Showing 114001 words to 117000 words out of 218311 words
Chapter 39 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
a gidan nan ya saka Saheeba kiran uwarta a waya. Dan Mamy gaba ɗaya ta kasa dawowa a hanyyacinta, kalaman Maanal da marin data ma Nuratun ne kawai ke mata kai-kawo a cikin idanu. Eh tasan Maanal dama tun tana mitsitsiyarta bata da kunya yarinyar, amma bata taɓa kawowa a ranta fitsararta zai iso gareta ba. Lallai tayi sake, matuƙar sakacin da har yarinyar nan ta zauna a gidan na wannan lokacin har ma da ciki. Gabanta ya faɗi tuna zancen ciki... Dai-dai nan Saheeba ta miƙa mata waya dan tunanin da tai nisa a ciki yasa bama tasan su Saheeban na waya da uwarsu ba........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣6️⃣
______________
.........“Maman Saheeba ta ce, “Aunty miyasa kikai haka? Ni da kinyi shawara dani wlhy bazaki kira yarinyar nan har sashen ki ki wani mareta ba.”
“Raina ne ya ɓaci Nana, babu kunya fa a gabana agaban kowa Ajwaad ya wani rungume yarinyar nan jikinsa na rawa, ya kuma ɗaga hannu ya mari Nuratu, Fadeel ya amshe kayan hannunta, yabi yarinyar nan da zagi shima. Haka ma Fawzan. Yanzu kodan ganin idona yaran nan bazasu raga ba. Su dukansu suka nuna goyon bayan ƴar iskar yarinyar nan......”
“Na fahimceki, amma da kema kinyi pretending kawai a wuce wajen. Dan wannan faɗan ba naki bane na tsakanin su yaran ne ai. Yanzu kuwa abinda kuka kira yarinyar kukai mata kamar kin buɗe mata cikinki ne kai tsaye. Karki manta yarinyar nan idonta a buɗe yake, tunda kema shaida ce akan halinta na baya, dan yanzu ta koma wannan sum-sum ɗin bai kamata ki sakankance da yawa haka ba. Rainon Fateema da Ajwaad ce fa, sannan jinin Asiya ce. Dole fa ki dinga ƙoƙarin control ɗin fushinki Aunty idan ba haka ba zamuyi wahalar banza, dan in dai mutanen nan suka gane akwai wani abu a tare dake wlhy auren nan bazai yiwu ba na Nuratu da Ajwaad, balle kuma akai ga Fawzan, kuma na tabbatar bazasu cigaba da barin Fawzan a haka ba zasu nema masa matar aure, Ajwaad na auren yarinyar nan, mi kike tunani, ke da Saheeba kaɗai zaku iya wasan ne? Bayan sun rinjaye Ku? To dole fa ki cigaba da yin kamar yanda kike yi, shi wannan faɗan ki barma yaran suyi, suma kuma a yanzu karda su sake cemata komai su barta sai ta sakankance sannan dan wannan marin sai Nuratu ta rama shi. Haba Aunty kamar bake ba, ke da na sanki tamkar ƙuli-ƙuli babu mai iya gane gabanki balle baya. Karki bari abubuwa suyi miki yawa ki fara sakin layi dan ALLAH. Yarinyar nan kuma ki fita a sabgarta in ba hakaba zata zame mana ƊAN HAKKIN DAKA RAINA tunda bata da kunya sam, kota zame mana RAINA KAMA KAGA GAYYA”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Mamy ta sauke, cike da gamsuwa ta ce, “Hakane kuma Nana na fahimceki. Amma maganganun yarinyar nan sun min zafi, dan tabbas bada su Saheeba take ba dani take, amma lokaci ne, zan nuna mata uwarta ma da Fateemar da suke taƙama da ita basu kai ba balle ita haihuwar jiya.”
“Karki wani damu lokacin cin ubanta na zuwa. Wannan cikin nata kuma na amso maganin zubar da shi amma sai zuwa bayan salla zai iso, dan so nake mu zubar da shi dai-dai sanda ake hidimar bikin Ajwaad da Nuratu”.
“Miye ma'anar yin hakan? Ni gwara kawai ya ɓare yanzu dan idan na kalleta wani irin zafi nake ji a ƙirjina wlhy Nana”.
“Karki wani damu ki kwantar da hankalinki Aunty, hakan da zamuyi nada ma'anoni masu yawan gaske. Ai gara cikin yay kwari ta yanda zataci azabar fitarsa, a kuma lokacin mu nuna tayi hakan ne dan kishi Ajwaad zai ƙara aure. Kai idan ma ta kama har Fateema sai tuggunmu ya shafa akan zubar da cikin nan”.
Wani sassauci Mamy ta ɗan ji a ranta, ta sauke numfashi da faɗin, “Shike nan hakan ma yayi, ALLAH ya kaimu”....
