Showing 120001 words to 123000 words out of 218311 words
Chapter 41 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
rungume Mamy data cika tai fam a zuciya itama. A bayyane yace mata happy salla, sai hakan ya sake ƙuntata ta taji a ranta wani abu ya faɗama Oum ita bai faɗa mata ba. Fawzan ma Oum ya ɗan fara rungumewa yay mata Happy salla kafin Mamy, sai Nibras data shigo yanzu cikin kwalliya dan yin hakan kamar al'adar gidan ce a duk irin wannan ranar. Sam hankalin Nibras a son ganin AA yake kawai, dan haka a fisge tacema Fawzan ɗin happy salla kawai ta matsa ta rungume Oum sannan ta matsa ga Mamy, Abah kuma ta risina ta gaisheshi shima tamai happy salla. A lokacin da Fawzan ke rungume Nibras ido suka haɗa da Najma. Ta wani ɗauke kai gefe idanunta cike da kishi. Murmushin yayi, kafin ya nufi ta inda take cike da iya taku yay kamar zai ɗauka abu a dining, cikin kunneta ya ce, “Sorry love a huce happy salla”.
Dai-dai nan Saheeba da Babban yaya da yara suma suka shigo........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣9️⃣
______________
.......Suma dai haka sukaje suka rungume su Oum Babban yaya harda Abah ita kuma ta risina ta gaida Abah, Fawzan da Babban Yaya ma suka rungume juna. Kamar an saita dai-dai nan AA ya shigo shima. Da Abah, Babban Yaya, Fawzan, AA ɗin duk farrar shadda ce da akaima ɗinkin babbar riga na zamani, sai dai kowa da kalar nashi design ɗin. AA bai damu da saka manyan kaya ba, shiyyasa idan ya saka sai su masa wani masifar ƙyau. A haka ma bai saka babbar rigar da hular ba duk suna a hannunsa. Sai wata ƴar shopping bag mai shegen ƙyau da tambarin MAWAAD a jiki a hannunsa. A kaikaice ya gama kalle falon amma bai hango zinariyarsa ba. Cikin dakewarsa ya ƙarasa ya fara rungume Oum tare da mata Barka da salla. Ta shafa fuskarsa da murmushi ta amsa masa. Shima murmushin yayi ya buɗe bag ɗin hannunsa ya fiddo wani ɗan ƙyaƙyƙyawan box fari tas ya buɗe. Haɗaɗɗen agogo ne new design daga MAWAAD ya ciro, hannunta ya kama ya cire agogon data saka ya saka mata wannan tare da zobensa shima mai ƙyau, sai ya kama hannun ya sumbata. Hawaye ne suka cika idon Oum, ta sake rungumesa tana sanya masa albarka.
Gaban Abah dake kusa da Oum shima yaje, ya rungumesa ya masa Barka da salla shima ya saka masa nasa agogon. Albarka sosai Abah yake saka masa harma da sauran ƴan uwansa. Sai Mamy data gama cika da kishi da baƙin ciki, a ganinta ita ya dace AA ya fara yima haka ba Oum ba. Sarai ya fahimci hakan a cikin idanunta amma sai ya basar ya mata murmushi itama yay hugging ɗinta yay mata barka d salla ya saka mata nata agogon. A taƙaice tace ALLAH yay masa albarka. Bai damu ba ya ƙarasa ga babban Yaya, shima dai haka yay masa, sannan Yaya Fawzan. Dai-dai yana sakin Yaya Fawzan dake masa raɗar shaƙiyanci a kunne Maanal da Batool suka shigo. Dama ta tsaya yima Batool ɗin kwalliya ne saboda barci data koma da ƙyar aka tadata tai wanka. Wani irin harbawa zuciyar Nuratu da itama take fitowa a lokacin cikin matsananciyar kwalliya da Nibras da AA sukai a lokaci guda. Dan harga ALLAH Maanal ɗin tayi shegen ƙyau a Abayar data sanya fara tas da ɗan kwalliyar ash kaɗan like kalar aikin jikin shaddar AA, sai handbag ɗinta itama ash mai shegen ƙyau designer, hakama takalman ƙafarta, duka suna cikin kayan da AA ya bata jiya kuma shine yace ta sanya su yanzu. Bata fahimci ma'anar hakan ba sai yanzu ta gane ashe anko yake son suyi. Sai ma taji kunya ta kamata ALLAH. Amma sai ta basar ta dake. Suna ma haɗa ido ya wani ɗage mata gira sama sai ta kauda kanta tana guntun murmushi ciki-ciki.
