Showing 48001 words to 51000 words out of 218311 words
Chapter 17 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
samu fiye da haka. Bakiga Oum ba, koda yaushe tana cikin farin ciki, saboda tana da ƙoƙarin ɗaukar jarabawa da sauƙi. Mamy muna sanki kamar yanda muke son Oum, yanda kuke treating ɗin rayuwarmu ne ya banbanta. Dan ALLAH ki ajiye komai kinji Mamyna”.
Kanta kawai ta jinjina masa, duk da kalamansa sun mata daɗi matuƙa a zuciya wani yanki na cikinsu sun mata zafi da ɗaci, ba komai ya kawo hakan ba kuwa sai jingina Oum da yayi a ciki har yana nuna mata yin koyi da ita. Cikin basar da komai ta ce, “ALLAH ya shige mana gaba Ajwaad! Kaga Nuratu?”.
“Amin ya rabbi, na ganta tana sashenmu”. Ya bata amsa a tausashe cikin danne komai, dan harga ALLAH ko sunan yarinyar nan baya son yaji ta ambata masa. Cikin tausasawa Mamyn ta katse masa tunani da faɗin, “Ajwaad kaga dai komai kace zan yisa domin samun farin cikinka, kaima ina son ka kula da Nuratu domin samun farin ciki na a ɗan zaman nan da zatayi da mu na azumi, Hajiya Turai ce zata umrah shiyyasa ta dawo nan ta zauna. Idan ka kwantar da hankalinka zaku fahimci juna a ɗan zaman nan da zatayi kafin bikinku. Ajwaad Nuratu na sonka sosai, irin son da duk yanda ka taƙwanrata zata maka biyayya, bar ganinta haka a tsaitsaye tana da hankali, gata ne kawai da Hajiya Turai ke mata na tsiya ya mata yawa. Amma nasan kai ɗin jarumi ne, zaka gyarata a yanda kake so yarona”.
Kansa kawai ya jinjina mata, dan baya son raunana mata zuciya, sannan yana son binta da wannan salon ko ALLAH zai taimakesa ta canja. Itama dai kusan tunani iri ɗaya sukeyi, dan tana ganin AA ɗin ya amshi batun nata da muhimmanci a yau, dan haka zuciyarta gaya mata take lallai tana da buƙatar canjawa, canjawa irin wadda Ajwaad ɗin keso kodan samun nasara a kansa, dan ta ƙarfin tsiya tabbas bazata taɓa samunsa ba, tunda ta gwada hakan tsahon shekaru kenan babu wani canji saima caɓulewar abubuwa. Ita dama bata jin su Fadeel, a ganinta duk a tafin hannunta suke. Ajwaad shine uban taurin kai da kafiya, sannan shine baisha nn ɗinta ba, zaifi mata wahalar janyewa fiye da su Fawzan da suka sha daga jikinta bayan dakon ɗaukar ciki dana haihuwa. Dan bazatace raino ba wannan kam Fateema tayi tare da cin kashinsu da fitsari. Dan in har batai ƙarya ba zata iya irga adadin wanke musu koda kashi da fitsari ne, shima sai in Oum ta fita wani uzirin ne ma.
AA nason tashi ya tafi sashensa ya watsa ruwa amma hirar da Mamy ke jansa da ita cike da farin ciki yasa ya haƙura ya zauna har akai kiran magrib, ƙarshe alwala ma catai yaje ɗakinta yayi. Haka kuwa ya haura saman yayo duk dan sanyata a farin ciki. Daya fito taita sanya masa albarka jitake kamar kada ta barshi ya tafi, sai dai hakan ya zama tilas babu yanda ta iya. Bayan fitarsa da wannan farin cikin ta kasance, tana idar da salla kuwa ta kira Maman Saheeba ta sanar mata komai. Suna yanke wayar daga can Maman Saheeba tace “Ina yaya Kamila bazai yiwuba, lokacin samun irin wannan farin cikin naki baiyi ba, ai idan har na bari kikai nasarar jawo Ajwaad jikinki to tabbas aurenshi da Nuratu bamai yiwu bane ba, nasan halin MAKIRIN yaron nan, tsaf zai juya miki tunani da hatsabibancin sa, dan yafi sauran ƴaƴanki taƙadaranci kema kina faɗar hakan da kanki. Kansa a buɗe yake matuƙa da sanin duniya, in har ba a yanayin da kuke ciki a baya ba lallai zai botsare ne”. Nanfa ta shiga kai-kawo na neman mafitar hanyar ɓata komai....
