Showing 105001 words to 108000 words out of 218311 words
Chapter 36 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
yasan wannan halin na Mamy sam. Sai dai kuma abinda AA bai sani ba komai a kunnan RK ya kasance, yana ganin AA ɗin zai juyo ne ya shiga bayan motoci ya ɓuya dan shima baya son AA ɗin yasan yasan halin Mamy a yanzun. RK na a wajen zuciyarsa cike da tausayin AA har sai da ya hangesa ya shige sashensa sannan ya fito. Shiru yay a wajen yana tunani, sai kuma zuwa can ya saki murmushi dan yana ganin zai fara aiwatar da plan a na shirinsa a yau ɗin nan. Shi ɗan faka-faka ne, dan haka kai tsaye sashen Abah ya nufa dan yasan yana gidan bai fita ba. Abah kuma bai wani damu da barcin safe ba sosai....
Cikin sa'a kuwa a falo RK ya samu Abah. Zama yay kusa da shi suka gaisa cike da ƙaunar juna. Sai kuma suka fara hira abinsu. A cikin hirar RK ya ce, “Yaya nikam sai yaushe zaka ba Ajwaad iyalinsa ne?”.
Murmushi Abah yayi idonsa akan television. “Zan bashi Rafeeq, akwai abinda nake jira ne. Amma dai bayan salla in sha ALLAHU. Tunda kaga ma ya riga ya nuna mana ya daidaita da matarsa tunda har ga ciki”.
Dariya RK yay a karo na farko, sai kuma ya ce, “Tom hakan dai yafi kam Yaya, a barsu haka nan kawai, na tabbatar komai zai ƙarasa dai-daita. Sai dai inada wata shawara”.
“Okay ta micece?”.
“Ba komai bane Yaya, inaga ya kamata a sake musu sabon biki, tunda kaga sanda akai wancan su kamar ma babusu a ciki Ajwaad na fama da kansa. Ajwaad mutum ne na mutane, ya kamata ace aurensa ya shiga lungu da saƙo na ciki da wajen ƙasar nan. Sannan yanda Ajwaad da Maanal suka rayu sun cancanci bikin aurensu ya ajiye babban tarihi a kundin masoya na duniya”.
Dariya Abah yayi sosai. “Kai ALLAH ya shirya ka dai Rafeeq, wato a kundin masoya na duniya?. Shawaranka yayi sosai, dan ni kaina ina yi wannan tunanin kodan ita Maanal ma. Wlhy bazan ɓoye maka ba duk cikin surukan nan nawa nafi ƙaunarta, kuma wannan ƙaunar tun tana yarinyarta nake mata ita, jinta nake tamkar ɗaya daga ahalina. Shiyyasa ko maganar auren Nuratun nan ba sonshi nake ba sam, dan bazan so zamansu tare ba sam...”
(Anzo wajen) RK ya faɗa a zuciya, a fili kam fuskarsa da murmushi ya ce, “A'a yaya ba'ace haka ba, tunda bamu san mi ALLAH ya shirya ba. Amma da zai yiwu kodan samun nutsuwar zamansu ka zauna da AA ɗin kaji ta bakinsa akan hakan. Idan ya nuna baya so to a bashi lokaci ana ƙara kwaɗaita masa auren Nuratun har komai ya dai-daita”.
“Uhmmm kuma hakan fa yayi Rafeeq. ALLAH yay maka albarka, shiyyasa a kullum nake faɗan kai yaro ne da halin manya.”
Murmushi RK yayi sosai, dai-dai nan babban Yaya yay sallama. Abah ya bashi izinin shigowa. Ganin su zaune kamar masu meeting ya ce, “Tunda meeting ake na ƴan uwan juna kona koma ne?”.
Dariya Abah da RK sukayi. RK yace, “Shigo ai mun gama”.
