Showing 93001 words to 96000 words out of 218311 words
Chapter 32 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
wani irin zugi dan baiyi mata da wasa ba. Kuka take irin wanda ita kanta bata san na minene ba. Sai dai wani gefe na zuciyarta sai maimaita mata kalman roƙon da take masa tana kiran cikakken sunansa yau harda su Yaya. Ita kanta kalaman dariya suke bata yanzu, tare da jin kamar bazata iya sake haɗa ido da shi ba. Amma yaya zatayi? Wannan itace kawai hanyar kuɓuta daga garesa, tabbas taji bata so aurensu ba a randa aka ɗaura, badan komai ba sai dan cika bakin da yay mata a asibiti, amma halin daya tsinta kansa na kusan mutuwa ya lausasa mata zuciya har taji ita wacece da wani zai rasa rayuwarsa a kanta, ai kamar tayima UBANGIJI butulci ne da ni'imomin daya bata kashi-kashi na rayuwa, kamar ta nuna masa bata amshi jarabawarta da hannu biyu ba, tunda tasan ƙulluwar auren ikonsa ne ba wani shiri ba. Na biyu nasihar mahaifiyarta da Daddy da Nene da hujjojin da suka kawo mata akan aurenta da Ajwaad shine rufin asirinta da su kansu musamman yanda zancen ya fara fita a lokacin bikin Ya Yazeed shima ya taka rawar gani wajen haƙura ta amshi auren batare da yin wani bore ba bayan wanda tayi. Sai dai tuna zuwan irin wannan ranar na tayar mata da hankali, na sakata jin tsoro da ɗunbin fargabar da jin anya zata iya yin biyayya ta bashi kanta kuwa. Dan wannan shi kaɗai ne hope ɗin daya rage mata wajen hukunta Ajwaad tsakanin ita da shi kamar yanda su Didi suka tabbatar mata. Dan sun nuna mata suma tabi maganar su Ammie, ta kwantar da hankalinta koda mutunci da darajar Abah da Oum. Itama ta zama jaruma yanda ya share ya nuna kamar komai bai taɓa faruwa ba ta biye masa itama suyi pretending ɗin tare, idan sun kasance a irin wannan gaɓar sai ta hukuntashi dai-dai da laifinsa har sai ya sauke nasa girman kan ya nema gafararta da afuwarta a sigar da ita kanta zataji ta gamsu da hakan sannan ta sallama. Ko a randa ta samu damar faɗama Didi Shahidah abinda taji akan Mamy ta girgiza, ta kuma tabbatar mata to lallai akwai wani abu da ya kamata su sani kenan, a hakan ma dan bata sanar mata wanda taji Mamyn na faɗama Ajwaad ɗin ba fa. Amma kalamansa na ranar sun raunanata, sun karya mata zuciya da duk wani burin horashi yanzu tausayi yake bata kawai...
AA ya jima sosai a bayin sannan ya fito, ko inda Maanal take bai kalla ba, dan ya tabbatar in yay hakan duk yanda yake jinsa a dauriya ALLAH sai ya mata fata-fata. Magungunansa da suka rage saura ya ɗauka yasha, daga haka ya koma ya kwanta batare da ya cire bathrobe ɗin jikinsa ba. Duk abinda yake kuma Maanal na jinsa, amma ta daure tai shiru, sai zuwa can ta miƙe dan jin alarm ya sake bugawa alamar lokacin gama sahur na gab da fita. Bayi taje tayo wanka itama, batare daya kalla abin sahur ɗin nasu ba ta ɗauka ruwa kawai tasha, dai-dai nan ya tashi shima daga kwanciyar da yay, sai taji kamar ta zura a guje, amma dai ta dake saboda sanin lokaci ya ceceta. Aiko shi sai baima kalleta ba, bathrobe ɗin ya zare ya ajiye, ya saka jallabiya ya tada salla. Itama sai kawai ta koma daga bayansa ta ɗauka Alkur'ani ta hau karatu.
