Showing 63001 words to 66000 words out of 218311 words

Chapter 22 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

haƙuri ta tabbatar masa tayi nadama kuma ta amshi laifinta. Haka ɗin kuwa akayi, bayan sallar isha'i yana zaune yana cin tuwonsa suna ƴar hida da iya dake gefe ta fito daga ɗakin iyan. Su duka kallonta sukayi, kafin Iya ta janye nata cikin taɓe baki. Shima Kawu Manun janye nasa yay ya koma ga cin abincinsa. Sum-sum tazo ta tsugunna a gabansu kamar wata munafuka, yi yay kamar bai ganta ba, dan haka ta fara magana cike da rawar muryar son yin kuka.
“Kawu dan ALLAH kayi haƙuri na tuba. Wlhy nabi ALLAH na biku bazan sake ba. Na maka alƙawarin zan zauna lafiya a ɗakina. Ba kuma zan sake biyema wata ƙawa ta kaini wajen kowa ba. Wlhy Kawu wasu abubuwan dole ce ke sani aikatawa. Tunda Daddyn Huznah ya auro amaryarsa gaba ɗaya baya mana adalci, ya tattare komansa ya tare gareta. Agololin ƴaƴanta sune kawai ƴaƴa a gidan. Koda kwatance baya yima ƴaƴanmu irin gatan da yake musu. Ni babu kamar ma nawa, dan ita Hajiya Sadiya yana tsoron mahaifinta tunda tana goranta masa sune tushen arziƙinsa. Sannan ɗanta shine akan komai na dukiyarsa, nidai nice a baya ga komai na gidan kamar mara gata. Yanzu kaga akan auren nan nasu Huznah, ƙiri-ƙiri ya ɗauka wanda zata aura ya bama agola dan ya birgesu. Ya haɗa Huznah da ɗan Sani bayan ko ku Kawu kun san Sani ba ƙaunata yake ba, tun ma kafin a auro ni ya nuna adawarsa, dana shiga gidan kuma suka haɗe kai da Hajiya Sadiya suka dinga cin mutunci na sai da na zama jaruma. Kawu ya ake so nayi, Huznah fa ita na fara gani a duniya matsayin gudan jini, bazan so ganinta a damuwa ba tunda na san bata son ɗan Sani, kuma kowa shaida ne a kan hakan tunda tun a shekarun baya bama ta gama Secondary ba yace yana sonta tace a'a nima kuma nace a'a....”
Cikin katseta Kawu Manu daya gama wanke hannu yace, “To yanzu ya kike so ayi?”.
“Ayi haƙuri Kawu a barni na koma ɗakina naje na rungumi ƴaƴana, sannan dan ALLAH kasa baki a raba auren nan na Huznah ALLAH nasan bata jin daɗin zaman nan”.
“Ita da kanta tace miki bata jin daɗin zaman? Duka yaushe ma aka kaita gidan auren da zata fara banbance daɗinsa da akasinsa? In ce gaba ɗaya yau sati na huɗu muke, koma wata guda ba'a ƙulla ba cif. Basariyya ki kiyayeni, ki kuma fita idona, niba dattijon banza bane. Ai dama tunda Mairo (Iya) ta dawo daga bikin ta sanar min iya shegen da kike zubawa nasan kin shirya sheɗanci a zuciyarki, to ni bazan hanaki kashe auren ƴarki ba, amma ki sani, ana sakota ta koma gidan ubanta kema zan kira Usman ya sakeki ki dawo nan, kuma wlhy anan ƙauyen zaki samu miji na aurar dake. Komawa kuma ba yanzu ba dan har yanzu bakiyi hankali ba, karma ki sake samuna da wata magana anan zakiyi azumi tashi ki ban waje shashasha da bata da wani girma sai na jiki. Shekaru na nuna kansu a jikinki har kin aurar da ƴa amma hankali sam babu a tattare dake sai shaiɗanci fal a zuciya. Da kike cewa shi Alhaji Usman ɗin yana fifita amaryarsa fiye daku tafi ƙyautata masa ne shiyyasa, ku kuma kun zauna baƙin kishi, har kuna wani gorantawa yara da kiransu agololi, su waɗannan agololin zata iya yiwu ma sune zasu tallafi rayuwarku ta gaba kosu taimaki ƴaƴanku, dan ka kiyayi ɗaukakar wanda mutane suke son ƙasƙantarwa jahilcin banza da wofi kawai....
