Showing 183001 words to 186000 words out of 218311 words
Chapter 62 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
har YouTube ma takan je. A WhatsApp ɗin ma yawancin groups ne na makaranta, sai sakwanin taya murnar aure da suka tura mata pc, da masu ƙorafin rashin gayyatarsu da batai ba, sai na addini haka da class na abubuwa data ɗan shiga ta koya, mafi yawama girke-girke ne sai harkar zane dan tana son girki, bayan zane-zane.
“Yanzu lokacin miji ne”.
AA dake hawowa gadon ya faɗa yana zare wayar daga hannunta. Kallonsa tayi a marairaice ta ce, “Hiran group fa kawai nake gani sai sakwannin taya murna”.
“Karki damu zan miki hirar ni, na kuma tayaki murnar auren”.
Baki ta ɗan tura kaɗan, zatai magana ya hanata. Hasken ɗakin ya kashe gaba ɗaya ya bar musu ta barci datai dummm sosai. Sai kuma ya sake matsota sosai a jikinsa ya rungume. Ajiyar zuciya suka sauke a tare, a cikin kunenta yay mata raɗar data sakata kife fuskarta a ƙirjinsa tana ƴar dariya. Ta ce, “Nidai ba ruwana kai da Abah”.
“Shima ya haƙura ya sallama. Alamar jikoki yake so da wuri”.
Ƙaramin dundu ta masa a baya. Tare da kai bakinta kan kunensa ta raɗa masa, “ALLAH ka canja hali”.
Shima sai ya raɗa mata. “Mudai canja, dan da an ganki da cikin ansan tare mukayi”.
Tureshi ta shiga yi tana tirza ƙafa. Wata ƴar ƙanƙanuwar dariya mai tada tsigar jiki ya shiga yi mata yana sake matseta a jikinsa. Yayinda shima kukan shagwaɓar nata ke yamutsa masa garkuwar jikin nasa. Sai kawai ya shiga laluben lips ɗin nata, cike da nutsuwa da tarin ƙauna da shauƙi ya rufesa ruf da nashi. Tun tana ƙoƙarin son ƙwacewa harta nutsu ta sallama tana sake ƙanƙamesa. Ita in dai iya haka ne normal ne zata bada haɗin kai. A zarce nan ɗin ne hankalinta ke tashi. Sai ko daya bari ya shagaltar da ita da salonsa ta miƙa wuya gaba ɗaya sannan ya ɗauki layin da take tsoron. Ai ko a take ta firgice masa. Tana ƙoƙarin masa magiya ya rufe kowacce ƙofar yin hakan. Ta riga ta tsorata da al'amarin tun farko, dan haka yake tayar mata da hankali. A haka yau ma ya bita a sannu saboda ba kamar waccan ranar da shima yake a wani yanayi ba. Amma duk da yanda ya lallaɓata, ya riritata sai da tasha azaba, ta kuma dinga masa kuka hawaye share-share. Addu'a ta dinga yi a ranta ALLAH yasa ma ta suma kamar ranar, amma addu'ar nan bata karɓu ba kuwa, dan sai da ya samu yanda yake so ya barta.
Ganin yanda ta galabaita ya sashi jin tausayinta sosai, dan shi da kansa yasan bana wasan yara bane tako wane fanni. Ita kuma dama can yasan tana da tsoro, duk tsiwar Maanal da iya takalar faɗa akwai tsoro, bata ƙaunar abinda zai taɓa jikin nan nata sam-sam. A wajen sit bath ma yasha shagwaɓa da kuka, shi har ma yayi tunanin koya sake ji mata ciwo ne. Bai samu natsuwa ba sai da ya dubata yaga lafiya lau sannan ya sauke ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana tunanin lallai akwai daru kenan in dai haka za'a cigaba da kasancewa. Dan Maanal akwai shegen raki. Dama duk mutum mai baki ai sai a hankali ne, zaka samesu akwai ɗan karen rakin tsiya da tsoro. Sai da ya bata magani tasha sannan ta fara sauke ajiyar zuciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya rungumeta yay musu addu'a sai barci.