Suna a wajen har lokacin sallar asuba yayi ya jasu salla kamar yanda ya saba, kowannensu yay azkar. Batare daya kallesa ba tace, “Ina kwana”.
Fuuuu ya wuceta batare daya amsa ba, itama sai ta taɓe baki. Gadon ya koma ya kwanta, dan tafiyar tasu ma sai 2pm ne. Itama sai tai kwanciyarta a sallayar kawai ta ƙudundune da hijjab ɗinta....
12pm
Ita ta fara farkawa, ta ɗan kalla gadon inda yake a kwance. Rufe yake da duvet har kansa, sai taji gabanta ya faɗi dan kasancewar bedsheet ɗin fari ƙal sai yay like gawa. Da sauri ta ture mummunan tunanin ta wuce bayi, wanka ta farayi ta fito bayan ta saka kaya daga can, ta gyara jikinta sama-sama ta kabbara nafila, tana cikin yi ya farka shima. Alhamdullah yana jinsa da sauƙi babu ƙullewar mara, kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kai, bayi ya shiga, sai kuma gashi ya fito lokacin tana tahiya. Kaf kayansu da suke da datti ya tattare harda underwear ya shiga da su bayin, a washing machine ya zubasu ya haɗa ruwan sabulai dake ajiye a bayin a ciki masu daɗin ƙamshi sannan ya kunna. Yana a tsayen har machine ɗin ya kashe kansa sannan ya shiga fiddosu ɗaya bayan ɗaya yana matsewa, sai da ya kammala tas ya sake ɗaurayewa sannan ya zuba a dryer dake a machine ɗin ta busar. Sannan ya fara wanka....
Maanal na zaune tana addu'a ta idar da salla ya fito da kayan a hannu. Mamaki ya kamata, dan tunda suka zo ita ke wanke musu. Sai dai batace komai ba ya ajiyesu inda akwatinsu yake sannan yay shiri kan Maanal a ƙasa harya saka jallabiya. Salla ya kabbara shima. Kasancewar ita ta idar sai ta miƙe zuwa wajen kayan nasu ta fara shiryawa, suka ɗai suka rage, duk wata siyayyarsu ya riga ya turata gida, tsaf ta kammala shiryawa kayan data ajiye masa dan ya sanya na gefe, ta shiga bayi ta sake duba komai nasu ta tattaro dan kar suyi mantuwa. Shima daya idar da sallar ba zama yay ba, shiryawa ya farayi a kayan data ajiye masa, hakan yasa ta koma gefe kanta a ƙasa harya kammala. Fita yayi daga ɗakin, ta ɗan bisa da kallo ƙasan ido, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana taɓe baki, daga haka ta maida hankalinta ga kallon tv. Fin mintuna ashirin sai gashi ya dawo, a wani ciki-ciki yace, “Muje” Yana kama hannun trolling bag ɗinsu da handbag ɗinta data ɗaura akai, zai ɗauka bag ɗin laptop ɗinsa ta rigashi ɗauka. A karo na farko suka kalla juna cikin ido, sai kuma kowa ya janye cike da basarwa suka fice....
Sosai Maanal ke jin kewar barin Shanghai, amma kuma tana matuƙar ɗokin komawa ƙasar haihuwarta. Ba wata tafiya mai nisa bace ta kawosu airport, bayan ƴan kunji-kunji na tsarabe-tsaraben tafiya a jirgi suka shige suka bar su Mr Li da kewarsu. Su duka su kowa yayi fresh abinsa, musamman ma mutuniyar taku da angonta. Dan ƴan kwanakin nan a Chaina kwanaki ne masu ɗunbin tarihi da suka taka rawar goge abubuwa masu yawan gaske a zukatansu musamman ga Maanal. Sosai ta ɗan rage jin zafinsa dake ƙasan zuciyarta, ta kuma sake fahimtar halayyen sabon Bestyn ta a yanzu. Shima dai hakan take, ya sake fahimtar abubuwa da yawa game da ita a yanzu. Sannan ya mata uziri akan abubuwa da yawa domin UBANGIJI ne kaɗai masanin gaibu. Kuma ko shine a matsayinta abinda zai yi kenan. Ya tabbata da ace su Maanal nada wani yaya namiji ba lallai ma ya yarda a sake bashi aurenta ba...
