Showing 180001 words to 183000 words out of 218311 words
Chapter 61 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
ayi tana so, amma tsakani ga ALLAH banda sha ƙundum, dan a tsorace take. Itama kimtsawa tai tayi sallar, tai zaman yin azkar. Tana a wajen har akai sallar isha'i sannan ta miƙe. A gurguje ta gyara jikinta ta canja kaya wanda suka dace dan sashen Oum zasu koma cin abinci.
★Maanal na kammala shiryawa sashen Oum ta wuce. Dan tasan shima ya wuce can tare da su Yaya Fawzan. Ta samesu su duka ukun kuwa a can, Anum na jikin AA yana mata homework. Tana yin sallama da shi suka fara haɗa ido, yanda yake kallonta babu ko kunyar yayunsa yasa ta ɗauke kanta. Cikin girmamawa ta gaida Babban yaya da Yaya Fawzan. Yaya Fawzan sarkin tsokana ya fara tsokanar tata kuwa. Cike da jin kunya tasa hannu ta rufe fuskar tata tana dariya. Dai-dai nan Nuratu da Oum suka shigo, Nuratun najan akwati. Su duka kallonsu suke, banda AA da yay musu kallo ɗaya ta ƙasan ido ya ɗauke idonsa. Yaya Fawzan ne daya kasa haƙuri ya ce, “Lafiya kuwa Oum?”.
Sai da Oum ta nunama Nuratu hanyar upstairs tana faɗin, “Jeki kai kayan sama sai kizo kici abinci”. Sannan ta zauna tana bama Fawzan ɗin amsa. “Faɗa suke da Saheeba acan shiyyasa nace ta dawo nan.”
Cikin ɗan ɓacin rai Babban Yaya yace, “To ta wuce gida mana dole ne sai ta zauna anan Oum?”.
Fuskar Oum da murmushi ta ce, “A'a Fadeel ba ayi haka ba, tunda tana son zama nan ɗin a barta. Kasan Hajiya Turai ba wani zama waje ɗaya take ba. Ga Nuratun ba isashen lafiya ba wazai kula da ita. Su Nana kuma suna nan suma balle ace taje Kano. Kuma muna nan ma ai ba'ace taje Kanon ba koda suna can”.
Babban Yaya dai da alama ba son zaman Nuratun yake ba, haka shima Fawzan sai da ya nuna hakan a fuska. Gwaska AA kuwa ma bai nuna yama san mi sukeyi ba balle ya tanka. Maanal kuwa murmushi tayi babu wani damuwa a fuskarta, amma acan ƙasan ranta ita tasan saboda AA Nuratun tace zata dawo nan ɗin da zama ko kuma akwai dai wata a ƙasa. Shekararsu nawa da Saheeba ɗin faɗan baisa tazo nan ɗin ta zauna ba sai yanzu. Amma babu komai zata iya da su, dan a yanzu kam a shirye take tsaf zata buga da kowa akan mijinta, kuma zata basu mamaki. Dan haka ta turama RK saƙo.
Ganin duk yanayinsu ya canja Oum tai murmushi, cike da kulawa ta ce, “Bana son ku koyi halin daba naku ba, ku manya ne, sai kun gyara na ƙasa zasuyi koyi. Ko'a fuska bana son wani cikinku ya nunama yarinyar nan wani abu mara daɗi. Fawzan bara na kira matarka a waya, itama kwana biyu naga duk ta tsangwami kanta.”
Kafin ma wani yay magana Oum ta fara kiran Nibras a waya. Tana ɗagawa kafin ma tace komai Oum ta ce, “Zo ina nemanki yanzun nan”.
Tamkar dama kiran Oum ɗin take jira zambar ta miƙe, cikin ƙanƙanin lokaci sai gata a sashen. Shi Fawzan ma sai abin ya bashi dariya. Amma bai ce komai ba, baima kalla inda take ba tunda ta shigo. Sai ga Nuratu itama ta sakko, wani kallon harara sukaima juna ita da Nibras ɗin kowa ya ɗauke kansa........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖8️⃣9️⃣
______________
........Koda Nibras ta gaida AA kansa kawai ya jinjina mata amma ko kallon inda take baiyi ba itama. Saima ya miƙe ɗauke da Anum datai barci ya haura sama. Ɗakin Oum ya kaita ya kwantar, Naufal dama yay barci shi tun a massallaci, suna shigowa Fawzan ya wuce da shi saman. Koda ya dawo kai tsaye dining ya nufa yana faɗin, “Besty zoki bani abinci barci nake ji”.
