Showing 15001 words to 18000 words out of 218311 words

Chapter 6 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

yace ma Oum ya kamata ta koma kan aikinta, dan shi ba ruwansa idan ta taka doka zai bari kamfani ya hukuntata ne. Hutun kwana goma aka bata, gashi yau suna neman sati biyu. Azumi saura kwanaki bakwai a fara shi kacal. Ita Oum ma tsayawa tai kawai tana kallonsa. Yayinda Maanal tai kamar bata falon ma. Dan tunda ya shigo ta gaida shi ta maida hankalinta ga karatunta, sai shi da Oum ke hirar. Yanzu haka take masa, idan dai ya shigo sashen zata gaida shi, daga wannan gaisuwar ko kallon inda yake bata sake yi komai tsahon zaman da zai yi. Ko kuma tana fahimtar lokacin shigowarsa yayi sai ta koma ɗaki abinta. Wannan abun na cimasa zuciya da ƙona masa rai, amma ya share kamar bai fahimceta ba. Dan ya riga ya sakama ransa daga ita har Aban nata zai iya dasu. Shiyyasa da Oum ta nuna damuwa akan rashi bashi Maanal ɗin zai shiga lallashinta da nuna mata shifa babu komai ta kwantar da hankalinta ta bama Abah dama yay yanda yake so. A ransa kuwa shi kaɗai yasan abubuwan da yake shiryawa.........✍️




_😂Dan Oum mi kake shiryawa? Dan bamu musha mana._








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖8️⃣




______________




.......A ɓangaren Mamy kam ranta fes akan hakan. Burinta ɗaya yanzu shine Maanal ta dawo sashenta da zama kamar yanda ta zunguri Abah da zancen. Sai dai kamar ya yarda da farko sai kuma taji bai sake maganar ba. Ta ɗan bashi kwana biyu ne ta sake zuwa masa da zancen, dan idan ta cika matsawa zai harbo jirgin ta ne kasancewarsa mutum mai tsarta. Ajwaad kuwa data fahimci kauce-kaucen sa zata tattarashi ne ta watsar, akwai gaɓar data tanada masa ne. Sun gama tsara Nuratu zatazo nan gidan tai azumi. Acewarsu mamanta zata shirya ta tafi umrah sai ace Nuratun tazo nan ta zauna kafin ta dawo. Gefe kuma cike suke da alwashin bayan salla da sati biyu koda tsiya-tsiya sai an ɗaura auren Nuratu da Ajwaad idan ba haka ba kuma suyi maganin Oum...
Oho ita bama tasan sunai ba. Duk da bata son haɗin auren Nuratu da Autan nata bata taɓa ji a ranta zatai wani yunƙurin hanawa ba. Fatanta ma ALLAH ya daidaita komai ya canja rayuwar Nuratu ɗin su zauna lafiya da Maanal da shi kansa Ajwaad data san baya son haɗin auren nan. Kai ko Mamy gani take bata so dan haka take nuna mata a zahiri. Da yake zuciyar Oum ɗin a tsarkake take kuma sai bata taɓa bin ƙwaƙwƙwafin Mamy akan komai ba sam...