Fuskar babban Yaya da murmushi shima ya ƙaraso. Abinda suka tattauna ɗin RK ya tisa masa amma banda batun Nuratu. Aiko babban Yaya ya bada goyon baya shima ɗari bisa ɗari. RK ya ɗaga waya ya kira Fawzan shima. Babu jimawa ya shigo da alama baima jima da tashi barci ba. Anan suka dinƙule suna shawarar shirya bikin. Shi ko AA bai san anayi ba, yana can sashensa yay wanka ya kwanta al'amarin Mamy na cizon masa zuciya....
★Bayan sun dawo tafsir har akai azhar Mamy bataga idon AA ba. Ranta sai ya ƙara ɓaci matuƙa. Ta ɗaga waya zata kirashi sai ga Fawzan ya shigo sashen. Duk yau basu gaisa da Mamyn bane shiyyasa yace bara ya shigo ya dubata dan fita zai yi. Ita kaɗai ce zaune a falon sai Anum na barci a kujera. Tunda ya shigo take kallonsa fuska da ɗan murmushi dan ta haɗiye ɓacin ran AA dake cimata rai da ƙyar. Zama yay yana gaisheta, ta amsa masa da kulawa, tare da tambayarsa fita zai yi?.
“Eh wlhy Mamy zan ɗan je wani waje ne, tun ɗazun naso fita sai kuma zafin ranar nan ya hanani. Yanzu naga ta ɗan risina shine zanje na samu na dawo da wuri bana son tafsir ya wuce ni”.
“Eh haka na da ƙyau kam. ALLAH ya taimaka ya bada sa'ar abinda za'a fita yi ”.
Cike da jin daɗi ya amsa da Amin. Sai kuma ya yunƙura zai tashi idonsa akan Anum yace, “A'a Babyna kuma ana nan ashe?”.
Cikin ɗan taɓe baki Mamy tace, “Tana nan ai yanzu ɗasawa muke yi, uwarce abu kaɗan ta make su gaba ɗaya ta koya faɗa kwana biyu, kuma ina zaton kamar ciki ne ya sata hakan”.
Cike da farin ciki Ya Fawzan ya ce, “Wow! Ciki Mamy. Kai Masha ALLAH abu yayi ƙyau, abinda ake ta fata”.
“Aiko dai ai dama komai lokaci ne da shi, balle ma tunda har anyi biyu dama sun so tada hankalinsu ne. Saura ku, ALLAH ya kawo muku naku.”
Murmushi kawai Ya Fawzan yay baice komai ba. Sai kuma ya fara ƙoƙarin miƙewa. Dakatar da shi Mamy tayi, kafin ta fara magana muryarta na ɗan rawa. “Fawzan amsa min zaka yi da amin ba shiru ba, al'amarin nan naku na damuna, ni dai da ace zakabi ta tawa da aure ka ƙara, kwanaki na maka maganar hakan ba kace min komai ba. To gaskiya na fara zuwa bango da zaman nan haka babu haihuwa. Shiyyasa ma duba nan”. Ta miƙa masa wayarta. Bai musa ba ya amsa wayar. Hoton ƙyaƙyawar budurwace da zata iya kai 29years haka. Daka ganta kaga ƴar gayu sannan gogaggun ƴan boko fitsararru. Fara ce tas dan duk da a hoto ne a kallo ɗaya zaka tabbatar da farar ce. Batare da nuna wani yanayi ba ya ɗago ya ce, “Na ganta Mamy wacece ita?”.
“Ita ce wadda nake maka sha'awar aure Fawzan”.
Wani kalar, dumm-dumm zuciyar Fawzan tayi, cike da mamaki ya ce,........✍️
_Tofa aiki ya biyo takan yaya Fawzan yau. Bari muga zai amshi batun Mamyn ko zai mata batun Najma🏃🏃🏃🏃🏃_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣2️⃣
______________
.........“Wannan ɗin Mamy?”.
