Showing 12001 words to 15000 words out of 218311 words

Chapter 5 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

komai, na AA dai ba haka yake ba, to bata sani ba ko nasu Fawzan ma da nasu tsarin. A hankali take taka stairs ɗin kamar wadda bata so, tana a kusan na biyar ɗin ƙarshe taja ta tsaya cak sakamakon shashshekar kuka, faɗuwa gabanta ya shiga yi, sai dai kafin tayi wani yunƙuri ta tsinkayi muryar Aunty Babba na magana cikin takaici.
“Wai Kamila kina da lafiya kuwa? Tamkar wata ƙaramar yarinya ki zauna kinama kishiya kuka! Ina jarumtar taki ne ta tafi?. Har wacece Fateema yanzu a gareki da zata baki tsoro. Sanda ma take jin kanta a Fateema Darma ɗin kin shigo gidanta kinyi rayuwa da mijinta, kin haihu sai yanzu ne zaki zama sususu akan ƙananun abubuwan nan.....?”
“Bazaki gane ba Aunty, wlhy Matar nan ta wuce dukkan yanda kike zato da tsammani. Ni wlhy a wannan gaɓar ƴaƴana nake buƙata tako wane hali, idan ba hakaba kuwa zan iya kashe Fateema.....”
Kaɗan ya rage Maanal takai ƙasa dan firgita. Dan wata muguwar hajijiya ce taji tana neman zubar da ita. ALLAH dai ya taimaketa ta dafe glass ɗin stairs ɗin da ƙyau. Anya bayan ƙaddarar data faru da ita tsakaninsu abaya akwai wani abu data taɓa jin ya girgiza zuciyarta kamar wannan? Mamy fa? Mamy dai Mamy dai ke furta zata iya kashe Oum. Mamy dai Mamy dai kalamanta ke bayyana akwai ƙullaliya tsakaninta da Oum.... Tunaninta ne ya katse jin abinda Aunty Babba ke faɗa.
“Kamila ki kwantar da hankalinki, na ɗau miki alwashin a wannan gaɓar sai munyi maganin Fateema. Babu maganar kisa a ciki, amma wlhy da ƙafafunta sai tabar miki gidan Aliyun da take taƙamar nata ne, ɗan uwanta ne tare da ƴaƴanki. Dan babu abu mafi ciwo a gareta kamar a shekarun nan ace Aliyu ya saketa, ya kuma rabata da ƴaƴan data gama wahala da su da sakankancewa nata ne....”
“Aunty bana katseki bane, amma tayaya Aliyu zai saki Fateema? Kada ki manta da jininsu ɗaya, iyayensu ɗaya. Zasu yarda ne ya saketa?”.
“Da gudun tsiya ma kuwa. Ko an faɗa miki haka zamu barshi ne? Ai sai mun juya masa kai daga garesu gaba ɗaya, ta yanda su duka babu wanda ya isa sakashi balle hanashi”.
“To ita kuma wannan ƴar iskar yarinyar da aka aurama Ajwaad fa? Kin fa san halin yaron nan da baƙin taurin kan masifa. Yanzu kina ganin tunda yasan a ƙulle nake da shi ko dubashi naje sashen sai ya hau barcin ƙarya. Kuma jira nake ya gama warkewa sai na sillesa tas, kuma ko yaƙi ko yaso sai ya rabu da annobar yarinyar nan. Dan har abada bazan taɓa son abinda ke tare da Fateema ba. Ba kuma zan haɗa jini da Asiya ba dan na mata tsana mai girma itama saboda kusancinta da Fateema”.
“ALLAH na tuba idan mun gama da Fateema wacece ita kuma wannan abar da uwarta. Ai ki fahimta wannan masifaffen son da Ajwaad kema yarinyar nan ba banza ba ne, tun suna yara suka tsafacesa ai. Shiyyasa ta tsara duka yaran su auri nata tsarin wato ƴaƴan munafukarta mai zuwa mata bin bokaye Asiya, kinga ya tabbata ke da su sai dai kallo. Matar nan fa yanda kika san NASARA haka take akan iya tsari, ke kuma sai ki sakankance sai abu na neman kwaɓewa. Yanzu dai ki muje ki kwanta dare yayi, ki ƙara nazari nima zanyi nawa. Amma dole ne Nuratu ta dawo gidan nan tai azumi. Wani ƙaramin wasa nake son a buga tsakaninsu da yarinyar nan, har itama waccan sakaran matar Fawzan dole ta shigo tawagar, facalanci nake so su buga ɗan gaske ta yanda sai ta tsani kanta a gidan nan daga ita har uwar ɗakin nasu. Tarewarta kuma ki riƙe wuta babu ita......”
“Ai ni so nake ma ta dawo nan gabana ta zauna, dan Ajwaad da kike ganin yaron nan hummm. Kuma tsarin nan naki yayi. Ai dama nafi son na fara gasama Fateema aya a hannu sai ta gama firgicewa da ni kafin tabar min gidan”.
“Yauwa ashe kin fahimceni, yanzu dai wayata nacan a sashenta na bari dan ta naɗar min maganganunsu, da safe nasan zamuji abubuwa da yawa”.
Ƴar dariya Mamy tayi da faɗin, “Kai aunty shiyyasa nake sonki”.
Idanu Maanal ta tsirama wayar, sai kuma tai murmushi tana mai kai hannu ta share hawayenta dake rige-rigen sakko mata........✍️




