Showing 210001 words to 213000 words out of 218311 words

Chapter 71 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

ya kuma san alaƙar Kamila da Fateema ta asali. Na barki lafiya mahaifiya”....
Iya kwatanta muku Mamy a cikin tashin hankalin da take ciki abu ne mai wahalar gaske, kawai dai kowa ya ƙiyarsta a ransa, dan kuwa Sille ya tafi ya barta a wani irin mummunan yanayi ne mara kwatankwacin kintace. Binne sirri mai girma irin haka a kai kaɗai batare da kowa ya taɓa sani ba, sai bayan tsahon shekaru kwatsam wani yazo yace maka shine wannan sirrin naka, har ya labarta maka exactly abinda ya faru a shuɗaɗɗen yanayin, bayan kayi imanin babu wani mahaluki daya ganka, tunda gashi har tsawon shekaru babu wani daya taɓa kwatanta maka ya sani ko'a fuska, shi kuma wannan yaron jariri yake sabuwar haihuwa da baya magana baya gane komai ai ruɗanin bashi da kwatankwaci. Yo ko gulma kayi da miji ko ɗa ta fita ya kake shiga ruɗanin mamaki balle irin wannan na Mamy, ai sai ka rasa ina zaka kama ina zaka riƙe ma gaba ɗaya. Ga zancen Sille ya tabbatar mana akwai alaƙa tsakanin Abah da Junaid ubansa, kenan dai akwai AJIYA A DUHU tsakanin amintakar Kamila da Oum ma tun asali tun fari. Babbar magana. Kumuje zuwa kudai, sannu a hankali komai zai warware kansa dai....


____★

Motar AA dake dawowa gida na shigowa gida Sille na ficewa. Da mamaki yake kallonsa, duk da ba fuskarsa ya gani da ƙyau ba kamar a gidan Hajiya Turai. Amma gaba ɗaya zubin mutumin da wata tafiyar rangajin tantirai da take bata mai ba. Kasa haƙuri yay sai da ya tambayi maigadi wanene?.
Kai tsaye maigadi yace, “Ranka ya daɗe mai gyaran ruwa ne. Pipe ne ya fashe a sashen Hajiya ƙarama shine ya gyara.”
Jimmm AA yay yana kallon Sille da yay nesa da gidan kaɗan ta cikin mirror ɗin motar, a ransa yana jinjina kalmar mai gyaran ruwan ƙwarai da gaske. Dan zubin mutumin sam bai masa kama dana mai aikin arziƙi irin wannan ba. Amma sai bai takura ba yaja motar ya shige ciki. Tarkacen daya sayoma ƴar rigimarsa ya ɗiba ya wuce sashensu. Samunta yay tana barci anan falon inda ya barta, ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kai. Kitchen ya wuce da kayan ya ajiye komai a inda ta dace, sannan ya dawo ya kwashe abubuwan data baza na ciye-ciyen da tayi suma yakai kitchen ɗin ya ɗauraye na wankewa ya ajiye na ajiyewa. Koda ya dawo ɗaukarta yay gaba ɗaya ya haura sama da ita. Dan yasan wannan kuma barcin in sha ALLAHU ita da farkawa sai kusan sha biyun dare, koda yayi barci shima sai ya tashi saboda wanka kawai take yi da salla tazo ta kanannaɗe jikinsa. Tana samun yanda take so zata sake komawa barci. To daga fa sallar asuba kuma bazata sake kwanciya ba sai wata yammar kamar wannan, idan kuma anyi sa'a ta daure yanayin magrib zata kwantan. Oum ma data fahimci yanayin nata ko nemanta batayi idan yamma tayi taji shiru. Wani lokacin kuma acan sashen take barcin sai sun gama hira da cin abincin dare yake ɗakkota su dawo nan..