Abah ta fara risinawa ta gaida, ya amsa mata da kulawa, tai masa barka da salla ya sanya mata albarka. Sai ta matsa ta rungume Oum dake ta kallonta dan kwalliyar ta mata ƙyau sosai. To dama kowa ai yasan Maanal da shegen son gayu da ƙyale-ƙyale. Duk da Hararar da Mamy ke mata a kaikaice yitai kamar bata gani ba taje itama ta rungumeta. Kafin ta gaishe da Babban Yaya sai Yaya Fawzan. Ta haɗa Saheeba da Nibras da duk ciwon hassada ya kamasu da ganin kaya masu mugun tsada da Maanal ɗin ta sanya a jikinta tun daga kan abayar har bag zuwa takalmi. Dan a yau kam sun sake tantance lallai AA yafi mazansu kuɗi, saboda ita Saheeba tana saida kaya tasan nauyin kowane irin kaya. Musamman su abayas, lass's, atamfa, da shadda da yadi na maza. Ita ko Nibras uwarta ƴar gayu ce kuma ƴar ƙarya da son ƙyale-ƙyale dan haka irin wannan manyan kayan tun suna yara koda bala'i uwarsu kan haɗa ta siyama kanta, ko koda kuɗin cuwa-cuwa na mutane😆😜.
Kan Maanal a ƙasa ta juyo domin gaida AA kawai bawan ALLAH ya rungumeta. A kunne ya raɗa mata, “Barka da salla and matsowar shiga daga ciki Mrs Ajwaad. You look great in white”. Gaba ɗaya sai taji ta daburce. Balle ma da Yaya Fawzan ya wani ce. “Aouwwwww!! Kaga Masoyan asali”.
Sosai kunya ta sake dabaibaye Maanal. Ta janye jikinta tana ɓoye fuska da veil ɗinta da tai rolling yay mata ƙyau kamar ka saceta ka gudu. Hannu AA ya kai zai ƙwace wayar Yaya Fawzan dake musu video. Yay saurin sakawa a aljihu yana dariya. Ganin haka sauran yaran dake musu hoto da videos suma suka shiga ɓoye wayoyin suna gimtse dariya. Oum, Abah, Babban Yaya ma dai murmushi duk suke. Yayinda Mamy ke jin tamkar zuciyarta zata fito ta baki. Nuratu zata juya ta koma ciki Saheeba ta riƙo mata hannu ta hanata. Nibras kam sai da ta ya share hawaye...
Zaman karyawa sukai, dama tea ne kawai sai ɗan abinda ba'a rasa ba. Kasancewar ciki duk a cinkushe saboda azumi da aka sha babu wanda yaci na kirki duk suka tashi. Kowa ƙara gyarawa yay suka fito domin shiga motoci. Maanal na ƙoƙarin shiga motar babban Yaya AA ya wani riƙo hannunta, juyowa tai ta kallesa dan a zatonta cikin su Najma ne. Ƙaramar harara ya sakar mata yaja hannunta kawai suka nufi tasa motar. Sai kawai Mamy catai itama Nuratu ta tafi can. Wani shegen murmushi Abah yayi, sai dai baice komai ba yay shigewarsa mota kusa da Oum dake waya bata san mike faruwa ba. Yayinda Babban Yaya da Fawzan sukabi Mamy da kallon mamaki. AA kam da sarai yaji Mamyn yi yay kamar baiji ba, sai ma buɗema Maanal yay ta shiga hannunsa na riƙe da bag ɗinta ya zagaya nasa mazauni ya zauna, ita kuma babbar rigarsa da hula na saman cinyarta ya ajiye.
