannunsa tana fashewa da kuka. Fisgewa yay ƙoƙarin yi ta riƙesa da hannu biyu duka da iya ƙarfinta kuma.
“Amma kin san zan iya marinki ko?”.
“Gara ka marenin, wlhy gara ka mareni da wannan fushin dai da kake yi dani. Ka tausaya min dan ALLAH ka duba min, wlhy ji nake kamar zuciyata zata tarwatse.” kuka mai ƙarfi ya sarƙeta. Shiru kawai Abah yay yana kallonta. Kamar wanda ya fahimceta sai kawai jitai ya zare hannunsa yay gaba. Sai da yaje zai shiga bedroom a kausashe ya ce, “Ki gayama ƴan uwanki akan wannan bikin wlhy-wlhy duk wanda ya nema ɗaga hankalin iyalina nima sai na ɗaga nashi. Ba kuma lallai dole bane sai ƴaƴana sun zauna da ƴaƴansu. Hanawa su ɗauki wani mataki akan yaran adalcina ne, amma a wannan gaɓar duk wadda tace zata kawo musu shirme zan basu damarsu ta ɗaukar matakin da duk sukai niyya dan ina son farin cikinsu. Dan ko kece kika ce zaki ɗaga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu. Idan kunne yaji jiki ya tsira”.
Yay shigewarsa. (Dan ko kece kika ce zaki ɗaga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu) Wannan kalma tai matuƙar dukan zuciyar Mamy da girgiza mata duniyarta. Ta kuma fahimci eh lallai da gasken gaske Abah yake yi. Itako ta shiga uku, shin mike faruwa ne? Anya kuwa? Anya ganin da Abah yay musu sun fito a sashen Ajwaad ne kawai matsalar kuwa? Kai da mamaki gaskiya, akwai lauje cikin naɗi. Dole akwai wani abinda ke a ƙasa. Batun Ajwaad da Maanal ya faɗo mata a rai. To kodai binciken da take tunanin zasu iya yi suka yin ne?. To amma ta ina? Inma zasu bincika ai Doctor ne kwai, jiya jiyan nan kuma Hajiya Turai ke sanar mata a binciken da tai Dr Tofa ma baya Nigeria kusan shekara biyar kenan. To kodai munafukar matar can ce tai mata wani ƙullin?. Zuciyarta tafi tsayawa a hakan, sai dai hujjar ta mata rauni da yawa. Amma ko akan batun auren nan ta tabbata akwai saka hannun Fateema. Kenan dai Fateema ta cita wasa. Ajwaad ya auri ƴar ƙawarta, Fawzan ƴar ƙanwarta, ga Fadeel ma zai auri ƴar ƙawarta. Shike nan yaƙinta na shekaru ya tashi a banza. Tunda ga Saheeba nata auren na rawa, Nibras ma bata sakata a sahun mata ko wanda take amfana. Auren Nuratu na tangal-tangal. Tana a ruwa fa kenan har yana shirin zuwa mata wuya idan bata tashi tsaye ba. Ga wancan batun duk da tana ƙoƙarin hidden ɗinsa yana nan daram a ranta, yana kuma cimata zuciya.....


________★


Anan ɓangaren Oum kam shirye-shiryen biki suke hankali kwance. AA ya riga yay order ɗin kayan lefen Fawzan tuni, yanzu kuma gana babban Yaya. Duk da zai iya yin hakan shima saboda kawai yaje ya ɗan huta da tashi amaryar sai suka tsiri tafiya Dubai wai haɗo lefe shi da RK da Maanal da Nuwaira. Sarai Oum ta fahimcesu, dan haka batace komai ba face binsu da addu'a. Shima Abah koda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login