______★


Washe gari tunda wuri ya mata wayo suka bar gidan zuwa MAWAAD. Ta haka ne ƴan kai lefe suka tafi lafiya bada saninta ba. Lokacin da suke dawowa gida bayan la'asar kuma sama-sama ta gaida Oum ma ta shige bedroom ɗinta ta kwanta sai barci.
Da daddare sunyi zaman cin abinci Babban Yaya ke tambayar Lilly fa? Dan tun jiya rabonsa da ganinta a gidan, kwana biyun nan kuma ya fahimci Nuwaira da Oum ke girkin dare banda Maanal ɗin. Oum ta ce masa tana barci a ɗakinta tunda suka dawo aiki. Dan ko sashensu ma bataje ba. Mamaki ya kama Babban Yaya, yace, “Bata da lafiya ne? Barcin yamma haka”.
Kafin Oum tai magana Yaya Fawzan da bakinsa baya iya shiru ya ce, “Anya Babban Yaya Lilly na lafiyar nan kuwa?. Barci dai barci dai maybe akwai malaria tare da ita”.
RK dake danne dariyarsa da ƙyar yay fuska da faɗin, “Sai fa malaria ɗin. Saurayen ne na yanzu ɗika-ɗika, da sun ciji mutum kuma sai ciwo ba sauƙi. ALLAH dai ya ƙaremu da lafiya”.
Harga ALLAH Oum bata gane shaƙiyancin RK ba. Kai shi kansa Yaya Fawzan bai hasko komai ba sai da yaga babban Yaya yayi wani miskilin murmushi kawai. AA ma da bai fahimta ba da farko ya ce, “Inaga ya kamata ai feshi a gidan nan gaskiya. Dan ɗan zaman da mukai jiya a waje nima sai da naji kamar zanyi zazzaɓin alamar nasha cizo”.
A wani ɗage RK ya ɗan dubeshi ya ce, “Ai tunda baka kwanta ba da alama kai naka cizon na musulmin sauro ne. Wanda ya ciji ƴar gidan Oum dai kamar yafi iya cizo”.
Yanzu kam sosai AA ya kallesa, hakama Yaya Fawzan. Ido RK ya kashema Fawzan. Yaya Fawzan ya kwashe da dariya dan ya gano kam yanzu. yace, “Ohhhhh na gane na gane, lallai wanan sauro kam ya iya cizo gallari”. Sai suka sake kwashewa da dariya shi da RK. Ƙasa-ƙasa suke zancen shiyyasa Oum bata jinsu. Shi kuma AA a tsakkiyarsu yake. Babban Yaya na kusa da Oum. AA da sai yanzu ya fahimci inda iskancin nasu ya dosa ya girgiza kai kawai. Bai sake magana ba saboda Oum da babban Yaya dake wajen, amma yayi alƙawarin sai ya rama su duka..


________★


Washe gari ƴan Kano da suka rabu biyu wasu suka tsaya Zaria gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho da amarya Najma, wasu kuma suka wuto nan abuja dan anan za'a ɗaura auren Ameerah da Maimoon dan sauƙaƙama mutane. Zasuyi tafiyar yamma ne saboda bikin da zasuyi suma can Zariya, anan kuma Abuja gobe za'ai kamu in sha ALLAHU anan gidan Darma. Asabar a ɗaura aure ai dinner, lahadi walima da safe, da yamma ai buɗar kai shike nan amare su shige daga ciki.
Ƴan Kano na gama hutawa aka kai lefen Ameerah. Lefen ya ƙayatar da kowa dan su Maanal sunyi ƙoƙarin saka abubuwa na girma. Sosai kuma Hajiya Shuwa da ahalinta da suka iso da ƴan Katsina suma da sukace komai ya wuce suka dai-daita da Hajiya Shuwan tun kai kuɗi da su Baba Sardauna sukai. Tukuyci mai tsoka su Maanal suka samo. Babu dai dangin Mamy ko ɗaya a ƴan kai lefe hakama Nibras ko ƴan Kano bata zo ta gaidar ba. Suna dawowa daga kai lefen Ameerah aka kuma biyosu da lefen Maimoon. Hummm shima dai su Hajiya Shuwa sun rigirgiza kayan arziƙi sai dai ace sambarka kam. Sai kuma abi ma'auratan da addu'ar zaman lafiya da zuri'a masu albarka.
A ɓangaren Mamy yaƙe kawai take da dauriyar dole har ta fito ta gaishe da ƴan Kano su Mah-mah, dan su Umma sune a Zaria zasu taho da amarya Najma gobe idan ALLAH ya kaimu........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣4️⃣