Wani irin abu ya tsayama Najma na takaici, dan tunda Uncle R da Maanal suka tattauna akan Mamy a gabanta duk da basu fito fili sun ambaci sunanta ba itama ta sakama dukkan motsin mamy ido. Sai kawai itama ta fasa shiga motar Fawzan datai niyya ta koma ta AA suka shiga a kusan tare da Nuratu. Kallon juna sukai, Najma ta watsama Nuratu wani shegen harara ta ɗauke kanta.
AA kam baiyi kamar yasan bayan shi da Maanal akwai wasu a motar ba, yana gama zama bag ɗinta a saman cinyarsa ya juyo yana kallonta, sai kuma a hankali ya kai hannu ya kamo haɓarta ya juyo da fuskarta inda yake dan da ta shagala ne da kallon design ɗin jikin babbar rigarsa da yay mata ƙyau.
“Nan zaki kalla zuciyar Ajwaad. Dan rigar da mai rigar duk naki ne ke ɗaya. Aikin ya miki ƙyau ne”.
Wani kasalallen murmushi Maanal ta sakar masa mai taɓa zuciya, cike da shauƙi ta kai hannu ta ja masa hanci kaɗan, “Duk ƙyan aikin kaine zaka sakashi yay ƙyau dan kai ke saka ƙyawu yayi ƙyau zuciyar maanal. I like you in manyan kaya”.
Ya arrahaman, ji AA yay kamar zai wani shiɗe, bai ma san ya matso da fuskarta gab da tashi ba ya manna lips ɗinsa kan nata ya ɗan sumbata kaɗan. Sosai kunya ta kamata sanin basu kaɗai ne a motar ba, shiko idanunsa har sun ɗan sirka. Maanal ta ɗan maida fuskarta gefe kawai tana ɗan murmushi. Dai-dai nan babban Yaya yayima AA ɗin horn dan shine a bayansa. Ajiyar zuciya ya sauke a kasalance yay ma motar key, Nuratu da zuciyarta ke neman tarwatsewa ta kama murfin zata buɗe dan ta yanke gara ta fita a motar kawai taji ya saka luck. Dole ta koma ta zauna dan tsoronsa take ji bazata iya cewa zata fita ba kai tsaye.
AA kam da shi yama manta da zamanta a motar a hankali yake mirza steering motar kamar baya so, dan gaba ɗaya Maanal ta gama kashe masa gaɓɓan jiki. Hannansa yakai a hankali ya kamo nata, sai ta juyo ta kallesa, shima kallon nata yay suka sakarma juna murmushi mai sanyi. Sai kowa ya janye, shi ya maida ga hanya ita kuma tana kallon waje har lokacin da murmushi a fuskarta dan ita kaɗai tasan mi take hangowa a cikin idanun ƴan maza. Najma kam cike da munafunci take musu video, dan wannan gulmar bazata gani ita kaɗai ba sai ta gumtsawa su Maimoo.. Sai kuma uban murmushin shaƙiyanci take zubawa da son ƙular da Nurry. Tako ci nasara, dan zuciyar Nurry har wani tururi take yi. Wata irin nadamar shiga motar take ji, ga zuciyarta fal bala'i amma babu damar nunawa tana tsoron shan mari a hannun AA Maanal ta samu na nata gori...
A haka suka iso massalaci. Nuratu ta fara ficewa AA na kammala parking, Najma ta bita tana ƴar dariyar ƙularwa. Maanal na yunƙurin fita AA ya riƙota. Juyowa tai tana kallonsa. Ya marairaice mata fuska kuwa da faɗin, “Idan kin fita wazai ƙarasa shiryani, bayan kin san ban saka bane saboda kema ki samu kada”.
