Showing 213001 words to 216000 words out of 218311 words

Chapter 72 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣4️⃣




______________




.....A yanzu gaba ɗaya hankalin Mamy ba'a kan auren nan yake ba. Dan Sille ya gama rikita mata al'amari gaba ɗaya. Amma dai tana ta ƙoƙarin danne yanayin ta dan bata fatan kowa ya san halin da take ciki a wannan gaɓar. Abinda ya bama Abah mamaki yanda ta sake ba kamar bikin Maanal da AA ba. Amma dai baice komai akan hakan ba.
A ɓangaren Sille kam a yanzu itace mai nemansa a waya ruwa a jallo. Amma abin mamaki kaf layukan da yake kiranta da su bata samunsa. Tun a daren ranar ta bashi 10m daya buƙata, dan ta fahimci zai yi dukkan abinda ya ambata. Amma ta saka ana mata bincike a kansa dama Junaid, duk da ita tafi kowa sanin abinda ta aikata ma Junaid ɗin. Amma hankalinta yaƙi kwanciya sam. Tana son fita a gidan tana tsoron idon mutane, wani gefe na zuciyarta kuma na tunatar da ita idan ma ta fita ɗin ina zata samo Sillen. Tunda shi dai ba wani waje da yake zaune ta taɓa sani ba. Haka dai ta daure tana sauraren sakamakon binciken data saka anai mata akan Junaid.....


________★


A washe garin da za'a iso da Najma da ƙyar Oum ta lallaɓa Maanal sukaje saloon. Wankin kai kawai ta yarda akai mata, kitso sai ta sakama Oum kuka. Ƙyaleta tayi suka dawo gida akai zaman mata ƙunshi ja da baƙi. A lokacin su AA da zasu ɗakko Najma nata shirin wucewa. Ya shigo sashen Oum ɗin cikin tsokana yace mata saura kitso ta sanya masa kuka. Ita Oum ma sai abin ya bata dariya, ta dai gimtse batai ba. Sai ma ta harari AA da shima yake danne dariyar da ƙyar.
“Yanzu dan ALLAH Auta banda neman faɗa ina ruwanka. Munce maka muna son kitso ne.”
AA dai ya sake danne tasa dariyar da ƙyar ya ce, “ALLAH ya baku haƙuri Oum nayi shiru. Bani keys ɗin in dai nine yanzu zan yi gaba”. Oum na bashi maimakon ya tafi da arziƙi sai ya faki idonta ya duƙo ta bayan kujera saitin kunnen Maanal ya raɗa mata magana”. Tare da sumbatar wuyanta. Kafin ta juyo ya fice, cikin ɗaga murya Maanal ta ce, “Sai na rama kuma zaka dawo ai”. Mai ƙunshi dai abin nasu sai ya bata dariya da birgeta. Dan daka gansu kaga ma'auratan dake matuƙar son juna....


_________★



A Zaria su Ammie sune amarori ƙirjin biki. Amarya Najma tasha gyara ɗan gaske ciki da waje sai ɗaukar idanun mai kallo takeyi. Dan Ammie babu wasa sai da ta fidda ƴar tata Masha ALLAH. Ƙamshi kuwa ba'a magana, dan bayan nata gana Hajiya Shuwa. A jiya Ammie ta maidata Zaria. Anyi kamu a jiyan da yamma, yau kuma suke ƙunshi da safe. Da yamma aka fara yinin bikin Hajiya Majdiya.
Gaba ɗaya ran kishiyoyinta su Maman Yaseerah a ɓace yake. Suma su Yaseerah dai ƙiri-ƙiri ƴan ubancinsu ya kasa ɓoyuwa akan shagalin bikin Najma ɗin. Dan sun san dai kam ta kere musu fintin kau kamar yanda uwarta ta kerema iyayensu a komai. Balle kuma ita Yaseerah zuwa yanzu tasan minene family ɗin Darma. Randa aka kawo lefen Najma habaice-habaice sukaita saki. Kallon inda suke Hajiya Majdiya batai ba balle kuma su Ammie da ke tsaye akan komai. Hajiya Basariyya kam ai ji take ina bashi yiwuwa, koda tsiya-tsiya sai ta kaso auren Huznah ta shiga wannan family na Darma. Sai kuma tura su Madeena ƙannen Huznah ɗin take cikin yaran family ɗin Darman wai suma ko sa samu mazan aure. Abin ya ba Maman Yaseerah haushi ta hau Hajiya Basariyya da masifa amma saita ƙi kulata. Dan ita lissafinta daban dana Maman Yaseerah a yanzu....