A wannan karon ma dai ta Qatar suka koma, tafiyar kuma ta ɗauki sabon salo a tsakaninsu ba kamar a zuwa ba. A vip section suke kamar wancan karon, sai dai kowa ya nema wajen zamansa suka ƙi zama da juna. Alkur'ani Maanal ta ɗauka taita karatu ma abinta har suka iso Qatar, dan duk da tanata hamma haka ta jure. Sunyi canjin jirgi yau ma, kuma Alhamdullah kamar a wancan karon ne babu jira. Baccin da yaci ƙarfin Maanal yasa ta kai kwance, sai lokacin shi kuma AA daketa aiki a laptop tunda suka taho ya samu damar zaman nasa karatun Alkur'anin bayan ya lulluɓa mata mayafi. Shima dai zuwa can barcin yaci ƙarfinsa sai ya ajiye Alkur'anin ya kwanta. Su duka basu farka ba sai da aka fara sanar da sauran mintinan da suka rage jirgi ya taɓa ƙasa.....
Alhamdullah sun sauka ƙasarsu ta haihuwa lafiya a cikin birnin Abuja. Kowa ka gani a cikinsu yay laushi, marasa juriya ma tuni sun karya azuminsu a hanya. Wanda basu karya ba irin su Maanal ganin safiya a Nigeria ne sai da suka girgiza, dan ƙarfe 7:30 na safe suka iso. Tab ɗin babbar magana, ga azumin awa kusan 15 a bakinsu. Wannan fa shi ake kira dare biyu. Manaal dake satar kallon AA sai taga ma shi daras yake mutumin nan babu wani rauni a tare da shi, suko duk sunyi yaushi abin tausayi.
Cike da girmamawa su AS sukai musu sallama suka nufi motar company da zata kwashesu takai kowa gida. Sun fito suma da shirin hawa taxi sukaci karo da Ya Fawzan, RK, da Najma sunzo ɗaukarsu. Cak AA ya tsaya yana kallon RK, shima dai kallon nasa yake yana haɗiye murmushi da ƙyar, a ransa yana faɗin (Dole ne mu tsaida wannan wasan ɓuyan haka Ajwaad) a zahiri kam sai ya nufoshi dan Yaya Fawzan na waya. Najma ma da gudu ta sheƙo ta ɗane Maanal suna murna, ai take Maanal taji duk wata gajiyarta da kasala ta ware a jikinta, ta ji daɗin ganin Najma a Abuja matuƙa gaya duk da dama sun gaisa kusan sau uku. Sai dai kuma ganin RK ya wani saka gabanta bugawa, amma ta dake abinta tana ambaton sunan ALLAH. Dai-dai nan Ya Fawzan ya iso wajen, RK kuma ya rungume AA. Abinka da maza, shima AA ɗin sai ya basar kawai, har yana ɗan hararar RK dake faɗin, “Ƴan gayu, honeymoon da azumi, abin naka azimun Oum's boy”.
