Showing 3001 words to 6000 words out of 218311 words

Chapter 2 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

zurfin ciki, maybe akwai abinda bamu sani ba game da al'amarin, amma wlhy mu shaida ne Ajwaad na son Maanal matuƙa. Kuma sai nake ga mata da miji sai ALLAH, kamar barinsu su kasance a taren zai sa su sasanta kansu kodan soyayyar da suke ma juna su duka”
“Humm wace soyayya kuma Fadeel, yana sonta zai watsar da al'amarinta ya zauna jan jiki a sanda ya sake ganinta, to Miye na girman kan, aure abin wasa ne? Barshi dai a bata tare ɗin ba, zai fi jin zafin wannan bulalar fiye da wadda kake hangen. Ina son hakan ya zama izina a garesa ya canja wannan halin nashi kodan yanzu shi mai iyali ne nanda wani lokaci haihuwa za'a fara masa”.
“Tabbas aure ba abin wasa bane Abah, mu kuma masu biyayya ne ga kowanne irin hukunci daga gareku. Amma idan mukai dubi da halin kawai daya shiga akan tsoron rasata abun muyi nazari ne. Ta wani ɓangaren ina tsoron kar dangin mahaifinta ne fa sukai masa wani abun tun wancan lokaci tunda dama kakarsu ta nuna bata son aurenmu da su Shaheedeh. Abah kasan zata iya bin kowacce hanya domin cin nasara, sannan shi kansa asiri gaskiya ne fa”.
Sosai Abah ke kallon babban Yaya. Zuciyarsa nata faman kai-kawo akan kalamansa. Sai dai kuma baice komai ba akan hakan illa nufar hanyar fita da faɗin, “Zanyi nazari, amma ina akan bakana na bazata tare ba yanzu ku cigaba da jiyyarsa ALLAH ya tashi kafaɗunsa”. Daga haka ya fice abinsa. Da kallo kawai Babban Yaya ya bishi, shi kansa al'amarin Autan nasu na damunsa, da rikita shi, amma dai koma miye ai ta ƙare tunda an ɗaura, komai mizai biyo baya mai sauƙi ne insha ALLAHU......


Murmushi mai faɗi da yalwa Mamy ta saki, dan dukan tattaunawar Abah da su Babban Yaya a cikin kunnenta ta kasance. Tayi matuƙar yin farin cikin yanda shirinta yay tasiri akan Abah cikin sauƙi haka, dan sam batayi zaton zai amshi batun da muhimmanci ba duba da sanda take tsara masa yin hakan yi yay kamar maganar tata bata tasirantu a gareshi ba. Shiyyasa taga ƴar gwal ɗin tashi har yanzu babu fara'a ashe an sake wargaza mata shiri ne. Wani murmushin ta sake saki haƙoranta na bayyana sosai, sai kuma ta gimtse fuska da gyara yanayinta ta ƙarasa shigowa falon sosai tana sallama.
A tare Fawzan da Babban Yaya suka ɗago suna kallonta tare da amsa sallamar. Cikin yanayin da take nuna musu na kawaici ta amsa gaisuwar da suke mata, tare da tambayarsu yaya mai jikin. Suma cikin girmamawar da suke bata suka tabbatar mata da sauƙi, yanama yin barci ne. Kai kawai ta jinjina musu, batare data sake cewa komai ba ta nufi bedroom ɗin AA ɗin. Barcin kuwa yake har yanzu, fuskarsa tayi fayau. Guntun murmushi ta saki a hankali, dan tasan tabbas ƙaunar da takemasa dabance a cikinsu, tun daga ɗaukar cikinsa har haihuwarsa duk da wahalar data sha shi ɗin na musamman ne a gare ta. A karo na biyu ta sake sakin murmushin, sai kuma ta kai zaune kusa da shi gab tare da kai hannun ta shafa yalwatacciyar sumar kansa dake a hargitse. Addu'ar samun lafiya tai masa mai ɗorewa tsahon mintuna kafin ta tashi ta fita....
A hankali AA da tun tsaiwar Mamyn a kansa ya farka ya buɗe idanunsa ya bita da kallo, sai da ta maida ƙofar ta rufe ya sake maidasu ya lumshe luuuu. Ya jima kafin ya sake buɗesu, sai dai sun masa nauyi sosai alamar barci bai gama sakinsa ba. So yake ya tashi zaune, sai dai kansa juya masa yake yi, dan haka dole ya sake maida idanun ya rufe barcin ya ƙara yin awan gaba da shi cike da mafarkin Mamy da haka kawai ganinta a kansa tsaye ya tsaya masa a rai duk da yasan ba wani abu mara ƙyau tazo tayi a garesa ba, amma dai zuciyarsa ta riƙe abun matuƙa..........✍️