Amsawa tai tana miƙewa, sai da taje dining ɗin ganin babu plates sai ta wuce kitchen ɗakkowa. Fawzan da Babban yaya ma sai suka miƙe. Sai da suka zauna kamar abin arziƙi Fawzan ya ce, “Babban yaya ina da tambaya”.
Babban Yaya da bai san mi za'a tambayesa ba ya ce, “Uhum ina jinka”.
Sai da Fawzan ya ɗan kalla AA sannan ya ce, “Dama ango na barci a farkon dare dan ALLAH?”.
Kallon AA dake hararar Fawzan Babban Yaya yayi, cikin son riƙe murmushin dake neman kufce masa ya ce, “Nikam ka tambayeni, tambayi Auta maybe shi yana da amsar baka”.
Dariya Fawzan ya tuntsure da ita ganin shima dai yau Babban Yaya ya ɗana. Cike da neman son ƙure AA ɗin Fawzan ya ce, “Auta ance na tambaye ka, dama ango na barci a farkon dare?”.
Waya AA ya ɗauka yana dannawa batare da ya bashi amsa ba, minti ɗaya ya ajiye wayar yana wani makirin murmushi da kallon Fawzan, sai kuma ya ɗage gira sama ya ce, “Ka duba na tura maka amsar”.
Wayar Yaya Fawzan ya ɗauka. Idanu sosai ya waro akan AA, sai kuma yace, “A lallai Auta kaci wake, ni ka turama wannan abun?”.
“Naga amsar da kake nema kenan?”. AA ya faɗa ciki-ciki.
Babban Yaya dake murmushi Yaya Fawzan ya kalla baki buɗe. Sai kuma ya miƙa masa wayar yana faɗin, “Kalla fa abinda ya rubutan Yaya”.
Fitt AA ya ɗauke wayar yana harararsa.
“Oh ashe ma kai ƙaramin mara kunya ne, ka bari Babban Yayan ya gani mana”. Fawzan ya faɗa yana dariya.
Isowar Oum dining ɗin ya samawa AA lafiya a wajen Yaya Fawzan. Sai ga Maanal ma ta dawo. Suma su Nuratu duk suka zauna. Daga nan tsokana ta ƙare akai zaman cin abinci. Bayan sun kammala sun koma falo su Inte suka gyara wajan. AA dama shi bai zauna ba, sallama yay ma Oum da babban Yaya, ganin Maanal bata da niyyar tashi ya zuba mata ido. Itako ta fiske. Oum na lure da su, sai kawai tai murmushi ta kalla Maanal, babu wasa tace, “Oya Baby tashi kuje sai da safe”.
A kunyace Manaal ta miƙe. Fawzan ya ce, “Auwwwwwn! Lillyn Babban Yaya ƴammata”.
Ai da sauri ta fice tana murmushi. Oum da Babban Yaya sukai murmushi suma. AA kam hararar Fawzan yayi da faɗin, “Girma dai ya faɗi”.
Yaya Fawzan dake dariya ya ce, “Naga kai a jaka ka zuba naka ka ɓoye”.
Sarai AA ya fahimci abinda Yaya Fawzan ya ke nufi, sai ma ya rasa abin cewa ya murmusa kawai yana ma Babban Yaya da Oum sai da safe yabi bayanta. Sai da suka fara zuwa sukama su Mamy sallama. Har sun miƙe Mamy tace ya zauna zatai magana da shi. Jin hakan yasa Maanal fitowarta a ɗakin, AA ya bita da kallon ƙasan ido. Mamy dake lure da shi ta sake ɗaure fuska zuciyarta na zafi. Cikin dakewa ta ce, “Gobe ka sayama Aunty ticket zata tafi”.
Da mamaki ya kalleta, sai kuma ya daure yace, “Baki gama warkewa ba fa Mamy miyasa zata tafi bayan itace mai ƙoƙarin kula da ke?”.
“Ni nace da kai ban gama warkewa ba? Baga Nana nan da Saheeba ba kuma”.
Ɗan jimmm yay na sakkani, sai kuma ya ce, “Shike nan ALLAH ya kaimu goben.”
A daƙile ta ce, “Ina maganar mu ta tsaya ta documents ɗinka?”.
Yanzu kam kasa jurewa yay sai da ya ɗago ya kalleta da ƙyau. Ganin yanda ta zuba masa ido sai ya ɗauke nashi. Baya buƙatar wani abu da zai ɓata masa wannan daren, dan haka ya miƙe yana faɗin, “In sha ALLAHU zan kawo miki ina kan tattarawa.”
“Hummm! Ka cigaba da raina min hankali zan baka mamaki. Kuma yarinyar nan bana buƙatar sake ganinta ta shigo dubani”.