★Ana idar da salla AA dole gida ya dawo domin yin wanka kafin isha'i, tunda Mamy ta cinye masa wancan lokacin. A tare suka shigo da Ya Fawzan, babban yaya bai dawo gidan ba har yanzu. Sashen Mamy Fawzan ya nufa domin gisheta, shi kuma AA ya nufi nasa sashen dan yin wanka.
Bayan Fawzan ya gaida Mamy zai tashi sai ta ɗakko masa hira, mamaki ne ya kama shi, dan sam babu hakan a tsakaninsu tun suna yara. Tsakaninsu da Mamy umarnine nayi ko bari kawai sai gaisuwa. Amma batun shaƙuwa ko hira ko wasa da dariya Oum ce kawai ke musu da Abah. Daurewa yay yana amsa mata sama-sama, tsulum sai ga Saheeba da yara, da yake fita tayi Mamy bata kawo komai a ranta ba. Dan sai yanzun ne suke dawowa, zama Anum tai a jikin Fawzan tana masa labarin inda zukaje, yayinda Naufal ya nufi Mamy, a mamakin Mamyn sai Saheeba ta nema wajen zama tana faɗin, “Washa Mamy na gaji”.
Murmushin yaƙe Mamyn tai mata kawai da sannu a taƙaice dan harga ALLAH batayi murna da zaman Saheeba ɗin ba, dan zuwanta ya katse mata kasancewa da Fawzan. Kiran sallar isha'i ya saka Fawzan miƙewa ya ajiye Anum data fara barci saman gadon Mamy, cike da kulawa yace ma Naufal, “Tashi muje massallaci my boy”.
Da kallo Mamy da Saheeba suka bisu, suna gama fita Saheeba ta saci kallon Mamy ta gefen ido. Baki ta taɓe kaɗan, sai kuma ta ƙawata fiskarta da murmushi dan kaf MAKIRCIN Mamyn ta iya itama. “Lah Mamy wai ina ƴar hutun taki? Banji motsimta ba”. Ta faɗa baki a washe.
Miƙewa Mamyn tayi, sai kuma a ɗan yanayin jin haushi ta furta, “Tana sashen ƙanwar uwarta Fateema”.
Cike da mamaki Saheeba tace, “Tomi ya kaita can Oum?”.
“Oho mata”.
Mamyn ta faɗa cike da takaici tana kabbara sallarta. Harara Saheeba ta dalla mata cike da jin haushi ta fice a ɗakin zuwa nata sashen....
★Nuratu dai tunda aka idar da sallar magrib ake dakon dawowar AA sashen, sai dai kuma taji tsitt. Sai faman hararar Maanal dake karatun Alkur'ani takeyi, itako bama tasan tanai ba. Lokacin isha'i yayi suka gabatar, suna idarwa Maanal ta shiga bayi da nufin yin wanka. Hakan da Nurry ta gani itama sai ta fito ta nufi sashen Mamy. Oum ca take ta tafi kenan, sai take cemata ya zata tafi bataci abinci ba. Batare data tsaya ba tace, “Oum ina zuwa yanzu zan dawo”. Daga haka ta ƙarasa ficewa da sauri. Sanda Nuratu ta koma sashen Mamy bata sani ba, sai da ta fito cikin kwalliya da uban ƙamshi daga ɗakin data sauka sannan Mamy ta ganta. Harara ta zuba mata, zata fara mata faɗa tai saurin rungumeta tana faɗin, “Mamy ki fahimceni, na zauna ne dan nayi maganin shegiyar can, kin san kuma Ya AA ma acan yake, dole na nema mana kusanci ai. Yanzu ma komawa zanyi. Sai na dawo”. Daga haka bata jira cewar Mamy ba ta fice a sashen. Sai Mamy ta samu kanta da sauke ajiyar zuciya kawai, ita kanta rawar kan da Nuratu keyi akan Ajwaad na damunta, dan tasan halinsa baya son mace a haka...
