Showing 24001 words to 27000 words out of 218311 words
Chapter 9 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
arziƙi bata iya tayi ba, tana ji tana gani kuma ya shiga yin yanda yaso da ita batare daya nuna damuwa da hawayen da take ba. Cikin sauƙi da nuna mata mazanfa maza ne yay kiɗinsa yay rawarsa tare da more sadakinsa. Itako tana faman kuka da zaginsa, zagi kuma na rashin mutunci. Nunawa yay bai damu ba, dan ta ceci kanta data kawo mutuncinta, harga ALLAH bai kumayi tsammanin hakan ba daga gareta, musamman idan yay dubi da wayewar yan gudansu ta tsiya. Sai dai kuma mahaifinsu mutumin kirki ne, dan tsaye yake akan tarbiyyarsu babu wasa. Hakama Yazeed yana nasa ƙoƙari kasancewarsa babba kuma namiji. Yaso taimaka mata amma taƙi yarda, dan haka yay ficewarsa yabar mata ɗakin ransa fes.
Kuka bana wasa ba Huznah taci, daga ƙarshe tai kiran wayar Hajiya Basariyya. A lokacin Hajiya Basariyya na zaria tare da ƙawarta cikin wani ƙauye wajen wani malaminsu. Sosai gabanta ya faɗi jin yanda Huznah ke kuka. A rikice tace, “Ke dan ubanki minene zakisa zuciyata ta buga”.
Kasa magana Huznah tayi, sai da ta sake jan wani ƙugin kukan sannan ta ce, “Ummy fyaɗe yamin”.
“Fyaɗe kamar ya?”.
“Wlhy Ummy fyaɗe, ina barci a ɗaki kawai yazo ya haike min, nayi duk yanda zanyi na ƙwaci kaina amma na kasa. Kuma da yake shi tsinanne ne ya fita yana min dariya. Wlhy ji nake kamar na kashe shi Ummi, gashi nan ko tashi na kasa yi wata irin azaba nake ji a jikina”.
Jagwab Hajiya Basariyya ta kai zaune, kafin ta ce, “Amma dai wannan yaro anyi matsiyaci ɗan iska. Munafiki sum-sum da shi. Wlhy Huznah kin cucemu kin cuci kanki. Yanzu duk faɗi tashin da nake na ganin kin baro wannan kurkukun gidan kin koma inda daula take ki huta muma ahalinki mu huta shine kikai saken da matsiyacin yaron nan ya ƙwace abinda shine kimar taki. Yanzu ubanmi zaki kaima AA Darma ɗin to?”.
Kuka sosai Huznah ta sake fashewa da shi mai ƙarfi ma kuwa tana faɗin, “Na shiga uku Ummi, wlhy ina sonshi, bazan iya haƙurin rasashi shi ba. Ki taimakeni ALLAH ba laifina bane ba, kullum rufe masa ƙofa nake kamar yanda Aunty tace nayi shine munafikin ya dawo da rana azzalumi dan ya cutar dani. Ummi dan ALLAH ki taimakeni kada na rasashi.....” kuka ya sarƙeta. Kasa magana Hajiya Basariyya tayi, sai Maman Yaseerah ce ta amshi wayar......
_________★
Mamaki ne sosai ya kama Maanal ganin inda AS ya kawota. Wato sabon Office da aka bata kafin tafiyarta hutu, ita sam tama manta da batunsa. Office ne madaidaici da aka ƙawata aka kuma haɗa mata komai daya kamata da zata iya buƙata. Kujerar zamanta da desk mai ɗauke da computer guda ɗaya, sai visitors chairs dake gaban desk ɗin. Ta gefen damarta haɗaɗɗiyar kanta ce ta show glass da aka shirya kayan buƙata irin wanda mai zane zai buƙata...., Hatta da pensul gasu nan tari-tari kamar a shagon sai dawa. Sai daga ɗan gaba yan kujeru guda biyu suma da visitors zasu iya zama ko ita idan tana bukatar hutawa, daga bayansu akwai fright da wata ƴar kanta ƙarama an ajiye dispenser da coffee machine sai kofuna a cikin glass kanta ɗin na shan shayi dana shan ruwa. Office ɗin a cikin jerin officers na Designers Directors yake. Daga floor ɗin nasu kuma sai nasu oga kwata-kwata dake a floor ɗin ƙarshe. A tsakaninsu ma ba sai ka hau lifter ba su steps ne kawai.
