Showing 51001 words to 54000 words out of 218311 words

Chapter 18 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

tanka masa ba. Sai da ya isheta ne takai hannu ta ƙasan table ɗin ta mintsinesa. Idanu ya ɗan rumtse tare da cije lips dan yaji zafi, kafin yasa shima nashi hannun ta ƙasan table ɗin ya riƙe natan dake mintsininsa, tayi-tayi ta kwace yaƙi saki, dole ta haƙura. Shi ko ya cigaba da murza hannun dan wani irin laushi da santsi yake masa. Yanda yake mirza hannun sosai tsigar jikin Maanal ke tashi, amma ta dake abinta..
Abinda Maanal bata sani ba tuni ƴan sa'idonsu sun fassara abinda hannayensu keyi a ƙasan table, musamman daya kasance lokacin da Maanal ta mintsini AA ya lumshe ido da cije baki. Itama kuma yanayinta ya canja da ya kama hannunta yana murzawa. Su duka ukun zukatansu yi suke kamar zasu babbake. Yayinda sam babban Yaya da Fawzan da Oum su basu san ma mike faruwa ba. Hasalima hirarsu sukeyi. Rashin saka bakin AA a hirar kuma sun san wannan normal ne daga halinsa. Ba kowace hira bace zakaji bakinsa sai idan yaso tankawa, balle ma su Saheeba na wajen, kowa yasan baya hira da su, daga gaisuwa babu abinda ke sake shiga tsakaninsa da su..
AA neman harmutsama Maanal jiki yake, dan haka babu shiri ta miƙe tana fisge hannunta wai ta ƙoshi. Kallonta Oum, Babban Yaya da Fawzan sukai, yayinda AA yay wani shegen murmushi yana cigaba da cin abincin sa. Murmushin nasa ya ƙara tabbatar ma da ƴan saka ido abinda suke hasashe, ta wani gefen kuma ya motsa zukatan Nuratu da Nibras dan abune da basu saba gani ba. Lallashin Maanal Oum keyi akan ta ƙara ko kaɗan. Cike da shagwaɓa tace, “ALLAH Oum da gaske na ƙoshi zan yi amai idan na ƙara”.
A mamakin kowa sai ji sukai AA yayi ƴar dariya. Shagala matan sukai a kallonsa, dan har Saheeba ma dai mamaki ne ya dabaibayeta wai AA da dariya. Babban Yaya kam murmushi yayi, zuciyarsa fes da ganin farin cikin Autansu nata dawowa. Fawzan kuwa tsokanar tasa daya saba yayi. Yayinda Maanal ke kallon Oum kamar zatai kuka.
“Oum kin ganshi yana mun dariya ko”.
Kallonta AA ɗin yayi, “Kefa matsalata dake sharri Besty, shike nan bazanyi dariya ba, to inba tsargar kai ba mi kikayi da zan miki dariya?”.
Harararsa tayi, fuuu tabar wajen. Dariyar ya ƙara sanyawa, cikin ɗan ɗaga murya yace, “ALLAH ya raka taki gona”.
“Amma fasa tafiyar to”.
Manaal ɗin ta faɗa tana dawowa. Sai dai kujerar gefen Oum ta jawo ta zauna yanzu. Hatta Oum dariya takeyi, hakama Babban Yaya da Fawzan. Su dai matan da alama abin haushi ma ya basu, dan kowacce ta ɗauke kai. Cike da lallashi Oum tace, “Kinga ƙyaleshi Babyna, ya kamata zuwa yanzu ki saba da halin Auta, dan yaga ma kina fushi shiyyasa yake tsokalarki. Kin bari yaga lagonki ne, amma ki bari muma zamu gane nasa ai”.
Gwalo Manaal ta masa tare da kashe ido ɗaya. Sai ya haɗe fuska yana harrarta. Akan lips ya furta, “Zan kama ki ne ALLAH ya kaimu Chaina”.
Tsaf taga abinda ya faɗa, dan wannan sigace da sukema juna magana a baya idan basa son wanda ke kusa da su ya fahimta. Sosai taji gabanta na faɗuwa. Ita dai wannan Chaina da tana da yanda zatai sai ta cire kanta a ciki ALLAH. Gashi taga Abah baida niyyar hanawa..


