Showing 60001 words to 63000 words out of 218311 words
Chapter 21 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
sama da ƙasa a lokaci guda cikin wuyansa. Idanun da yake faman rumtsewa ya buɗe, sai kuma a hankali ya ture laptop ɗinsa gefe can ƙuryar maƙoshi ya shiga kiran sunanta cikin taushi da sauƙin sauti dake fita cike da kasala da ƙyar..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣9️⃣
______________
.......Tun Maanal najin tamkar ana kiran sunan nata a nesa ko cikin barci harta fara jin saukar sautin a cikin kunnenta. Numfashi irin na mai ƙoƙarin farkawa ta sake tare da fara buɗe idannunta a hankali. Tun tana ɗan jansu luuu ta maida kuma ta lumshe harta buɗe gaba ɗaya a kan fuskarsa daya ɗan duƙo yana kallonta shima. Sake maida idanun tai ta lumshe, sai kuma ta buɗesu da ƙyau, cikin sa'a kuwa suka shige cikin nashi dake a kaɗe daya zuba mata. Itama nata ɗin sun kaɗe tare da ƙara girma sun ɗan kumburo ta fatar saboda barci. Samun kansu sukai da kallon juna, kallo irin mai shiga jikin nan da tsinka jini. A tare yanayin jikinsu ya fara canjawa, cikin ƙarfin hali AA ya motsa nashi lips ɗin can ƙasan maƙoshi da sauti na mai raɗa girarsa ɗaya a ɗan ɗage ya furta, “You still pretending to be sleep?”.
Baki ta ɗan tura tana lumshe idannunta, sai kuma ta ɗan kifa kanta a jikinsa tamkar wadda taji kunya ƙasa-ƙasa da murya irin ta wanda ta tashi a barci ta ce, “Uhm… sorry. Ban san na kwanta haka ba.”
Gefen lips ɗinsa ne ya motsa kaɗan alamar son yin murmushi, sai dai baiyi ba, Da wani irin sake sauƙaƙa murya ya ce, “Hmm kinji na tambayeki yanda kika kwanta ne?. Barci yay daɗi kin haye VIP jiki.”
A yanda yay maganar ya sata ɗan ɗagowa ta ɗan kalle shi da ido ɗaya, cikin ɗan waro masa idanun da shagwaɓe fuska ta ce, “Na haye? Ni wlhy sharri kamun”.
Ɗan sunkuyowa yay fuskarsa gab da tata yana kallon cikin idonta a hankali, cikin zolaya ya furta, “To ko jikina ya janyo ki ne? Dan da alama yana da ɗumi sosai tunda har kika zaɓeshi fiye da bargo.”
Idanunta ta janye daga cikin nasa tana mai kai hannu ta sosa goshi dan kunya, sai kuma ta ɗan juya gefe tana jin kamar ta saki kuka dan kunya ciki-ciki ta ce, “Ni dai sharri aka mun tunda ban hau ba, ƙilama bugar dani akai dan a ɗaura ni”.
Yanzu kam sai da ya ɗan murmusa tare da lumshe ido, yana jin daɗin yadda take jin kunya. Cikin sake sauke murya ya ce, “Shiyyasa naga an kanannaɗe ni ai ko Madam pretender! Maimakon ki ce (thank you for being so comfortable Besty) ki bani sumba mai zafi na godiya”.
Hannunta dake jikinsa tai saurin warwarewa, sai kuma ta yunƙura zata tashi. Maidata yay ya hanata hakan, cikin son ɓoye fuskarta ta ce, “ALLAH ni ka daina kana bani kunya”.
Cike da basarwa cikin magana ɗaɗɗaya kamar ba daga bakinsa take fitowa ba ya ce, “Kunya mai ƙyau ce musamman idan tana zuwa daga fuskar da na fi son gani.”
Yanzu kam kasa jurewa tai sai da ta kallesa, shima kallon nata yake, suna haɗa ido ya wani ɗage mata gira ɗaya sama. Ai babu shiri ta ture hannunsa dake riƙe da kafaɗarta ta tashi zaune. Komai bai sake ce mata ba, sai ma laptop ɗinsa daya ɗauka ya cigaba da aikinsa jijiyiyin jikinsa na wani mimmiƙewa. Amma ya danne komai da tsiya-tsiya kamar ba shine ya gama zuba zance ba. Itama tashi tai ta shiga toilet batare data yarda ta sake kallon ko sashen da yake ba. Ta jima a bayin kafin ta fito. Batare data yarda ta kallesan ba ma yanzu ta ɗauka book ɗinta ta zauna ɗan nesa da shi.
