Showing 117001 words to 120000 words out of 218311 words

Chapter 40 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

yanzu ta ɗauka ɗamarar zama masa mar'atussaliha in sha ALLAHU. Sun jima a haka kafin ya ɗagota. Fuskarsu ya gaɗe a waje guda goshinsu, hancinsu na gogar juna. Ɗan sumbatar lips ɗinta ya sake yi kaɗan, sai kuma cike da shagwaɓa ya ce, “Please my Babie nayi missing ɗinsu ALLAH, nayi kaɗan?”.
Cikin tata shagwaɓar ta ce, “Ai matsalan kai baka san kaɗan bane, kuma ma fushi nake da kai”.
“Nasan kina fushi dani shiyyasa zanyi lallashi ai.”
Kafin ma ta samu damar sake cewa wani abu ya mamane lips ɗinsu waje guda. Cike da nutsuwa da kewa ya fara sumbatar ta. Itama dai yau jin abun tai har tsakar kai, bama tasan ta fara bashi haɗin kai ba. Ya subahannallah ji AA yay kamar ana masa kiɗan general a sama. Baima san ya kamata ya ɗaga gaba ɗaya ya zaunar akan katakon mirror ɗin ba ya wani riƙe kanta da duka hannayensa biyu. Yi yake kamar zai haɗa har lips ɗin nata ya cinye kawai. Sunfi mintina shida a haka kafin ya haƙura ya rungumeta, itama rungumesan tayi tsam suna sauke numfashi a tare. Wata irin nutsuwa da farin ciki na zagayesu. Duk da shi dai oga AA ta ƙarƙashin ƙasa gobara ce ke niyyar tashi. Amma dai yanata ƙoƙarin tausar zuciyarsa da lallashin gangar jikinsa. Sai ALLAH ya taimakesa ya ɗan samu lafawar yanayin nasa a wannan rungumar. Maanal ce ta fara ƙoƙarin janye jikinta, bai musa ba shima ya barta. Sam taƙi yarda ta kallesa, kanta a ƙasa, jitake kamar ta nutse a wajen dan kunya. Cikin wani irin nishaɗi AA yaja hancinta kaɗan tare da sumbatar gefen fuskarta sannan a raɗa yace, “Sarkin kunya”. Murmushi tayi tana ƙara duƙar da kanta. Shima sai ya bar wajen yana murmushin. A zuciyarsa ko mamakin canjawarta yake yau. Dan zai iya cewa bata taɓa bashi haɗin kai yayi yanda yake so cikin salama irin yau ba. Duk da dai kunyar na nan babu abinda ya canja. Jallabiya ya sanyo a jikinsa, sannan ya dawo inda take. Cak ya kamata ya sauke daga saman mirror ɗin, sai kuma ya kama hannunta suka nufi bakin gado. Sai da ya zaunar da ita sannan ya zauna shima. Cike da kulawa ya ce, “Bani abincin yunwa nake ji”.
Kanta kawai ta jinjina masa, ta jawo basket ɗin abincin ta zuba masa kunu, sai farfesun naman talo-talo da sukayi. Sai uban ƙamshi yake gashi gwanin sha'awa a ido. Kunun kawai ya amsa, naman ya buɗe mata baki alamar ta bashi. Ƙaramar harara tai masa, sai ya shagwaɓe fuska. Ta dungure masa kai tana murmushi. “ALLAH Besty ka canja hali”.
Murmushi yayi mai ƙayatarwa, zai yi magana ta zuba masa naman data ɗebo a bakin dole yay shiru ya shiga taunawa. Sai wani kallonta yake, dan ji yake kamar an canja masa ita. Alhamdullah addu'arsa ta amsu kenan. Dan kusan a ittikafin nan addu'oi sa akan Maanal ne. Yaci naman sosai, itako da ya nuna zai bata tace masa ta ƙoshi taci abinci. Bai takura mata ba. Wani ƙyaƙyƙyawan leda dake gefen gadon ya jawo gabanta.
“Ga kayan sallarki tashi ki gwada”.
“A ina ɗin?”.
Ta faɗa tana waro idanu waje. Cike da tsokana yace, “A gabana mana, ba mijinki bane?”.
“Hu'um ALLAH bazan iya ba. Kadai bari naje sashen Oum duk wanda na gwada zan maka hoto”.
Murmushi yayi mai faɗi, sai kuma ya ɗan laɓe baki yana fara fiddo kayan da faɗin, “Ni za'ama wayo kenan. To naƙi ɗin”.
A marairaice ta ce, “Please Yaya AA”.
Dariya yayi, sai kuma ya dakata da fiddo kayan yana kallonta. “Ni dai wannan yaya da aka saka min bai ma ko dace da ni ba. A kirani da Besty na nafi so”.
“Oh dama ka samu nake cemaka Yayan”.
“Na yafe bana so. Tunda dama badan ALLAH kika fara faɗa ba ko a waccan ranar”.
Kanta kawai ta juyar tana murmushi batace komai ba, sai kayan data fara amsa tana dubawa. Kala biyar ne, duk kuma sunyi ƙyau dan sun sami ɗinki na nutsuwa kuma mai ƙyau. Godiya tai amsa sosai da addu'a. Yaji daɗin addu'ar tata kuwa... Dai-dai nan Oum tai kiran wayarsa. Yana ɗagawa tace, “Auta turo min yarinyata tazo ta kwanta da safe ba wani isasshen barci za'a samu ba”.
Sai da ya ɗan murmushi yana kai hannu ya shafa fuskar Maanal ɗin sannan ya ce, “Okay Oum gata nan zuwa”. Daga haka ya sauke wayar. Kayan ya maida a ledan ya ce, “Tashi muje na rakaki kafin Oum ta biyo sahu”.
Dariya Maanal tayi, shima yana murmushi suka fito hannunsa ɗauke da ledan ita kuma basket ɗin. A compound daga can jikin motoci Maanal ta hango Najma da Yaya Fawzan. AA da sam hankalinsa bai kai wajen ba ta taɓa. “Besty kalla”.
Juyawa yay ya kalla inda ta nuna ɗin, aiko yay wani tsai yana kallon ikon ALLAH. Maanal dake murmushi tace, “Mika fahimta?”.
Maimakon bata amsa sai ya kama hannunta suka nufi wajen. Babu zato kawai su Yaya Fawzan suka gamsu. Daburcewa Najma tayi, dan suna tsoron AA sosai saboda ba sabgarsu yake shiga ba. A ɗan rikice taima Maanal alamar miyyasa ta bari yazo. Murmushi Maanal tayi, AA kam yay wani kalar tsaiwa ne yana kallon Yaya Fawzan irin kallon wana kama ɗin nan............✍️