Hawaye sosai Hajiya Basariyya ta miƙe tanayi, zuciyarta kuwa tamkar zata kama da wuta saboda zagin ƙare dangin da Kawun yay mata. A ranta kuwa alwashi take ɗauka ko guduwa ne sai tayi wlhy. Dan bazatai azumi a wannan garin ba ta mutu a banza....


__________★


CHAINA (Shanghai)


Sosai zuciyar Maanal ta shiga kai kawai. Kalamansa ta shiga son fassarawa, (Hum! K! A komai sai kin yi kamar za ki gudu ne?. Ba kullum ba ne. Amma a wannan gaɓar maybe ya kasance tare da ke watakila) jitai kamar zuciyarta zata ɓare dan tsoro, sai kuma ta shiga ƙalubalantar kanta aka amsar data bashi. Wayyo ita kam taga takanta, mi mutumin nan ke son maida ita ne, yama barta da gajiyar tafiyar nan ta awanni mana, amma sai ya takaleta da rigima. Waiwayawa tai ta ɗan kallesa, dai-dai yana zare shirt ɗin jikinsa, ay da sauri ta juya zuciyarta na bugawa, sai kuma ta rumtse idanunta da ƙarfi dan ingarman jikinsa yaƙi barin cikinsu. Eh sunyi wata rayuwa a baya a bigiren ƙuruciya, duk da ba sa'anta bane ko a wancan lokacin amma dai yaron ne shima. A lokacin da ƙaddarar rabuwa tazo musu yana a gaɓar kammaluwar zama cikakken namiji ne, kuma sam baya tu'ammali da gym a wancan lokacin, sannan bai taɓa yarda ya zauna a gabanta koda da dogon wando da singlet bane ba. Dan zata iya rantsewa bata taɓa ganinsa ba kaya jikinsa ba, sanin ma tana shigar musu ɗaki a wasu lokutan kafin ma Oum ta hanata idan zaiyi wanka sai ya kulle ƙofa, ko yace mata zaiyi wanka karta sake ta biyoshi, itama kuma data fara mallakar hankalinta ta fahimci mi yake nufi tuni ma irin waɗan nan yanayin take zille masa.......
“Tunanin mi kike yi?”.
A ɗan zabure Maanal ta juyo gareshi, dan a bazata taji saukar muryar tasa a cikin kunnenta. Babu shiri kuma ta sake juyawa tare da matsawa a kusa da shi ta koma jikin window ɗin sosai. Muryarta har ɗan rawa-rawa take wajen faɗin, “Wai dan ALLAH mi kake son maida kanka ne? Hakan fa baida ƙyau kana zuwa gabana babu kaya kai ko kunya ma baka ji”.
A hankali AA ya kai hannunsa kan gashin gemunsa daya zagaye har zuwa kumatunsa yana ɗan jansa kaɗan-kaɗan, yayinda ya zuba mata idanu a wani irin yanayi. Jin shiru yasa ta ɗan sake juyowa a tunaninta ya bar wajen, sai suka sake haɗa ido, ai a sukwane ta sake juyar da kanta. Ji take kamar ta saki kuka, ALLAH kunyarsa take ji, haba jama'a Bestyn ta fa, wlhy al'amarin ya mata girma. Sai kawai taji hawaye na cika mata idanu ma, dan harga ALLAH ita dai wannan zuwa Chaina ya zame mata alaƙaƙai.