Bayan la'asar kaɗan tawagar su AA da abokan Yaya Fawzan suka isa Zaria. Zuwa lokacin an gama shirya amarya Najma dake ta shan kuka tsaff cikin lafaya. An kaita gaban iyaye an mata nasiha. Lokacin da aka kaita gaban Hajiya Majdiya suyi sallama sai kawai ta rungumeta tana kuka mai ban tausayi, ita ko Hajiya Majdiya ta dake abinta, acewarta ai Najma gida zataje minene na ɗaga hankali. Kuma itama dai gobe nan da safe zata wuce Abujan dan ai bikin su babban Yaya da ita. Da ƙyar Ammie ta cire Najma a jikin Hajiya Majdiya aka fito da ita. AA da RK ne zasu ɗauki amarya, ga Ammie itace riƙe da amarya ita da Aunty Rufaidah.
Kunya ta kama AA, dan yanzu wani nauyin Ammie yake ji na musamman. Ko a waya ya kirata yata sum-sum da murya kenan. Itama dai Ammien nauyin nasa take ji. Cike da shaƙiyanci RK ya ce, “Babbar magana, suruki zai ɗauki suruka a mota”.
AA dai bai kula shi ba, dan su Ammie sun riga sun kawo gab da su. Itama kuma sai a lokacin ta farga da shi. A zuciyarta tace (Ya subahannallah ya akai haka) a fili kam ta daure ta saka Najma a motar. Har inda yake AA yazo ya rissina yana gaisheta. Ta amsa masa da kulawa da tambayar yaya hanya. Yace Alhmdllh. Haka dole ta shiga motar, ya rufe mata murfin da kansa sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver dan RK ne ya kawosu, yanzu kuma yace bazai maidasu ba ya gaji sai dai AA ɗin ya tuƙa. Haka dole ya amsa dan Ammie da zata kasance a motar, sai kuma alƙawarin da yay ma Yaya Fawzan na shi zai kawo masa Najma har gida. Yana ƙoƙarin yima motar key kiran Maanal ya shigo masa. Sai da ya saci kallon Ammie da hankalinta ke akan lallashi Najma dake a jikinta sannan ya ɗaga kiran. Ƙasa-ƙasa dan AA ya iya munafuncin magana a ƙasan maƙoshi ya ce, “Zuciyar Ajwaad yaya ne?”.
Daga can a shagwaɓe Maanal dake hammar barci hayaniya ta hanata zama sashen Oum ta gudo sashensu duk da nan ma cike yake da ƴammata ƙawayen Maimoon da aka taho da su daga Kano, amma da yake a ƙasa suke babu wanda ya hau mata sama sai ta haye saman ita. Tace, “Kun taho?”.
“Uhm-uhm! A nan zamu kwana”.
Ya faɗa cikin tsokana. Muryar Maanal harta fara rawa ta ce, “Kwana fa?”.
Murmushi yayi jin za'a fara masa kukan shagwaɓar. Cike da lallashi ya ce, “Wasa nake, ga amarya nan ma a mota yanzu zamu taho”.
Ajiyar zuciya ta sauke, tare da sakin hamma. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Barcin ne?”.
“Uhmm”.