Murmushi yayi mai ƙuna, cike da girmamawa yace, “In sha ALLAHU bazata sake zuwa ba kiyi haƙuri”. Ya nufi ƙofa abinsa ya fice. Ya yi tunanin Maanal ta wuce, sai ya sameta suna hira da Aunty a falo sunata dariyarsu hankali kwance. Su dukansu basu da wata shaƙuwa da dangin Mamy saboda ba wani shiga sabgarsu suke ba, badan suna talakawa ba ne, kawai dai tun farko Mamyn ba zuwa take dasu sabgohinsu ba, koda yake itama bason shiga take ba sai ta zaɓa, a karo na farko yaji Auntyn ta shiga ransa yau, dan duk wanda yaso Maanal da Oum to shima zai so shi kuwa. Sai da ya gama kallesu sannan ya ƙarasa in da suke. Miƙewa tai sukaima Auntyn sallama suka wuce, ta bisu da kallon sha'awa, a karo na farko taji haɗin nasu ya mata dai-dai kuma ya birgeta....
Ta riga shi haurawa sama, ya tsaya kashe wuta da rufe ƙofa, lokacin da yake iskota ɗakin hatta shiga bayi tana yin brush. A haka ya shigo ya sameta. Tsayawa yay ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallon ta kawai. Ta cikin mirror ɗin ta zuba masa ido itama. Sai kuma ta ɗage masa gira alamar (kallon fa). Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, ya cigaba da kallonta kawai. Bayan ta kammala ta saka masa makilin ɗin a jikin nasa brush ɗin, ta matso gabansa, hannunsa ta kama ta saka masa brush ɗin sannan tai ɗiɗɗishe ta hure idanun, “Kallon ya isa haka”. Ta faɗa tana zagayesa ta fice. Da kallo ya bita, sai kuma ya saki ɗan murmushi mai sanyi. Ya matsa jikin mirror ɗin kawai ya fara brush ɗin shima. Kafin ya fito harta shirya cikin kayan barci ta ƙarama jikinta turaren Hajiya Shuwa. Sai dai yau kala uku kawai ta sanya dan Hajiya ta gargaɗeta sosai. Sai dai duk da haka bata gane ma'anar turaren ba. Ta gama shiryawa tana gaban mirror tana warware gashinta ya fito. Gaban mirror ɗin yazo shima ya tsaya a gefenta, kamar yanda yay a bayi yanzu ma hannaye ya harɗe ya wani ɗan jingina da katakon mirror ɗin yana kallon yanda take yamutsa fuska, dan a duniya Maanal fa ta tsani abinda zai taɓa mata kan nan koda itace da kanta. Jin idanun nasa sun mata yawa a jiki ta juyo tana kallonsa itama. Sai kuma ta tura baki cike da shagwaɓa da jin zafin taɓa kan da take ta ce, “Wai mi kake kallo?”.
Cikin ɗan motsa lips kaɗan ya ce, “Matata mana”.
“Tana ina?”.
Ta faɗa tana waigawa gefe-da-gefe like tana neman matar tasa. Wani miskilin murmushi ya saki yana kauda kansa gefe da cije lips kaɗan, sai kuma ya sake maido dubansa kanta ya wani bita da kallo tun daga ƙafafunta har zuwa saman fuskarta. Sake ɓata fuska tai tana harararsa, yay murmushi, cike da son sake kunnata ya kai hannu ya shafa gashin nata da faɗin, “Ya kamata ama gashin nan kitso, dan yafi ƙyau”.
Rau-rau ta kallesa idanunta cike da hawaye ta ce, “Ni ALLAH bana so. Kai ka cika tada zaune tsaye”.
Cikin ɗan waro idanu ya ce, “Yanzu Besty kitson ne tada zaune tsaye? K dan baki san kitso na miki ƙyau bane ba....”
“Ni dai bana so”.
Shiru bai sake cewa komai ba ya zuba mata ido kawai. Sai kuma taga kamar yay fushi. Juyowa tai riƙe da cumb ɗin tana kallonsa. Sai ya ɗauke kansa gefe. Yatsa tasa tana ɗan takalar hannunsa dake harɗe a ƙirjinsa har yanzu. Irin ɗan gocewar nan yayi kamar yara na fushi ana son lallashinsu, ta ƙara takalarsa, ya sake gocewa. Sai itama ta haɗe fuskan ta kauda kanta. Fuuu ta yunƙura zata bar wajen ya riƙota da sauri.
Fisgewa take ƙoƙarin yi yaƙi barinta. Cikin ƴar shagwaɓa ta ce, “Ni ka sakan, ina maka magana ma kana min wulaƙanci danma kaga ina kulaka zaka wani mun fushi”.