Shi ko AA a wannan gaɓar dariya ma ta soma bashi, amma dai baiyi ba, fuskar tasa ma babu walwala kamar dai yanda ta kasance take tun barowarsu gida. Sai in yaso yin murmushin ne yake yin taƙaitacce. Barin wajen yayi yana ƙarasa kunce belt ɗinsa, dan shi da dogon wandon kawai suka rage sai na ciki. Belt ɗin kawai ya cire ya nufi bayi da dogon wandonsa, ƙarar rufe glass door ɗin ya saka Maanal da komai ke neman ƙwacewa sakin nannauyan numfashi. Magana ta ALLAH bazata iya zaman nan ba, wlhy a takure take matuƙar takura, ita dai bara ya fito, zata roƙesa ya barta ta koma wani ɗakin kawai, dan zamansu tare anan zai iya sakawa zuciyarta ta buga ne, sannan zai iya karya mata lago da shawarar su Didi. Jin ƙafafunta sun fara sagewa cike da sanyin jiki ta baro wajen window ɗin, a ɗaya daga cikin sofas ɗin ɗakin dake tsare matuƙa takai zaune, sai ta juya ma ta inda zai fito baya, wayarta ta ciro ta fara game, duk da ba fahimtarsa take ba gara tayi dai. Ƙarƙashin zuciyarta kuwa kewa take ji, kewar su Oum da Ammien ta. Ashe sanda tana Abuja dan suna waya ne da Ammien a koda yaushe shiyyasa take jin damuwar rashinta a kusa da ita kaɗan-kaɗan, yanzu kam sunyi nisa da juna, ta yanda bama tasan yaya zasuyi koda waya ba tunda ba layin ƙasar ne da ita ba..........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣1️⃣




______________




.......Maanal ta matuƙar shagala a tunaninta AA ya fito a bayin, sanye yake da bathrobe golden yellow, gaba ɗaya ƙamshin sabulunsa na shower gel ya mamaye ɗakin, ɗan kallon Maanal data juya baya yayi ya ɗan taɓe baki yana cigaba da goge kansa da ƙaramin towel. Hankalinsa kwance yaje inda take ya zauna a wata kujerar daban. A dakensa ya furta, “Ki tashi kije kiyi wanka dan zamu fita shopping ɗin abubuwan buƙata”.
Batare data yarda ta kalleshi ba ta girgiza kanta. Sai kuma muryarta ƙasa-ƙasa kamar zatai kuka ta ce, “Ni ba sai nayi wankan ba, dan ALLAH mizai hana na koma wani ɗakin koda na kusa da kai ne, kaga zamanmu anan kai zan takura maka ai....”
“Ni nace miki na takura?”.
Shiru tayi dan yanda yay maganar miryarsa da ɗan tsauri sai taji wani kalar shakkarsa.
“Dake nake fa! Kuma nasan kin jini”.
Yanzu kam kanta dake duƙe ta girgiza masa, dan taƙi yarda ta ɗago ta kalla koda sashen da yake ma. Ciki-ciki shima yaja tsuki da yazo masa a bazata, kafin a daƙile ya ce, “In kuma kina da kuɗi sai kije ki kama wani ƙofa a buɗe take”. Daga haka ya miƙe ya bar mata wajen. A bakin gado ya zauna ya shiga gyara jikinsa zuciyarsa na zafi, haka kawai yaji haushin maganarta, wai miyasa bazata sassauta ma zuciyarta ba, miyasa bazata fahimcesa, abubuwa sun masa yawa matuƙa, yana son raba koda wani yankin ne na damuwarsa da ita amma taƙi bashi fuska, bai gajiya ba yana cigaba da binta dan yasan shi mai laifi ne a gareta, amma koyaya bazata tausaya masa ta sassauta masa ba ne.
Maanal da tunda ya maka mata baƙar maganar in tana da kuɗi taje ta kama ɗaki taji hawaye sun cika mata ido, sai kuma suka gangaro a hankali. Veil ɗinta tasa ta ɗauke su, sai kuma ta ajiye wayar ta miƙe, bayin ta nufa. Ya ɗan bita da kallon ƙasan ido harta shige. Tana maida ƙofar ta rufe ya janye idanunsa yana sauke ajiyar zuciya...