Yau ta kasance lahadi, dan haka Oum ta samu Abah da batun komawar Maanal aiki gobe idan ALLAH ya kaimu. A cewarta da zaman nan gara ta koma aikin sai ta samu nutsuwa sosai. Da farko Abah shiru yayi, dan sai ya dinga hango ai zuwa office ɗin zai saka Ajwaad yaga ya samu wata dama akan Maanal ɗin ne. Shiru ya ɗanyi na wasu sakanni, sai kuma cikin jinjina kai ya ce, “Okay zan yi tunani akan hakan”.
Miƙewa Oum tayi tana masa sallama, dan har yanzu basu koma dai-dai da Abah ɗin ba. Ta dai daina fushin da take yi da shi. Da kallo kawai ya bita yana murmushi da girgiza kansa. A ransa yace (Fatete na rigima kenan) da murmushin Oum ɗin Mamy dake da shi yau ta shigo ta samesa. Koda yake tun ma bikin su AA ɗin Oum tace ta bar mata Abah ɗin har sai Maanal ta tare. Hakan ba sabon abu bane ga Oum. Dan haka kawai idan ta bushi iska sai tace ta barma Mamy Abahn na sati biyu koma na sama da hakan. Wani lokacin Abahn ne ma ke gajiya ya balbaleta da masifa yace shi bai yarda ba kamar dai yanda ya sakata kwana a gunsa dole randa yayar Mamy ta kwana a gidan.
Sosai ran Mamy ya sosu da murmushin nasa, wanda tasan akan Oum ɗin ne tunda sun haɗu a waje. Tarasa ya zata raba wannan shaƙuwa da soyayyar, duk da haihuwar da tayi, da kwantar da kai tana musu bauta su duka biyun har yanzu Oum ta fita matsayi da girman iko a wajen Aliyu. Sam baya iya ɓoye ƙaunar da yake mata koda a gabanta ne ita Kamila. Baya shakkar yabon Oum ko sanya mata albarka ko yin kwatance da ayyukan alkairinta. Hira goma zaka zauna da shi zai ambata maka sunan Fateema so takwas ne kansa tsaye. Cikin takaici ta haɗiye ɓacin ranta ganin ya juyo gareta, a hankali ta maye fuskarta da sassanyan murmushi cike da makirci take tambayar fitar Oum ɗin wai taga ranta a ɓace. Ikon ALLAH sai Abah ɗin yay nauyin baki yau, dan murmushi kawai ya mata baice komai ba. A ƙasan ransa kuwa hankalinsa na'a kan Oum ɗin ne, buƙatarta yake a jikinsa ƙwarai da gaske, yana kewar sassanyan ƙamshinta da kulawarta a garesa. Badan wai Mamyn bata masa ba ita, kawai dai yana jin na Fateema a garesa special ne. ALLAH shine kaɗai yasan irin son da yake ma Fateema da ƙauna a rayuwarsa, shiyyasa yake kallon al'amarin Ajwaad da Maanal tamkar nashi da Fateema ne. Dan soyayyar yaran gaba ɗayanta tamkar gado ne daga tasu soyayyar, abinda kawai ya banbanta shine shi da Fateema jini ɗaya ne...
Haushin ganin ya tafi zurfin tunanin nasa wanda Mamy tai imanin akan Oum ne yasa ta miƙe ta wuce bedroom ɗinsa. Dan tana fara ganin irin wannan signing ɗin a garesa a duk lokacin da Oum ta bar mata shi take fahimtar ya gundura da ita hankalinsa nakan matarsa. Tasha zargin kodai Oum tana musu hakan ne dama dan wani tarko nata ko shiri, amma idan ta nutsa a bincike sai ta gano sam ba hakan bane ba..
Abah ya jima kafin ya dawo daga duniyar tunanin nashi, sai sannan kuma ya farga babu Mamy. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya ɗauka wayarsa ya tashi ya fita domin kiran ɗan uwansa suyi shawara akan batun Oum ɗin na komawar Maanal aiki. Wato Uncle Mahmud.....


____________★


Kuka bana wasa ba Nurry tasha da jin batun ɗaga bikinta dana AA har sai zuwa bayan salla. Wani irin tsanar Oum da Maanal ta ƙara faɗi da kauri a zuciyarta. Nanfa ta shiga ɗaukarma kanta alwashi kala-kala na gasama Oum da Maanal aya a tafin hannunsu. Dan ta tabbatar kamar yanda taji iyayenta na faɗa makircin Oum ne kawai. Bata sami nutsuwa ba har sai da sukai waya da Mamy da Saheeba da suka kwantar mata da hankali da tabbatar mata aure na nan babu fashi. ALLAH dai ya kaimu bayan sallar da sati guda za'ai ma ba biyu ba.. Sannan a gidan zatai azumi kuma...
Hakan ya ɗan sakata jin sanyi da sassauci a cikin ranta. Harta ɗan saki jiki ta cigaba da harkokinta musamman a media. Harda su tsara write-up ta turama ƙawayenta da abokan arziƙinta cewar biki sai bayan sallah saboda har yanzu ango babu lafiya.....