Babban Yaya ne ya fara barin sashen, dan yace ya gaji barci yake son yi. Sai Oum ta kora Saheeba ta bisa. Maanal ma bata zauna ba ta tattare kayanta ta wuce ɗaki, acewarta aiki zatayi. AA ne ya zama na huɗu, acewarsa shima zaije yay aiki ne. To dama dai Nibras da Nurry dan shi suke zaune, sai dai da kunya ai su ce suma zasu wucen. Dan haka suka ɗan daure suna taya Oum hira. Dan AA yaja hannun Fawzan sun fice tare kamar zasuyi magana ne ya dawo shima dai shiru. Dole suma cikin dabara sukama Oum sallama suka gudu. Da kallo kawai Oum ɗin ta bisu, sai ma duk taji sun fara bata tausayi musamman ma Nibras, zata cigaba da mata addu'a ALLAH ya cire mata shaiɗancin nan a zuciyarta, za kuma ta dinga bata shawara a cikin hikima ko ALLAH zai sa ta gane ta tsaida hankalinta waje guda ga mijinta.....


_________★


Matuƙar zafi rayuwa tama Hajiya Basariyya. Dan tana dira gidan Kawu Manu dake wani ƙauye a ingawa local government ya ƙwace wayoyinta duka. Ya kuma shimfiɗa mata sharuɗan zaman gidansa. Zata hau yimasa magiya daban haƙuri yace baya buƙata. Lokacin da suka iso dambun tsakin masara sukai mai daɗi, yaji zogale da gyaɗa abinsa kuwa ga man ƙuli mai ƙamshi ɗan asali. Amma ita ƴar rainin wayo sai cewa tai bazata ci ba. Babu wanda ya kulata kuwa. Da dare akai tuwo na dawa mai daɗi nan ma. Harda naman zabuwa a miyar, dan duk da Kawu Manu na ƙauye miyar gidansa kullum da nama. Kiwo yake sosai na dabbobi kala-kala. Nan ma ƙin ci tayi, taci biscuits ɗin data ɓoyo a kaya da drinks. Duk bawai ya isheta bane ta dai daure. Washe gari da safe ana idar da sallar asuba da kansa ya kwankwasa mata ɗaki, yanda ta fito ya fahimci bama tayi salla ba. Aiko ya balbaleta da masifa, ya kuma tabbar mata shi ba'a masa lallaci a gida musamman na ibada. Dan haka ta tattara ta koma ɗakin Iya matarsa. Sosai hankalinta ya tashi da jin hakan, amma babu yanda ta iya. Haka taje tai salla, tana idarwa yace ta fito, tsintsiyar kwakwa ya jefa mata ya nuna mata tsakar gidan alamar shara, ya koma kan ɗan dutsen da yake zama a tsakar gidan daga can gefe ya zauna. Ba ƙaramar raunana zuciyarta tayi ba, dan tasan babu abinda ya damu Kawu Manu da shekarunta horata zai yi yanda ya kamata. Shiyaysa taso ta gudu gidan mijinta. Babban tashin hankalinta kayayyakin da suka amso da Maman Yaseerah suna can ta baro a Kaduna gidan yayanta, ga Huznah bata san a halin da take ciki ba a yanzu. Haka dai tai sharar s jigace saboda abune da ita kanta basan adadin shekarun data ɗauka batayi ba, ga tsakar gidan ƙaton gaske kun san dai gidan ƙauye akwai yalwar albarka. A gidanta komai yan aiki ke mata. Wataran ma suyi tace baiyi ba sai sun maimaita. Tana gama share ƙaton tsakar gidan yace ta shiga turken dabbobinsa dake zagaye da danni na itace. Wani irin amai ta dinga ji na masifa na taso mata, dan sunyi ɗanyen kashi ya haɗe da fitsari abin ba'a magana. Sai kawai taji hawaye sun ciko mata ido. Haka ta duƙa tayi sharar, da ƙyar ta gama, sai da ta koma tayi amai sosai. Yi kawu Manu yay tamkar bai jiyota ba, balle kuma Iya daketa hada-hadar ɗora wainarta ta sayarwa ta safe da take yi. Gefe kuma ta dama koko ta ɗaura ɗumamen tuwo na gida.
Hajiya Basariyya na kammala sharan Kawu ya shigo turken, ɗakin dake a gefen wajen ya nuna mata, yace ta fiddo abinci ta raba musu, ta kuma wanke manyan kwatanniyar dake wajen guda biyar ta haɗa musu ruwan dusa a ciki. Daga haka yay ficewarsa ya barta..........✍️










