Showing 174001 words to 177000 words out of 218311 words
Chapter 59 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
“Karaya da ƙonewa kuma?”. Sai suka juya suna kallon su Maman Saheeba alamar tambaya. AA kam yama gagara cewa komai. Cikin ƙarfin hali Oum ta ce, “Aunty amma bakuce mana da ƙuma ba ai, batun karaya nasan maybe wancan likitan ne bai san aikinsa ba”.
Cikin ƙarfin hali Aunty ta ce, “Wlhy bamu san da ƙunar ba muma Oum Fawzan (da haka take kiran Oum kafin Mamy ta nuna bata so). Amma tabbas tea ya zuba mata a jiki babu kuma wanda yay tunanin zai ƙonata, ita kuma batayi magana ba”.
RK ne ya ce, “Ai shi ruwan zafi ba'a rainashi gaskiya. Yanzu dai an kira wanda zai yi ɗorin karayar kun san mu anan asibitin muna aiki da ɗorin karayar gargajiya ne saboda mai yi mana aiki na wannan fanin yasan aikinsa. Zamu jirashi dan yana a suleja ne. Amma gaskiya likitan can da kuka kira ya dubata bai san komai ba, kuma da ƙafar nan takai wasu kwanaki a haka komai zai iya faruwa. Dan haka ina baku shawara ku kiyaye, kusan da waɗanne irin likitoci zakuyi mu'amula musaman wanda kuke iya kira gida su muku aiki.”
Daga haka ya juya ya fita ransa a ɓace. Ita kanta Oum ranta ya ɓaci, dan tun ɗazu dama yanda sukai ɓoye-ɓoyen halin da Mamyn ke a ciki yanata mata kai-kawo a zuciya. A ganinta mizaisa suyi hakan? In dama ƙaramin ciwo ne sai ace. Shi kansa Abah ta fahimci ransa a ɓace yake. Ture tunanin tayi daga ranta gaba ɗaya ta ƙyautata musu zato kawai da yardar ma zuciyarta abinda suka faɗa a ɗazun. (Wannan shine babbar halayyar Oum dake saka mata kwanciyar hankali akan zamanta da kowa, take kuma iya hakuri da dukkan jarabawarta. Tana da ƙoƙarin ƙyautatama mutum zato. Ko abu akai mata a gabanta mara ƙyau kai tsaye bazata saka jin zafin mutum a ranta ba, sai taita kawo uzirin maybe kaza ne, ko kaza yasa yay haka. Sai kaga zuciyarta ta samu salama da kwanciyar hankali. Mu gwada kasancewa haka zamu sha mamaki wlhy koda akan mazajen aurenmu ne ma🙏😀).
Waya ta ciro ta kira Abah ta sanar masa komai. Yace mata suna masallaci idan sun idar da salla zasu zo. Daga haka ya yanke kiran. Mamaki ya kamata jin babu wata damuwa a cikin muryarsa. Amma sai ta ture tunanin kawai. Ta kalla su Fawzan tace suje suyi salla suma....
Sai bayan sallar isha'i mai ɗori yazo, lokacin suma su Abah na asibitin harma da Babban Yaya. Su Hajiya Majdiya da su Umma ma sun iso asibitin jin shiru su Oum basu dawo ba.
Ƙafar Mamy tayi tsami sosai, ta yanda ana taɓa ƙafar sai da ta saki wani ihun da har reseption sai da aka ji. Ashe ma karaya har biyu ce ba ɗaya ba. Dole sai da su AA suka shiga aka riƙeta, a haka ma RK yaji tausayinta an mata wata allurar kashe zafi. Sumarta biyu dan azaba. Su kansu su AA ƴan riƙeta sunyi sharkaf da zufa duk da acn dake a ɗakin. Shima hannun an gyara mata, shi kam targaɗe ne. Matuƙar tausayi dole ta baka. Allurar barci aika mata bayan sun farfaɗo da ita.