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣




______________




........Mamy kam a inda tabar su Fawzan anan ta samesu, sai dai yanzu Nibras ta ƙaru.
Ɗan tsurama Nibras ɗin datai mata wani iri idanu tayi, sai kuma cikin tausasawa ta furta, “Nibras baki da lafiya ne?”.
Kallon Nibras ɗin Fawzan da Babban Yaya suma duk sukayi saboda jin furicin Mamyn. Cikin damuwa Fawzan ya ce, “Mamy gara kam ki tambayeta ke, dan tun jiya nima nake fama da ita amma sai tace ba komai gajiyar biki ce wai.”
Cikin jinjina kai Mamyn tace, “Itama gajiyar bikin akwaita ɗin ai, dama sai a hankali zata saki kowa duk da ga wani na tunkarowa kuma dai. Kinga kije ki samu ki gasa jikinki da ruwa mai zafi sosai sai kisha pracitemol ki kwanta abinki kiji. ALLAH ya ƙara sauƙi”.
Ji Nibras tai kamar ta zageta, amma sai ta daure ta jinjina mata kai kawai da faɗin, “To Mamy”. Daga haka ta juya ta fita zuciyarta na mata zafi da ƙuna matuƙa. Tazo ne dan taga fuskar AA ko zataji sassaucin abinda ke cizon zuciyarta, amma Mamyn ta wani korota. Ba komai zata dawo ne, dan in har yau Fawzan anan zai kwana ALLAH sai dai su kwana tare a sashen AA ɗin. Koba komai ta rage raɗaɗin kishin dake dafa mata zuciya. Sau ƙin ma har yanzu ko sau ɗaya bataga Maanal a sashen nashi ba..