*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣5️⃣




______________




25




.......Sosai Rabilu ya gigice da tsawar da Sen.. Bukar ya buga masa. Shi ko cikin matuƙar rufewar idanu da shiga tashin hankali mara misaltawa ya cigaba da faɗin, “Kai wawan inane da bazaka kirani ka sanar min ba tun a lokacin Rabilu, sai yanzu zakazo kana gaya min wannan shashashar maganar. Aiko wlhy ko ɗan uban wanene wanda ya auretan sai ya saketa, dan ban taɓa san wata mace kwatankwacin yanda nake son yarinyar nan ba”.
Cikin girgiza kai Rabilu ya ce, “Ranka ya daɗe kayi haƙuri, nima na rasa ta yanda zan isar maka da saƙon nan ne wlhy, tunda kaga tunda ka tafi bamuyi waya ba balle na samu lambar. Amma ka gafarceni. Auren yarinyar kuma yazo da ƙura, dan in har akace za'a ƙwatota akwai rikici. Saboda AA Darma ta aura”.
“AA what?!!”.
Sen.. ya faɗa cikin matuƙar zabura jijiyiyin jikinsa na mimmiƙewa. Dan baya jin a kusan nan an taɓa faɗa masa abinda ya girgiza masa zuciya kamar wannan da yaji a yanzu. AA Darma ne ya aura ƴar shularsa fa. Eh lallai akwai yaƙi kenan a Abuja. Tsabar yanda Rabilu ya sake firgicewa da yanayin ogan nasa shi kansa jikinsa rawa yake yi. Sai da yaji dana sanin ma sanar masa zancen. To amma yasan dole ne ya sanar masan, kodan yanda tun jiya ya fahimci yanda ya matsu da jin wani abu a bakinsa game da Maanal ɗin. Yau kuma yana fitowa a gida shi ya fara nema yace yazo office ya samesa. A ɗarare kuwa yazo amma bashi da damar zillewa dole ya faɗa.
“Munafuki tashi ka fitar min a office. Kuma karna sake ganin fuskarsa sai na nemeka”.
A rikice Rabilu ya fara bama Sen.. haƙuri, amma bai sauraresa ba, sai ma cewa yay idan bazai fitan ba zai sa security suzo su fidda shi. Yasan zai iya, dan Sen.. bashi da kirki, shi kansa alaƙarsu tayi tsaho ne saboda yana samo masa irin matan da yake so ne a kuma duk lokacin da yake buƙata. Haka ya tashi ya fito jikinsa a sanyaye. Dan wannan hanya dai shi kam itace hanyar cin abincinsa. Gashi tafiyar Sen... Ɗin wata da watanni ta sashi a halin rashin kuɗi, ya dawo da tunanin yanzu zai jiƙe ga kuma wannan akasi ya shigo. Amma ba komai zaije yay tunanin hanya mai bullewa, yasan wutar da zai kunno ta yanda dole Sen... zai nemosa da wuri-wiri......