Ganin yanda tai kamar bataga abincin ba ya sashi yin ƴar gyaran murya, ƙasa-ƙasa yana kallonta da idon daya san sirrin zuciyarta. Cikin yanayin rashin walwalar da har yanzu ke mamaye da fuskarsa ya furta, “To Madam barci, za ki ci abincinki ne ko har yanzu jikina ya fisa daɗi?”
Baki ta ɗan tura gaba tana kallon shiryayyen abincin, “Wannan abincin ai ya huce tuni fa. Kawai bana ma jin ci”.
Idanunsa da ke lausashe da wani yanayi mai wahalar fassara ya zuba mata, sai kuma ya janye su a slowly ya maida ga screen ɗin laptop ɗin yana kai hannu ya gyara zaman glashinsa. “Na tashe ki kice na miki rowar lallausan jiki bayan na sanki da mita”. Yay maganar cike da basarwa. Koda ta ɗago ido ta kallesa yama fiske abinsa sai ka rantse ba shine ya faɗa maganar ba. Jitai bazata iya barmasa ba itama, cikin nata yanayin basarwar ta ce, “Humm sai cika baki, kana jin kamar jikin naka wani katifa ne”.
Kaɗan ya taɓe baki batare daya bar aikin da yake ba ya ce, “Ai ni sai dai ma nakira kaina 'His Royal Mattress'.”
Rasama abin cewa Maanal tayi, sai kawai ta zaɓi yi masa shiru. Shima bai sake tankawar ba, sai danna abu da yay a hankali table ɗin da aka shirya abincin ya matsa gabanta zuu. Kallonsa tayi, shima dai-dai ya ɗago ya kalleta bayan ya kalla agogon dake ɗaure a hannunsa. “1:7min ya rage mana sauka Doha”.
Kanta kawai ta ɗan jinjina, sai kuma ta ajiye book ɗin ta fara bubbuɗe abincin. Tana cin abincin kaɗan-kaɗan shi yana aikinsa da kallonta lokaci-lokaci batare da yayi magana ba. A haka ta tsakuri abincin ta ajiye dan sam jitai ma bai mata wani daɗi ba ita kam. Ganin lokaci ya gabato shima ya tattare aikin ya ajiye tare da maida komai inda yake. Itama veil ɗinta ta ɗauka ta naɗa bayan ta maida ribbon ɗinta. Dai-dai nan aka sanar da isowarsu ƙasar Qatar. Sun sauka a Hamad international airport dage birnin Doha. Babu wani zaman jira da zasu yi, dan daga jirgin ma wani jirgin suka shiga da in sha ALLAHU shine har ƙasar Chaina. Nan ɗin ma dai vip section ne ita da shi, sai dai na wannan jirgin ma yafi wancan matuƙa, dan harda gadon barci da yaji shimfiɗu na alfarma. Sai Maanal taji duk ta samu kanta da tsarguwa. Amma a zahiri ta wani dake abinta sai gajiya da jikinta ya fara nunawa na zama waje ɗaya.
Sosai Doha ta birge Maanal, duk da bazata iya ƙarar da komai na cikinta ba daga jirgi ma take kallonta, gashi dare ne sai dai tako ina akwai haske fayau kamar ka yarda allura ka ɗauka abarka. A wannan tafiyar an samu canjin yanayi, domin kuwa AA ne yay barci a yanzu, yayinda Maanal tai zaman kallon wani american film da yay mata daɗi sosai, daga ƙarshe itama dai ta sake ɓingirewa barcin a kujerar da take. Tafiya ce ta awanni takwas daga Doha zuwa Shanghai da zasu sauka ta ƙasar Chaina. Dan haka AA ya samu barci isasshe, dan sai asuba ya farka, ganin itama Maanal barcin take sai ya samu kansa da zuba mata ido. Ya jima yana kallonta kafin ya miƙe domin gabatar da alwala. Koda ya fito itama tashinta yayi tayo alwalar, duk da inda son samu ne zataso yin wanka ma, amma a wannan jirgin babu alamar akwai wannan damar, dan haka ta ɗan gyagygyara inda zata iya sannan ta fito. Salla suka gabatar, bayan sun idar kamar yanda ta saba ta ciro Alkur'ani dake a handbag ɗinta ta fara karatu, idanu kawai ya lumshe yana sauraren daddaɗan sautinta dake fidda ƙira'a dalla-dalla. A haka lokaci yayi, aka fara sanar da saukarsu nan da awa ɗaya kacal. Addu'a tayi tare da azkar suka kimtsa komansu duk da ba wani tarkace bane ba iya na hannu ne bag ɗinsu na ƙasa....