Fitar Nibras ya saka Mamy ma yunƙurin tafiya, amma sai Babban Yaya ya dakatar da ita cikin ladabi. Tsayawa tai tana kallonsu su duka. Fawzan ya ce, “Mamy dan ALLAH magana zamuyi ne”.
Wani irin sanyi mai silalar da kuzari ne ya shiga bin jijiyiyin jininta yana gauraye jikin ta. Yayinda wani farin ciki ke cika zuciyarta tamkar kumfar omo a cikin ƙaton bahon wanki. Yau itace yaranta ke faɗa mata suna son yin magana da itane iya su kaɗai babu matar can a tsakkiyarsu. Ya rabba, ita kam mizatace da UBANGIJI yau. A zahiri kam sai ta dake babu wani alamun komai a fiskarta ta dawo ta zauna. Babban Yaya ne ya fuskanceta da ƙyau cikin nutsuwarsa.
“Mamy akan Ajwaad ne dama muke son dan ALLAH kisa baki a tsakanin rikicin Abah da Oum. Dan ALLAH ki taushi Abah akan ya bari Maanal ta tare a ɗakinta gobe idan ALLAH ya kaimu, dan gani yake kamar Oum ta kasa fahimtarsa ne saboda soyayyarmu ta rufe idonta, Auta na buƙatar matarsa a kusa da shi ya fahimci Oum dan ALLAH”.
Sosai kalmar soyayyar nan ta daki zuciyar Mamy, dan saida ta maimaitata a zuciya yafi sau uku. A fili kam sai ta sake raunana fuskar tata ta ce, “Oh dama wani abune ke faruwa? Ai ni na zata dan bashi da lafiya ne kawai bata tare ɗin ba. Yau gajiya tasa sau ɗaya kawai muka haɗu da Oum ɗin. Amma gaskiya ai Abahn naku ya faɗa, Mamanku ta cika rigima akan al'amarinku.....”
Cikin ƴar dariya Fawzan ya ce, “Kai Mamy kema haka zaki ce”.
“Ai gaskiya ne Fawzan, ita idan kaga tana fushi a gidan nan abu ya shafi ɗayanku ne. Karku damu zan sameshi muyi magana in sha ALLAHU. Itama zuwa da safe zan zauna da ita. Ni bara naje na ɗan kwanta nima kamar Nibras ɗin gaɓɓaina duk ciwo suke min”.
Godiya sukai mata da sai da safe. Fitarta babu jimawa Oum ta shigo itama. Su duka miƙewa sukai sukai kanta ganin har yanzu fiskarta a cinkushe, ga idannunta kamar wadda tayi kuka. Take suma duk fuskokinsu suka sauya. Murya a rauanne Babban Yaya ya ce, “Oumna Please ki cire damuwar nan, kin san fa Abah wani lokacin dan kawai ya kunnaki ne bawai abinda ke ransa kenan ba.”
“Amma Fadeel ya tausaya masa mana, kwance fa yake baida lafiya. Shin ALLAH ma ba muna masa laifi ba ya kuma gafarta mana saboda rahamarsa”.
“Hakane Oum shima zai huce”. Cewar Fawzan yana mata murmushi da kama hannunta ya sumbata. Haka sukaita lallashinta har sai da tayi murmushin itama. Kafin su nufi bedroom ɗin AA ɗin. Ganinsa zaune a bakin gado yasa ta ƙarasa shiga ciki da sauri, kusa da shi ta zauna tana mai riƙo hannunsa daya dafe kansa da shi, dan yaji duk zancen Mamy da su Babban Yaya. Mamakin Mamy da halinta ke sake raunana masa zuciya, amma yana mata fatan shiriya kafin lokaci ya ƙure mata. Yasan duk abin nan fa Abah keyi daga cikin shirinta ne, zai kuma bama kowa mamaki in sha ALLAHU cikin sauƙi.
“Auta yaya akayi? Kanne har yanzu dai?”.
Karan farko ya kalla Oum ya sakar mata murmushin ƙarfin hali, sai kuma ya kwantar da kansa a saman kafaɗarta. “Ya daina Oum”.
Ya faɗa acan ƙan maƙoshi.
“To Alhamdullah, ALLAH ya ƙara lafiya baby na kaji, yanzu mi kake son ci?”.
“Oum tea kawai”.
“To ba damuwa bara Fawzan ya haɗa maka”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya kalla Babban Yaya da Fawzan. Murmushi yay musu kaɗan, suma dake kallonsa suka maida masa murtani suna tambayarsa yaya jikin nasa. A samman laɓɓa yace da sauƙi. Daga haka Fawzan ya fita haɗa masa shayin. Kallon Oum ya ɗanyi, har ya janye idanun sai kuma ya tsira mata su, kafin tai ƙoƙarin dai-daita fiskarta har ya furta, “Oum kinyi kuka”.
“Kukan lafiya Auta ”. Ta faɗa tana ɗan harararsa cikin yanayin son basarwa. Ina bai gamsu ba, cikin rashin kuzari ya zamo ƙasan lallausan carpet ɗin gaban gadon ya zauna yana mai zuba mata idanunsa dake a shanye. Zatayi magana ya girgiza mata kai, “Oum Please ki daina damuwa, nasan a kaina ne ko? Dan ALLAH ki bari naji sauƙi fa, ki tambayi babban Yaya ma”. Ya ƙare maganar yana kallon babban yaya a raunane.
Cike da tabbatarwa babban Yaya ya jinjina kansa shima yana kaiwa zaune kusa da Oum ɗin, Fawzan ma yazo ya miƙama AA kofin tea ɗin daya haɗa masa suka zagayeta kowa na mata nashi daddaɗan kalamin, idan ka gansu abin sha'awa da birgewa sojojin yaƴanta zagaye da ita, basu barta ba har sai da fiskarta ta washe da fara'a kamar yanda suke so. Shima AA sai ƙoƙarin ƙarfafa kansa yake yanda hankalinta zai ƙara kwanciya. Ganin dare yayi Oum da babban Yaya suka baro sashen suna ƙara tattaunawa aka bar Fawzan da zai kwana da shi. Bayan wucewar tasu ne Fawzan ya zayyanema AA komai dake faruwa ana rikicin da Abah keyi akan tarewar Maanal kamar yanda ta buƙaci ji. Murmushi AA yayi mai faɗin da har ya saka Fawzan zuba masa idanu baki buɗe.
“Oh abin ma kai nishaɗi ya baka kenan?”.
Cewar Fawzan cike da mamaki. Murmushin AA ya sake saki a karo na biyu, sai kuma a hankali ya jingina da fuskar gadon yana kai hannu ya ɗan shafo gashi kumatunsa. “To yaya Fawzan in bai sakani nishaɗi ba kuka kake son nayi, banda ma abin Oum minene abin ɗaga hankali anan, ta bar masa ƴarsa mana”.
Dariya Yaya Fawzan yayi da faɗin, “Oh hakama zakace? ALLAH yasa ya jika, kaga idan sati ɗaya yay niyyar horaka sai ya maida shi wata uku kadai san halin Abah”.
Murmushi kawai AA yayi kaɗan batare daya sake cewa komai ba. Fawzan kuwa ya tasashi gaba da tsogumi...