“Ƙwarai Fawzan. Yarinya ce mai tarbiyya sannan ƙyaƙyawa. Dan wlhy tafi Nibras komai. Za kuma ta baka farin ciki fiye da ita. Dan zuwa yanzu na sake yarda Nibras sakaran yarinya ce, uwarta ta riga ta mata tarbiyan banza da mugun gata. Sam bata da alƙibla ta kula da miji kamar ba mace ba, abinda kawai ta sani cin kwalliya ta tafi office...”
A zuciya Fawzan yace (wannan kadai kika fahimta Mamy) a fili kam sai yay murmushi. Babu wani damuwa a tare da shi ya ce, “Mamy ai muna zaman lafiya, sannan haihuwa ta ALLAH ce kuma lokaci ne. Yau baga Ajwaad da Maanal ba, rayuwarsu ma aya ce a garemu bayyananniya.”
Cikin ɗan kaushin murya Mamy ta ce, “Na fika sanin haka Fawzan, sai dai kamar yanda na faɗa na gaji da ganin ka haka babu yara, dan haka umarni nake baka akan yarinyar nan, sunanta Amani, a Kano take, ɗiyar ƙanwar sarkin Kano ce uwa ɗaya uba ɗaya, babanta ma nada tashi sarautar dan shima ɗan gidan ne kozin suke da Sarkin auren zumunci ne da uwarta. A U.S aka haifeta, can tai dukkan karatunta. Dan tana aikinta babanta yasata ta dawo Nigeria saboda auren yake son yay mata. Ni bance ka rabu da matarka ba, amma yana da ƙyau kayi auren nan don a tantance a ina matsalar take”.
Gaba ɗaya Fawzan ya zama kamar wanda aka zaunar a wajen domin tarihi kawai yana kallon Mamy. Wani irin mamaki take bashi, miyyasa a komai na rayuwarsu bata nuna tana da alaƙa da su ne? Amma a kan aure itace mai zaɓa musu mata?. Kallafa yanzu akan Ajwaad, an wani ƙaƙaba masa Nuratu yarinyar da sam bata da tarbiyya. Kalla abinda Nibras ke masa, kwanciyar aure bai iya yayi da ita ba sai ya saka mata ƙarfi, sannan wai ƙaninsa take so saboda bata da hankali. Kalla Babban Yaya, duk da shi bamai yawan magana bane wasu lokutan akan fahimci ƴar tsamarsa da Saheeba a gidan. Dukansu fa zaɓin Mamy ne, amma bata taɓa hango illar yaran ba balle tunanin suna jin daɗin zama da su ko basa ji. Oum itace ta rainesu, itace dukkan wahalarsu a rayuwar nan. Duk wani abinda ɗa yake yi akan abin uwa da nata suke yi, a kwai wani lokaci daya shiga tarnaƙin ƙuɗi sunyi wata kwangila kuɗaɗensa suka maƙale gwamnati taƙi biya, ya shiga matsi sosai yaƙi kuma faɗama kowa Oum ce ta fara harbo jirginsa. Haka ta zauna ta dinga masa faɗa daga ƙarshe ta ajiye masa atm ɗinta tace yaje ya ɗiba ko nawa yake so, yama riƙe atm ɗin ya dinga amfani da shi har sai komai ya warware. Daya nuna mata bazai amsa ba sai ta saka masa kuka akan mi yake nufi tana mahaifiyarsa ta bashi abu ya maido mata. Haƙuri ya dinga bata ya ɗauka, haka ya dinga amfani da card ɗin tsahon watanni babu wanda yaji ko ya gani har sai da komai ya daidaita masa sannan ya maida mata, daya saka wasu ƴan kuɗi a ciki catai idan bai cire ba saita cimasa mutunci. Haka dole ya cire su. Amma wlhy Mamy zai iya cewa bata taɓa damuwa da kana da shi ko baka da shi ba umarni kawai zata baka ka tura mata kuɗi, ko ka turama cikin ƴan uwanta kuɗi kaza.....
“Wai tunanin mi kake yi ne?”.