★An buɗe ƙofar jirgi da sanyi mai ɗauke da iska mai ɗan zafin canjin yanayi na sabon gari ya bugi fuskarta. Ita tana kallon komai da yanayin sabo, mamakin ganin rana ce yanzu anan Chaina , mutanen da ke tafiya da sauri, harshen da ba ta fahimta ba, da kuma sautin rayuwar da bata saba da shi ba. Shi kuwa gogan naku, ya sauka kamar wanda yazo gida – a yanayi na izza mai nutsuwa, cikin shigar da ba ta da yawa amma tana da nauyin kamanni. Ba ya magana da yawa, amma idanunsa na bin komai cikin salo. A tare su Yaqub suka iso inda suke suna gaishesu cike da girmamawa. Ita dai kanta a ƙasa, dan girmamawar da suke bata kunya take bata musamman su CMO. CFO dai taƙi yarda ta kalla inda suke, dan ba ƙaramin danne zuciyarta take ba akan wannan ƴar tatsitsiyar yarinyar dake neman ɓata mata aiki. Sai dai a zahiri bazaka taɓa fahimtar yanayinta ba dan mace ce wayayya mai kuma wayo da iya taku.
Taji matuƙar daɗi data fahimci a hotel ɗaya zasu zauna su dukansu. Manaal tayi mamakin motar da tazo ɗaukarsu, ƙyaƙyƙyawar gaske baƙa wulik mai aiki da caji ba fetur ba. Kasare tai tana kallon chainawan da suka fito su biyu suna gaishe da AA cike da girmamawa. Shi ko ya amsa musu cikin yanayinsa na riƙe girma, sai kuma ya ɗan kalla Maanal dake gefensa da harshen Chaines da Maanal bata san ya iya ba sai yau ɗin nan ya sanar musu ga matarsa. Sosai farin cikinsu ya sake bayypana, suka juya suna gaishe da Maanal cikin harshen turanci da girmamawa. Ita kam da ƙyar ma ta iya fahimtar turancin nasu, ta amsa musu a taƙaice sai dai da kulawa. Sake maida hankalinsu sukai ga AA, cikin yaren da ba fahimta take ba sukai masa magana. A mamakinta sai taga yay ɗan guntun murmushi kawai. Samun kanta tai da ɗan shagala a kallonsa, yana yin kamar zai juyo ta kauda kanta gefe.
A mamakinta daga ita sai shi ne suka shiga motar, sauran kuwa bata san yanda suka kare ba.....
Sannu a hankali motar ke tafiya bisa lafiyayyen titin mai faɗin gaske da yalwa ta yanda motoci keta kai kawonsu cike da watayawa. Motar tayi shiru. Hankalin AA naga tab ɗin da ɗaya a ƴan cainar suka bashi, Maanal kam ta maida nata hankalin ga waje tana kallon gine-gine masu ban mamaki da ƙawa. Eh lallai ga inda gini ke amsa sunan gini, duk da kuwa Abuja ba daga baya ba a ƙyaun gine-gine da tsarin anguwanni sai taga can ya koma mata local. Duk yanda taso danne shauƙinta hakan ya gaggara, a bazata batare da tasan da matsowar AA gab da ita ba da murya mai laushi, amma cike da basarwa ta tsinkaye sa a cikin kunenta yana faɗin, “Kar kiyi kamar zaki ɓata mana. Ina nan a kusa dake, ki tuna.”
A hankali ta ɗan murmusa a ƙasan maƙoshi. Sai kuma ta ɗan juyo ta kallesa cikin ido tana mai ɗan ɗage gira sama ta ce, “Lah nazata ai a Nigeria na baroka ma ni, kasan abinka da baƙauye yazo birni.”
Yatsa ya kai zai ɗalli hancinta, tai saurin juya fuskarta gefe ta hanashi damar hakan. Lips ya ɗan cije, sai kuma ya koma ya zauna da ƙyau cike da basarwa.
Sai da suka iso hotel ɗin taga su Yaqub, sai dai basu tsaya a inda suke ba su sukai ciki bisa jagorancin yan chaina ɗin nan. A jere ita da shi suke tafiya a dogon corridor ɗin dake shiru babu hayaniyar komai, sai dai komai a tsaftace yake ƙal kamar kaci abinci a ƙasa. Card ɗaya ya miƙa masa yana nuna masa ƙofar ɗakin da suka tsaya cikin yaren su. Shi kuma ya gyaɗa kai kawai yana amsa batare da yace komai ba. Hannu suka ɗaga mata alamar bye suka wuce. Ita kuma tai ɗan murmushi da jinjina kanta kawai a taƙaice.