Ta faɗa can ƙasan maƙoshi. Murmushi yayi, zai faɗa mata tare suke da Ammie yaji ta fara sauke numfashi alamar barcin ya fara ɗaukarta. Wayar kawai ya katse ya tada motar. Sai suka haɗa ido da RK. Kallon da yake masa na shaƙiyanci ya sashi hararsa kawai ya ɗauke kansa. Haka suka ɗakko hanyar Abuja da amarya gwanin sha'awa. RK da Aunty Rufaidah ne kawai ke hira a motar. Ammie nauyin kasancewar AA da shi kansa ma RK ɗin ya sata yin shiru. Haka shima AA ɗin tuƙinsa kawai yake. Duk da dama bamai yawan magana bane ba kowa ya sani.
Duk da uban gudun da sukai basu shigo cikin Abuja ba sai gab da sallar isha'i. Dan ma sunyi dabarar bi ta jere ne suka fito ta dutse. Maanal nacan na shaƙa barci bata san mi akeyi ba. A ƙofar sashen Oum AA yay parking. Auntyn su Mamy da a yammacin nan. Ta iso, kuma a sashen Oum ta sauka wannan karon ita ce ta fito ta tarbi amarya Najma ta nuna kara ma Oum. Aiko hakan da tai ya saka kowa jin daɗi sosai, hatta AA sai da ya murmusa. Oum kam Ammie ta rungume cike da jin daɗi, AA ya bisu da kallo yana sauke ajiyar zuciya. Ƙaunar dake a tsakanin Ammie da Mamy dabance a rayuwa. ALLAH yayi wannan haɗin kam.
Ya matuƙar gajiya, ga Maanal na ransa dan tunda bai ganta a ƴan tarbar Najma ba yasan tana can tana barci. Sashen nasu ya wuce, ƙawayen Maimoon na falo duk da wasu sun fita saboda shigo da Najma sai ɗai-ɗai da akaima ƙunshi bai ƙarasa bushewa ba yana shigowa sukai ɗif. Sai kuma suka shiga gaisheshi da masa sannu da dawowa. Hannu kawai ya ɗaga musu ya haura sama ko kallon basu isheshi ba. Yanda Maanal ta hana kowa hawo musu sama ba ƙarin daɗi yay masa ba, sai ya ƙara fahimtar Bestynsa nada hankali. ACn data ƙure a ɗakin ya kashe gaba ɗaya, yayi yayi ta daina hakan taƙi, sai dai idan ya shigo ya kashe. Ya matsa gaban gadon yana kallonta, tayi luf a cikin duvet tana sauke numfashi a hankali. Gently yakai zaune gefenta, tare da shafa kanta sai kuma ya duƙa ya sumbaci idanunta da lips ɗinta. A hankali ta motsa, sai kuma ta buɗe idanunta dake cike da barci ta zuba masa kamar ƴar maye. Murmushi ya sakar mata mai sanyi, cikin raɗa ya ce, “Wakey wakey, beautiful”.
Murmushi ta sakar masa, cike da kasala takai hannu ta shafi fuskarsa. Cikin muryar barci da shagwaɓa tare da tasowa ta dawo jikinsa ta ce, “Not yet, I'm still sleepy. Ƙamshinka ne ya tashe ni”.
Murmushi yayi sosai, tare da kaiwa kwance ya sakata a cikin jikinsa sosai ya rungumeta. Sai kawai ta matso da fuskarta gab da tashi, idanunta a lumshe alamar barci sosai ne a cikinsu ta ɗaura lips ɗinta kan nashi. Babu musu ya amshe dan dama yau gaba ɗaya rowa ake masa. Rabonsa ma da ita tun jiya da safe.........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣6️⃣




