Showing 147001 words to 150000 words out of 218311 words
Chapter 50 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
😂To Manaluwa ALLAH ya rabamu da tsautsayi da aikin danganci🥱🤫🤭🤣🤣
_______★
A dai-dai lokacin da AA ke fita a ɗakin Maanal da wancan kaya dai-dai nan Mamy ta farka a barcin da allura ta sanyata. Maman Saheeba kawai ta gani a gefenta tana latse-latsen waya. Cikin sanyin murya irin na mai tashi a barci ta kira sunanta. Maman Saheeba ta juya da sauri ta kalleta, sai kuma ta saki murmushi da faɗin, “Lah Aunty kin tashi? Bara na kira Aunty Babba ALLAH yasa basuyi barci ba”.
Riƙo hannunta Mamy tayi a hankali tana girgiza mata kai, sai kuma ta buɗe baki da ƙyar ta ce, “Ajwaad fa?”.
Ɗan zuba mata ido Maman Saheeba tayi, sai kuma ta taɓe baki da faɗin, “Yana sashensa mana Aunty, yazo miki sallama kina barci ai”.
Zaramm kuwa Mamy ta tashi zaune jikinta na rawa. Sai kuma jiri ya kwasheta luuuuu ta tafi zata faɗi dole ta koma ta kwanta tana dafe kai. Muryarta na fita da ƙyar ta ce, “Shine kuka barshi Nana? Shine baku tasheni ba”.
“Aunty kenan, wa kike ganin ya isa a cikinmu ya hana Ajwaad zuwa ga matarsa ne? Sannan ke kuma taya zamu tasheki baki da lafiya....”
“Bani wayata”.
Mamyn ta faɗa da ƙyar. Miƙewa Maman Saheeba tai ta ɗauka mata wayar, haka Mamy ta amsa duk da daƙyar ma take iya kallon screen ɗin wayar saboda ciwon kai da idanunta dake gani bishi-bishi ta shiga lalubo sunansa. Dialing no ɗin tayi, cikin sa'a kuwa ta shiga, dan haka takai kunne tana jiran a ɗaga. Sai dai me harta tsinke ba'a ɗaga ɗin ba. Sake kira tayi, amma nan ma tsitt kake ji. Haka ta dinga jera masa kira a dukkan layukansa ma amma anƙi ai picking. Sosai ranta ya ɓaci, hankalinta ya tashi. Gefe ga Maman Saheeba na faɗin, “Aunty kema kin san bazai ɗauka ba shi da ke da amarya duk da dai ba sabon waje bane, amma ai bazasu barsa haka ba sai da sabon shiri...”
“Nana rakani sashen nasa”.
Jimmm Maman Saheeba tayi, sai kuma ta ce, “Okay muje”. Ta ajiye wayar tana miƙewa. Itama Mamy ɗin ta taƙarƙara ta miƙe sai juwa kuma ta ɗebeta ta maida akan gadon. Kan ta dafe sosai, dan ya wani sara mata na bala'i. Muryarta can ciki ta ce, “Bari juwar nan ta sakeni Nana ban ruwa”....
Mamy dai juwa ta hanata motsin kirki, dole Maman Saheeba ta bata shawarar yin wanka ko hakan zai taimaka mata, batai musu ba tace ta haɗa mata ruwan. Aiko haka ta miƙe taje ta haɗa mata sannan ta dawo ta taimaka mata ta kamata har cikin bayin. Dama ta ajiye mata komai da zata buƙata ta fito ta barta. Wayar sahiba ta kira sukai ƴar magana ƙasa-ƙasa ta kashe. Sama-sama Mamy tai wankan nan, dan hankalinta gaba ɗaya yana wajen AA ne, ta riga tama kanta alƙawarin bai isa ya kwana da Maanal ɗin ba yau, wanda yay a baya har ta samu ciki yayi na ƙarshe. Kai itafa a wannan daren take son Ajwaad ya saki Maanal saki uku duk ma wacce za'ai sai ayi, shima kuma Fawzan sai ta tabbatar masa itace ta haifi abinta shi da duk masu ɗaure masa ƙugun yin auren. Haka ta lallaɓa tai wankan sama-sama, tai kiran Maman Saheeba dake ƙofa tana jiranta. Shigowa tai ta taimaka mata suka fito, da taimakonta ta ɗan shafa mai kaɗan saboda bushewar jiki, ta bata doguwar riga ta saka, ta kuma haɗa mata tea tace tasha ko zata ɗan samu ƙarfin jikinta. Batayi musu ba kuwa ta amsa tasha dan itama ƙarfin take nema ruwa a jallo. Bayan ta gama sha magani ta bata shima ta sha, tace mata taɗan kwanta yabi jikinta sai su tafi.....