___________★


WASHE GARI.


Safiyar yau Litinin har Oum ta fidda ran Abah zai bar Maanal ɗin ganin tun jiyan baice mata komai ba. Haka shima AA ɗin baima saka ran komawar Maanal ɗin yau ba. Kawai dai ya tashi da nasa shirin ne. Bayan sallar asuba daga massallaci Abah sashen Oum ya nufa. Kasancewar yasan yanzu ita da Maanal ne a ɗakin ba kai tsaye yake shiga ba. Dan haka yay sallama bayan yin knocking a ƙofar bedroom ɗin sannan ya koma falo ya zauna. Babu jimawa kuwa sai ga Oum ta fito daga ɗakin sanye cikin dogon hijjabin sallarta. Tunda ta doso shi ya zuba mata idanunsa da suke a narke. Itako sarai data san halin kayanta da gejin da yake kawai na haƙuri da rashinta a kusa da shi sai ta basar kamar bata fahimci magiyar da yake mata da idanun nasa ba. Ɗan nesa da shi ta zauna, sai kuma ta ɗan zamo a kujerar kaɗan cike da neman magana ta ce, “Yaya Aliy ina kwana” (haka take kiransa lokacin ƙuruciya). Hararta yay da faɗin, “A'a baba Aliy ba yaya ba. Saboda kina son a faranta ran ɗanki zaki ce dani wani yayan gulma”.
Ƙaramar dariya Oum tayi, amma batace komai ba. Shima fuskarsa da murmushi ya ce, “Kun tashi lafiya?”.
“Alhamdullahi”.
Ta bashi amsa. Kansa ya jinjina cike da gamsuwa. Kafin ya cigaba da faɗin, “Akan maganar ki ce ta jiya. Na bada dama Maanal ta koma aiki, amma da sharaɗin driver zai dinga kaita ba ɗanki ba. Dan bana son wata alaƙa ta haɗasu. Ki kuma gargaɗesa babu ruwansa da yarinyata a office balle ya takurata, na saka securityn da zan san duk motsinsa akan hakan, idan ya karya min doka kuma zan ƙara yawan kwanakin suspension ɗin”.
Murmushi Oum tayi a karo na farko. Hakama AA da yazo sashen sai dai yana hawowa stairs ɗin yaji muryar Abah dan haka ya dakata. Idanunsa ya lumshe, tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Ayya Abah koba security ba. Badai ka yarda taje ba, ai sai abinda ka gani kawai Aban Maanal”. Daga haka ya juya ya koma abinsa domin yin shirin office ɗin....