A falo Nuratu ta sami su Oum, Maanal na zaune a ƙasa ta baje takardu da laptop tana aiki, sanye take da simple riga mara nauyi tashan iska milk color, sai veil ɗin rigar siriri data naɗa a kanta, ɗan zamawar da yay baya ya bama kwantaccen gashin goshinta damar fitowa. Sam babu ɗigon kwalliya a fuskarta, babu alamar ma ta shafa mai dan fuskar tai irin fayau ɗin nan. Hatta lips ɗinta a ɗan bushe suke kaɗan. Sai ƙamshi mai sanyi dake fita ƙasa-ƙasa. Gaba ɗaya sai Nurry tai sororo tana kallon ta, dan tayi tsammanin zata dawo taga Maanal ɗin ta caɓa kwalliya ne kamar mai shirin fita waje. Amma sai ga akasin hakan.
Itako Maanal ɗin ma kallo ɗaya datai ma Nurry ɗin sai ta bata dariya. Kwalliya fa ta ciwo sosai abinta. Anci uban shadda da yaji aikin stones sai ƙyalli suke. Kwalliya sosai a fiskarta harda lipstick ja da brawn sama gira tasha jagira, gashi ido a tsaitsaye an baza masa maskara a hakan ma na ƙari ne dan sunyi dogaye sosai. Anci ɗaurin ture kaga tsiya harda ɗan karkatashi gefe akai. Ƙamshi kam ba'a magana duk ta bulbule falon. Ita Maanal ma sai ta bata dariya, a zuciyarta tace (Aiki ja) a fili kam murmushi ta saki mai sanyi hankalinta a aikinta bazaka taɓa cewa da Nuratun take ba.
A haka babban Yaya da sai yanzu ya shigo gidan ya samesu. Shi kansu sai da ya kalla Nuratun da ƙyau, ganin kallon da yake mata ta shiga gaisheshi. Amsa mata yay da kulawa tare da tambayarta mutanen gida. Dan shi a zatonsa ma yanzu ne tazo shiyyasa. Sannu da zuwa Maanal tai masa, tare da gaisheshi. Itama ya amsa mata da kulawa yana tsokanarta da cewar “Lilly yau kuma aikin office ɗin ne har a gida haka?”.
Fuskar Maanal da murmushi ta ce, “Yaya ina ragewa ne, saboda yau na taso aiki da wuri”.
“Masha ALLAH haka ake so, ai gara kada ki koya over time ɗin tsiya ɗin nan na Auta”.
Sosai Maanal tai ƴar dariya tana nufar freight ɗin dining da faɗin, “Ai bazan koyaba Babban Yaya”. Dai-dai nan Oum ta fito daga hanyar upstairs. Itama dai kallon Nuratun tayi da ƙyau sai kuma ta janye ta maida kan babban yaya tana murmushi irin na manya. Ruwa Maanal ta miƙama Babban Yaya ya amsa yana sanya mata albarka, cike da farin ciki ta gyaɗa masa kai ta koma wajen zamanta ta cigaba da aikinta. Shi kuma suka fara gaisawa da Oum. A haka AA da Fawzan suka shigo sashen. Zama duk sukayi, cike da iyayi Nuratu tai musu sannu, sai kuma ta miƙe ta nufi freight kamar yanda taga Maanal tama babban Yaya suma ta ɗakko musu ruwan. Fawzan ne kawai yace mata “thanks”, shima kuma rabin hankalinsa naga duba takardun Maanal datai zane daya ɗiba yana kallo. AA kam ko kallon ma inda take baiyi ba, magana suke da babban Yaya ƙasa-ƙasa. Koda Babban Yaya ya miƙe Oum tace ya bari suci abinci tukkunna tunda Saheeba sai daren nan ma ta dawo gidan shi kuma yace ya gaji kwanciya zaije yayi yau bazai dawo hira ba AA bai tashi ba har sai da su dukansu suka isa dining ɗin. Maanal ma dai tana haɗa takardunta ne. Ita bama tasan AA ɗin bai tashi ba, sai da ta yunƙura zata miƙe suka haɗa idanu. Harrarta yay ita kuma ta taɓe baki. Dan tasan bawai ya daina jin haushin nata bane daman, ko ɗazun saboda ganin Oum ne.