Gabanin asuba kuwa ya farka cikin wani matsanancin yanayi, jinta a jikinsa kam ya sake tunzura. Cikin barci ta farka a firgice. Kuka ta sanya masa. Bai kuwa ƙyaletan ba dan ya fahimci sai ya mata da gaske zasu dai-daita, saboda ya daɗe da fahimtar yanayinsa. Kuma bashi da sha'awar ajiye mace fiye da ɗaya, kenan dole ya cire tausayi ya horar da ita a irin layin da zata iya ɗaukar lalurar tasa tako wane irin yanayi. Aiko rikicin datai masa yanzu sai da yafi na daren sosai. Sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so nan ma sannan ya koma lallashinta. Yanzun ma shine ya gyara mata jiki, ya ɗakkota ya ajiye har kan abin salla dan langyare masa tai bazata iya ba. Shi ko yace yaji ya gani duk zai iya. Yana fita salla ta sama ƙofar key, salla tayi a gurguje tai azkar ta miƙe bama ta ƙarasaba ta haye gado ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, anan ta ƙarasa azkar ɗin. Koda ya dawo ya ji ƙofar a rufe dariya ta bashi, amma koba komai ta tsira, dan da ace bata rufe ɗin ba babu abinda zai hanashi sake ziyartarta a safiyar nan. Fuskarsa da murmushi ya koma ɗayan ɗakin dake matsayin nata ya kwanta. Duk da dai yanzu sun raba kayansu biyu kowanne ɗaki akwai na kowa, dan yace babu batun raba ɗaki bai yarda ba. Sai dai duk inda suka so kawai suyi zamansu.
Itama tafi gamsuwa da hakan, dan ko shi ya zaɓi su raba ɗin bazata yarda ba....
_________★
GIRO
A guje Sule ya shigo gida. Gwaggo na ƙofar ɗakinta zaune tana gyara ganyen kuka ya tsallaketa ya shige ɗakinta. Tana ƙoƙarin yin magana kawai ƴan sanda suka afko musu. Sosai gidan ya kacame matan dake a tsakar gida suna harkokinsu duk sun tarwatse sun afka ɗakuna sun banko ƙofa. Jikin Gwaggo ya fara rawa, ko ada sanda Babu ke zuwa da kaki ma tsoro take ji ta dinga masa masifa kenan har sai ya ciresu balle yanzu da tsufa ya sake razanata. Cikin tsawa ɗan sanda yace mata ina Sule. Fitsari na zuba mata zuuuu a zane ta nuna ƙofar ɗakinta. Ga hawaye share-share ta shiga rantsuwa da faɗin ita wlhy koma mi Sule yay babu hannunta a ciki. Su nemi uwarsa bata da alaƙa da Sulen. Ko takanta basu biba suka afka ɗakin, babu wani jimawa suka fito da Sulen, handcuffs suka sanya masa. Aiko ya tsaya yayma Gwaggo wani shegen kallo, cike da taurin kai da rashin ji ya ce, “Ke kuma zamu haɗe ne, ki jirayi dawowata na kwanaki ne. Kin san ALLAH garama kikai kanki maƙabarta kafin na fito. Ba dai ni kika tonama asiri ba, kika ce kuma baki da alaƙa da ni ko? Hummmm!!”. Ya cije baki. Tisa ƙeyarsa sudai ƴan sandan sukayi. Aiko matan gida sai leƙe ta windows, ga mazan duk basa nan suna daji ana gyaran gonaki saboda ruwa dake ta haramar sauka. Haka aka tisa ƙeyar Sule aka wuce da shi. Sai da suka tabbatar sun bar kusa da gidana gaba ɗaya sannan aka shiga fitowa kowa baki cike da gulma. Akan daɗe ba'a kama Sule ba saboda yana da shegen wayo, dan ko kame ƴan sanda suka shigo ƙauyen yasan yanda zai gudu. Yau ma dai da alama mamayarsa sukayi gaskiya. Dan in ba haka ba kama Sule ga ƴan sanda ai jidali ne babba. Amma koba komai ai suma sa ɗan huta. Ga Sailu bata gidan tana can yawan biɗiɗinta na tsiya. Hakama Haƙila tun safe ta fita da cin-cin da fara har yanzu ba'a dawo ba, dama tace Suru zataje.
Rashin jin motsin Gwaggo yasa aka leƙata, sai gata zube a ƙasa firgici ya sakata sumar wucin gadi. Ruwa aka shafa mata ya farfaɗo, sai kuka wiwiwi tana jama Sule ALLAH ya isa. Kowa dai yasan dan taga baya nan ne ta samu baki. Su dai suka kamata suka shiga da ita ɗaki suka koma cikin gida gutsiri tsoma.
A gigice Sailu ta dawo gidan, dan kuwa tun a hanya aka tareta aka sanar mata ƴan sanda sun kama Sule kuma Gwaggo ce ta tona. Tab ɗin, ai tana shigowa gidan Gwaggo ta taƙarƙara ta fito yin alwalar azhar kawai Sailu ta wanke fuskar tsohuwar nan da mari sai da Gwaggo ta zube ƙasa. Jikin Gwaggo na rawa kar-kar ga hawaye ta kalla Sailu ta ce, “Ni kika mara Sailu? Ni dana haifa miki Habibu kika daka?”.
“An dake kin munafukan tsohuwa annamimiya, idan kika ƙara magana ma sai na sake wanka miki wanda haƙwaranki zasu zuba a ƙasa. Kuma wlhy ki sani in har wani abu ya sanar min yaro kema ki jira sakamako”.