_Tofa yau dai Maanal taji ainahin Mamy, mi kuke tunani?🏃🏃🏃_




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*


*09032345899*


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣




______________




.......Tsam ta miƙe daga zaunen da take a step ɗin, babu buƙatar ta bada wayar yanzu, dan haka ta fice a sashen. Da alama Haule ma ta shige ta kwanta dan har ta kashe wuta. Maanal taji daɗin samun Oum na wanka, sai kawai ta adana wayar ta kwanta. Koda Oum ta fito likimo tayi kamar mai barci, duk maganar da tayi kuma ta fiske. Hakan yasa Oum ɗin fahimtar tadaiyi barcin.
Shirin barci tayi, dan Abah sai kiran wayarta yake. Babu yanda ta iya dole ta kimtsa ta tafi. Saboda ya tabbatar mata yau idan batazo sashensa ba shi zaizo a gaban Maanal ya ɗauketa. Tasan halin kayanta, dan haka ta haƙura kawai tai shiri ta tafi. Sai da tama Maanal addu'a ta shafeta sannan ta rage mata hasken ɗakin ta daidaita mata ac kamar wata ƴar Baby. Aiko tana fita Maanal ta rushe da kuka. Wani irin tausayin Oum mai tsanani na ratsa mata zuciya matuƙa. Tabbas ta taɓa jin Oum ba ita ta haifi su Babban Yaya ba Mamy ce, amma bata taɓa sake tuna hakan ba ko kallon hakan a zuciya balle a zahiri saboda babu wani alamu dazai nuna hakan koda ga Mamyn ne balle Oum data gama sakankancewa. Itafa ganin komai take tamkar almara ko mafarki. Duk yanda taso yin barci hakan ya gagara, dole ta zauna kawai a zaune tana nazartar abubuwa. Daga ƙarshe ta ɗakko wayar nan ta goge recording ɗin da suka saka, yako naɗa da yawa dan harda maganganun Abah da Oum bayan fitar su Mamyn. Batamayi nisa a ji ba ta goge kawai ta ajiye wayar. Mikewa tai ya shiga bayi ta ɗauro alwala tazo ta shiga miƙama UBANGIJI kukanta. Kusan ma dukkan addu'oin ta akan Oum ne....