______________




.....A yanzu gaba ɗaya hankalin Mamy ba'a kan auren nan yake ba. Dan Sille ya gama rikita mata al'amari gaba ɗaya. Amma dai tana ta ƙoƙarin danne yanayin ta dan bata fatan kowa ya san halin da take ciki a wannan gaɓar. Abinda ya bama Abah mamaki yanda ta sake ba kamar bikin Maanal da AA ba. Amma dai baice komai akan hakan ba.
A ɓangaren Sille kam a yanzu itace mai nemansa a waya ruwa a jallo. Amma abin mamaki kaf layukan da yake kiranta da su bata samunsa. Tun a daren ranar ta bashi 10m daya buƙata, dan ta fahimci zai yi dukkan abinda ya ambata. Amma ta saka ana mata bincike a kansa dama Junaid, duk da ita tafi kowa sanin abinda ta aikata ma Junaid ɗin. Amma hankalinta yaƙi kwanciya sam. Tana son fita a gidan tana tsoron idon mutane, wani gefe na zuciyarta kuma na tunatar da ita idan ma ta fita ɗin ina zata samo Sillen. Tunda shi dai ba wani waje da yake zaune ta taɓa sani ba. Haka dai ta daure tana sauraren sakamakon binciken data saka anai mata akan Junaid.....


________★


A washe garin da za'a iso da Najma da ƙyar Oum ta lallaɓa Maanal sukaje saloon. Wankin kai kawai ta yarda akai mata, kitso sai ta sakama Oum kuka. Ƙyaleta tayi suka dawo gida akai zaman mata ƙunshi ja da baƙi. A lokacin su AA da zasu ɗakko Najma nata shirin wucewa. Ya shigo sashen Oum ɗin cikin tsokana yace mata saura kitso ta sanya masa kuka. Ita Oum ma sai abin ya bata dariya, ta dai gimtse batai ba. Sai ma ta harari AA da shima yake danne dariyar da ƙyar.
“Yanzu dan ALLAH Auta banda neman faɗa ina ruwanka. Munce maka muna son kitso ne.”
AA dai ya sake danne tasa dariyar da ƙyar ya ce, “ALLAH ya baku haƙuri Oum nayi shiru. Bani keys ɗin in dai nine yanzu zan yi gaba”. Oum na bashi maimakon ya tafi da arziƙi sai ya faki idonta ya duƙo ta bayan kujera saitin kunnen Maanal ya raɗa mata magana”. Tare da sumbatar wuyanta. Kafin ta juyo ya fice, cikin ɗaga murya Maanal ta ce, “Sai na rama kuma zaka dawo ai”. Mai ƙunshi dai abin nasu sai ya bata dariya da birgeta. Dan daka gansu kaga ma'auratan dake matuƙar son juna....