Hummmmmmm!!!!! Ashe anan ma ya kamata muyi addu'ar ALLAH ya kiyaye tsautsayi da gangancin ba wajen manalu kawai ba🥱🤣
_______★
Lokacin da kiran Mamy ke shigoma AA a waya duka wayoyinsa suna anan ɗakin Maanal kuma a silent suke. Dan yau ko a vibration bai saka su ba. Shi kuma yana can a nasa ɗakin bayan ya ajiye kayan barcin nan da ledar magunguna a zuciyarsa yana saƙa yanda zai sille RK da safe dan ya tabbatar iskancinsa ne saka kayan barcin nan da maganin ya faɗa bayi yay sabon wanka da shirin barci shima. Ya baɗe jikinsa da turarurruka masu shegen ƙamshi da saka zuciya nutsuwa daya tanada domin wannan rana kawai. Ya gyara sumar kansa da kwantaccen sajensa, sai lokacin ma ya ɗan shiga neman wayoyin sai ya tuna ya barsu ɗakin Maanal. Baiyi niyyar koma mata yanzu ba, yaso sai tayi barci dan yanda take a firgicen nan baiso hanata samun nutsuwa a barcinta kasancewar yana son bata damar sakin jikinta yanda ya kamata. Fitowa yay domin ɗaukar wayoyin sai ya dawo ya ɗan kwanta anan har sai yai barci ya koma. A dai-dai lokacin da yake tura kai cikin ɗakin bakinsa da sallama ciki-ciki ita kuma Maanal ta fito a bayin bayan ta gama leƙenta ta tabbatar bai dawo ba. Sai dai me tana gama rufe ƙofar ta juyo kawai ta ganshi tsaye a ƙofar shigowa ya wani zuba mata ido. Cak ta tsaya kamar yanda yake shima cak a tsaye. Sai kuma ta duƙar da kanta tare da runtse ido tana jin kamar ta zura da gudu ta koma wani sashe na zuciyarta na kwaɓarta da tuna mata AA ne fa Bestyn ta mijin nan nata da suka kasance tare a Chaina, a ɗaki ɗaya, gado ɗaya ba wani sabo daban ba.
Shi ko mayataccen ƙamshin turarenta ne ya wani irin dokar masa brain gaba ɗaya kasalar jiki data zuciya ta dabaibaiyesa cikin. Ga ƙyawun da kayan barcin sukai mata tamkar an zanata a cikinsu. Wani irin sulululu... Jinin jikinsa ke sulalewa a cikin jijiyiyinsa. Cikin sakanni komai na jikinsa ya canja. Wanda suke a sume domin gajiya duk suka farfaɗo. Idanunsa kam sun kasa barin kanta, sai ma takawa daya shiga yi a hankali har inda take. Yana gab da isowa ta juya da sauri da nufin komawa cikin bayin. A wani irin hankali ya kama hannunta, muryarsa na shaƙewa ya furta, “Ina zaki je?”. Yay maganar yana juyo da ita gaba ɗayanta ya tsayar a gabansa cak.