Mamyn ta katse masa tunani. Ajiyar zuciya ya sauke. Sai kuma ya miƙe yana faɗin, “Shike nan Mamy ki bani lokaci zan kirata a waya naji idan zamu iya dai-daitawa.”
“Ya dai fi maka”.
Ta faɗa a gatsine tana ɗauke kai. Jiki a sanyaye ya fice a sashen. Sai ya ji bama zai iya zuwa sashen Oum a haka ba dan zata gane a yanayin da yake. Mota kawai ya shiga ya fice a gidan.....
Mamy bataga AA ba sai gab da Asr, dan da shirinsa ma na fita massallaci ya shigo mata. Tasan yayi haka ne dan karya daɗe. Cike da takaici ta cije lips ɗinta tana harararsa. Shi dai sai ya ɗauke kansa kawai yana kaiwa zaune yace mata “Ina yini”. Bata amsa masa ba, sai ma cike da zafin rai ta ce, “Ajwaad ni zaka wulaƙanta ko?”.
Jiyay gaba ɗaya zuciyarsa na masa ɗaci. Kansa ya girgiza mata. “Mamy har abada kinfi ƙarfin wulaƙanci ga wani ma balle ni. Ko takalmin da kike sakawa daraja ce da shi a wajena balle ke. Kiyi haƙuri ina kwance ne kaina na ciwo shiyasa ban shigo ba, na kuma san kema a ɗan tsakanin nan kina barci ne.”
“Idan ka kare kanka anan shi kuma cikin da kaje kaima waccan ƴar iskar yarinyar ba wulaƙantani kayi ba kenan? Ajwaad har ni zan maka gargaɗi akan taɓa yarinyar can amma kaje ka taɓata harda ciki! Maybe ma tun kuna a gidan nan ne”.
“Mamy a gidan nan kuma. Amma kowa zai iya zama shaidar tunda Maanal tazo gidan nan da sunan matata bata taɓa zuwa sashena ba sai sau biyu. Na farko ita da Oum ina cikin ciwon nan. Na biyu shara da nace Oum ta sakata tamin lokacin kuma ina office ma. Tunda kuma kika hana ban sake sakata ba...”
“Idan bataje sashenka ba ai ka ɗauketa a mota kun fita ko. Sannan kuna zuwa office. Ranar daka nuna min ban isa ba agaban kowa na gidan nan ka fita da ita. Tunda kasan ba budurwa bace dan ka ɗauketa kunje kun sheƙe ayarku har wa zai gane. Balle tunda wancan abun ya faru dama ta cigaba da rabawa ƴan iskan Abuja waje duk ya buɗe.....”
Wani irin runtse idanu AA yayi, zuciyarsa kuwa sai wani duka take a cikin ƙirjinsa da sauri. Amma bawan ALLAH cike da jarumta sai yay murmushi. “Mamy kiyi haƙuri, koma miya faru ko ta aikata dai duk ya wuce tunda yanzu a gidan aure take. Sunanta matar ɗanki. Abinda kuma kike tunanin shima nayi kimin afuwa.”
“Haka ka iya amaka afuwa! A maka afuwa kullum, amma sai iya shege fal cikinka.”
Murmushi kawai shi dai yay mata dan darun Mamy da ban ne. Aiko taji haushin murmushin nan, sai ta sake hawa ta balbalesa da masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba. Faɗan kuma duk akan Nuratu ne da maganar kiranta data sharɗanta masa amma tunda ya tafi ko flashing baima Nurry ba, sai batun ciki da yaƙi cewa komai akai. Akwai randa ya kirata bayan sun gama magana tana cewa ga Nuratu ya yanke kiran da wayar ma gaba ɗaya. Shi dai kansa na a ƙasa harta gama. Ta dawo kan batun Documents ɗinsa da batun sunan Maawad.
“Mamy dan ALLAH kibar maganar nan, shi sunan companyn minene amfanin saninsa? Sannan documents ɗin nan dan na amshesu a hannun Oum mi zakiyi da su? Su dai ba abinci bane balle ace za'a ci”.