WASHE GARI yanda su Mamyn sukazo gaida Oum cike da makirci bakuna a washe sai Maanal ta shagala a kallonsu. A ranta tana jinjina lallai maƙiyin ɓoye shine ainahin maƙiyi, dan zai taima rayuwarka illa batare daka sani ba. Balle ace yana a jikinka, tare da kai matsayin masoyi na zahiri. Gara wanda zai zo ya kalleka ya ce maka wane BANA SONKA BANA ƘAUNARKA. Kasan baya ƙaunar taka zaka kiyaye komai tsakaninka da shi. Koda suka nema waya sai ta basu, da Oum tai magana sai tace ai taje kaima su Inte ɗin ta samu sunyi barci shiyyasa ta dawo da ita.
A cikin zuciyarta kuwa faɗi take (Oum baki san su wanene waɗan nan mutanen ba. Sunfi duk wani abinda kike kallo a matsayin haɗari haɗari. Amma kada ki damu, ba sunce YAƘIN SUNƘURU bane abun, muje zuwa yanzu ne za'ai wasan na gaskiya. KAREN BANA SHINE ZAI MAGANIN ZOMON BANA. Ni Maanal Habib Giro, na ɗauki ɗammara da alwashin sai waɗan nan mutanen sunyi nadamar sake dawowata RAYUWARSU. idan su aya sukai alwashin gasa miki a hannu ni zan gasa musu ƘARFE ne a tsakiyar kawunansu. Sai sun san ZURU BATA CIN ZURU SAI SAI DAI A HAƊU AI ZURU-ZURU. Ƴaƴa kuma tunda ALLAH ya mallaka niki tofa naki ɗin ne. MUJE ZUWA WASA).


🤣🤣Tofa nace ba. Ƴar mutan Giro fa tace muje zuwa wasa, da alama ainahin MAANAL zata dawo🥱. (Maanal dama in an MUTU ana dawowa😜?)


😂😂🏃🏃🏃


____________★
KANO


Tsaye yay kawai yana kallon ƙofar daya gama mummurɗawa ya ji a rufe. A karo na farko ransa ya fara ɓaci da salon iskancin Huznah. Wai mi take nufi da shine halan? Ɗan iska ta ɗauke shi ko mi? Yau kwana ɗai-ɗai har takwas kenan da kasancewarta a gidan, amma tunda baƙi ƴan biki suka tafi da magriba tayi sai ta shige ɗaki ta kulle kanta. Da rana kuwa ita da kowa dake shigowa faran-faran. Hatta shi da rana tsakaninsu normal ne, da farko ya dauka kunya ce da kawaici irin na yaranmu, duk da baiyi zaton samun hakan daga Huznah ba, musamman idan akai dubi da shekarunta da wayewar zamani.. Wani ɗan murmushi yayi a karo na farko, ya sake sakin murmushin a karo na biyu saboda abinda zuciyarsa ta sake hasko masa. Baice komai ba yau ma ya juya ya koma ɗayan ɗakin dan dama bedrooms ɗin biyu ne a gidan sai falo, kitchen, ƙaramin store. Gini ne dai irin na mai rufin asiri ba irin wanda su Hajiya Basariyya suka jima suna fata ba.
Yana barin wajen Huznah da duk ke ankare da motsinsa ta ballama ƙofar harara. Cike da tsana ta ce, “Maye, in dai nice mu zuba, wannan jikin kuma ƙwalelenka na AA ne. Dan wlhy sai na sameshi, sai na sabauta rayuwar agolar yarinyar can ta yanda bazata taɓa moruwa ba. Idan Ummi tabar uwarta tana yanda taso a gidanmu ni sai na tabbatar mata KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA. Daga haka ta koma ta kwanta tana cigaba da charting dinta da take yi daman. A dai-dai nan kira ya shigo wayarta. Zaune ta tashi ganin wanda ke kiran. Sai da ta gyara zama sannan ta ɗaga. Murya ƙasa-ƙasa ta ce, “Sille ya akayi?”.
Daga can wanda ta kira Sille ɗin cikin muryar ƴan daba ya ce, “Normal ne uwar ɗaki. Kawai zance miki Nurry fa babu wani bayani a ƙasa kan bikin nan nata da AA. Dan a majiya mai ƙarfi ance har yanzu bashi da lafiya yana gida yana jiyya sai an kwantar sai an tayar. Babu kuma wani yunƙurin ma za'a sake biki a gidan a wannan satin. Kai ita ma agolar gidan taku tana sashen babarsa bata tare turakarsa ba”.
Sosai hankalinta ya tashi da jin har yanzu AA ba lafiya. Cike da mamaki kuma ta ce, “Amma Sille kai bala'i ne, dan ALLAH ya akai ka samo wannan sirri mai girma haka?”
“Hahaha uwar ɗaki kenan, karki manta a hannun Nurry kika ƙwaceni, amma bari na baki a buɗe, ina da yarinya a gidan dake aiki ta dalilin Nurry.”
“Anya Sille bai kamata na fara tsoronka ba”.
Dariya ya ƙyalƙyale da ita jin abinda Huznah ta faɗa. Kafin ya ce, “Haba uwar ɗaki, ai ke ta dabance. Kin ganni nan duk rintsi bana manta alkairi. Sannan amana ɗaya ce”.
Sosai Huznah ta sauke ajiyar zuciya. Tai masa godiya da tabbatar masa zaiga saƙo ta account ɗinsa daga haka sukai sallama.....