Maimakon bashi amsa sai ta ɗago idanunta da suka tara ƙwalla ciki ta kallesa. Kauda nasa yayi, sai dai ina zuciyarsa tabbatar masa take bazata bashi haɗin kai ba. Hakama gangar jikinsa gaba ɗaya. Kuma harga ALLAH bai niyyar taɓata a yau ba dan shi kansa a gajiye yake barci kawai yake son yi. Amma a yanzu daya kasance a cikin yanayin ƙaulani bashi da tabbacin hakan sai abinda ALLAH yay kawai. Jawota yay jikinsa ya rungume ko zai ɗan samu sassauci, amma ina komai ma sake yin tashin gauron zabi yayi cikin ƴan sakkani, farashin ya sauya daga ainahin farashinsa. Tuni yama manta da wani batun ɗaukar wayoyi da komawa can ɗakin. Cirota yay da ƙyar a jikin nasa ya kaita bakin gado ya zaunar, sai kuma yay mata nunin ta kwanta.
Kamar mai shirin yin kuka ta ce, “Bana jin barci”.
Murmushin gefen baki ya ɗan saki, sai kuma ya girgiza kansa kaɗan. Sake matsowa yay kusa da ita sosai, ya matsota ya saka a cikin jikinsa. A tare suka sauke ajiyar zuciya, hannunsa na shafa gadon bayanta ya furta, “Yau gadin gida zamuyi ke nan?”.
Ƙasa-ƙasa ta ce, “A'a kai ka kwanta kayi barci”.
“Ke kuma fa?”.
Shiru tayi taƙi yin magana.
AA da dariya ke cinsa sosai yana dannewa dan wannan asanyayen data koma abin dole ya baka dariya, “Anya wannan amaryan rowanta baiyi yawa ba?”.
Baki ta ɗan tura kaɗan, sai kuma ta ɗan ɗaga ido ta kallesa, shima kallon nata yayi, amma tai ƙoƙarin janye nata dan bazata iya kallon juyayyun idanunsa ba. Ƙin bata damar cire idanun nata yayi, ya sarƙesu da nata dake cike da rauni da fargaba. Rau-rau suka cika da hawaye, maimakon ya tausaya mata ya barta sai ma ya sake narke nashi dake cike da salon shauƙi da buƙata. “Miyasa bazaki iya cigaba da kallon idona ba Besty? Babu abin da zai same ki a cikin su sai natsuwa.”
Cikin raɗa, da muryarta mai rawa ta ce, “Ina jin tsoro”.
“Why? Zaki ji tsoro Maanal, Ajwaad ne fa, Bestyn ki. Ni ba ƙarfe bane mai dukan farin ciki ko ruguzashi. Ni ruwa ne, mai goge tsoro, in shayar da kwanciyar hankali musamman a duniyarki”.
A hankali hawayen da suka cika mata ido suka gangaro, sai kawai ta samu damar lumshe idanun tare da kife fuskarta a ƙirjinsa. “Kalamanka nasa zuciyata tana bugawa da sauri, kamar tana son faɗin wani muhimmin abu a kanka, amma bana jin kalmanta sam.”
Murmushi ya saki mai taushi, tare da motsawa ya ɗagata cak ya maida saman gadon ya shimfiɗar, kanta na a saman damtsen hannunsa, sai ya ɗan rufu a kanta hannunsa kwance a saman ƙirjinta ya kai yatsun yana wasa da gashin kanta mai laushi da santsi........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣3️⃣
______________
........Gefen fuskarta ya sumbata kaɗan, cike da raɗa ya furta, “Kar kiji komai, zan saurari bugun zuciyarki har sai ta tsaya cikin nutsuwa. Zan jira fitar sautin kalmanta har su bayyana a cikin kunnuwana. Kin manta na faɗa miki zan iya jira na har abada ba a matsayin mijin da ke da HAƘƘI ba, domin ke nake kallo a matsayin ke ba surar jiki ko manufar sauke buƙata ba”.
Numfashi ta sauke mai ɗan nauyi, sai kuma ta buɗe idanunta kaɗan tana kallonsa yanzu, cikin ido. Idonta yana ɗauke da yanayin nuna tausayawa a gareshi da kuma ɓoyayyar fargaba. Shi ko kallonta yake kamar yana karanta rubutu a cikin idanun nata.