Murmushi kawai Maanal tayi da ɗan girgiza kai, batare da tace komai ba ta ɗauka babbar rigar dake jikinta ta shiga warwarewa yana kallonta ƙuri kamar ya haɗiyeta yake ji. Amma dai ya daure dan yana son tsira da alwalarsa. Nuni ta masa da idanu ya duƙo, babu musu ya ranƙwafo sosai yanda zata ji daɗin saka masa ta saka, cike da kulawa batare data yarda sun haɗa ido ba ta gyagygyara masa duk da yana a zaune ne harda naɗo duka gefen biyu ta ajiye masa a kafaɗa duk da bawai babbar rigan nada faɗi bane. Dan anyita ne ƴar cif-cif babbar rigar zamani dai da faɗin nata duka baya wuce gwiwar hannu. Hula ta ɗauka ta shiga mata kari dan ta iya, tun suna yara tana masa karin hula, shiko sai kallonta yake, nan ma kan ya duƙo mata ta sanya masa, cike da kunya tasa yatsanta tana gyara masa ɗan gashin daya fito gefe-da-gefe kaɗan.
Batare data yarda ta kallesa ba ta ce, “An gama”.
Wani ƙaramin box ya miƙa mata, cikin raɗa muryarsa na sake komawa ƙasan maƙoshi yace, “Saura agogo da turare”.
Batace komai ba ta amsa box ɗin ta buɗe, irin na su Yaya Fawzan ne shima, hannunsa daya miƙo mata ta amsa a cikin nasa kunya na sake rufeta, tadai daure ta saka masa sannan ta ɗauka turaren dake ajiye a tsakkiyarsu ta shiga fesa masa. Sai da ta ajiye turaren ta ɗago ta wani kallesa, sai kuma ta kashe masa ido ɗaya ƙasa-ƙasa,...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣0️⃣
______________
.........“Ka cinye wannan zangon, kaine gwarzon shekara ƙyawawa na duniya my bestie”. Ta faɗa tana haɗe yatsunta babba da manuniya🤏.
“Kin fini ƙyau ai Matar AA”.
Ya faɗa cike da kasalar jiki data zuciya. Tare da kamo hannunta ya kunce agogon data saka ya saka mata wani mai shegen ƙyau dake tare da abin hannu sun sha stones farare sai ƙyalli suke, kaida da gani kasan ba normal stones bane ba. Baki ta saki kawai tana kallon hannun nata, sai kuma ta kallesa idannunta na ciko da ƙwalla. Tana motsa lips ɗinta da nufin yin magana yayma bakinsa alamar zipping. Dai-dai nan akai knocking glass ɗin motar. A hankali ya furzar da numfashi tare da cirar tissue ya miƙa mata sannan ya gyara zamansa ya sauke glass ɗin. Yaya Fawzan ne, cike da shaƙiyanci ya duƙo saitin kunnen AA yace, “Babu dai wajen canja sabuwar alwala anan a dinga tunawa ehe”.
Rasama abin cewa AA yayi, sai kawai ya cije lips ya buɗe motar ya fito hannunsa riƙe da bag ɗinta. Itama Maanal fita tayi tacan. Kallon bag ɗin Fawzan yay cike da tsokana, sai kuma ya wani riƙe haɓa tare da faɗin, “Ni dai ka rufa min asiri karka cinye min ƙanwa ita kaɗai garan mace. Yau zan maka addu'a Abah ya baka ita mu huta dai kodan Baby”.
Karaf a kunnen Maanal data matso domin amsar bag ɗinta a hannunsa, ai da sauri tai ƙoƙarin juyawa AA daya ɗan harari Yaya Fawzan ya riƙota. Bata juyo ba, shima baiyi magana ba ya saka mata bag ɗin kawai a hannu ya saketa. Kamar ƙyaftawar ido tabar wajen. Dariya Fawzan yayi kawai.....