Wayar na yankewa daga can Sille ya ƙyaƙyace da wata muguwar dariya. Sai da yay mai isarsa sannan ya ce, “Yaro bai san wuta ba kenan sai ya taka. Daga ke har Nurry ɗin kune kuke min aiki bani ke muku ba. Ina amfani da kune kawai na samu kuɗaɗe. Kuna nan kuna jira baku ankara ba sai dai kuga gawar shegen AA ɗin naku kwance a gabanku. Wannan alƙawari na ne, sannan gaba ce ta tsawon shekara takwas ni da shi.. kai yama kamata nasan agolar yarinyar nan ta gidan ku da akace ya aura”. Wayarsa ya sake ɗauka ya shiga tafa saƙo. Babu jimawa akai masa flashing. Kiran number ɗin yay black, kafin ma ta gama ringig ɗin farko an ɗaga. Daga can ƙasa-ƙasa muryar mace ta bayyana.
“Baby miya faru ne naga kace na maka flashing idan ni kaɗai ce? Faka-faka kafin wannan ƴar sa idon ta fito wanka”.
“Ke nifa yarinyar nan idan tace zata takura miki a gidan nan ALLAH zan aikata barzahu”.
“A'a ka rufa min asiri babu ruwan ka da ita. Sannan itama tana da nata amfanin da take mana ai. Yanzu dai miya faru?”.
Tsaki yaja mai kauri, kafin ya ce, “Hoton amaryar gidan nan nake so?”.
Hankali a ɗan tashe ta ce, “Wai Matar AA”.
“In ba ita ba akwai wata amarya ne a gidan?”.
A sanyaye ta ce, “A'a. Amma Baby kasan hakan akwai haɗari ko? Taya zan ɗauketa hoto nikam?”.
“Kefa wasu lokutan gaja ce wlhy, kuna gida ɗaya baki san yanda zaki shiga jikinta bane?”.
“Tab wlhy Baby hakan zai yi wahala. Itafa irin miskilayen mutanen nan ne na gaske. Sannan zan iya ƙirga maka ganinta da nai a gidan nan. Koda yaushe tana ɗaki ko falon sama kuma a sashen Oum take bana Mamy ba”.
“K ni hakan bai dameni ba. Kawai hotonta nake buƙata na kuma baki kwana biyu kacal”. Daga haka ya yanke wayar yana huci. Itako daga can sai ta zuba uban tagumi zuciyata na kai-kawo. Sille ya zamewa rayuwarta bala'i, itako miya ja mata shigowa bariki. Ƙiri-ƙiri da uwarta da ubanta a duniya saboda neman duniya su sun kasa tanƙwara rayuwarta ga wani ƙaton banza ɗan daba na juyata yanda yake so kuma dole tabi. Tabbas ta ƙara yarda da kalmar nan ta malam bahaushe dake cewa WANDA BAIYI SHARAR MASSALLACI BA YAYI TA KASUWA. To ita a ganinta ta kasuwar ma ai mai sauƙi ce, TA BARIKI yafi dacewa ace....