Bata sake kallon inda yake ba ta nufi dining ɗin, sai lokacin shima ya miƙe. Kujerar kusa da Maanal ɗin yaja ya zauna, Fawzan dake kallonsa cike da neman tsokana ya wani ɗage masa gira ɗaya. Harararsa AA ɗin yayi ya ɗauke kai. Shima Fawzan ɗin sai yay gyaran murya, kallonsa duk sukai, sai kawai ya basar. Babban Yaya daya san halin tom and jarry ɗin ƙannen nasa kansa kawai ya girgiza, dan ya tabbatar da AA Fawzan ɗin yake. Kowa zai fara ƙoƙarin zuba abinci karaf Nuratu ta miƙe acewarta bari ta saka musu. Babu wanda ya hanata, dan haka ta fara zubama Oum, sai babban yaya da Fawzan, gaban AA ta dawo har tana ɗan duƙo masa wai zata ɗauki plate. Wani irin zafi ne ya turniƙe zuciyar Maanal, shiko AA ɗin ma hankalinsa ba'a nan take ba, waya yake latsawa, tabbas yana jin ƙamshin turare mai ƙarfi a kusa da shi, amma baima san na wanene ba duk da ya fahimci baƙon ƙamshi ne bai taɓa jinsa a wajen kowa ba a gidan. Nibras ce ta shigo da sallama a cikin tata kwalliyar.........✍️
_Maanal tamu kenan, gaki kuma a tsakiyar kuraye😂, bari muga yaya wasan zai kaya🏃🏃🤣_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣4️⃣
______________
........Cikin ladabin son birge AA ta shiga gaida Oum, da kulawa Oum ɗin kuwa ta amsa mata tana tambayarta yaya aikin?
“Alhamdullah Oum, tumma ɗazun na tashi na biya ta gida ne ganin Mom da tace ƙafanta na ciwo”.
“Wayyo ashsha ALLAH ya bata lafiya, yaya jikin nata?”.
“A Alhamdullah da sauƙi sosai, bama a kwance take ba”. Ta faɗa tana harrar Nuratu dake zubama AA abinci, tunda ta shigo akanta idannunta suka fara sauka, ji tai kamar ta shaƙo shegiya, dan tayi ma mamaki ubanmi ya kawota gidan. Maanal da itama dai ta shaƙa ɗin da iskancin Nuratu amma ta fiske babu wani alamar komai a fuskarta atare ita da babban yaya suka jajantama Nibras ɗin batun jikin mamanta. Sai Nuratun itama tayi mata jajen. AA dai kamar ma bai jisu ba sai da Oum ta kallesa, a taƙaice batare daya ɗago ba ya ce, “Sorry ALLAH ya bata lafiya”. Cike da sanyaya lafazi Nibras ta amsa, kallonta Maanal tayi ta gefen ido, dan bata sani ba ko ita kaɗaice ta fahimci Nibras ɗin ta canja murya wajen amsa AA ɗin. Sai ko amamakinta taga hankalin Nibras gaba ɗaya akan AA yake. (ikon ALLAH) Ta faɗa a ranta, a zahiri kam kamar ma bata san mike faruwa ba a wajen. Sai ma Nuratu data kawo hannu zata zuba mata itama, fuskarta da murmushi ta girgizama Nuratun kai murya ƙasa-ƙasa ta ce, “No barshi ma na Besty zai ishemu”. Tai maganar tana ɗaukar spoon ɗin da Nurry ta sakama AA, ita kuma ta ɗauka wani ta saka masa.