*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣8️⃣




______________




.........Dariya yay Fawzan yay tare da shafa kansa ya taɓe baki. AA ya wani ɗan ɗage masa gira. Harga ALLAH abun yazo ma Yaya Fawzan a bazata, dan haka yama kasa magana. Shi kansa AA yanda Yaya Fawzan ɗin yayi ya bashi dariya, amma sai ya dake dan yau shima sai ya ɗan rama ko yayane daga tsiyar da Yaya Fawzan ɗin ke masa kullum.
“To Abah kallon ya isa haka mana”.
Ya Fawzan ya faɗa yana hararar AA. Murmushi AA yay a karo na farko, cike da neman magana ya ce, “Yaushe aka fara?”.
Baki buɗe Ya Fawzan ya ce, “Mi ɗin?”.
Gira AA ya ɗaga masa tare da faɗin, “Ai ka gane. Yau dai ALLAH ya kama min kai”.
Dariya sosai Fawzan ya sanya, sai kawai ya rungume AA ɗin. Shima AA ɗin sai kawai ya hau dariya. Kusan minti biyu suna a haka kafin Ya Fawzan yaja hannun AA ɗin suka shiga mota. Ran AA fes da farin ciki ya ce, “Amma Yaya bata maka ƙanƙanta ba?”.
Murmushi Fawzan yayi idonsa akan ƙanin nasa. “Ajwaad ai ita mace bata ƙanƙanta wa namiji. Kamar yanda mace bata yima namiji girma. Najma sa'ar Maanal ce fa. Kai ba gashi harka galla ma Lilly cizo ba tana mana amaye-amaye”.
Murmushi kawai AA ɗin yay shima ya girgiza kai. Shima Ya Fawzan ɗin sai yay dariya kawai, dan yasan Ajwaad da rashin son magana. Da ƴar damuwa ya ce, “Ina sonta sosai, dan tanada tarbiyya. Zan iya cemaka ma kusan tarbiyyarmu iri ɗaya ce. Dan abubuwan Aunty Majdiya da yawa suna kamanceceniya dana Oum. A lokacin bikinku muka dai-dai ta, Ajwaad sam bana samun farin ciki irin na magidanci a gidansa. Bawai bamu samu haihuwar bane damuwata, nasan wannan lokaci ne, amma ita Mamy wannan take kallo kawai, shiyyasa ta sake zaɓa min wata matar”.
Da sauri AA ya kallesa, “Wata matar?”.
Kai Fawzan ya jinjina masa yana murmushi. “Jiyan nan ta bani hotonta da number ta akan nayi magana da ita. Ajwaad bazan ɓoye maka ba, wasu abubuwa na Mamy a ɗan tsakanin nan na saka zuciyata girgiza. Miyyasa take damuwa da sai itace zata zaɓa mana matan aure? Miyasa Oum ita bata taɓa kwatanta haka ba. Sannan abinda ke cimin zuciya matan ma duk bana ƙwarai ba. Kalla Babban Yaya, ALLAH nasan sam baya jin daɗin zama da Saheeba, kawai dai bazaiyi magana bane. Kalla wannan yarinyar da ake neman manna maka Nuratu, wlhy ban ƙara jin tsanar yarinyar nan ba sai a wannan zaman. Kuna Chaina ɗin nan fa sai da naci ubanta wai ita zatama Oum rashin kunya....”