Matsawa AA yay jikin ƙofar ya saka card ɗin. Ita kuma ta ɗan tsaya sororo.........✍️
_To mun ido Chaina kuma, bari nima na shiga nawa ɗakin na watsa ruwa sai mu ɗora labari 🏃🏃, karku damu ɗakina kusa dana su Maanal ne komai zan jiyo muku 😂._
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣0️⃣
______________
.......Cikin mamaki da ɗan daburcewa ta ce, “Wai ɗaki ɗaya?” ta tambaya fuskarta cike da rauni.
Juyowa yay yana kallonta kai tsaye, sai kuma ya basar cikin zurfin furuci ya ce, “Basai kin damu ba, sunansa ɗakin barci kawai, ba ɗakin yin wani abu ba.”
Baki ta tura gaba tana ɗan kau da idanunta, shima sai ya tura ƙofar kawai ya shiga, ɗan juyowa yayi, ganin tana tsaye cikin yanayin ƙaulani har yanzu, “Ko ɗauka kike so?”
“Ni ban ce ba”.
Ta bashi amsa idonta a ƙasa, sai kuma ta motsa a hankali zuwa gaban ƙofar, jatai ta sake tsayawa, batare data kallesa ba ta ce, “Amma ba gado ɗaya ba?”.
Yanzu kam kansa ya ɗan girgiza yana kallonta da ƙyau, sai kuma ya ɗauke idanun ya ɗan kalli gefe. Da alamun ƙosawa ya ce, “You can sleep on your pride if the bed makes you nervous”. Daga haka ya matsa mata alamar ta shiga. Haka kawai ta samu kanta da sanyi jiki. Cikin ɗari-ɗari ta shiga, numfashinta na sizen, zuciyarta kam rawa take a hankali kamar wadda ke jira ace mata ar ta feta a guje. Tana jin ya maida ƙofar ya rufe ta wani lumshe idanunta. Sai kuma ta samu kanta da matsawa jikin window ko zata samu iska ta bugeta abinda ya tokare mata nunfashi ya narke. Shiru tai tana kallon hasken rana daya fara buɗewa dan yanzu ana nufar kusan ɗaya na rana ne a ƙasar.
Cike da takunsa na ƙasaita da izza ya ƙaraso inda take, tsaye yay kawai a bayan ta yana cire agogon hannunsa kamar wanda ba ya cikin gaggawa. Shima dai idanunsa na kallon garin ne zuciyarsa cike da wadatuwa da iskar dake buso su. Shiru ne ya mamaye ɗakin, ba motsi, ba rikici, sai shauƙi da tambayoyi dake cike taf a zuciyar Maanal marasa ma'ana da shiga ƙaulanin furta wa a bayyane.
Tamkar mai raɗa muryarsa a ƙurya cikin kalamin dake fita ɗai-ɗai ya furta, “Hum! K! A komai sai kin yi kamar za ki gudu ne?”.
Baki ta ɗan taɓe batare data juyo ba ta ce, “Kai kuma kullum sai ka dinga yi kamar kana son a biyo ka ba”.
Yanzu kam murmusawa yay, sai kuma ya laɓe baki kaɗan, da murya ƙasa sosai ya ce, “Ba kullum ba ne. Amma a wannan gaɓar ya kasance tare da ke watakila.”
Da sauri ta juyo tana kallonsa. Sai kuma kamar a tsorace ta ce, “Wai me kake nufi?”.
Gira ya ɗage sama yana wani ƙanƙance ido ya bata amsa da, “Duk abinda zuciyarki ta baki. Dan anan babu Aban naki dai kin sani. Garama ki lallaɓa a rabu lafiya in ba haka ba kuma jiki magayi”. Yana gama faɗa ya wuce yana wani shegen makirin murmushi irin mai saka kaɗuwar hanjin wanda ya tsargun nan......
__________★
Cikin ƴan kwanaki kaɗan Hajiya Basariyya tai wata irin rama da baƙi, ba komai ya jawo mata hakan ba sai zafin rana da uban aikin da take lafta a gidan kawu Manu. Dan takai yanzu har gona idan zaije tasa ƙeyarta yake su tafi tana taya shi da ƙananun ayyuka. Taƙi sakin jiki taci abincin gidan, ga biscuits ɗin nata sun ƙare. Sarai iya na lure da ita, amma tai kamar bata ganin ba dan itama ba shiga dabgarta take ba, ai yunwa ba ƙanwar uban wani nace ba, magana ma sai ta zama dole yake haɗa su. Tun Hajiya Basariyya na dauriya da tunanin ai kawun zai barta koda a sati guda ne harta fara gazawa. Hankalinta a tashe yake sosai da ganin ana niyyar ma ɗaukar azumi a jibi idan ALLAH ya kaimu. Ita ko tasan idan aka ce a gidan nan zatai azumi ai tagama mutuwa....
Da daddare ta yanke shawarar samun Kawu Manu ta bashi