Ganin ba wani abu ake buƙata ba RK yace zasu iya tafiya gida tunda anyi gyaran. Dan allurar da sukai mata ta awa goma sha biyar ce, ita da farkawa sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Auntyn su Mamy kawai aka baro a asibitin, sanda suka iso gida sha biyu saura. Kowa sashensa ya nufa, Saheeba tabi Babban Yaya, wani kallo daya watsa mata bama tasan ta tsaya cak ba. Dama mamarta ce tace ta bishin. Aiko bataga fuska ba dole ta wuce sashen Mamyn duk da hararar da maman tata ke mata.....
_______★
Tun bayan fitar Hajiya Shuwa hankalin Maanal a tashe yake, ta kira wayar Oum ba'a ɗaga ba. Ta kira ta AA shima haka. Ta kira Yaya Fawzan shima bai ɗaga ba sai taji matuƙar damuwa da tunanin ko dai wani abu ne ya samu Mamyn. Dan yanda Hajiya Shuwa da su Didinta suka bata labarin halin da Mamyn ke ciki abin ya tsaya mata a rai. Tun tana kallon agogo da cigaba da kiran AA harta sare, a haka ta lallaɓa ta fito falo, ta window ta leƙa compound babu kowa sai hasken fitulu, motocin gidan ma duk an fita da su sai huɗu kawai dake a lulluɓe, sai maigadi na gyangyaɗi gidan shiru sosai. Har zata saki labulen idonta ya sauka akan Nibras dake tsaye a barandar sashensu ta upstairs. Idanu ta zuba mata sai taga gaba ɗaya hankalinta na'a sashensu ne. Tsaki Maanal taja da faɗin, “Wawuya”. Ta bar wajen. Sai kawai ta sakko ma falon ƙasa cike da dauriya, a hakan ma da sauƙi dan tana jin daɗin gashin nan na Hajiya Shuwa. Anan ta kwanta cikin kujera, tun tana kallon agogo har barci ya saceta...
Tunda AA ya shigo idanunsa suka sauka a kanta. Zuba mata su yay shiru yana kallonta na tsawon lokaci. Sai kuma ta bashi tausayi. Ƙarasowa yay inda take. A nutse ya saka hannu ya ɗauketa gaba ɗayanta. Sama ya haura da ita yana tafiya a hankali dan kar ta tashi. Har ko ya kwantar da ita a gadon ɗakinsa bata farka ɗin ba, duvet yaja ya lulluɓa mata tare da duƙowa ya sumbaci lips ɗinta da goshinta sannan ya wuce closet ɗinsa yana cire kaya. Sosai yake jin damuwa akan halin da Mamy ke ciki, haka ya samu yay wanka yayo alwala. Shafa'i da wutri yay ƙoƙarin yi, yana idarwa kiran Oum ke shigo masa. Ɗagawa yay, Oum tace ga abinci nan zata saka a kawo musu hankalin kowa a tashe an manta ko Maanal ba'a kawoma abinci ba........✍️
AJIYAH A DUHU 2
86...
........Maanal ɗin ya kalla, sai kuma cikin taushin muryarsa dake fita ƙasa-ƙasan nan ya ce, “Oum tama yi barci ita, kawai a barshi nima na ƙoshi zan sha shayi dare ya riga yayi”.
“Auta kasan bana son zama da yunwa ko, itama zata iya farkawa anjima ta nema abincin”.
“Oum ALLAH bana jin yunwa, itama kuma inta farka sai ta sha tea ɗin kiyi haƙuri”.
“Shike nan ALLAH ya tashemu lafiya”.
Sallamar yay mata shima ya ajiye wayar yana miƙewa. Shima baibi takan tea ɗin ba ya nema wajen kwanciya dan barci ne a idonsa sosai. Sai dai me yana kwanciyar ya saka Maanal a jikinsa sai yaji kuma yanayinsa na sauyawa. Sosai yake jin buƙatarta, amma ya danne da tsiya-tsiya kodan bayanin da RK ya masa akan dole ya kauda idonsa akanta harta warke. Sannan shi a kanran kansa tausayi take bashi sosai. Dan yasan jiyan nan bai mata da wasa ba sam. Da ƙyar ya samu yay barci, gabannin asuba kuma ya sake farkawa a yanayin matsuwa sosai, sai kawai ya shiga bayi ya shashsheƙa ma kansa ruwa yayo alwala yazo ya hau nafilfili da karatun Alkur'ani. Hakanne ya bashi ƴar nutsuwa har lokacin salla yayi. Sai da ya tada Maanal ya taimaka mata tayo alwala sannan ya fita salla.....