_😂Wannan ciki dai da ake son a zubar kota ina aka samo shi. Koda yake AA ɗan baiwa ne maybe a mafarki ya lallaɓo🥱😜😆🏃._
________★
Wannan tattaunawa ta RK da su Maanal ta taka matuƙar rawar gani akan abubuwa da yawa. Duk da tako wane ɓangare kowa akwai abinda ya damesa. Aranar dai Mamy da su Nuratu basu je aiki sashen Oum ba. Nuratu kuwa tasha uban bori akan sai taje har sashen Oum ta daki Maanal. Da ƙyar Mamy da Saheeba suka lankwasata bayan an kira Hajiya Turai a waya itama ta sake yin nata. Sai da Oum taje har sashen Mamy ta bata haƙuri da lallashinta sannan tace ita fa ba wannan bane ya ɓata mata rai bata jin daɗi ne. Ita dai Oum ta sake bata haƙuri ta taho. Sai kuma hakan ya damu Mamy ɗin, dan da ciwo kaga kanata hauka akan mutum shi ko'a jikinsa, (kamar dai yanda Maaanal tace AJIYA A DUHU kenan😂) washe gari suka fito akaje tafsir tare aka kumayi girki tare. A ɓangaren Fawzan shima dai ransa danƙare yake da al'amarin Mamy dan abin sai ya zame masa biyu. Wanda tai masa, da wanda ya faru akan marin Nuratu da AA yayi. Shi ko babban Yaya iya na marin Nuratun ne kawai ya bashi mamakin. Sai kuma ya ɗauka kawai Mamyn ta fusata ne saboda Nuratu na jininta. A ɓangaren Mamy kam abin da ya tsaya mata a zuciya Abah ne. Dan daga wannan nasiha bai sake cemata komai ba, hatta borin kin zuwa aiki da tayi na kwana ɗaya da ƙin zuwa shan ruwa sashen Oum ko'a fuska bai nuna mata ba balle ya tanka. Sai hakan ya girgizata ya kuma tsaya mata a zuciya taketa hasashe-hasashe ta kasa gane komai. Gefe ga tsanar Maanal da maganganun data gayama su Saheeba yana ƙara yima Mamy ciwo bama su Saheeba ɗin kawai ba. Sun kuma rasa ta yanda zasu rama duk da sun ɗauki alwashi kala da iri Saheeban da Nuratu. Na ƙarshe AA, matuƙar ciwo abinda ya farun yay masa. Dan haka ma a jiya ya shirya tafiya Lagos ya bar musu gidan. Dan baya buƙatar yin wata magana da Mamy in ba hakaba ALLAH sai zuciya ta kwashe shi yama Nuratu dukan mutuwa ya kuma koreta a gidan duk da Oum ta masa faɗa da nasiha sosai a washe gari. Itama Maanal karanta jotter ɗin da RK ya bata ya sakata kuka sosai jikinta kuma yayi sanyi matuƙa, dan haka ta ɗauka ɗammarar gyara abubuwa da yawan gaske...
Kwanakin azumi sun cigaba da tirzawa, wasu na ibada wasu zukatansu cike da burikan sharri. A randa aka shiga goman ƙarshe AA ya dawo gidan, zuwa dare kuma ya sake barin gidan acewarsa ya shiga ittikafi. Bai yarda wata keɓantacciyar gaisuwa ta shiga tsakaninsa da Maanal ba itama kuma bata nuna ta damu ba a zahiri duk da hakan ya mata ba daɗi, dan yanzu so take su daidaita sosai. Ita kanta Oum bataji daɗin yanda AA yayi ba amma batace komai ba. Shi kuma a ganinsa hakan da yay zaifi alkairi dan a cikin wani irin matsananciyar buƙata yake shiyasa ya zaɓi duk hanyoyin hana keɓancewarsa da Maanal sam.