Oum ma bayan tafiyar Abah ɗaki ta koma tace Maanal tai shirin office Abah ya bari. Duk da zama waje ɗayan dama ya isheta sai taji gabanta ya faɗi. Na farko dai tana jin kunya da tunanin yanda zata kalla ƴan company a yanzu. Dan tasan dai sun gama sanin ita ɗin matar ogansu ce a yanzu. Na biyu yaya rayuwarta a companyn zata kasance a yanzu kuma tsakaninta da mai kamfanin. Tunda a gida ya rasa kowace dama a kanta acan da babu idanun Abah kuma fa?.....
“Ko baki son komawa ne Baby?”.
Oum ya katse mata tunani. Ƙasa tai da kan nata tana ƙaƙaro murmushi. Sai kuma ƙasa-ƙasa ta ce, “A'a Oum. Kawai dai ina jin nauyin ƴan kamfani ne”.
Dariya sosai Oum ta sanya da faɗin, “Oh oh! Har yanzu dai Babyna na nan da wautarta. Ina ruwanki da su bayan yanzu ke oga ce. Matar oga ai oga ce ko. Tsakaninki da su sai girmamawa ai. Dan haka ki kwantar da hankalinki ki riƙe girmanki, ki ƙara ƙwazo da himma akan aikinki. Kiyi abinda ya dace na rike martaba da girmanki domin kare mutincinki dana mijinki. ALLAH yay miki albarka”.
Cikin jinjina kai Maanal ta ce, “Amin”...
Wanka ta shiga, Oum kuma ta fita zuwa kitchen haɗa musu breakfast dan tasan Auta baya wasa da fita akan lokaci, duk da Abah ya kafa dokar ba tare zasu tafi ba tana son Maanal ɗin ta koyi yanayin fitar tashi tunda na ɗan lokaci ne zasu koma fita a taren..


Zuwa bakwai ta kammala komai daya kamata. Ta fito fes da ita cikin Abaya maroon color datai mata matuƙar ƙyau da haska chocolate color skin ɗinta data sha gyaran aure ta sake kwanciya luff-luff. Ga wani ni'imtaccen sassanyan ƙamshi dake tashi a jikinta. Sam batayi wani kwalliya ba a fuskar, iya hoda ce sama-sama sai kwalli da ɗan lips-gloss kaɗan. Dan ko taje girarta ma batai ba. A dining ta zauna kamar yanda Oum ta bata umarni, ta ajiye ƙaramar handbag ɗinta saman table ɗin dining ɗin itama. Dai-dai nan shima AA ya shigo, tun kafin su ganshi mayataccen ƙamshinsa daya gama manne jikinsa da komai nasa ya iso hancinansu. Yayi matuƙar ƙyau cikin Maroon suit shima sai long sleeve shirt fara tas. Harga ALLAH sai da zuciyar Maanal ta ɗan motsa. Amma sai ta dake abinta tama fara ƙoƙarin zuba abincin a ranta tana ƙunƙunin (wayace ya sake airin kayanta)
“Auta har an fito?”.
Oum ta faɗa dai-dai isowar AA dining ɗin. Kansa ya jinjina mata, tare da kamo hannunta ya sumbata yana mai ɗan bata side hug. Sai kuma a ƙasa-ƙasa ya furta, “Barka da safiya my everything”.
Murmushi Oum ta sake masa, tana mai amsawa da, “Ka tashi lafiya ya ƙarfin jikin?”.
“Alhamdullahi Oumna, ai ɗanki ya warke sarai in sha ALLAHU ”.
“Masha ALLAH haka muke fata ai Auta”.
A hankali Maanal data ƙi sake kallon inda yake duk da zuciyarta na cike da zumuɗi da maradin hakan ta ce, “Ina kwana”.
Batare daya kalleta ba shima ya ce, “Lafiya”. Daga haka ya kalla Oum a ɗan shagwaɓe ya ce, “Oum yunwa zata cinye hanji na”.
Ƙaramar dariya tayi tana kallon Maanal, itama Maanal ɗin dai-dai ta ɗago ta hararesa. Dan itace ke faɗar haka idan tana jin yunwa. Gira ɗaya ya ɗage mata irin (Ni ɗin kike harara?) sai ta sake murguɗa masa baki sannan ta ɗauke kanta. Ita dai Oum wurin tai ƙoƙarin bar musu tana faɗin, “Bestynka ta zuba maka abincin zanje nayi wanka ne”.
Kamar Maanal zatai kuka tabi Oum da kallo. Sai dai batace komai ba. Sai da ta shige sannan ta ɗauke idanun nata. Tsohon minti ɗaya kafin tace, “Me zaka ci?”.
Shiru kamar bazai amsata ba hankalinsa akan waya. Kamar wadda taji haushi ta ɗago manyan idannunta ta zuba masa. Kaifin idanun nata da tasirinsu a garesa ya sashi kasa jurewa shima ya ɗago lumsassun nasa ya zubasu cikin natan. Bata iya ta janye nata ba suka shiga ma juna kallo mai taushi da kassarasa kuzarin jiki. Lips ɗinta ta sake motsawa a hankali batare data raba idanun nasu ba ta ce, “Nace mi kake so?”.
Cikin kasala da tausasawa kamar baya so shima ya motsa lips ɗin nasa ƙasa-ƙasa ya furta,
“Ke!”...........✍️