_________★
1 WEEK LATER
Alhamdullahi satin AA guda ke nan cur da angwancewa. Ba ƙaramin dauriya yay da juriya ba na kauda kai akan Maanal ba. Idan ka cire ɗan sumbatarta iya lips hatta kissing ɗinta dainawa yay, dan tunda yay hakan a washe gari bayan ya dawo sallar asuba ya ƙare da ciwon ciki bai sake kwantatawa ba. Sauƙinsa ma ciwon Mamy da zaryar zuwa dubata asibiti tana cimasa lokaci. Idan kuma ya dawo gida sai ya hau aikin office. Hakan bai damu Maanal ba dan itama harga ALLAH tana son ko zai nema wani abu kuma daga gareta to ya kasance ta warke tas kamar yanda kullum Hajiya Shuwa ke gargaɗinta, dan ta kula shauƙin soyayya na ɗawainiya da yaran. To Alhamdullah gashin da take mata ya taka rawar gani sosai ga kuma jikinta baya riƙe ciwo a cikin kwana huɗu ma zaren ɗinkin ya gama fita tas a jikinta. Sannan bata jin zafin komai sai ma wata nutsuwa ta musamman. Zuwa yau da take cika sati kam ras take jinta, kamar yanda doctor da tazo ta duba ta ma ta tabbatar ta warke sarai, dama tun shekaran jiya Hajiya Shuwa tace ta ga warke ɗin. Amma tai gum da bakinta.
Zuwa yanzu kam dai su kaɗai ne a gidan nasu. Sai Auntyn su Mamy dake jiyyarta ita da Maman Saheeba dan an sallamota yau kwana biyu kenan zata ƙarasa jiyya a gida, badan ma jininta da yaƙi sauka ba su RK nata fama da kwana uku zatai su sallameta a asibitin, anyi-anyi ta faɗi mike damunta taƙi. Da ƙyar dai da lallashin da AA ke mata da kulawa aka samu jinin nata ya dai-dai shine aka sallamosu. Fuskarta ta saɓe raunikan sun warke, hakama hannunta har an kwance ƙafarce kawai dai da ɗaurin karaya, itama nan da kwana biyu ake saka ran kwancewa saboda bata da ƙan jiki. Maganar hotunan nan kuwa da sun zo mata a rai sai ta turesu da tsiya-tsiya. Kai da ka ganta kasan abin duniya ya isheta. Amma sai kowa ke ɗauka ciwon ne, itako ita tasan tashin hankalinta.
Har ƴan hutun Oum duk sun wuce ba kowa. AA daya fahimci zamansa a gida akwai matsala jiya ya koma aiki. Dan haka yau ma yana fita Maanal ta shirya ta wuce sashen Oum. Jiya ma acan ta yini har sai da ya dawo. Sashen Mamy ta fara zuwa. A falon ƙasa duk ta samesu har Saheeba dan tana sashen Mamyn har yanzu Baban Yaya ya murje idanunsa. Abah kuma yaƙi saka musu baki ya kuma hana Oum yin magana. Har Nuratu tana gidan itama, taji sauƙi sosai sai uban ramar da tayi da duhu. A down stairs ɗin Mamy ke jiyyar, dan tunda suka dawo asibiti aka gyara mata cikin ɗakunan ƙasa taƙi yarda ta hau sama saboda tsoron sake kallon hotunan nan.
Tun kafin Maanal ɗin ta shigo ƙamshinta ya iso musu. Duk sai suka zubama ƙofar ido kuwa. Sai ko gata ta bayyana garesu cikin gayunta kamar ka saceta ka gudu. Ga wani irin ƙyau dama da amarcin ya sata ta wani ƙara fresh abinta. Ga uban gyaran jikin Hajiya Shuwa na nan raɗam tamkar yau akai mata sabo. Nuratu ce ta fara kauda idonta tana jan siririn tsaki zuciyarta na raɗaɗi. Sai itama Mamy ta ɗauke nata. Saheeba da Mamansu ma suka taɓe baki suna ɗauke kai. Aunty ce kawai tai murmushi da faɗin, “Ɗiyata kece?”.