Sallama AS yay mata bayan sake tayata murnar sabon office duk da a waccan ranar duk sun mata. Karan farko tai guntun murmushi tare da amsa masa. Yana fita ta sakama ƙofar key, sai kuma ta jingina a jikinta tana murmushi. Wannan fa shine DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE. Tayi wata biyar kacal matsayin Junior watch designer yau gata a wanan matsayin. ALLAH kaine abin godiya, kai ke maida bawa sarki, kai ke badawa ga wanda kaso a lokacin da kaso. Kai ke sauya al'amura daga wautar tsarinmu zuwa ƙyaƙyƙyawan ikonka. Ya rabbi ka cigaba da jagorantar rayuwata bisa ikonka ba wayona ko dabarata ko tsarina ba...
Takawa ta cigaba da yi cikin office ɗin a nutse har zuwa kujerar zamanta mai laushi da ƙyau tanata sheƙi na sabunta. Sai da tai addu'a sannan ta zauna, ta lumshe idanunta tare da yin wani kalar juyi tana dariya ƙasa-ƙasa. Sai kuma ta tura kujerar jikin desk ɗin sosai ta ɗauka wayarta. Sai da ta duba taga Didi Shahidah da Amaal da Ammie duk a online sannan ta shiga group ɗinsu tai video call. Babu ko ɓata lokaci duk suka shiga yin joining. Sun san da zaman office su duka, amma basu taɓa ganinsa ba. Aiko ta shiga nuna musu komai daki-daki. Sai da aka gama murna sannan Ammie ke tuhumarta miyyasa ta dawo aiki haka da wuri, kwana tara fa kenan.
A shagwaɓe ta ce, “Ammie su Oum ne fa sukace na dawo”.
“Shi Ajwaad ɗin fa?”.
Shiru tai ta kasa cewa komai. Ammie ta ce, “Humm. Maanal nidai zan baki shawara kibi mijinki, abinda ya faru ya riga ya faru, kar kiga Aban Fadeel nata baki kariyar nan kice kin samu damar bijirewa kema. Bance kada kibi umarninsa ba, amma ki ƙyautata alaƙarki da mijinki kinji”.
Sosai idanun Maanal suka cika da ƙwalla. Muryarta na rawa ta ce, “Amma Ammie shike nan komai da yay min yasha ruwa? Har yanzu fa babu wata nadama a tattare da shi. Ganin komai yake tamkar ma dolene a tsakanina da shi. Idan shi dake namiji bai sauke girman kansa ba Ammie sai ni na zubar da kaina a garesa?.”
“Ni bance ki zubar da kanki ba. Amma ki kula da duk abinda zai dinga kasancewa a tsakanin ku. Maanal kawai kinƙi yarda ne, amma Ajwaad ya jima da yin nadama, sannan yana sonki fiye da zaton kowa. Bafa dole sai namiji ya buɗe baki yace ma mace yana sonta bane zata yarda. Irin su Ajwaad a aikace suke nunawa musamman idan akai dubi da yanayin shaƙuwarku”.
Baki sosai Maanal ta tura gaba, “Ammie kawai dai baya laifi ne a wajenki”.
“Oh haka kikace? Shike nan nayi shiru. ALLAH ya daidaitaku cikin sauƙi. Ni bara naje gidan Nene zanje ALLAH ya sanya albarka. Sai a sake riƙe gaskiya a kumayi aiki tuƙuru”.
Kai ta jinjina tare da faɗin, “In sha ALLAHU Ammie”.