Kafin ta fito ya shirya abinsa tsaf cikin ƙannan kaya. Dogon wando ruwan ƙasa ya saka t-shirt mai v neck mara nauyi data kwanta a jikinsa matuƙa ta fiddosa a ingarmansa. Turare ya saka sannan ya shiga ɗan gyara sumarsa sama-sama da kwantaccen gashin kumatunsa. Ficewa yay a ɗakin bayan yayi sallar azhar dan ya tabbatar bazata fito ba in har yana ciki tunda har yanzu tana a ciki a maƙale, samun kanshi yay da girgiza kai kawai. Wai yau shine Maanal ke jin kunya, yarinyar da a gabansa ta fara dukkan abinda take ɓoye masan a yanzu. Yarinyar da yasha yima tsarki. Yarinyar da yasha wanke ma underwear. Yarinyar da yasha goyawa a bayansa. Oh-oh duniya-duniya, Maanal ɗinsa, Bestyn sa na jin kunyarsa. Koda yake shi hakan ya masa, yana son mace mai kunya, dan wannan noƙe-noƙen da take masa ƙara daraja take a idanunsa, irin wannan hallayar tatace tayi ƙaranci a tattare da ƴammatan yanzu shiyyasa ya tsani mafi yawancin su. Kaga yara ƙanana tun basu tafasa ba suna neman ƙonewa, masu ɗan ƙoƙarin ne suke gama Secondary da wannan yanayin, ana shiga jami'a sai a fifirce su wayayyu. Humm mutane da shirme, rawar kai da rashin kamun kai ne wayewa wai. Wannan abu na ƙona masa zuciya. Ai a baka yarinya a ɗanyarta bata san komai ba na rayu, koda ta sani ɗin wannan kunyar ta hanata iya bayyanawa a gabanka shine ka more alaji. Amma ka aureta kafin ka kai mata kiss ta miƙo maka baki, kafin ka kai hannu jikinta ta sallama maka jikin kaico. Ai yarinya ta dinga jin kamar zata nutse a waje idan kuna tare, koda ta san mi kake nufi ta nuna bata sani ba, duk iliminta duk wayewar zurfin karatunta a gabanka ta maida kanta bata san komai ba shine zaka dinga jinka a wani shauƙi da ƙasaitar cikakken namiji. Ka dinga kallonta tamkar wata baby doll a gabanka, ka koya mata karatunka idan akazo gaɓar da zata goge sai akai matsayar da ita zatai maka bita. Amma an kawo maka yarinya tana nuna maka ita tasan komai idonta a buɗe suke ai akwai matsala, idan kai wasa ma wata sai ta maka fyaɗe, ko kuma kaita zargin kanka da ita kodai tama taɓa yi ne a waje kafin kai. Dan ko ta kawo maka mutuncinta zuciyarka zatai ta tunanin an ɗan sha minti gaskiya.....
Ƴar karar Maanal ta maidosa hayyacinsa daga dogon tunanin da ya tafi, ƙofar ya kalla, sai kuma ya murɗa handle ɗin a hankali ya tura ya shiga. Daga bakin ƙofar ya hango yanda take kici-kici da riga alamar zip ne ya sarƙafe mata a gashi. Numfashi ya ɗan furzan, sai kuma ya shiga takawa a hankali har inda take, hakan yay dai-dai da tuntuɓe da tai da bakin lallausan carpet ɗin gaban gadon saboda yawon da take ɗanyi a wajen na kici-kici. Riƙota yay jikin nasa, yay mata zobe da hannunsa ɗaya a kan ciki, ɗayan yana ƙoƙarin kaishi ya riƙe hannunta da take kici-kici cire rigar.
A ɗan rikice ta ce, “Na banu waye?”. Sai kuma tai ƙoƙarin sunkuyawa, hakan ya bama ƙirjinta damar kwanciya a tsintsiyar hannunsa dake a saman cikinta. Harga ALLAH ji yay yana neman daburcewa, amma sai ya danne da ƙyar, cikin cije lips da ƙanƙancewar murya ya furta, “Mijinki”.
Dama zuwa yanzu ta nutsu, dan ƙamshin turarensa ya isar mata shi ɗin ne tun kafin ya faɗa. Miƙewa tai tsaye sosai ta tsaya da ƙafafunta. Shima sai ya sauke numfashi a rarrabe ya kamata ya zaunar a bakin gadon shima ya zauna. A mayuƙar kasalance ya shiga zare gashin a zip ɗin. Ajiyar zuciya sosai Maanal ta sauke lokacin da ya gama zarewa rigar ta sauka. Suna haɗa ido ta kauda kai da sauri, ƙasa-ƙasa ta ce, “Thanks you”.