Murmushi ya mata mai nauyi da isar da saƙo kakkaifa, ita ma sai ta maida masa murtani a karo na farko. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa saboda murmushin nata ya shigesa, cike da iya sarrafa harshe da wayo cikin siririyar murya ya furta, “Na fahimci idanunki suna cike da tambayoyi. Bari na amsa su da yanayin da kika fi buƙata a maimakon magana. Ki ce da ni kawai (Kana tare da ni Besty?). Niko nayi alƙawarin zance da ke, (Har abada)”.
Murmushi ta sake sakar masa a hankali, zuciyarta na ɗan sakewa, gangar jikinta na rage tsoron, haka ma bugun zuciyarta na saisaita a cikin ƙirjinta. Kanta ta kauda gefe a cike da kunya, ciki-ciki ta furta, “Kana da wayo sosai”.
Murmushin yayi shima, sai kuma ya rungumeta a hankali. Babu matsawa. Babu gaggawa. Sai nutsuwa da shauƙi mai sanyi, a cikin kunnenta ya ce, “Duk wayona na kaiki ne, keda kika ɗauka buhunnan alƙawurra gashi kina neman ɓigewa da zame-zame.”
Ƙoƙarin janye jikinta tayi, sai ya hanata yin hakan ta hanyar sake rungumeta da ƙyau. “Ina kike ƙoƙarin guduwa? Bayan naji wani abu mai sanyi yana ratsani, kamar numfashinki. Rungumarki ce kuma tamkar addu’ar da ta yi karo da cikar amsar da nake nema. Ina so ki cigaba da zama a haka a kirjina, ba dan yau kawai ba, sai dan in cigaba da tuna cewa kece sassanyan lambun da zuciyata take so ta huta daga yau har zuwa ƘARSHEN RAYUWA. Na miki alƙawarin in sha ALLAHU zaki cigaba da kasancewa anan. A duk lokacin da duniya ta rikice, zan ajiyeki a wannan mafakar ta jikina babu mai damunki koda da harara”.
Hawaye ne suka gangaro mata a hankali, tsigar jikinta na ƙara tashi saboda salon da yake mata a cikin gashi mai nauyi ne. Muryarta a ƙurya sosai ta ce, “Kafin wata rana ina kallonka ne a matsayin garkuwa ta, amma a yanzu sai na ji kamar zuciyata na rawa da zama cikin ƙaulanin ƙila wa ƙala musamman a gaɓar tuna rana mai girma da tarihi ya ajiye mana”.
Fuskarsa ya cusa cikin wuyanta, cikin dunƙullen amo ya furta, “Ki bar ni na lallaɓa maki tunanin da ke yawo cikin gangar jikinki, na shafe miki wancan tarihin dake a zuciyarki, na ajiye miki sabon tarihin da zan tabbatarma duniya ke ɗin SARAUNIYAR mata ce. Tanadina mai girma ne a kanki, mai kuma muhimmancin da zai fitar da saƙon daya daɗe AJIYE A DUHU ne Maanal. Ki yarda da ni, duk wata fargaba da ta zo da tsoro ko rashin tabbas, zan shafe ta a yau cikin wannan daren. Ina taɓa gangar jikinki ne tamkar yadda ake taɓa ZINARE a tsakiyar talalaɓuwar ƙasa. Saboda a cikinki akwai daraja da tsarki da bai kamata a yi gaggawa da shi ba.”
Ajiyar zuciya ta sake saukewa, fargabarta da tsoro na sake daidaituwa a cikin gangar jikinta. Ɗagowa tai a hankali ta zuba masa ido, shima kallon nata yake a cikin ɗan hasken ɗakin mara ƙarfi. Lips ta motsa a hankali zatai magana ya ɗaura yatsarsa a kansu yana wani lumshe mata idanun da buɗewa. “Ba sai kince komai ba. Idanunki suna gaya min abubuwan da baki ba zai iya furtawa ba ma. Na ga fargaba, tsoro, juyayi, tausayi, rauni, karaya, amma na fi ganin ƙauna da sha’awa mai tsarki.”