_______★


Washe gari kasancewar Maanal tasan ba fita aiki zatai ba tana idar da sallar asuba ta sake komawa barci bayan taba Oum saƙon wani document taba AA. Oum bata hanata kwanciyar ba, dan taga raba dare tai jiya tana aiki, sai da ma tace ta kwanta sannan tace to. Amma badan haka ba ai bazata barta kwanciyar nan ba. Dan ta ɗauki ɗamarar hana Maanal zama irin su Nibras a gidan, tana son babynta ta horu da kula da mijinta, duk da tasan Ammie ma ba wasa bace wajen tarbiyyar yara, hakan ma a bayyane yake ga Maanal ɗin.
Yau Oum ita kaɗai ta haɗa breakfast ɗin da taimakon su Inte. Bayan ta kammala ta bar musu su shirya a dining ita kuma ta nufi yin wanka, dan tasan itama Abah na hanyar dawowa tunda yace shigar safe zaiyi. Har yanzu Maanal na ƙudundune a duvet tana barcinta hankali kwance...
Bayan kammala wankan Oum ta shiryawa ta samu Fawzan kawai a falon yay zaman karyawa, dan yana son fita da wuri-wiri ne acewarsa. Gaishe da Oum yayi, ta amsa masa da kulawa tana tambayarsa iyali. Shima ya tambayeta Maanal tace tana barci.
“Oh na manta Oum tace yau bazata aiki ba tana hutu”.
“Eh, ai kasan saboda tafiyarsu gobe ne”.
“Wai Chaina ɗin dai?”.
“Eh, duk da bamu da matsaya dan Abanku baice komai ba har yanzu”.
“A Oum karki damu zaima barta, ai aiki ne”.
“To ALLAH yasa Fawzan Abanku ne rikicinsa yawa garesa”.
Ƴar dariya Ya Fawzan yayi, dai-dai lokacin kuma AA ya shigo da sallama. Yau dai normal shiga akai ta yadi ruwan toka mai duhu sosai. Kai daka kallesa kasan an sayesa da kuɗaɗe masu tsada, dan ya kwanta luff-luff kamar ajiyayyar ƙanƙara. Rigar ba wata mai tsaho bace, hakama hannunta gajere ne ko gwiwa bai kai ba. Babu dai hula amma yayi ƙyau sosai. Briefcase ɗinsa ya ajiye a saman kujera kusa da wadda ya ja zai zauna cikin muryar nan tasa mara hayaniyar sauti ya ce, “Good morning Oum, Ya Fawzan morning”.
A tare suka amsa masa, Ya Fawzan ya ce, “Ya dai Autan Oum naga kanata kunbura?”.
Ƙin kulashi AA yayi, sai ma jan flaks ɗin gabansa da yay ya buɗe dan yasan maybe kunu ne. Sai Oum ce ta bama Fawzan ɗin amsa da, “Fawzan kadai sakama autana ido a gidan nan”.
Da ƴar dariya Fawzan yace, “Oum babu wani sa ido, shi ɗin ne sai a hankali, yanzu haka fushin nan dan Lilly bazata aiki bane yau.”
“Oum ALLAH zan bar masa wajen”.
AA ya faɗa cike da shagwaɓa. Dariya Oum ta danne ta ce, “Kaga manta da shi my baby, ci abincin ka. Ni zan maka maganinsa. Dan kawai mutun ya tashi da ɗan rashin son maganarsa sai kuma a fassara shi”.
Dariya sosai Fawzan yake yi, sai ma ya miƙe abinsa dan ya kammala karyawa, duƙowa yay saitin kunnen AA ɗin cike da raɗa ya ce, “Saboda kai kwar-kwar ne shine ka tsara su Oum da sunan aiki kai da Lilly a Chaina ko, to ka turan hundred k kona tonaka cewar honeymoon zakaje ehe”. Yana gama faɗa yay gaba, sai da ya je ƙofa sannan ya juyo, kamar yanda yay zato kam harararsa AA ɗin keyi.