Murmushi mai ƙayatarwa Maanal ta sakar mata. Cike da girmamawa ta ce, “Eh Mama sannunku”. Sai kuma takai zaune a kujerar dake kusa da ita ta ce, “Mama ina kwana! Ya mai jiki?”. Cike da kulawa Aunty ta amsa mata, dan tama kanta alƙawarin canjawa ita kam, shiyyasa ko jiya da Maanal ɗin ta shigo cike da kulawa ta tarbi yarinyar, hakama idan sukaje asibiti duba Mamyn ita da AA dan ya kaita a da daddare a washe garin da aka kwantar da su, daga nan kullum da dare suke zuwa. Maanal ta juya tana gaida Mamy da tambayarta jiki. Ciki-ciki ta amsa mata. Ko'a jikinta ta juya ta gaida Maman Saheeba. Ƙin amsa mata tai ita kam, nan ma Maanal bata nuna damuwa ba. Ba kuma ta kalli ko inda Nuratu da Saheeba suke ba balle ta gaida Saheeba ɗin. Hakan sai yay ma Saheeba zafi. Itama Mamansu haka, ta kalla Maanal ɗin cike da ɓacin rai zatai magana kira ya shigo wayar Maanal. AA ne, dan haka ta ɗan lumshe ido ta buɗe bata ɗaga ba harta tsinke, kiran ya ƙara shigowa a karo na biyu. Yanzu kam tasan dole ta ɗaga dan maybe wani abun ya manta. Aunty dake murmushi ta ce, “Ɗaga wayar mana Daughter”.
Murmushi Maanal tayi tare da ɗagawar takai kunneta.. “ZUCIYAR Ajwaad ina kika shiga haka?”.
Abinda AA ya fara faɗa kenan tana kai wayar kunne. Gashi bata san sound ɗin yayi hight ba. Aiko a kunnen kowa wannan furuci nashi, ragewa tai, kafin ƙasa-ƙasa ta ce, “Ina sashen Mamy idan na fita zan kira ka”.
Ɗan jimm AA yay daga can, sai kuma ya ce, “Okay 2-minutes kawai na baki fa.”
Murmushi tayi kawai ta yanke kiran. Ɗagowar da zatai taga kowa ya cika yay fam banda Aunty dake murmushinta. Sai kawai ta kalla Auntyn da murmushi ta ce, “Aunty bara naje, Mamy ALLAH ya ƙara lafiya”.
Aunty ta amsa mata da amin tana sanya mata albarka, Mamy kuwa bata tanka ba. Maanal ɗin na fita Saheeba da Nuratu har haɗa baki suke wajen zaginta. Da mamaki Aunty ta ce, “Datai muku mi zaku zageta? Kunga ku kama kanku, da wannan halin ke kike so ki shigo gidan nan? Ke kuma dake ciki idan baki sani ba raini kike siyama kanki a wajen yarinyar nan, kina matsayin matar yayan mijinta amma baki san yanda zaki riƙe girmanki ba. Ke ko Kamila ina ƙara nuna miki ki rufama kanki asiri ki daina nunama yarinyar nan ƙiyayya ƙuru-ƙuru. Kina dai ganin abinda kikai mata a asibiti ranar sai da Ajwaad yay magana, kawai ya shanye ɓacin ransa ne saboda girma irin na uwa. Sannan ke kanki raini kike jama kanki a wajenta wlhy. Ni banga aibunta ba, yarinya mai natsuwa da hankali. Ai wlhy yaron nan Ajwaad ya more da mata dai-dai da halayensa. Hakama baiwar ALLAHn nan Fateema idan ta shigo kita ɗaure fuska da ɗauke kai, ko ki hau barcin ƙarya, a tunaninki bata san ciwon kanta bane ko bata lura da komai ƙyaleki kawai take yi, ki cigaba, kina dai ganin mijin naku banda ran farko da aka kaiki asibitin yaje kin sake ganin shi inda kike? Ko sannu bata haɗa ku ba har yanzu, yana gidan ma baya nan baki sani ba. Maimakon ki gyara zuciyarki kodan abinda ya faru ɗin nan ƙoƙarin buɗema kanki aiki kike kowama ya fahimci mike ranki, to ALLAH ya baki sa'a kin san dai familyn Darma ba Ƙanwar lasa bane. Ga matar Fawzan nan sanadinki ta shigo gidan amma saboda wannan saɓanin ko sau ɗaya bata zo ta dubaki ba har muka gama zamanmu na asibiti muka dawo gidan nan. Ita ko fa, tana fama da kanta amma kullum sai sunje sun dubaki hakama jiya zuwanta uku sashen nan, harda yo miki abinci. Ga Saheeba nan tare damu take kwana tana tashi ko ruwan shayi ta taɓa dafawa dan ki sha......”