Harararsa AA yayi, dai-dai shima Ya Fawzan na nako masa nasa sherin. Shima harararsa yayi, suka kwashe da dariya suna tafawa. Kafin su juya ga Maanal dake gaishesu a tare, dan taƙi yarda ta kalla sashen RK sam. RK bai damu ba, dan yasan dole su kasance a ƴar hakan kafin su saki jiki da juna kuma. Itama tsokanarta Fawzan ya fara, ta shiga ɓoye kanta a jikin Najma dake musu dariya.........✍️
To mun dawo NIGERIA, kowa yazo ya amshi tsarabar sa.💃💃🏃🏃🏃
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣6️⃣
______________
........Mota suka nufa, RK driver Ya Fawzan kusa da shi, AA ya shiga baya Maanal a tsakkiya kusa da shi Najma a gefenta. Tafiyar mintoci da bata kai awa ba ta kawosu gida, sun sami ko'ina shiru dan kowa na barci, Oum ce ma kawai tasan da fitarsu tarbo su AA ɗin dan RK ma a gidan ya kwana yau. Ma'aikatan gidan ne kawai dake gyare-gyare ke kai kawo, aiko motar na tsayawa suka iso suna musu barka da zuwa cike da farin ciki, ba'a dangi kawai ba hatta masu musu hidima ALLAH ya saka musu soyayyar AA a zuciya, ba komai kuma ya kawo hakan ba sai kasancewar sa mutum mai alkairi da sauƙaƙawa. Bai da yawan magana, da wahala ka ganshi a sabgar da ba tashi ba, amma mutum ne mai sauƙi gana ƙasa da shi. Ƙyawawan halayyarsa harga wanda ba musulman ba a bayyane take, dan yana iya ƙoƙarin sa wajen kamanta musu iya hurumin da UBANGIJI ya umarce mu yi a garesu. Tuni sun wuce sashen Oum, dan duk inda AA zaije a rayuwa ya dawo sai ya fara dangana da Oum sannan wani ya gansa a gidan, sai dai idan anyi sa'a ya samesu a tare ne.
Duk da sashen a cike yake da ƴan hutu ko'ina a tsaftace yake su Inte sun gyara sun saka turaren wuta da air freshener masu sanyin daɗi kamar ba safiya ba. Dan har yanzu bai wuce tara na safe ba. Nan ɗin ma dai shiru dan samarin yaran dake a ƙasan barci suke yi. Su duka sama suka haura, hakan yay dai-dai da fitowar Oum daga bedroom hannunta riƙe da kaskon turare. Ina ai da gudu Maanal ta nufeta ta rungume, AA ma da yaji bazai iya haƙura sai Maanal ta gama nata ba haɗawa yay ita da Oum ɗin ya rungume. Aiko mi su RK zasuyi ba dariya ba. Tuni farin ciki yasa idanun Oum tara hawaye, wlhy ita kanta bata san irin ƙaunar da takema yaran nan ba, Ajwaad da Maanal daban suke a zuciyarta, tana jinsu ƙololuwa a ranta ta yanda ita kanta bata san ta yanda zata musalta irin soyayyar da takema yaran ba. Duk da gidan cike yake da zuri'arta zuciyarta cike take da kewarsu kawai tana daurewa ne. Sun jima a haka kafin ta ɗagosu, tare da kai hannu a tare ta shafa fuskokinsu tana murmushi. A tare suka risina domin gaisheta, sai kuma suka kalla juna dan yanda sukai ɗin abin yazo musu ne a bazata, murmushi sukayi ma juna kamar yanda Oum ke murmushin, su Yaya Fawzan kuwa na dariya. Fawzan harda juyawa ya kalla Najma ya ɗan ɗaga mata gira, ƙasa ta duƙar da kanta tana murmushi. RK godiya yakema ALLAH a zuciyarsa da bai zama sanadin raba wannan ƙauna mai ƙarfi ba, dan tabbas ya ƙara yarda Maanal sai Ajwaad, Ajwaad sai Maanal. Wannan haɗin ALLAH sai dai a bisu da ƙyaƙyƙyawar addu'a kawai.
Ƴar hayaniyar ce ta tada yaran suka shiga fitowa a jere. Wayyo zokaga ihun murnar ganin su Yaya AA sun dawo. AA akwai farin jini kam Masha ALLAH. Rungume Maanal suka shigayi kowa na mamakin canjawar ɗan uwansa, kafin su shiga gaishe da AA dake kallon su kawai a dakensa dan ba sabgarsu yake shiga ba, baya sake musu fuska, amma a hakan sonshi suke dan shi mai alkairi ne a garesu, rashin yawan magana kuwa kowa yasan ɗabi'arsa ce shi da babban Yaya da ma wasu a yaran family ɗin da suka gado su. Tuni suma samarin suka shiga haurowa, sukam ai rungume AA ɗin suke, karan farko yay musu murmushi, yana binsu ɗai-ɗai ya shafa kansu. Fahimtar yanda sukai laushi yasa Oum tambayarsu suna azumi. Maanal ce ta amsa da eh, Oum tai mamaki ƙwarai da gaske, tare da jinjina ƙoƙarinsu dan awannin da yawa ai. Jin hakan tace to abarsu suje su watsa ruwa su kwanta su huta.