Ammie na fita Amaal da Shahidah da suke sauraren faɗan Ammie suka shiga tsarama Maanal abubuwa. Dan suma dai suna goyon bayan kada Maanal ta sake tayi sake har sai ya kwantar da nashi kan. A cewarsu ita Ammie bata san halin mazan zamanin nan ba ZUMA NE SAI DA WUTA. Balle ma irin su AA miskilai ga giyar kuɗi na hura su.
Kiran wayar da akai ya saka Maanal tuna a office take, haka suma su Shahidahn duk suna wajen aiki. Ai babu shiri sukai sallama akan idan sun koma gida ayi zaman. Wayar ta ɗaga, Director Mustapha ne. Bayan sun gaisa yake sanar mata akwai meeting nasu na designers zuwa 12 inji HOD. Yanda yake mata magana da girmamawa sai ma abin ya bata dariya. Itafa su rufa mata asiri suna oganninta bai kamata suna mata haka ba. Maganar aiki daban da matsayin da suke kallonta da shi yanzu. Dan haka ta ɗauki aniyar yin maganar a wajen meeting ɗin in sha ALLAHU.
Ganin akwai sauran lokaci ta fara duba ayyukanta na baya, wanda ta fara bata ƙarasa ba da wanda zatama gyara. Sosai take aikinta a nutse, cike kuma da shauƙi. Akwai aikin da suka fara fa Yaqub, basu kuma kammala ba, tana ganin kafin aje wajen meeting ɗin kuma ya kamata su kammala shi. Kan waya ta ɗauka bayan ta duba cote ɗin department ɗinsu tai kira. Bayan an ɗaga tare da gaisheta batare da tasan wanene ba ta buƙaci ganin Yaqub a office ɗinta, ba kuma tare da jiran amsa ba ta ajiye..
Cike da gulma daga can Zaharadeen ya ce, “Matar boss ce fa da kanta.”
Kusan su duka idanu suka waro, Yaqub ne kawai yay kamar ma bai jisu ba. Zaharadeen ya cigaba da faɗin, “Yaqub kai take nema, dan ALLAH idan kaje ka nema mana damar ganinta, dan ya kamata muje mu miƙa gaisuwa mu taya murna muyi ALLAH yasa alkairi ko ALLAH zaisa ta manta da abinda ya faru baya”.
Miƙewa Yaqub yayi yana mai girgiza kansa. A fili ya furta, “Oh ko kunya ku bakuji ba yanzu ko ita da kanta tace kuzo sai kuje dan neman kusanci da ita”.
“Da gudu ma kuwa. Ko tunani ka kai kaɗai zakaci arziƙin?”.
Cewar Ema..
Murmushin takaici Yaqub ya saki, batare da yace komai ba ya nufi hanyar fita abinsa ɗauke da folder ɗin daya haɗa drawing pappers ɗin daya san zata nema a wajensa. Yana gama ficewa Jameel ya ce, “Ɗan baƙin ciki, idan fa bamuyi da gaske ba guy ɗin nan sai ya kankane komai ta yanda ko kallonmu bazata ringa yi ba balle ta tuna munrayi tare anan matsayin abokan aikinta. ALLAH dai yasa ta manta da abinda ya faru baya. Ni damuwata ma randa ta kamamu muna gulmarta ni da Teemo da Hafiz”.
Caaa kowa yay yana faɗar albarkacin bakinsa. Sai dai duk suna cikin fatan ALLAH yasa Maanal ta yafe musu sudai. Daga haka suka ɗora da gulmar ashe Maanal ɗin tasan abinda ta taka akwai alaƙa tsakaninta da boss shiyyasa take musu girman kai. Gashi nan cikin ƙanƙanin lokaci tazo ta samesu ta kuma shallake abinta matsayin ogarsu. Kai kai wannan al'amari da taɓa zuciya yake..........✍️
_😀 ALLAH ya shirya yan gulma a duk inda suke🤣😂_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣
______________
......A office ɗin Maanal kuwa sai da taima Yaqub magana sannan ya ɗan saki jiki suka ƙarasa aikin a ɗan gurguje saboda lokacin meeting ɗinsu yayi. A tare da shi suka fita a office ɗin. Hakan yay dai-dai kuma da sakkowar AA daga sama, da'alama daga office ya fito. Bayansa CFO ce da Bussines Director. Da alama suma wani abun zasuyi mai muhimmanci, dan elevator suke ƙoƙarin nufa. Wani irin zuba musu ido AA yayi ɗan guntun sakewar dake fuskarsa na ɓacewa. A ransa ko ayyanawa yake, (Yarinyar nan bazata fita sabgar yaron nan ba ko?). A zahiri kam yanda ya wani ɗauke kai sai ka rantse baima gansu ba. Amma ita Maanal tana gannin kallon banzar daya watsa mata na fisha ta ƙasan idon. Amma itama sai ta wani basar kamar bata gansu ba ta nufi hanyar conference room tana cigaba da wayarta. Dan magana take da Amrah data kirata suna fitowa.