_________★



A Zaria su Ammie sune amarori ƙirjin biki. Amarya Najma tasha gyara ɗan gaske ciki da waje sai ɗaukar idanun mai kallo takeyi. Dan Ammie babu wasa sai da ta fidda ƴar tata Masha ALLAH. Ƙamshi kuwa ba'a magana, dan bayan nata gana Hajiya Shuwa. A jiya Ammie ta maidata Zaria. Anyi kamu a jiyan da yamma, yau kuma suke ƙunshi da safe. Da yamma aka fara yinin bikin Hajiya Majdiya.
Gaba ɗaya ran kishiyoyinta su Maman Yaseerah a ɓace yake. Suma su Yaseerah dai ƙiri-ƙiri ƴan ubancinsu ya kasa ɓoyuwa akan shagalin bikin Najma ɗin. Dan sun san dai kam ta kere musu fintin kau kamar yanda uwarta ta kerema iyayensu a komai. Balle kuma ita Yaseerah zuwa yanzu tasan minene family ɗin Darma. Randa aka kawo lefen Najma habaice-habaice sukaita saki. Kallon inda suke Hajiya Majdiya batai ba balle kuma su Ammie da ke tsaye akan komai. Hajiya Basariyya kam ai ji take ina bashi yiwuwa, koda tsiya-tsiya sai ta kaso auren Huznah ta shiga wannan family na Darma. Sai kuma tura su Madeena ƙannen Huznah ɗin take cikin yaran family ɗin Darman wai suma ko sa samu mazan aure. Abin ya ba Maman Yaseerah haushi ta hau Hajiya Basariyya da masifa amma saita ƙi kulata. Dan ita lissafinta daban dana Maman Yaseerah a yanzu....