“Haba Aunty wannan kuma maganar miya kawota, nifa na fahimci kamar akwai abinda kikeji a kaina da ƴaƴana a zaman nan. Haka fa ranar kika zage Nuratu a asibiti shiru kawai nai na ƙyale dan a zauna lafiya. Yanzu kuma kina nuna wata banza can bare kamar ta fisu...”
Kallon Maman Saheeba mai maganar kawai Aunty keyi, sai kuma ta girgiza kai tai murmushi da faɗin, “ALLAH ya ƙyauta. Nana yanzu ƴaƴanki ba nawa bane, dan na tsawata musu su gane abinda ya dace shine kuskure? To ALLAH ya baki haƙuri maida wuƙar an bari in sha ALLAHU”. Daga haka Aunty ta miƙe tama bar musu falon.
Babu wanda bai rakata da harara ba cikinsu, Nuratu kam harda ƙunƙunin zagi. Mamy dai batace komai ba, dan ita kam duk sun isheta sotake ma su tafi ta samu filin baje matsalarta da neman hanyar maganceta amma taga basu da niyyar hakan............✍️
Nima fa na ƙagara hankalinki ya dawo kan hotunan nan Mamy😌, kun san mu duk inda gulma take nan muke amma a Nobel😮💨😜koya kuka ce🥱
AJIYAH A DUHU 2
87....
........Maanal kam na fita sashen Oum ta wuce. Kamar ko yaushe ko'ina na zuba ƙamshi ne. Babu kowa a ƙasa sai su Inte dake kitchen suna gyara, da alama yau sun makara aiki. Suna jin motsinta kuwa suka leƙo suna gaisheta. Amsawa tai da kulawa, cike da tsokanarsu tace, “Wane shagali ake haɗamana a kitchen ɗin?”.
Dariya sukayi, duk da zasuyi sa'anni da ita Aunty suke kiranta saboda girmamawa. Inte tace, “Aunty wainar fulawa zamuyi kin san Joy tunda ta iya ci kowa ya bani”.
Maanal na murmushi ta ce, “Ato ayi dani nima. Bara na duba Oum na dawo”.
Da girmamawa sukace mata to, suna son Maanal dan sam bata da damuwa, ba girman kai, ba wulaƙanci, huɗɗa take da su tamkar ƙawaye. Bata samu Oum a falo ba sai ta leƙa bedroom. Wanka take dan haka ta dawo falo ta zauna, sai ga kiran AA ya sake shigo mata. Ɗagawa tai tana murmushi da kaiwa kwance a cikin kujerar ta ce, “Na tuba”.
Daga can ya ce, “Oh kina ma sane kenan?”.
“Ni na isa. Na bari na zauna ne kasan ita wayar Sarki babu girma a ɗagata ana tafiya ko ana tsaye”.
Murmushi yayi har tana jin sautinsa. Sai kuma cikin sake tausasa murya ya ce, “Yanzu kina ina?”.
“Falon Oum”.
“Ƴar gata mai aure kusa da Mamanta”.
Murmushi tayi mai ƙayatarwa, sai kuma tace, “Yanzu ya akai ta samu ne?”.
“Zadai ta samu anjima. Yanzu kam kewar ZUCIYATA nake yi shiyyasa nace bari na ji sautinta. Gaskiya