Shi dai Yaqub ɗan matsawa yay ya gaishesu. CFO ce kawai ta amsa da Bussines Director. Boss yi yay kamar baiji ba ta shige elevator. Kasancewar shi Yaqub ba kallonsu yake ba bai san yaya boss ɗin yake ba. Sai da suka shige ƙofar ta rufe sannan shima ya nufi conference room ɗin.....
_________★
Rafeeq na zaune Nuwaira a jikinsa tana masa hira amma shi hankalinsa na wani tunani daban. Maganar zuwan Najma Abuja ce keta masa kai-kawo a rai. Kodai zai yi amfani da wannan damar ya sata tai masa wani aiki. Wani gefe na zuciyarsa kuma na farin ciki da fatan tabbatuwar abinda yake hasashe a tsakanin Najma ɗin da Fawzan. Dan auren wani ƙarin GARKUWA ne ga aunty Babba bayan na AA da Maanal. Tun jiya yake son yin waya da Maanal, dan yana son su tattauna wasu abubuwa masu muhimmanci sai dai bai san a yanda zata kalli al'amarin ba. Sannan alaƙarsa da ita kafin aure zai iya saka AA yaji wani abu a ransa idan yaga kiran duk da yasan har abada Ajwaad bazai kawo mummunan abu a garesu ba, amma yana da ƙyau ya kiyaye. To amma a yanzu batun Najma sai ya zaburar da shi, a ganinsa hakan wata hanya ce mai sauƙi da saƙon da yake so zai isa ga Maanal ɗin dan ita kawai yake so a wannan gaɓar tasan hakan saboda ya yarda da ita ɗari bisa ɗari, ya kuma gamsu da tarbiyyarta da soyayyar da takema ƴar uwarsa, soyayya ce irin ta ɗa da mahaifi.....
“Babie!”.
Nuwaira ta kirashi a cikin kunne cike da shagwaɓa. Kallonta yay da sauri, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sakar mata murmushi ya sake jawota jikinsa. Hancinta ya kama ya ɗan ja. “Kefa yarinyar nan shagwaɓaɓɓiya ce. Minene kuma?”.
Baki ta ɗan tura masa. “Bakai ne ka tafi tunani ba inata kiranka bama ka jina. Minene ke damunka wai? Ina lure da kai tun jiya baka da sukuni”.
Sake lakace mata hanci yayi. Tare da faɗin, “Tunaninki nake fa”.
Tai murmushi mai ƙayatarwa. Duk da tasan ba hakan bane cike da farin ciki tace, “Godiya nake Babie. ALLAH ya ƙara mana farin ciki da kwanciyar hankali”.