Tsayar da ita yay a gabansa yana wani binta da kallon ƙurulla, cikin muryarsa data fara canjawa saboda yanayin daya fara shiga ya ce, “Ni nace ina fushi ne, kawai na tafi wani tunani ne daban.”
Yanzu kam nutsuwa ta ɗan yi tana kallonsa ta ce, “Nami to?”.
Sai da ya ɗan ja mata hanci sannan ya ce, Naki mana”. Ya ƙare maganar yana binta da ɗan iskan kallon daya bata kunya. Matsawa tai daga kusa da shi tare da faɗin, “Haramm irin wannan kallon baida ƙyau ALLAH”.
Haka kawai ya tuna randa ta masa bore a asibiti, murmushi mai haɗe da ƴar dariya ta kufce masa. Sai ta tsaya tana kallonsa tare da sake ɓata fuska. “To miye na min dariyar?”.
Cikin son danne dariyar da tsiya-tsiya yay zipping bakinsa da faɗin, “Na bari na bari. Kawai na tuna randa kika min rashin m ne a asibiti. Kai yarinyar nan idan kika birkice kina da wahalar sha'ani dan darunki bala'i ne, ranar kinfa kunna ni fiye da yanda kike zato, tsabar ɓacin rai kwana nai ban barci ba. Rafeeq kuma ya sake tunzurani a washe gari, ai ko kaɗan ya rage na fasa masa baki”.
Dariya Maanal ta shigayi, ta ce, “Kai jama'a ban taɓa ganin ɗan daya raina kawunsa ba irin ka, nima ɗin ka kunna nin ai, dan ji na dingayi kamar na faffaleka da maruka, dama ina ciki dakai sosai ta yanda ka ke wani basar da ni like bama ka taɓa sani na ba. Sai kuma kazo ranar kana wani min gadara kai miye-miye, harda wani cewa ba mai shiga gonar da ka shiga, idan na auri wani zaka min fatalwa ne ma ko mi kace... Hummm da gaske fa baka da kirki Besty”.
Hannunsa ɗaya ya cire yakai shi saman fuska ya shafo gemunsa. Yana binta da wani kallo mai ƙarfi da laushi, sai kuma ya saki murmushin “Humm bazaki gane ba ne.....”
“To ganar da ni”.
Tai maganar tana ɗan hararsa. Matsowa yay jikinta sosai ya mannata da mirror ɗin, ya kamo hannunta ya zare cumb ɗin. Sai kuma ya ɗagata cak ya ajiye saman katakon mirrorn ya cigaba da taje mata gashin a hankali. Amma duk da hakan sai da ta riƙe hannunsa tana yamutse fuska kamar zata saki kuka. Daina tazan yay ya tsaya yana kallonta, ta sake cuna masa baki gaba da faɗin, “Besty! Wai mata basa aski?”.
Dariya sosai ta bashi amma baiyi ba. Sai ya sumbaci bakin kaɗan yana kallonta gira a ɗan ɗage.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣0️⃣
______________
.........“Ke yanzu idan akace kiyi aski sai kiyi?”.
“ALLAH da gudu ma”.
“Ai da yake baki da man kai”.
“Eh naji ɗin banda shi, kai baka san zafin kitso bane”.
Cikin wani shegen salon iskanci da iya shege ya sake narke idanunsa cikin nata. A yanyin raɗa ya furta, “Duk zafinsa ya kai DAREN AIKAIRI ne”.
Wani kunya ne na bala'i ya lulluɓe Maanal. Da sauri tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. “ALLAH baka da kunya. Nifa ƙanwarka ce”.
“Da an shigo cikin ɗaki nake tashi daga Yaya ai, dan haka ni ba yayanki bane yanzu.”
Ƙoƙarin tureshi tai zata sauka ya riƙeta yana dariya. Sai kawai ta kife kanta a ƙirjinsa. Murmushi yake mai ƙayatarwa, sai kuma ya samu damar tufke mata gashin nata a hakan. Yana gamawa ya kamata cak ya sauke a ƙasa. Aiko fitt tabar masa wajen. Bai dakatar da ita ba ya fara ƙoƙarin cire kayansa kawai domin canjawa zuwa na barci..
Maanal kam data gudu haye gadon tai ta kwanta, sai kuma ta ɗauka wayarta. WhatsApp ta shiga tana ɗan duba sakwannin, dan shi kaɗai take yi, bayan anan bata da account a kowanne shafi na media sai dai ta shiga ta ɗan yi kallon abu buwa a TikTok da Instagram tunda bata saye bata sayarwa,