__________★


KADUNA


A Kaduna ƙiri-ƙiri Ammie ta hana Daddy sukuni sai rigima take masa akan dawowar su Hajiya Yaya. Shi kuma yayi biris da ita. Da yaga tana neman saka masa rayuwa gaba sai ya shirya yabar mata kasar ma. Wannan abu kuwa ya masifar ƙona mata zuciya. Harda kiran Nene tana kuka. Sai da Nene ta gama saurarenta tsaf sannan ta ce, “Ai ni hakan da yay ya min dai-dai Asiya, tunda nace ki fita a maganar su kin ƙi ko. Su idan sune hakan ta fari dake har fati inaga sai sun shirya bama murna kawai ba. Ba gaban iyayensu suke ba? To ki nutsu idan zaki nutsu kinji na faɗa miki. Kuma nima kada ki sake zuwa min da zancensu. Haka kawai ki dinga ɓatama kanki rai da mijinki akan waɗanda basu ƙi ki faɗi ki mutu ba.... Haka Nene taima Ammie tas sannan ta yanke kiran. Ta kuma tabbatar mata ta kira Daddy ta bashi haƙuri idan ba haka ba zatazo har gidan ta sameta.
Wannan faɗa na Nene shine ya kawo ƙarshen rikicin Daddy da Ammie suka shirya ta waya. Sai dai duk da hakan rashin dawowar matan gidan na damunta kodan yaransu dake zuba mata rashin mutunci. Dan ma bata kulasu bata shiga harkar su. Amrah ce kawai babu ruwanta....


__________★


“Mabera! Wai nikam mike damunka kwana biyun nan? Gaba ɗaya baka da sukuni sai tunani da lissafe-lissafe”.
Numfashi mai nauyi Daddyn Nazeefa ya sauke, kafin ya juya yana kallon abokin nasa shaƙiƙi da shi da shi suka san juna na haƙiƙa dan kar-tasan-kar ce. “Himm Bakori kenan, kaima ai kasan maganar gizo bata wuce ƙoƙi. A lissafin auren Nazeefa da yaron Alhaji Usman Chalawa wata uku kenan yau cir, kasan dai lokaci yayi da aikina zai fara a kansa ai. Wannan shine lissafe-lissafen da nakeyi. Sai kuma baban naman dana hango yanzu ya shigo a tarko”.
“Tofa babban nama kuma? Waye hakan?”.
“Ba yanzu zaka sami ba. Sai na gama da Chalawa tukunna. Jiya nayi waya da Nazeefa tace azumi na goma zasu dawo gida. Dan yace mata zasuyi Umra. Dan haka nake shiri, da sun dawo zata fara min nata aikin”.
Murmushi Bakori dake kallonsa yayi, a ransa yana mamakin hatsabibancin aminin nasa, ta gefe tausayin yarinyarsa da yake son jefawa a ramin zamba cikin amincinsa yake. Shifa duk iskancinsa ALLAH bazai iya hakan ba. Dan iyalansa nada muhimmanci mai girma a wajensa......


(Humm dan baka san iyalin naka tare kuke raba dai-dai da aminin naka bane Alhaji Bakori🏃🏃🏃🏃)
_________★


Alhamdullah jikin AA yay sauƙi sosai, koma muce ya warke sai abinda ba'a rasa ba na tsakanin ruhi da gangar jiki. Kamar yanda yay alƙawarin bama Abah dama ya bashi ɗin. Dan ya tattara al'amarin Manaal ya ajiye gefe kamar ba shine yasha ciwo akan rasata da yaga zai yi ba. Gefe kuma baice komai game da batun ɗaga aurensa da Nuratu sai zuwa bayan salla ba. Sai dai yaƙi yarda su zauna da Mamy duk yanda taso. Da zarar ya fahimci zasu keɓe sai ya zille abinsa. Fahimtar akwai gaɓar da za'azo ya nema mafita ya rasa ya sashi shirin komawa kan aiki. Itama kuma Maanal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login