Tana gama faɗa ta fice a gidan. Shiru Gwaggo tai a zaune tama kasa kuka. Babu abinda ke dawo mata a rai sai fuskar Ammie. Ta tuno randa ta hana Babu zuwa inda Asiya take, sai cikin dare ya lallaɓo ya shiga, kawai gabannin asuba ta fito fitsari suka haɗe da Babu ɗin da Ammie sun fito daga bayi alamar wanka sukai tare. A fusace ta wani ɗauke fuskar Ammie da mari, ta sake ɗauketa da na biyu. Amma baiwar ALLAHr nan ƙasa kawai tai da kanta har ta wuce su ta shige bayin. Sai da ta shiga sannan Ammie ta wuce ɗakinta yana sharar hawaye, Babu kuwa tsoron Gwaggon bai barshi ya koma ba haka ya fice... Sharrr hawaye suka sake gangaroma Gwaggo, tabbas ta cuci kanta, ta tsige Asiya jinin Lubabatu da Umar daga jikinta, ta aurowa Habibu wadda ranta ke so, ga shi nan itama tana mata yanda take so ita da ɗan nata. Jikokin kuma da take ƙauna take ganin sunfi ƴaƴan Asiya suma suna tisa karatun uwarsu a a garesu........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣1️⃣
______________
........Duk yanda AA yaso Maanal ta fita aiki yau dole ya haƙura. Dan da gaske fa ya jigatata. Haka dole bayan ya tashi ya haɗa mata break fast mai sauƙi da kansa, da ƙyar ya lallasheta tazo ta buɗe masa ƙofar data rufe. Duk da yana ganin zai makara haka ya haƙura ya taimaka mata ya gasa mata jikinta taci abincin ya bata magani sannan yay nasa shirin ya fita. Aiko ko Oum ta waya yay mata sallama. Hakama Mamy ta waya ya kirata yace tai haƙuri ya makara ya wuce.
ALLAH sarki Oum ita sai ta fahimta tai murmushi kawai da binsu da addu'a. Mamy kuwa sai ta shaƙa. Amma batai magana ba saboda Aunty dake wajen. Dan yanzu sun haɗema Auntyn kai ita da Maman Saheeba da Saheebar basa zancen komai a gabanta. Shiyyasa ma tace zata wuce yau dan tana son ta tsira da mutuncinta....
Koda AA ya isa company yau a makare staff ɗinsa sun sha gulma. Dama kwanakin nan haka suketa gulmarsa wai ya ƙara ƙyau yay fresh na angwanci, sun ƙagara Maanal ta dawo aiki kullum cikin fata suke. Amma sunji tsitt. Babu kuma mai ido da kwallin iya tunkararsa da tambaya.
AS kansa yau sai da yay gulmar makarar boss ɗin a zuciyarsa, dan hakan abune mai matuƙar wahala da zakaga AA yayi. Oga AA da bai san sunayi ba kam akan aiki kawai ya dira, sai dai kaɗan-kaɗan ya saki murmushi. Dama kuma fuskar tasa yau da sauƙin ɗaurewa. A haka AS yay masa knocking. Izinin shiga ya bashi, koda ya shigo yaga yanda boss keta murmushi sai yay ta satar kallonsa. Har sai da AA ɗin ya tsargu ya ɗago a bazata ya kamashi, sai AS ya wayance.
Komai AA baice masa ba ya duba file ɗin daya kawo masan ya saka masa hannu. Ganin AS ɗin yaƙi tafiya ya ɗago ya kallesa. Ƙasa AS yay da idanunsa. A dake AA ya ce, “Akwai wani abu ne kuma?”.
AS ya girgiza kansa. Sai kuma cike da girmamawa ya ce, “Boss dama zan sanar maka za'a kai kuɗin aurena weekend ɗin nan, shine Abbana yace na sanar maka idan baka da uziri sai kuje”.
A mamakin AS sai ji yay AA ya ce, “Humm munafuki wato kaima aure kake so, no wander naga ka fara ajiye gemu kwanan nan kana kuma saka manyan kaya”.
File AS ya saka ya rufe fuskarsa yana dariya, ransa fal mamakin yau Boss na masa wasa tab ɗin. Lallai Amarya Manaal ta shayar da boss zumar soyayya original mara gauraye. Shima AA dake murmushi sai ya ɗan taɓe baki yana maida hankalinsa ga computer ya ce, “Okay ALLAH ya kaimu tunda naga nine ma surukin naka, fita min a office”.
Fitar kuwa AS yay batare da ya yarda ya buɗe fuskarsa ba. AA dake binsa da kallo ƙasa-ƙasa a fili ya ce, “Yaro kayi ƙyan kai, dan koni da nasan haka aure yake aljannar duniya da ban yarda na cika ashirin a tuzuru ba. Amma ba damuwa, ko yanzu ma zamu fanshe shekarun mu tsaff in sha ALLAHU”. Ya wani lumshe idanun ya buɗe yana jin nutsuwa da wani sabon feeling na farin ciki. Waya ya ɗauka ya turama Maanal guntun message ya cigaba da aikinsa...