A ɓangaren Abah da Uncle RK da su babban yaya kam suna ibada suna kuma shirya biki batare da sanin kowa ba. Yayinda suma dai ta ɓangaren Mamy bikin suke shiryawa acewarsu babu ɗaga ƙafa sati ɗaya da salla. A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, azumi nata bankwana su Maanal nata ƙara dagewa a yin ibada. Duk da ita ma a farkon goman tai period, ALLAH dai ya taimaketa kwanansa uku ya tafi ta cigaba da azuminta. Tun azumi na goma sha biyar tela yazo ya gwada ƴan hutun su Oum bisa umarnin AA. Batare da kowa yaga kayan da za'a ɗinka ɗin ba kuma. Yau da azumi ke ashirin da bakwai ana saka ran salla nan da kwana biyu ko uku sai ga ɗinkuna sun iso kowa da sunansa. Zokaga murna da tsalle wajen yaran. Abinda ya ƙona ran Mamy babu Nuratu a ɗinki, duk da taga babu Maanal itama hakan bai dameta ba. Tako ƙara ƙullatar AA sosai a ranta, gashi dama ta fassara barin gidansa da wai yana haushi da ita ne. Bata san bawan ALLAH abinda ya damesa daban ba. A ranar shima Yaya Fawzan ya kwashe su da dare yin shopping na takalma da sauran tarkace. Harda Maanal da Oum akaje, nan ma baƙin ciki kamar zai kar Mamy. Duk da dai ta danne bata nuna ba a fili, harda kuma su Saheeba da Nuratu da Nibras. Kowa kuma ya zaɓo ra'ayinsa, Oum kuma ta zaɓo nata dana Mamy data ƙi binsu wai ita kawaici sai na Aba. Fawzan ya ɗauka musu shi da Baban yaya da AA dan Uncle RK ya fece Kano yace kansa bazai murfi ba ranar salla sabon amarcin shi da Nuwaira 🤣. Shi kuma babban yaya washe gari ya lodo uban cefane da kaji gyarru sai uban jan nama. Tuni sun hutar da Abah yin komai a gidan nan. Dan shi kansa bai san yaushe ne last da ya sai wani abu na abinci ko sutura ba koda ma kansa a gidan. Hatta da ƴan uwansa duk salla sai su babban yaya sun aika musu da kaji da cefane na abincin salla. Wannan sallar ma hakan ce ta faru, tuni nasu sun wuce Kano. Batare da sanin kowa ba kuma AA ya tura Kaduna da uban kaya ma Daddy kamar yanda suma su Babban yayan kanyi ga nasu surukan duk shekara...
Tunfa a daren masu aiki suka iso, dan duk salla su Oum na ɗaukar masu tayasu aiki saboda abinci akeyi bana wasa ba kasancewar ana fita da wani wa bayin ALLAH, kuma a cikin azumin ma akwai inda ake dafa abinci a raba duk lokacin shan ruwa batare fa kowa yasan daga su bane. Bayan ɗanyan abinci da shi kansa AA ke rabawa duk shekara shi da sauran ƴan uwansa. Dan asusu garesu na tara kuɗaɗe domin hakan kawai sai shekara ake ciresu ai hidimar taimakon bayin ALLAH. Oum kuma kaɗai tasan suna yin hakan.
Masu aiki sun kama aiki, Oum ta kaɗa ƴammatanta saloon da kitso. Mutuniyar taku dai nata daru, Oum tace babu fashi sai an mata. Itako aka fara wanke ma kan sannan akai kitso bamai yawan ba. Dan Oum tace a mata kaɗan tunda za'ai na tariya kwanan nan. Haka ma ƙunshi a yatsu kawai akai mata ja shike nan. Ta koma gefe yana sauke ajiyar zuciya ga haushin AA dama na cimata rai. Suma sauran duk an musu harda Oum, basu dawo gida ba sai la'asar, babu ɓata lokaci suka shiga haɗa abincin buɗa baki...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣7️⃣
______________
.......Alhamdullah ƙarfe biyar akace anga wata a saudia, yara suka fara murna da fatan ALLAH yasa a Nigeria ma a gani. Hakan kuwa akai, kafin ma tara sanarwa ya iso kunnen kowa daga Sarkin Musulmi cewar anga wata muma a Nigeria gobe salla. Ai fa tuni gida ya yamutse da murna. Zuwa tara sai ga AA ya dawo gida. Tunda ya shigo Maanal kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kai, yanda ƙannensa suka gaishesa itama ta gaishesa ne ta basar. Shi dai kallonta kawai yake ta ƙasan ido, Oum tace mizai ci ya miƙe yana faɗin,
“Komai ma na samu amma mara nauyi, bara naje na watsa ruwa Besty ta kai min can dan zata amshi saƙonta daga can, idan kinzo ina sama”. Ya faɗa maganar ta ƙarshe idonsa akan Maanal
Cikin rashi damuwa Oum data san da saƙon tace to. Shima sai ya fice bayan ya ɗan kalla Maanal ɗin karaf kuwa yaga hararar da take masa. Da sauri ya janye idanun yay gaba yana cije lips. Umarni Oum ta bata nata tashi ta haɗa masa abincin. Badan taso hakan ba ta amsa da to tana miƙewa. Shi ko AA sashen Abah ya nufa, acan ya samu Mamy tare da shi, ƙin yarda yay su haɗa ko ido. Kansa a risine ya gaisheta bayan ya gaida Abah. Idon Abah ya sakata amsawa kamar babu komai a ranta, amma ta ciki na ciki. Bai wani jima ba yace ma Abah zai je ya watsa ruwa yayi aski yana jin gashi duk a jikinsa. Abah ya sanya masa albarka ya fito. Sai da ya kalla sashen Oum sannan ya wuce nashi sashen.