__________★


Washe gari da safe Alhamdullah Oum ta tashi da sauƙin damuwa ba kamar jiya ba. Dan tunda ta kira Mah-mah a ɗazun da asuba ta sanar mata sai Mah-mah ɗin ta tausheta da mata nasiha akan ta sakama Abah ɗin ido, ta bashi damarsa matsayin mahaifi dan ko yaya shima bazai yi abinda zai cutama Ajwaad ɗin ba ai, sannan kuma tunda a gida ɗaya suke ai babu wani abun ɗaga hankali in dai yaran yanzu ne masu ƙarancin kunya, shi da kansa ma zaice ya ɗauki matarsa basai ta ɓatama kanta rai ba. Ji tai zuciyarta ta rage jin haushin Abah ɗin, ta kuma ɗau alwashin daidaita komai a tsakanin AA ɗin da Maanal ta yanda Abahn da kansa zai tattarasu ya kora sashen nasu batare da alwashin nasa ya cika ba.
Yau ɗin yanda Manaal take ta faman sinne-sinnen kai ya saka Oum kamata ta duddungure da faɗin, “Wai Auta ni kike son maidawa surukarki a gidan nan, jiya na saka miki ido ne kawai naga iya gudunki, to kar naji karna gani. Maza tashi muje kitchen ki haɗama mijinki abinci yau kije ki duba jikinsa dai kada mu take doka”.
Murmushi Maanal tayi tana ɓoye fuskarta a jikin Oum ɗin, itako Oum na mata dariya. Atare da Oum suka shirya abinci mai sauƙi ma AA ɗin har kala uku, sai wanda suma zasu ci, dan yauma Abah a sashen Mamy zai karya. Suna kammalawa Oum tace taje tai wanka, yayi da masu aiki keta faman kimtsa sashen kamar yanda suka saba. Ba wata kwalliya Maanal tayi ba, ta dai gyara fuskarta ta ɗan saka kwalli da lipsgloss, sai tai simple ɗaurinta daya zauna mata ɗan kwantaccen gashinta ya ɗan fito ta gaban goshi kaɗan. Tana ƙoƙarin saka turare kiran Amaal ya shigo mata. Ɗagawa tai cike da shagwaɓa dan haushinsu take ji a Kano sunce zasu dawo amma sukai mata wayo. Dariya Amaal ɗin taita mata, sannan ta kwantar mata da hankali akan ai next week in sha ALLAHU suna nan tafe da sauran kayanta, dan Daddy yace sai zuwa ƙarshen sati za'a kai kayan gararsu ita da Huznah. Duk da dai Oum tace a ɗan saurara akwai sauran biki da zasu yi anan Abujan shiyyasa ma bata tare ba. Sosai ita Maanal ma abin ya bata mamaki, yanzu duk wancan kaikawon da akasha na Kano bai kuma isa ba. A fili kam sai suka cigaba da maganar su da Amaal. Tana ajiye wayar mai aikin Oum ta shigo tai kiranta, mayafi ta ɗauka ta sanya, dan haka kawai taji tana jin kunyar fita a haka matuƙa. Tayi ƙyau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan ƙamshinta daban ne, ga ƙunshinta raɗam yanata ɗaukar ido daga baƙin har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autanta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai ɗorewa kuma. ALLAH ya kawo zuri'a masu albarka..........✍️