“Amin my angel, harma da soyayyar juna”. Ya faɗa yana ƙanƙameta a cikin jikinsa. Wata irin soyayyarta na ratsa jini da ɓargonsa. A tabbas har randa aka ɗaura masa aure da ita zuciyarsa Maanal take so, amma ganin halin da suka samu AA ya sake sakashi ɗaukar ɗamarar yaƙi da zuciyarsa akan sadaukarwarsa. Dan ya sake tabbatar da AA ya fisa buƙatar Maanal. Shine kuma ya cancanci samunta ɗin. Koda ya shigo ya samu Nuwaira a ɗakinsa matsayin mallakinsa baiyi wani yunƙuri ko tunanin zasu sami juna ta sauƙi ba, sai dai kuma labarin ya canja saboda karfin tasirin nasihar iyayensu a garesu, gashi shi kuma yana a cikin wani hali na buƙatar abokiyar rayuwa. Cikin ƙudirin samawa kansa sauƙi kawai ya yarda ya tunkareta, sai dai a lokacin da komai ya kankama sai labarin ya canja, dan tamkar ya shiga sabuwar duniya ne da zazzafar soyayyarta. Na biyu haƙurinta da biyayyarta, Nuwaira bata da kwaramniya, ga sauƙin kai da kyakkyawar fahimta. A ɗan kwanakin da suka samu tare ya fahimci hakan sai soyayyarta ta ƙara tasirantuwa a zuciyarsa. Dan haka yake baje kolin amarcinsa yanda ya kamata, itako tana nuna juriya da dattako..
Ɗaukarta yay cak ya nufi bedroom. Zizzilewa ta farayi cikin dariya tana faɗin, “My R please Aunty Rufaidah fa zanje na taya aiki a kitchen”.
“A nan ma ai aikin zakiyi, yama fi na Aunty Rufaidah lada”. Ya faɗa yana tura kai cikin ɗakin da sumbatar goshinta......
__________★
Tattaunawa ce sosai ta kasance a zaman meeting ɗin na su Maanal. Domin abubuwane masu muhimmanci da suke son kawowa na gyara a matsayinsu na artists ɗin companyn. Daga ƙarshe Director Mustapha ya sanar dasu batun da za'aje ƙasar Chaina a kansa. Wadda tun kwanaki CEO ya gabatar, ya kuma bada damar kowanne ɓangare su bada mutane biyu da zasu samu horaswar ta kwanaki goma kacal in sha ALLAHU. To zuwa yanzu kowane department na ƙoƙarin kai nasu, dan haka suma ya kamata sukai nasu ɗin. Dan haka aɗan nazari da su manyan sukayi cikin satin daya gabata, da ayyukan kowa da suka duba da ƙwazonsa sun yanke waɗanda suke ganin sun cancanci zuwa.
Aifa nan kowa ya shiga gyara zama da fatan ya kasance shine. Duk da kuwa wasu a cikinsu an taɓa zuwa dasu wasu ƙasashen akan irin hakan. Dan ba sabon abu bane duk bayan wata shida Company na irin wannan zuwa ƙaro sanin kai da kai ɗin dan ƙaruwar ilimi ga ma'aikatansu. Director Steven ne ya miƙe yay bayanin waɗanda suka samu wannan dama. Wato Maanal Habib Giro da Yaqub Nuhu. Tuni fuskokin su Zaharadeen sun canja, ko tafin da akayi ma da ƙyar suka tafa. Maanal da Yaqub suka nuna farin cikinsu. Duk da ita dai Maanal bata so haka ba. Musamman data tuna maganar da AA ya taɓa mata akan tafiyar. Sai dai tana fatan ALLAH yasa bada shi za'ai ba.
Suna tasowa a meeting ɗin yay dai-dai da lokacin break. Ransu Zaharadeen a ɓace suka wuce. Kowa naji a ransa akwai makirci a wannan tsarin. Dan a ganinsu kawai an zaɓi Maanal ne dan tana matar boss a yanzu, ita kuma ta zaɓi Yaqub saboda suna tare. To aiko lallai zasusha mamaki, dan ko zasuyi amfani da wannan damar akan Yaqub game da alaƙarsa da Maanal ɗin sai yabar Companyn nan da ƙafafunsa. Ai sun san dai boss ba mahaukaci bane ba zuciyarsa ba dutse bace zaiji kishi...
Salla kowa yay ƙoƙarin zuwa gabatarwa. Bayan an idar masu tafiya cin abinci suka tafi, masu komawa office suka koma. Harda Maanal kuwa a masu komawar, duk da yau batazo da abincin nata ba. Hankalinta kwance ta