Anyi sallar idi bayan khuɗuba mai ratsa zuciya. An kuma sha addu'oi sosai. Koda aka idar ɗai-ɗai ahalin Darma suka dawo inda motocinsu suke. Salim ya fiddo Camara ɗinsa yace sai anyi hotuna. Babu wanda ya musa dan kowa yasan Salim mayen iya ɗaukar hoto ne. Tun ma Uncle Mahmud na masa faɗa harya haƙura ya saya masa camara ya kuma saka shi yay training class akan hakan. Tsaf ya saita camara ɗin ya ajiye shima ya dawo cikinsu akai hoton. Sunyi kamar biyar sannan suka shige motoci idan anje gida sai a cigaba. An dai yi waɗan nan ɗinne a filin idi domin tarihi...
Yanzu kam babu wanda ya shiga motar AA, dan Mamy ma bata fargaba Nurry ta afka motar Babban Yaya. Ganin haka sai Najma ta shiga ta Yaya Fawzan daketa mata gargaɗi da ido. Aiko suna shiga abinka da gilashi mai duhu AA ya wani jawo Maanal ya rungume tsam, dan ɗazun yana sassautawa ne saboda alwala. Sai kuma ya ɗagota ya manne lips ɗinsu waje guda ya shiga bata zazzafar sumbata mai tsayawa a ƙahon zuciya. Sai da yaga yana neman sakin layi jikinsa kuma na neman canja yanayi sannan ya saketa. Sam kasa haɗa ido Manaal tayi da shi har ya tada motar yabi bayan sauran. Shima bai sake cemata komai ba har suka iso gida. Anan compound aka yada zango, hotuna aka fara ɗauka kamar babu gobe. Maanal nata dojewa kar suyi daga ita sai AA, sai dai hakan bai yiwu mata ba, dan an gama ɗaukarsu ita da shi da Oum, Oum ta juya zata bar wajen saboda magana da Babban Yaya ke mata itama Maanal ta yunƙura zata gudu AA ya riƙo hannunta, kanta ta juyo kawai a hanka ta kallesa shima yana kallon nata kawai Salim ya ɗauka ƙitt. Aiko hoton yayi masifar ƙyau. Ya juyo da ita tazo dab da shi kanta a ƙasa yana kallonta nan ma Salim ya sake ɗauka. AA ya ranƙwafo sai tin kunenta zai mata magana nan ma aka ɗauka. Matuƙar ƙyau hotunan nan sunyi. Takaici kamar Mamy zata haɗiyi zuciya ta mutu. Kowa fuskarsa da farin ciki itako tata sai baƙin rai. Ko hotunan ba kowanne ta shiga ba, ta koma gefe ta zauna tana ta sauke ajiyar zuciya. Koda ta turo Nuratu su ɗauka da AA Salim na shirin ɗaukar hoton dan wulaƙanci AA ya juya baya yana amsa waya sai bayansa da Nuratun aka ɗauka. Bai kuma tsaya ba yay gaba. Nurry ta bishi da kallo idannunta na ciko wa da hawaye. Sai kuma ya juya tana kallon Mamy. Wani irin daɗi Nibras taji da hakan ta faru, duk da zuciyarta kamar ga kama da wuta akan hoton AA da Maanal. Tana can tana kishi mara amfani Fawzan na nan yana ɗaukar nasa da Najma. Ɗaukar hoton data ja hankalin Abah da Oum kansu. Dan kai tsaye suka fahimci akwai wani abu a tsakanin yaran. Wani kalar daɗi Abah yaji, sai yaji kamar ya tashi ya goya Fawzan. Oum ma jitai hawayen daɗi na ciko mata idanu, koba komai Finally shima Fawzan ɗinta zai samu mai share hawayensa. Mamy kam baƙin zuciya da sakama AA da Maanal ido datai yasa