Bayan la'asar kaɗan tawagar su AA da abokan Yaya Fawzan suka isa Zaria. Zuwa lokacin an gama shirya amarya Najma dake ta shan kuka tsaff cikin lafaya. An kaita gaban iyaye an mata nasiha. Lokacin da aka kaita gaban Hajiya Majdiya suyi sallama sai kawai ta rungumeta tana kuka mai ban tausayi, ita ko Hajiya Majdiya ta dake abinta, acewarta ai Najma gida zataje minene na ɗaga hankali. Kuma itama dai gobe nan da safe zata wuce Abujan dan ai bikin su babban Yaya da ita. Da ƙyar Ammie ta cire Najma a jikin Hajiya Majdiya aka fito da ita. AA da RK ne zasu ɗauki amarya, ga Ammie itace riƙe da amarya ita da Aunty Rufaidah.
Kunya ta kama AA, dan yanzu wani nauyin Ammie yake ji na musamman. Ko a waya ya kirata yata sum-sum da murya kenan. Itama dai Ammien nauyin nasa take ji. Cike da shaƙiyanci RK ya ce, “Babbar magana, suruki zai ɗauki suruka a mota”.
AA dai bai kula shi ba, dan su Ammie sun riga sun kawo gab da su. Itama kuma sai a lokacin ta farga da shi. A zuciyarta tace (Ya subahannallah ya akai haka) a fili kam ta daure ta saka Najma a motar. Har inda yake AA yazo ya rissina yana gaisheta. Ta amsa masa da kulawa da tambayar yaya hanya. Yace Alhmdllh. Haka dole ta shiga motar, ya rufe mata murfin da kansa sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver dan RK ne ya kawosu, yanzu kuma yace bazai maidasu ba ya gaji sai dai AA ɗin ya tuƙa. Haka dole ya amsa dan Ammie da zata kasance a motar, sai kuma alƙawarin da yay ma Yaya Fawzan na shi zai kawo masa Najma har gida. Yana ƙoƙarin yima motar key kiran Maanal ya shigo masa. Sai da ya saci kallon Ammie da hankalinta ke akan lallashi Najma dake a jikinta sannan ya ɗaga kiran. Ƙasa-ƙasa dan AA ya iya munafuncin magana a ƙasan maƙoshi ya ce, “Zuciyar Ajwaad yaya ne?”.
Daga can a shagwaɓe Maanal dake hammar barci hayaniya ta hanata zama sashen Oum ta gudo sashensu duk da nan ma cike yake da ƴammata ƙawayen Maimoon da aka taho da su daga Kano, amma da yake a ƙasa suke babu wanda ya hau mata sama sai ta haye saman ita. Tace, “Kun taho?”.
“Uhm-uhm! A nan zamu kwana”.
Ya faɗa cikin tsokana. Muryar Maanal harta fara rawa ta ce, “Kwana fa?”.
Murmushi yayi jin za'a fara masa kukan shagwaɓar. Cike da lallashi ya ce, “Wasa nake, ga amarya nan ma a mota yanzu zamu taho”.
Ajiyar zuciya ta sauke, tare da sakin hamma. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Barcin ne?”.
“Uhmm”.
Ta faɗa can ƙasan maƙoshi. Murmushi yayi, zai faɗa mata tare suke da Ammie yaji ta fara sauke numfashi alamar barcin ya fara ɗaukarta. Wayar kawai ya katse ya tada motar. Sai suka haɗa ido da RK. Kallon da yake masa na shaƙiyanci ya sashi hararsa kawai ya ɗauke kansa. Haka suka ɗakko hanyar Abuja da amarya gwanin sha'awa. RK da Aunty Rufaidah ne kawai ke hira a motar. Ammie nauyin kasancewar AA da shi kansa ma RK ɗin ya sata yin shiru. Haka shima AA ɗin tuƙinsa kawai yake. Duk da dama bamai yawan magana bane ba kowa ya sani.
Duk da uban gudun da sukai basu shigo cikin Abuja ba sai gab da sallar isha'i. Dan ma sunyi dabarar bi ta jere ne suka fito ta dutse. Maanal nacan na shaƙa barci bata san mi akeyi ba. A ƙofar sashen Oum AA yay parking. Auntyn su Mamy da a yammacin nan. Ta iso, kuma a sashen Oum ta sauka wannan karon ita ce ta fito ta tarbi amarya Najma ta nuna kara ma Oum. Aiko hakan da tai ya saka kowa jin daɗi sosai, hatta AA sai da ya murmusa. Oum kam Ammie ta rungume cike da jin daɗi, AA ya bisu da kallo yana sauke ajiyar zuciya. Ƙaunar dake a tsakanin Ammie da Mamy dabance a rayuwa. ALLAH yayi wannan haɗin kam.
Ya matuƙar gajiya, ga Maanal na ransa dan tunda bai ganta a ƴan tarbar Najma ba yasan tana can tana barci. Sashen nasu ya wuce, ƙawayen Maimoon na falo duk da wasu sun fita saboda shigo da Najma sai ɗai-ɗai da akaima ƙunshi bai ƙarasa bushewa ba yana shigowa sukai ɗif. Sai kuma suka shiga gaisheshi da masa sannu da dawowa. Hannu kawai ya ɗaga musu ya haura sama ko kallon basu isheshi ba. Yanda Maanal ta hana kowa hawo musu sama ba ƙarin daɗi yay masa ba, sai ya ƙara fahimtar Bestynsa nada hankali. ACn data ƙure a ɗakin ya kashe gaba ɗaya, yayi yayi ta daina hakan taƙi, sai dai idan ya shigo ya kashe. Ya matsa gaban gadon yana kallonta, tayi luf a cikin duvet tana sauke numfashi a hankali. Gently yakai zaune gefenta, tare da shafa kanta sai kuma ya duƙa ya sumbaci idanunta da lips ɗinta. A hankali ta motsa, sai kuma ta buɗe idanunta dake cike da barci ta zuba masa kamar ƴar maye. Murmushi ya sakar mata mai sanyi, cikin raɗa ya ce, “Wakey wakey, beautiful”.
Murmushi ta sakar masa, cike da kasala takai hannu ta shafi fuskarsa. Cikin muryar barci da shagwaɓa tare da tasowa ta dawo jikinsa ta ce, “Not yet, I'm still sleepy. Ƙamshinka ne ya tashe ni”.
Murmushi yayi sosai, tare da kaiwa kwance ya sakata a cikin jikinsa sosai ya rungumeta. Sai kawai ta matso da fuskarta gab da tashi, idanunta a lumshe alamar barci sosai ne a cikinsu ta ɗaura lips ɗinta kan nashi. Babu musu ya amshe dan dama yau gaba ɗaya rowa ake masa. Rabonsa ma da ita tun jiya da safe.........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login