Wani irin kallon ɓacin rai AA kema Yaya Fawzan, shifa da'a taɓa Oum garama duk uwar ubanda za'ai ayi. Fawzan ya cigaba da faɗin, “Wlhy kuwa, amma abinda ya bani mamaki da naje ina zaginta a sashen Mamy sai Mamy ta canja fuska, har tana faɗin muma ni da babban yaya yanzun mun fara koyon halinka na ƙin danginta. Nayi ƙoƙarin ta fahimta amma wlhy tama korini wai na bar mata sashe. Na jima abin nan na cimin zuciya. Ni yanzu babban tashin hankalina ban san yanda zan yi da wannan yarinyar data kawo ba, nama rasa ina tasan yarinyar wai daga gidan sarkin kano take, ko miye alaƙarta da ƴan gidan oho”.
Gaba ɗaya ma AA ya kasa magana, dan bai taɓa tunanin Mamy zata bar sauran ƴan uwansa su fara fahimtar wacece ita ba. Ya jima shiru, kafin ya kalla Yaya Fawzan da shima ya tafi tunani. Cikin lallashi ya furta, “Yaya badai kana son yarinyar nan ba?”.
Cikin sauke ajiyar zuciya Ya Fawzan ya ce, “Sosai Ajwaad, ɗan zan iya cewa bayan Amaal Najma itace mace ta biyu da nake jin sonta har ƙasan zuciyata.”
“Tunda har kana sonta ka daina damuwa da batun Mamy, sannan kada kama yarinyar magana barni da su.....”
“Uhm-uhm Ajwaad bana son kama nuna ma Mamy na maka wannan maganar, dan bayan ni ɗin bana son ta fahimci wani yasan wata matsala makamanciyar wannan game da ita, sannan ka sani Mamy duk da ta bama Oum mu na har abada hakkinta na uwa na nan a kammu bai kau ba, kuma dole ne mu saukesa in har muna son zama lafiya. In har auren yarinyar shine zai sakata a farin ciki zanyi sai na haɗa da Najma ɗin”.
Murmushi mai ciwo AA yayi, sai kuma ya girgiza kansa. “Yaya in dai har ba kaine ke da ra'ayin tara matan haka ba baka da wani dalilin yin hakan saboda umarnin Mamy, eh ita uwace, komai zamu iya yi a gareta, amma addini bai yarda harda cutuwa ba. Koka faɗa ko kai shiru kai hakan a gareka cutuwa ne. Ban sani ba ko ni kaɗai ne keda wannan matsalar a cikinku, bazan iya zama da mace fiye da ɗaya ba dan ina da ƙyanƙyami, zan ma iya rantse maka bayan Manaal bazan iya haɗa jikina da kowace mace ba, dan ita kaɗai ce nake jin yin nutsuwar hakan batare da jin komai a raina na ƙyanƙyami ba. Amma mizaisa kace zaka haɗa mata uku kaje wajen waccan kai amfani da ita ka koma wajen waccen like wani namamajo haba. Ai ko addini daya bamu damar yin hakan yace idan zamuyi adalci, sannan ga waɗanda basa iya kauda kansu ga wasu mata. Ni kuma harga ALLAH ma nasan ko na sakan ɗaya bazan iyama wata adalcin haɗata da Maanal ba. Dan haka Yaya be a man Please, ka rasa soyayyarka ta farko kayi haƙuri kayi juriya daga kai har Babban Yaya da ni na kasa a cikinku, sannan kunyima Mamy biyayyar amsar zaɓinta, ya kama a wannan karon ka bama zuciyarka abinda take so kodan ka samu farin ciki, dan banga ta inda wannan wawuyar matar taka zata canja ba (Kayi hakuri na zageta a gabanka)”.