Idanu ta zaro sosai. Ya kashe mata ido ɗaya. “Yes! Na ga wata murya a cikinsu da ke cewa, (KA KULA DA NI! KA BANI GARKUWA!) kuma na rantse, zan kula Besty, zan baki garkuwa daga ɓangaren kowanne abun hari kina barci ko ido biyu..”
Sosai ta wani kalar lumshe idanu tana ɗan murmushi, dan yanda bakinsa ya buɗe yake zuba zance sai take jin shauƙin hakan. Shima murmushin yake, sai kuma ya kai yatsarsa a saman idanunta yay kamar yana sosawa, hakan ya sata ta ɗan lumshe ta sake buɗewa a cikin nashi. Shima lumshe nasan yayi ya sake buɗewa a cikin nata. “Idanunki sunyi shiru, amma tawa zuciyar nata amsa dukkan abinda suke son isarwa. Bari mu kalli juna har duniya ta manta da lokaci. Saboda ni da ke mun ishi juna a wannan ƙyaƙyƙyawan dare har zuwa sassanyar safiya. Kice kin amince ni kuma zan baki tabbaci”.
Cikin wani irin tausayinsa da kasalliyar murya ta ce, “Na amince” ta faɗa tana ɗan sumbatar lips ɗinsa, sai kuma tai yunƙurin ƙwace jikinta zata juya dan kunya. Sai kawai ya wani riƙota da saura ya ɗaura tausasan lips ɗinsa akan nata.
Alhmdllh kamar yanda yay fata batayi musu ba, sai ma ajiyar zuciya da take saukewa a jajjere. Sannu a hankali ta miƙa wuya tare da sake shigewa jikinsa harma da maida murtani, hakan sai ya ƙara masa ƙaimi da armashi, gaba ɗaya yaji duniyar tai wani irin zama shirun da su kaɗai yake zaton sun rage a raye a cikinta.....
(Ikon ALLAH AA mu duk mun mutu kenan, kai dai AA ka dinga tsoron ALLAH ☹️🥱😏)...
_____★
A lokacin da can AA kema tunanin duk mun mutu sai shi da Manaluwa gyatumarsa ta haihuwa Mamy ce a yanayi irin na matattu, dan duk yanda taso zuwa sashen nasa da alama jiri bazai barta ba. Cike da zuga Maman Saheeba ta ce, “Yaya kiyi kwanciyarki kawai bara ni naje na kira miki shi kawai. Dan wannan juwar zata iya kadaki a hanya”.
Cike da gamsuwa Mamy ta amince, Maman Saheeba ta miƙe ta ɗauka hijjab ta zura ta ɗauka wayarta, “Ki ajiye wayarki a kusa idan yay gaddama zan kiraki”.
Kai Mamy ta jinjina mata kawai. fitowa daga sashen Maman Saheeba tai, ta nufi sashen AA. Tana zuwa kofar kitchen ɗin sashen ta baya Saheeba da Nuratu da'a daren nan tazo gidan duk ta rame tai duhu na tsaye na jiranta. Murmushi suka sakarma juna, ƙasa-ƙasa tace ku muje. Sai da suka gama bin gidan da kallo suka tabbatar ko'ina tsitt hatta masu gadi sun kwanta sannan sukai wuff ta suka shige ciki. Cikin sa'a kuwa ƙofar a buɗe take. Cak Mamman Saheeba ta tsaya tana bin kitchen ɗin da kallo saboda ta cikinsa suka shigo, itam Nuratu sai ta tsaya tana kallon komai, dan kuwa dai komai yaji, daka gani kuma kasa na ƴar gata ne. Maimakon su wuce abinsu sai Saheeba catai, “Eh lallai wannan daka gani kasan kuɗin Ajwaad ne da aka wawura bara muga store ɗin shi kuma uwar mi suka ajiye mata tunda anje an tile kayan gara sashen haɗamatu (Wai Oum). Nuratu batai niyyar shiga ba, sai ta ja kujerar work table ta zauna, ga ƙasan zuciyarta na cigaba da bata shawarar ta