★ Koda Maanal ta nema Najma tai mata rakkiya ƙi tayi, tace, “Tab, sokike Yaya AA ya koroni da tsarabar mari.” badan Maanal taso ba haka ta tafi ita kaɗai. Garin yayi sanyi sosai yau saboda hadarin da aka haɗa sai ya zama iska ba'ai ruwan ba. Sanye take da hijjab har ƙasa royal blue dayay mata ƙyau sosai, sai ɗan basket ɗin data riƙe na abincinsa. Tana gab da shiga idonta ya sauka akan Nibras dake zaune a barandar sashensu ta upstairs ko ubanmi take a wajen oho. Ɗauke kai Maanal tayi abunta ta cigaba da tafiya, batai wani zaman yin knocking ba ta shiga da sallama. Babu kowa a falon ƙasan kuwa sai dai ko'ina a gyare tsaf, har yanzu kuma dai sauran kwalayen kaya da ba'a gama shiryawaba suna nan. Saman da yace zata samesa ta nufa, duk da zuciyarta na wani ɗas-ɗas na tsoro tadai dake. Shiru falon saman ko wuta ma ba'a kunna ba, sai da ta haska fitilar wayarta ma sannan ta kunna wutar. Zama tai a kujera tana fatan fitowarsa, fin mintuna biyar shiru, gashi tana son zuwa ta kwanta kodan kasancewar gobe idan ALLAH ya kaimu salla. Akwai fita idi da wuri, kuma tana son ya barta ta wuce gidan Didi ta yini. Fahimtar bafa fitowar zai yi ba yasa ta miƙe, ƙofar ɗakin ranar taje tai knocking. Shiru babu ko motsi, sai ta tura ƙofar kawai ta leƙa. Babu kowa a ciki sai uban sanyin ac. Ɗan jimm tayi a wajen, sai kuma ta shiga kawai zuciyarta na raya mata ta ajiye masa kawai idan ma wanka yake in ya fito ai zai gani ita kuma sai ta koma falo. Tana maida ƙofar zata rufe kawai ta ganshi tsaye a wajen ashe bayan ƙofar ya ɓoye. Da farko ma ita tsorata tayi, dan har zata fasa ƙara yay saurin faɗin, “Hy relax! Hajiyar tsoro”.
Baki ta tura sosai, kanta a ƙasa saboda daga shi sai towel a ƙugu ta ce, “Haa'a to miye na ɓoyewa anan ɗin?”.
Gabanta ya taka ya tsaya, sai ta matsa baya saboda kusancin nasu yayi dab da yawa. Ƙara matsowa yay, itama ta matsa, sai kawai abin ya saka shi nishaɗi ya cigaba da binta har suka dangane da jikin katakon mirror. Sai data runtse idanu, sai kuma ta ɗaura duka hannayenta a katakon tai baya da jikinta kamar zata jingina da madubin. Shima nasa hannayen duk biyu ya dafe katakon mirror ɗin da su ya shiga biyota yana ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata amma taƙi yarda da hakan. A yanda ya ranƙwafo ɗin da yanda take sai yay kamar zai kwanto a jikinta, ga fuskarsu dab da juna suna busama junansu nunfashi.
“I miss you Everbloom”.
Ya faɗa cikin raɗa yana hura mata iska a kan idanunta. Wani yarrr taji a illahirin jikinta. Dole ta buɗe idannunta dake wani mar-mar-mar. A cikin nasan da yake so suka shige, tai ƙoƙarin janyewa ya hana hakan. Dole ta shiga gaishe shi lips ɗinta na ɗan rawa. Matsar da nasa lips ɗin yay ya sumbaci nata kaɗan. Sai kuma ya sake ɗagowa yana kallonta. Cike da raɗa ya ce, “Na sha?”.
Kanta ta girgiza masa alamar a'a.
“Why?”.
Ya faɗa a hankali idanunta a cikin nasa. Itama a hankalin tace, “Ba yanzu ba”.
“Sai yau she?”.
Duk da maganar na mata nauyi ta daure cikin raɗan tace, “Sai randa aka kawo maka ni”.
Murmushi ya saki mai sanyi tare da lumshe idanun ya sake buɗewa a kanta slowly. Yanzun ma ƙasa-ƙasa yace “Anya zaki iya cika alƙawuran da kika ɗauka wannan ranar kuwa Besty?”.
Murmushi tayi da jinjina masa kanta, sai kuma tasa hannu ta rufe fuskarta. A haka ta ce, “In sha ALLAHU duk zan iya. Kai dai kawai kayi fatan zuwan ranar”.
Ajiyar zuciya ya sauke mai fita a hankali, sai kuma ya miƙe da ƙyau ya kamota kawai ya rungume a cikin jikinsa. Bata hanashi ba, itama tai luf dan zuwa