_Ehemm-eheem nace ba, 1+1 nawa kenan? An bamu assignment ne a makarantar islamiyyar mu ne ni kuma ban gane lussahin ba😌😣, shine nace bara na tambayeku🫣🏃🏃🏃🏃🏃🏃._








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣




______________




.......Daburcewa taso yi, ta kuma rasa yanda zata fassara amsar ta shi. Cikin suɓutar baki ta ce, “Ban gane ni ba!”.
Wani ɗan iskan gajiyayyen murmushi ya saki a iya lips ɗinsa. Kafin ya sake narke idanunsa dake sarƙafe da nata har yanzu. “Kince mezan ci? Me nake so? Nace KE!”. Ya faɗi (ke) ɗin da wani kalar sanyin murya yana ɗan waro fararen oily idanunsa da ƙyau cikin natan. Ai babu shiri ta janye nata zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Sai taji gaba ɗaya ma jikinta na neman fara rawa. Shi ko tsaf ya fahimci halin data shiga, dan haka ya saki murmushi cike da ƙeta. A ransa kuwa rayawa yake (Ba Abanki yace bazai bani ba sai na horu. Kafin na gama horuwar kema sai kin horu yarinya) a fili kam harɗe hannayensa yay a ƙirji kawai ya zuba mata ido. Ita dai ta miskile tana haɗa masa abincin a gabansa. Can ƙasan ranta luguden daka kawai zuciyarta keyi, jitake kamar ta zura da gudu, amma bazata yarda ta zubar da kanta a garesa ba...
“Ehheem! Ehemm!!”.
Gyaran muryar Fawzan ta maido AA daya zubama Maanal idanu a hayyacinsa. Janye idanun yay luuu ya maida kansa, Fawzan ya ɗage gira yana murmushi. Shima sai AA ɗin ya ɗage masa tasa girar irin (Miye?) ɗin nan. Dariya Fawzan ya sanya, tare da jan kujera kusa da AA ya zauna. Maanal data ɗan rage ɗaure fuskar da tayi ta ce, “Good morning Yaya F”.
“Morning Ƙanwar Yaya F, Baby Oum, Autar Abah, sannan kuma Bastyn Besty”.
Duk yanda taso dannewa bai yiwu gareta ba sai da ta saki murmushi tana turama AA duk abinda ta zuba masa, sai dai bata yarda ta kallesa ba. Sai ma hankalinta data maida kan Fawzan ta ce, “Yaya miza'a zuba maka?”.
“Ai duk abinda kika san yayi daɗi zuba min kawai Lilly.”
Murmushi Maanal ɗin tai tana jinjina kai. Sai da ta kammala zuba masa sannan ta koma cin nata. Suna gab da kammalawa Oum ta fito, duk da Maanal dama ba wani tana ci sosai bane ba. Oum na fitowa ma ta miƙe kamar wadda ke akan ƙaya. Cike da tsokana Fawzan ya hau yima Oum kirari, kafin ya gaidata. Itako tana dariya abinta cike da farin ciki. Sai ga babban yaya da su Naufal dake cikin shirin makaranta. Saheeba biye da su. Suma Oum ɗin suka shiga gaidawa cike da girmamawa, yaran kuma sukaje suka rungumeta. Itama Nibras ta shigo cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login