Wajen ƙarfe sha biyu AS ya shigo office ɗin, batare da AA da aiki yayma yawa ba ya ɗago ya kallesa ya ce, “Badai lokacin meeting ɗin yayi ba?”.
Cike da girmamawa AS ya ce, “Aa Sir, baƙo gareka. Na nuna masa aiki ne da kai sosai, kuma yau babu ma ganin kowane baƙo a tsarinka, amma yaronsa na neman yin hayaniya”.
A karo na farko AA ya ɗan ɗago ya kallesa, sai kuma ya maida kansa, da ƙyar ya iya motsa lips ya ce, “Waye?”.
“Senetor Bukar Kaugama”.
Karo na biyu AA ya sake ɗagowa ya kallesa. Sai kuma cikin cije lips ya ce, “Barshi ya shigo”.
Sosai AS yay mamaki, amma sai baice komai ba ya amsa da girmamawa ya fita. Aikinsa ya cigaba da yi hankali kwance, tsahon mintuna goma akai knocking ƙofar. Sai da ya mula dan kansa sannan ya bada izinin a shigo. AS ne ya fara shigowa, sai Sen.. Bukar da matashin ɗansa da bai wuce 26years ba, dan zai yi sa'a da AS. Tsabar wulaƙanci AA baima nuna yasan da shigiwarsu ba har Sen.. ya zauna shi da ɗansa da kusan minti ɗaya sannan ya ɗago oily fararen idanunsa ya kallesa, fuskarsa da wani ɗan munafukin murmushi, da maganar nan tasa mai fita ciki-ciki da ƙasaita tamkar baya so ya ɗan lumshe idanun da ɗan rissinar da kai sannan ya buɗesu slowly ya ce, “Barka ranka ya daɗe”. Sai kuma ya ɗan kalla hannun yaron Sen... Bukar ɗin daya miƙo masa wai su gaisa amma AA ɗin ya watsar bai bashi nashi ba.
Wata irin fusata ce ta zoma Sen.. a maƙoshi, ji yake tamkar ya shaƙo AA ya kashe ya huta. Tunda yaga video ɗin bikin aurensa da ƴar shilarsa yake jin irin wannan fusatar, da ƙyar ya yarda da shawarar abokansa akan ya biyoma AA ɗin ta ƙasa. Su kuma zasu dafa masa baya su ƙulla masa. Shima yaron yaji zafin abinda AA ɗin yay masa naƙin bashi hannu, amma ya basar yace masa “Barka da safiya”.
A dake AA ya amsa ciki-ciki ya ɗauke kansa. Sen.. Bukar ma ya dai-dai ta kansa shima yana sakimma AA ɗin murmushi da faɗin, “Fatan kana lafiya. Kayi haƙuri na maka zuwan bazata harda baƙo”.
Murmushi AA ya saki shima, ya ce, “No babu damuwa ranka ya daɗe, ai mu ƴan kasuwa ne munfi son ma bazata”.
“Hakane kam, dan kuwa nima bussines ɗin ne ya kawoni yanzu. Kaya nake so, masu nauyi kuma. Dan yarona ke son fara irin business ɗinku. Sunansa Afeef. Muna son fitaccen design”.
AA dake masa wani irin kallon ƙasan ido yay murmushin gefen baki tamkar baiji sunan yaron ba ma ya ce. “Okay baka da damuwa ranka ya daɗe. Idan kuna da sample zaku iya bamu, idan kuma mune zamu baku zaku bamu kwanaki. Sai dai zaku bamu bayanan dukkan abinda kuke buƙata kayanku suzo da shi.”
“Bamu da wani sample mu a hannu gaskiya, sai dai abinda muke buƙata kayan yazo da shi wannan zamu baku.”
Kai kawai AA ya jinjina, ya ɗauka kan waya yay kiran AS. Babu jimawa kuwa ya shigo. AA daya maida hankalinsa kan screen na computer ɗinsa ya ce, “Kaje da shi ku ƙarasa duk abinda ya dace”.
“Okay boss”.
Cewar AS cike da girmamawa. Dan kallon Sen... AA yay fisha cikin girmamawa ya ce, “Mungode ranka ya daɗe”.
Murmushin yaƙe Sen... Yay zuciyarsa na ƙuna. A ransa faɗi kaye (zanyi maganinka dan ubaka. Sai na ruguza wannan izzar taka ta inda bakai zato ko tsammani ba. Sai na talautaka har ubanka ma ta yanda zaku dawo bara akan titi).
Sen.. Bukar da AS na fita a office ɗin AA