“Uwar ubanka zan yi da su!!”.
Ta faɗa a tsawace. Ba ƙaramin dukan zuciyarsa zagin yay ba, dan abinda bata taɓa masa ba kenan zagi. Barta dai da masifarta da sharuɗɗa. Kalamanta ne masu tsauri suka cigaba da kekketa masa zuciya duk dai akan Maanal da Oum daya rasa mi suka tare mata a wannan rayuwar..
“Wlhy a wannan karon zan iya tsine maka Ajwaad, zan iya cireka a cikin ƴaƴan dana haifa na manta da kai. Badai ni kake nunawa karuwar yarinyar nan mai wulaƙantattun iyaye da Fateema sun fini ba, zanyi maganinka wlhy. Dan ubanka tashi kaban waje shashasha da bai san kishin kansa ba...”
Tsam AA ya miƙe cike da girmamawa ya furta, “ALLAH ya huci zuciyarki”. Daga haka ya juya ya fice. A ƙofa suka ci karo da Abah. Gaban AA yay mummunar faɗuwa. Babu shiri ya haɗiye yanayinsa tare da fisgo jarumtar dole ya ce, “Abah barka da yamma”.
Idanu Abah ya ɗan zuba masa na sakanni, sai kuma yay murmushi da amsa gaisuwar sannan ya ce, “Dama baka tafi massallaci ba ɗan Oum?”.
Murmushi AA ya ɗanyi, “Yanzu zan wuce Abah, na shigo na gaida Mamy ne tun safe bamu gaisa ba saboda mun fita da Uncle, sanda muka dawo kuma zasu je tafsir”.
Sam AA bai iya ƙarya ba, dan haka ko yaya yayita sai ka gane masa, shiyyasa akan abu koda bazai faɗi ainihin gaskiya ba, zai faɗi wani yanki na abun da bazai sa ka damu da son jin wancan ba. Yanzun ma murmushi kawai Abah yayi, sai kuma ya ce, “Okay muje to kawai idan na dawo na zo, dama zan ma Kamila magana ne amin farfesun kayan ciki wajen yin abincinsu.”
“To Abah bara na gaya mata mana”.
“Kaga barta zan tura mata saƙo gashi can za'a tada salla”. Daga haka yaja hannun AA ɗin suka wuce. Wata irin wawuyar ajiyar zuciya Mamy ta sauke. Dan tunda taji maganar Abah ta miƙe zambar zuciyarta na gudu a ƙirjinta......
__________★
KADUNA
Al'amarin Yazeed ya girmi kowa a gidan, dan tsohon kwana uku kenan da dawowarsu amma ko leƙe bai shiga ya gaida kowa na gidan ba. To dama dai Ammie ce sai ƙannensa sai Daddy. Ko abinci da Ammie ta aika musu a randa suka dawo, dawo mata da shi akai tare da gargaɗin karta sake kawowa inji Aunty Sabuwa. Aiko Ammie bata sake maimaitawa ba.
Hankalin ƙannensa a matuƙar tashe yake. Suna kuka suka kira Hajiya Yaya suka sanar mata komai. Sosai hakan ya bama Hajiya Yaya mamaki, amma sai ta danne tace su barshi ai zaizo gaisheta zatai masa magana.
A randa suka dawo ne akai wanan waya, amma har yau kwana uku Hajiya Yaya bataga ƙeyar Yazeed ba a gidansu. Koda ta tuntuɓi mahaifiyarsu da maganar sai tace ita ina ruwanta kuma. Dan dama tunda Hajiya Yaya tazo gidan babu ruwanta da ita. Ita dai ba'a sakata aikin komai, amma babu mai mata magana a tsakanin Baba da Mamansu, aikinta kuma masu aiki bazasuyi ba ita takema kanta komai hatta girki.........✍️
*_AJIYA