Murmushi Fawzan yayi, wata irin ƙaunar ƙanin nashi na ratsa shi. Tabbas sune yayunsa, amma Ajwaad ya fisu ƙarfin zuciya da rashin tsoro, shi fa in dai addini bai hanashi abububa to babu mai tankwarashi yinsa. Ko iyayensu bazai ce bazayi ba kai tsaye, amma zai bi ta hanyoyi daban-daban ya gujema abin. Kalla aurensa da Nuratu, kusan shekara shida fa kenan ana abu ɗaya amma yaron nan yasan duk ƙulumboton da zai yi ya zame. A yanzu ma da yake tunanin ya miƙa wuya gashi yana tabbatar masa bazai taɓa haɗa Maanal da wata ba, shi ƙyanƙyamin ma matan yake, chai akwai badaƙala kenan a gidan nan, yanda dangin Mamy suka shiryama auren nan ashe AA zai taro musu match. Aiko duk ma mi za'ayi sai dai ayi suna bayan ɗan ƙaninsu....
A hankali ya kai hannu ya dafa kafaɗar AA dake danna waya yana wani ɗan munafukin murmushi. Sai kuma ya ɗan leƙa yaga uwar mi yake kallo. Hotunan Maanal ne da alama kuma yanzu take turosu, yana leƙowar AA ya kife wayar cike da shagwaɓa ya ce, “Yaya ba ƙyau fa leƙen asiri”.
Dariya Fawzan yayi sosai, ya ce, “Ganin Lillyn ne leƙen asiri kenan. Kai ni fa wlhy kallon Maanal nake kamar tare aka haifemu a gidan nan, dan ko sanda bama tare sai na dinga jin kamar an cire mana wani ɓangare na gidan ne, data dawo sai naga mun cika cif, kai tsaye mu huɗu nake kallo a matsayin ƴaƴa a gidan nan. Ban sani ba kodan a gabammu ta tashi ne oho”.
Murmushi AA yayi yana sauke ajiyar zuciya kawai. Yaya Fawzan ya cigaba da faɗin, “Na gamsu da shawarar ka Auta, amma kai ya kake ganin zamu ɓullowa al'amarin, ni bana son Mamy ta fito da al'amarin nan fili harma wani ya kalleta da wani abu daban, dan tunda har na fara wannan tunanin na miyasa take son zaɓa mana mata ALLAH wasu ma zasuyi. Ko kai na tabbata zakaje kaita tunane-tunane ne yanzu”
Tausayin yaya Fawzan AA yaji a ransa, dan da yasan yanda yasan wacece Mamy da bai faɗi haka ba. A fili kam sai ya ce, “Karka damu ka bar komai a hannuna”.
“Ka faɗa min me zakayi mana?”.
“Zanyi magana da Aba, bayan sallar nan kawai ayi biki”.
“Kai baiyi kusa ba Auta, yarinyar fa bata kammala makaranta ba”.
“Ba wani kusa Yaya, makaranta kuwa ta gama a ɗakinta. Ai aure bai hana karatu, haka karatu bai hana aure. Mu shaida ne akan hakan tunda Oum hatta Secondary a gidan aure tayi”.
“Hakane na fahimta. ALLAH ya shige mana gaba”.
“Amin ya rabbi. Yanzu yarinyar mika bata na gift ɗin salla”.
“To baban soyayya, ka manta nace maka ko Oum bata sani ba”.
“Tadai barku Yaya, Oum ai ba uwar banza bace idonta na'a kan dukkan notsinmu. Manta da wani kar kowa ya sani muje a saya mata gift”.
Yay maganar yana kallon agogon hannunsa. Murmushi kawai Fawzan yayi, a ransa yana jin daɗin samun Ajwaad a matsayin ƙani. Key ya lalubo a jikinsa ya tada motar suka fice a gidan......