______________




....Ba ƙaramin narkewa Hajiya Basariyya data biyo ƴan kawo amarya tai ba da ganin gidan Darma. Yo ashe ma yara sun rage mata abubuwa da yawa kenan a labari. Tirƙashi lallai wannan fa shine ake kira da wani baban wani, wani ma kakan wani. Gefe kuwa yanda kowa ke nan nan da Ammie tun a Zaria ke bata mamaki da shakka. A zuciya sai ayyanawa take (wannan shegiyar mata akwai iya asiri, ita ko ina kowa dai sonta yake). Tana zagin Ammien amma tana nane da ita har bedroom ɗin Oum. Oum dai batace komai ba, amma a zuciyarta ta ƙudiri dole ne Hajiya Basariyya ta basu waje dan hirar zuminci zasu sha da ƙanwarta (Ammie).
Hajiya Basariyya dai nata baza ido taga Maanal amma shiru. Tadai kasa haƙuri sai da ta tambaya a kaikaice.
Murmushi Oum tai da faɗin, “Wannan kam inaga barci take yanzun, dan tun ɗazu da suka gama cin abinci da Mah-mah bayan an gama mata ƙunshi ban sake ganin giccinta ba. Amma bari na taɓa mijin naji”.
Ammie na jinsu amma saboda kawaici batace komai ba. Sai ma kiran Shahidah daya shigo mata a lokacin ta ɗaga.....


★ Kiran Oum daya shigo wayar AA ne ya sashi raba lips ɗinsa da na Maanal da ƙyar. Sai da ya ɗan ja sakanni ya dai-daita yanayinsa sannan ya tashi zaune yana ciro wayar a aljihu. Kiran Oum ɗin yay back. Duk da ƙoƙarin kaurara muryarsa da yay sai da Oum tai ɗan jimm da jin yanayinsa. Amma sai ta danne cike da kulawa ta ce, “Halan Baby barci take yi?”.
Maanal ɗin dake lumsha idanu ya kalla, sai kuma ya jinjinama Oum kai tamkar yana gabanta, kafin ya ce, “Eh Oum”.
“Okay to barta karka tasheta, da safe taga Ammien. Ga abinci nan yaro zai kawo maka dan nasan kaima ɗin dai ba sake fitowar zakai ba. Sai da safe”.
Murmushi yayi mai sanyi, ƙaunar Oum na sake ratsa masa zuciya. Sai kuma ya ajiye wayar tare da juyawa yana kallon Maanal. Ai shi ma yasan idan ya faɗa mata Ammie na gidan nan akwai daru, shiyyasa yay gum da bakinsa. Miƙewa yay ya fara zame kayan jikinsa dan ko magrib basuyi ba. Yana ƙoƙarin wucewa bayi kira ya sake shigowa wayarsa. Ganin Babban Yaya ne ya koma ya zauna a bakin gadon yana amsa wayar. Sun ɗan jima kafin su kammala. Cak ya ɗaga Maanal, tana turjewa da kukan shagwaɓar ita ya barta barci take ji bai kulata ba ya wuce da ita bayi. Shi yay mata wankan dan da gaske barci take ji, alwala ma da ƙyar ya samu tayita suka fito. Haka ya taimaka mata ta saka doguwar riga sukai salla. Suna idarwa a nan kan sallayar ta sake kwanciya. Ya girgiza kai kawai yana tashi ya fita. Babu jimawa ya dawo da basket ɗin abincin da Oum ta aiko musu, dan har nan falon sama Salim yazo ya ajiye.
Babu lallashin da baima Maanal ba amma abincin nan bai ciyu ba, iyakarta 2spoon ta saka masa kuka dole ya ƙyaleta. A ransa yana mamakin wannan barci. Gashi komai abin kuka ne a wajenta, abu kaɗan zakaga tana hawaye. Shi kam dai abincin yaci sosai dan yunwar yake ji, sannan ya ɗagata ya maida saman gado ya lulluɓeta. Shima ya canja nasa shirin ya zauna, aiki ya ɗan taɓa sannan ya kwanta da gobe yasan basu da wani isasshen hutu kuma...