🏃Da suwa zamuje sashen AA ɗin ne?.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣




______________




.......Basket ɗin da aka shirya masa kayan abincin Maanal ta ɗauka, kai kace wani anguwa zasu je ba cikin gidan ba. Sun fito gwanin sha'awa daka gansu kaga uwa da ɗiya ba uwar miji da matar ɗa ba. Oum tasan Mamy na sashen Abah dan haka bama tace Maanal taje ta gaida su ba, shiru ma gidan alamar kowa na sashensa, sai ma'aikata dake ta ƙoƙarin kimtsa ko'ina, sunta gaishesu har suka isa sashen AA. Haka kawai Maanal ke jin kamar tace bazataje ba, amma bazata iyama Oum musu ba duk tsanani. Kai tsaye Oum ta shige dan tasan bazasu sami kowa a falon ƙasan ba, Maanal dai biye da ita zuciyarta na mata wani nauyi. Dan kana shiga da sallamar sabon fenti dana sabbin kaya zaka fara cin karo. Tabbas dole ne mai kallo ya furta Masha ALLAH, dan kuwa dai Daddy yayi matuƙar ƙoƙari, daga Maanal ɗin har Huznah ya zuba musu dukiya. Duk da asace Maanal ke kallon komai sai da taji hawaye sun cika mata ido sosai, wata irin ƙaunar Daddy da Ammie na ratsata, falon ƙasa ma kenan, bata san yaya kitchen yake ba, kuma su Didi sun sanar mata daga saman har ƙasa Daddy ya cika mata su da kaya. Zuciyar Maanal bata ƙarasa fashewa ba sai da suka hawo upstairs ɗin, ya subahannallah komai yaji, a hakan ma nan ba'a kammala aikin ba dan ga manyan kwalaye nan a ajiye gefe an tule, zama sukai a cikin kujerun dan su an riga an shiryasu, dai-dai nan Fawzan ya shigo shima da alama yaje sashensa ne.
Cike da tsokana yace, “Inyee kaga Lilly amaryar Auta”.
Da sauri Maanal ta ɗan waro masa idanu, sai kuma ta ɓata fuska. Dariya Fawzan yake yi, Oum dake tayashi ta ce, “Ni ban taɓa ganin yaya irinka ba Fawzan, anya kuwa bazan turaka hutu Kano ba ka bar min yara su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login