Miƙewa kawai yayi batare da yace komai ba ya ɗauka jacket ɗinsa mara nauyi da scarf dan yasan zuwa anjima kaɗan zasu iya jin sanyi duk da garin Shanghai ba gari bane mai yawan sanyi ya nufi ƙofa. Sai da ya buɗe zai fita sannan ya furta, “Jiranki nake”. Daga haka ya maida mata ƙofar ya rufe. Duk ji Maanal tai babu daɗi, dan ta fahimci kamar a cikin fushi yake har yanzu, bayan kuma ya fara sakkowa lokacin suna a jirgin Nigeria zuwa Qatar, bata san kuma miya ƙara ɓata masa rai ba tunda suka iso. Jikinta dai duk a sanyaye ta ƙarasa shiryawa, dan sam bata son a dalilinta taga wani a ƙunci, kodan ta ɗanɗana zafin hakan taji a shekarun baya oho, tayi ƙyau sosai cikin doguwar rigar atamfar, daka ganta kaga cikakkiyar ba'afirikiya. Bayan tai ɗaurin zarah buhari ta yana gyalenta sannan ta ɗauka handbag ɗinta ta fito. A bakin ƙofa ta ganshi tsaye, ya jingina jikinsa da bango tare da ƙafarsa ɗaya, ɗayarce kawai a ƙasa, sai hannunsa ɗaya jacket ɗinsa ce a saƙale, ɗayar kuma yana latsa waya.
“Na gama”.
Ta faɗa cikin ƙaramin sauti ganin baiko motsa ba duk da tasan yaji fitowarta. Kaɗan ya waiwayo kansa ya kalleta, sai kuma ya ɗauke yana mikewa tsaye sosai ya zura wayarsa a aljihu. Tafiya suka fara yi a nutse, kowa zuciyarsa na tunani daban, har suka gama shanye rabin corridor ɗin sannan suka iso ga elevator. Shine ya danna ya fara shiga, kafin tabi bayansa sannan ya sake dannawa ƙofar ta rufe. Cikin abinda baifi minti ɗaya ba suka iso, ƙofar na buɗewa ta yunƙura zata fita ta tsinkayi shigar lallausan tafin hannunsa a cikin nata. Ciki-ciki kowa ya sauke ajiyar zuciya, sai kuma suka kalla juna a lokaci guda. Fin seconds goma suna kallon junan cikin ido, motsin masu jiran su fito suma su shiga ne ya maido su hayyacinsu, itace ta fara janye nata, kafin shima a slowly ya maida ga mutane biyu dake a ƙofar. Ƴammata ne su biyu, suka wani bishi da kallon ƙurulla, hannun Maanal ɗin ya sake damƙewa suka fice. Dai-dai suna barin wajen ɗaya a cikin ƴammatan ɗaya takai bakinta wajen kunnen ƴar uwarta tai mata gwargwaɗe daya sakasu yin ƴar dariyar shaƙiyanci daya tabbatar da maganar tasu akwai iskanci a ciki. Basu ƙarasa jin abinda suke faɗan ba dan sunyi nisa. Maanal dai jitai zuciyarta ta ƙuntata da dariyar yaran, dan ita yara zata kirasu duk da ta tabbatar bazasu girmeta ba dan suma dai bazasu wuce 20+ ɗin ba kamar ita.
Ganin sun fito a hotel ɗin gaba ɗaya a ƙafa har sun fara tafiya a titi Maanal ta dakata. Shima tsayawa yay sai kuma ya ɗan kalleta. Cike da shagwaɓar da ta saka tsigar jikinsa tashi ta ce, “Wai babu a bin hawa?”.
Idanunsa masu laushi ya zuba mata, cikin wani irin kallo dake mata tasiri a cikin jiki, ganin bashi da niyyar tanka mata sai ta sake narke fuska. Kamar zatai kuka ta ce, “Wai mi akai maka kaketa fushi ne tun a gida?”.
Sosai yanzu kam ya lumshe idanunsa ya sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login