“Harareni da ƙyau nidai inji alert, idan ba haka ba zakaga tone-tone yau”. Yay ficewarsa. Karan farko AA ya saki murmushi tare da girgiza kansa. Har cikin ransa yana ƙaunar ya Fawzan ɗinsa. Dan soyayyar ƴan uwansa ta musamman ce a garesa. Abincinsa ya cigaba da ci suna ƴar hira da Oum, shigowar Nuratu ya sashi yin shiru. Sosai ƙamshin turaren data bulbula ya fara hawa masa kai, dan ko kaɗan bai kalla ma inda yasan take ba. Gaisheshi ma da tayi hannu kawai ta ɗaga mata. Tabbas yana son ƙamshi, amma ba irin wannan mai hawa kan ba na mahaukata, balle ma ga mace, shiyaysa kaf turaren da Maanal ke amfani dasu suna masa daɗi da saukar masa nutsuwa, musamman ma traditional. Sallamar Nibras itama da nata salon gayun yasa shi miƙewa badan ya kammala cin abincin ba, matsawa yay inda Oum take ya kama hannunta ta sumbata. “Oum yimin addu'a”.
Addu'ar ta masa harma da sauran ƴan uwansa sannan ya mata sallamar tafiya. Har ya nufi ƙofa ta ce, “Af Auta na manta. Akwai takardu da Baby ta ajiye na baka, suna nan a side drawer na manta na fito da su. Kansa kawai ya jinjina mata, a ransa kuwa faɗi yake, (Lallai ƴar Oum ta gama rainani, ina boss ɗinta a wajen aiki amma ni zata aika na kai mata aikinta. Ba komai zamu haɗe ne). Da wannan tunanin ya shiga bedroom ɗin Oum. Saukar idanunsa a kanta ya sashi sauke ajiyar zuciya duk da bawai yana ganin fuskarta bane. Sai kuma ya shiga takawa a hankali har zuwa gaban gadon. Dai-dai fuskata ta ya tsaya cak, samun kansa yay da zubama ƙyaƙyƙyawar fuskarta datai wani fresh fararen idanunsa. Yanda ta ɗan tura baki gaba baima san ya saki murmushi ba. Sai kuma ya kai duƙe gaban gadon a saitin fuskar tata. Yatsarsa manuniya ya ɗaura a saman lips ɗin da suka ɗan bushe suka sake takurewa waje guda ya shiga shafawa, kafin ya janye ya maida saman goshinta ya gyara mata gashinta da suka ɗan barbaje har saman idonta. Duk yanda yaso daurewa ya kasa, sai da ya kai nasa lips ɗin a slowly ya sumbaci natan. Sai ko kamar tasan mike faruwa ta motsa, idanunsa ya ɗan rumtse dan sam baya son ta farka ta ganshi. Sai kuma ALLAH ya taƙaita abun kwanciya aka gyara. Shima miƙewa yay ganin ta cigaba da barcin, inda Oum tace file ɗin yake ya ƙarasa ya ɗauka. Daga haka ya fito. Oum kawai ya cema “bye”. yay ficewarsa ko kallo Nurry da Nibras basu ishesa ba. Da baya ya dawo, hakan yasa su duka sake kallonsa. Ya ce, “Oum idan Besty ta tashi Please ta min shara. Sashen yayi daty”.
“A'a bola fa? Yanzu ya daina gyarawa?”.
“No Oum na dakatar da shi, saboda akwai banbancin da da yanzu ai ko”.
“Eh gaskiya hakane kuma Auta na. Babu damuwa zata share in sha ALLAHU. ALLAH ya bada sa'a”.
Da “Amin” ya amsa yana wucewa. Oum ma sai ta miƙe tabar Nibras da Nurry dake ta faman ƴar hararrar juna..........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login