Hakan kuwa akai, AA ya fito zuwa sashensa, yasan dai su Mamy na barci har ma Abah da su Babban Yaya. Maanal kuwa ɗakin Oum ta shige tunda dama anan take. Yaran kuma Oum ta kaɗasu suje suyi wanka lokacin tafiya tafsir yayi....
Su Mamy basu san wainar da ake toyawa a gidan ba. Dan ita bata san yau ne su AA ɗin ma zasu dawo ba. Saboda rabonta da shi tun shekaran jiya data gama zuba masa tujara, dan tunda ALLAH yasa ya kira waya kullum sai ta kirashi ta tisa masa gargaɗi a kan Maanal. Shi dai yakan bata haƙuri kawai yace ta kwantar da hankalinta. Ko a fuska bai taɓa bari Maanal tasan Mamy na kiransa a waya ba. Sai dai abinda bai sani ba Maanal ɗin ta taɓa jinsu har sau biyu, ta ga kuma text message ɗin Mamyn akan wai miyyasa bai cika mata alƙawari na kiran Nuratu ba. Bataga ya bada amsa ba, dan haka tai murmushi kawai tana mamakin al'amarin matar nan.
Ƙarfe goma su Oum suka fito, hakama Mamy da Saheeba da Nuratu dan gaba ɗaya suke tafiya tafsir ɗin. Nibras ce kawai babu dan tana zuwa aiki. Kasancewar kuma yau ma juma'a ce sai gata ta fito zata bisu wai bazata fita aiki ba. Sai lokacin su Mamy ke jin dawowar AA da Maanal gidan. Wani abu ne ya tokare maƙoshin Mamy, har fuskarta ta gagara ɓoyewa, amma Oum na kallonta sai tai murmushi. Sai dai Oum ta riga ta ga canjawar fuskar Mamy ɗin, itama a ranta sai taji lallai basu ƙyauta ba, amma harga ALLAH tayi hakane dan tama kowa surprise a gidan, kuma shima AA daya sanar mata yace karta faɗama kowa har su Abah da Babban Yaya. Fawzan ma shine ya gaya masa. RK, ko Fawzan ya fito dan zuwa ɗakkosu yagansa a compound yana waya, shine dalilin tafiyarsu tare. Najma kuwa shine ya kirata yace yazo ta masa rakkiya wani waje, itama sai da akaje airport ɗin ta sani.
Fita sukai massalaci, Maanal dai bata bisu ba. Dan tana gama wanka kwanciya tayi, hakama AA yana can ya kwanta. Har suka dawo daga tafsir basu tashi ba, lokacin sha ɗaya da rabi dan yau juma'a an tashi da wuri saboda sallar juma'a. A compound suka iske Babban Yaya da Abah da RK suna shan iska, Fawzan ma barci yake. Cike da tsokana Abah dake kallon Oum ya ce, “Ashe ɗanki ya dawo min da yarinyata, irin wannan bazata haka”.
Dariya Oum tayi da faɗin, “Yanzu ai sai hankalinka ya kwanta, ka yarda mu masu cika alƙawari ne”.
“Na yarda kam sosai”.
Abah ya faɗa murmushi yalwace a fuskarsa su Babban Yaya na taya shi. Babban Yaya yace, “Ai nima Abah na ƙagara su tashi a barcin naga shi da Lillyn wa yafi wani ƙiba yanzu”.
Dariya aka sanya, Oum tace, “Oh ni kowa dai ya sama Autana ido a gidan nan. Fadeel ina yabonka salla karka kasa alwala