Idan Nuratu tace bataji kamar ta shaƙo wuyan Maanal ba tayi ƙarya, dan tuni annurin daya cika fuskarta sanda take zubama AA ɗin abinci a yanzu ya ɓace ɓat. Ɗauke kai Maanal tayi kamar bata ganta ba, sai ma kai hannu da tayi ta zare wayar AA ɗin ta ajiye a gefenta. Ɗagowa yay ya kalleta, itama kallon nasa take, dan haka suka ɗan zubama juna idanu har sai da Fawzan yay gyaran murya. Maanal ce ta fara janye nata cike da basarwa ta ɗauka spoon ɗin ta fara cin abincin, shiko yaƙi daina kallon nata. Fiiiyyy Nuratu tabar wajen ta koma wajen zamanta, Nibras ma sai da taji ƙwalla sun cika mata idanu. Zuciyarta raya mata take anya bazata kashe Maanal ba a gidan nan wataran. Dan sam idanun AA basa iya ɓoye abinda ke cikin zuciyarsa game da ita. Jitai gaba ɗaya abincin ya fitar mata a rai, amma tasan tana ƙin ci Oum zata dameta da tambaya ita da Fawzan.
Duk abinda kowa keyi Oum na karance da shi. Oum ta jima tana auna abubuwan da Nibras kema AA, musamman idan ta shagaltu da kallonsa ko idan tana masa magana. Sai dai duk da abinda zuciyarta ke fassara mata takan ture hakan a ranta. Amma a kwanakin nan sai irin kallon da take jifan Maanal da shi ke tsaya mata a rai, dan kallon yana kama da irin kallon kishi da jin zafi. A ganinta ko kishi ne irin na facalanci bai kamata a yakasance haka ba, dan kishin facalanci ga wanda ya saka kansa kusan na hassadar mijinki yafi mijina ne, ko mijinki yafi miki hidima fiye da nawa. Abu na ƙarshe yanda sam Nibras bata acting irin na matar gida ga mijinta a wajen Fawzan. Fawzan kullum a nan sashenta yake cin abinci safe da yamma, weekend harda na rana, itama kuma nan ɗin take zuwa taci. Sannan ko zaman cin abincin akai bazata tashi ta zuma Fawzan ba, sai dai ya zuba da kansa. Kai zasu iya zaman awa biyu a sashen ma bakaga sunyi magana da juna ba, amma idan AA na nan da yayi magana ko bada ita yake ba zata saka baki. Idan kuma har AA baya sashen ko yay tafiya to bazaka ƙara ganin Nibras a sashen ba. (Ya ilahil alamin, ALLAH kada kasa abinda nake hasashe akan yarinyar nan hakane. Lallai data cika mara hankali kuwa, da auren Fawzan a kanta ta ringa jin son wani namiji, namijin ma ɗan uwansa. Kai kai wannan kwamacala basa fatanta kuwa koda a mafarki).. shigowar Saheeba da yara ya katse Oum daga tunani, fuska cike da murmushi ta kamo su Naufal jikinta, Saheeba kuma ta zauna tana gaisheta. Itama dai abincin ta zuba, Oum ta girgiza kai kawai. Wannan lalace na surukansu na bata mamaki, matsayinsu na tsoffi su basu dafa sun kawo musu ba, sai dai kullum suzo sashensu su ci. Koda yake nan ɗin ma dai ne suke zuwa, dan ita Mamy bata ɗauka ma kanta hakan ba. Hasalima faɗa take akan ya kamata Oum ɗin ta taka musu birki. Itako sai dai tayi dariya kawai dan bazata iya ba, koba komai da yaranta su wahala da rashin abinci daga matansu gara suzo nan su ci ɗin hankalinta zai fi kwanciya.
Kowa nata cin abincinsa hankali kwance, sai dai hankalin Saheeba, Nibras, Nuratu, duk akan AA da Maanal ne, yayinda su kuma hankalin baya kan kowa, abincin su suke ci kawai a plate ɗaya, ƙasa-ƙasa AA na takalarta wai abincin babu wani daɗi. Itako tana harararsa ƙasa-ƙasa batare data