_________★


YAU TAKE SALLAH


Ta kowane ɓangare yau bakunan ɗaukacin musulmai a buɗe yake da murmushin farin cikin zagayowar wannan babbar rana da akan risketa ne sau biyu rak a shekara. Farin ciki ne da baya ɓoyuwa a fuskokin yara da manya maza da mata. Tako ina anguwanni sun kacame da ƙamshin girke-girke na musamman. Sai kuma shiri da kowa keyi na sallatar idi.
Anan gidan Darma ma hakan take, dan tunda akai sallar asuba Oum bata bar kowa ya koma barci a yaran ba. Tuni masu wanka sun fara, masu taya aikin haɗa abinci sun fara. Zuwa bakwai kowa ya gama shirinsa gwanin sha'awa kamar ka sacesu ka gudu. Baka jin komai sai ƙamshin turarurruka masu ratsa zuciya. A irin wannan ranar tako wace shekara abincin da ake karyawa da shi kafin tafiya sallar idi ana samar da shi ne daga sashen Mamy, dan haka kowa na kammala shirinsa can yake tafiya. Dama masu aiki duk can suke tattaruwa a haɗa abincin. Su kuma masu haɗa abincin salla suna anan sashen Oum ne, idan an dawo anan ake yada zango.
Tuni Hajiya Oum tauraruwar Abah ta kaɗa kan yammatanta zuwa sashen Mamy ɗin. Tayi ƙyau harta gaji, kodan Oum ɗin ba haihuwa tayi akai-akai ba tana nan da ƙyanta da ƙyawun jiki kai kace ma itace amaryar gidan. Dan koda suka shigo harga ALLAH sai da Mamy taji zuciyarta ta motsa da salon gayun Oum ɗin, ba yaune farko ba, koda fita zasuyi tare har shakkar kwalliyar Oum take ji dan Oum akwai gayu. Cike da dakewa Mamy ta ƙawata fuskarta da murmushin dole suka rungume juna ita da Oum ɗin tare da yin happy salla. Dai-dai nan Abah da Yaya Fawzan suka shigo, babu kunya ya rungume Oum yana raɗa mata happy salla a kunne. Murmushi tayi ta amsa masa cike da jin nauyin yaran. Matsawa yay ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login