Waya da Oum tayi da AA ya rufe bakin Hajiya Basariyya, amma fa a zuciya sai jinjina lamarin take da faɗin (A lallai yarinya ta samu waje. Dan mulki tun farkon daren nan ki shige da miji wai barci. Asiya duniyar ALLAH, ke dai kin dace da boka kam. Kina baza capacity Yaya na bazawa suma. To bari mu sakawa sarautar ALLAH ido muga da safe kuma karfe nawa za'a fito ni Basariyya....


______★


A lokacin da ake bidirin isowar amarya Najma acan, anan sashen Mamy Yaya Fawzan ne yasa akai masa kiran Saheeba sashenta bayan ya gama roƙon Babban Yaya da bashi haƙuri. Naufal ya aika yay kiranta. Tunda ta shigo falon Babban Yaya yana zaune shi da Fawzan suna cin abinci da hira. Gaishesu tai a sanyaye dan gaba ɗaya yau jikinta yayi matuƙar sanyi, ta tabbatar dai da gaske wannan aure babu fashi. Asirin babu irin wanda basu zubaba amma shiru kake ji. Yaya Fawzan ne kawai ya amsa mata. Babban Yaya kam sai ma ya ɗauke kansa. Tana nan zaune shiru har suka kammala cin abincin nasu. Kafin Yaya Fawzan ya maida hankali a kanta bayan yaci serious. Nasiha yay mata mai ratsa jiki, tare da nuna mata muhimmancin zamanta lafiya a ɗakinta koda zuri'a data gitta. Ya nuna mata ita fa kishiyar nan ba wani bala'i bace ba, yanda ka ɗauki zamanta a tare dakai haka zaka sameta, sannan koba komai itace babba a gidan, sai ta riƙe girmanta matansu suma zasu girmamata. Sannan dukkan abinda tayi dashi zasuyi koyi. Yay mata misali da Umma a cikin family, matsayin matar Baba Sardauna take, amma a yanzu itace tamkar uwa ga kowa na family ɗin kamar yanda ake ɗaukar Baba Sardauna uba. Sannan Oum, itace matar Abah dake matsayin ɗa na farko a family ɗin, duk da kamar itace mai bi masa ata biyu dama yanda suka riƙe girmansu yasa kowa ke girmamasu. Babu wani ɗa dazaiyi abu a family ɗin sai da say ɗinsu. Kafin a bari wani abu yaje gasu Baba Sardauna sai idan ya gagari Abah da Oum ne sannan. To itama idan ta gyara ta riƙe kanta a matsayin babba dole haka matansu zasu girmamata. Mamy uwa ce a gareta, huruminta daban. Shi kuma babban yaya miji ne nashi hurumin daban. Sai tasan a yanda zata riƙe matsayin kowa a tare da ita. Abu na ƙarshe haɗin kan iyalansu, itace zata zama tushen wannan, basa son wata fitina ta dinga ɓullowa. Idan har tayi hakan suma bazasu taɓa bari sauran su takata ko mata jayayyaba a matsayinta na babbarsu..
Cikin share hawaye Saheeba ta tabbatar masa da cewar zata kamanta. Za kuma ta kiyaye. Tana kuma roƙonsa ya roƙar mata Babban Yaya yayi haƙuri ya yafe mata bazata sake kwatanta abubuwan da suka faru a baya ba. Yaya Fawzan baiyi ƙasa a gwiwa ba ya juya inda Babban Yaya yake. Cike da girmamawa ya ce, “Babban Yaya ayi haƙuri a yafe mata, kai ne second Aban mu, muna yin koyi da komai daga gareka ne muma. Tayi kuskure amma tayi nadama. Gashi kuma tayi alƙawarin bazata ƙara ba. Kaine ke tausarmu akoda yaushe akan al'amarin mata, to dan ALLAH ayi haƙuri kaima yau”.
Sai da Babban Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login