Showing 54001 words to 57000 words out of 218311 words
Chapter 19 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣6️⃣
______________
........Manaal bata gashi ba kuwa sai 11, wanka ta fara yi sannan ta fito. Babu kowa a sashen sai motsin su Inte a kitchen. Kitchen ɗin ta nufa, suka shiga gaisheta da girmamawa duk da kuwa ta tabbatar zasu girmeta. Amsa musu tayi da tambayar ina Oum.
“Tana sashen Abah daya dawo babu jimawa”. Cewar Joy.
Maanal tace, “Oh Abah ya dawo, bara na gaisheshi to”. Daga haka ta fice. Hijjab taje ta ɗauka sannan ta nufi sashen Abah ɗin. Bayan tayi knocking tai sallama, sai da aka bata izini sannan ta shiga. Yana zaune da matansa, tunda ta shigo yake mata murmushi, itako cike da jin kunya ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafun Oum ta shiga gaisheshi. Amsa mata yay da kulawa sosai, kafin ya ɗora da faɗin, “Yau ana hutu ko ƴar Abah, shiyyasa na shiga sashen Mamanku kinata barci”.
Murmushi Maanal tayi cike da jin kunya, sai kuma ta juya ta gaida Mamy data cika tai fam. Ko'a kwalar rigar Maanal dan ita a yanzu kallonta kawai take yi. Da ƙarfin hali Mamyn ta amsa mata, dan cike take taf da takaicin maganar tafiyar ta da Oum ke tuntuɓar Abah yanzu. Kuma Aban baiyi wani jayayya ba yay addu'a da fatan alkairi. Ita kanta Oum tayi mamakin sallamawar tasa kai tsaye, balle Mamy da sai yanzu ne take sanin fa tafiyar. Ita dai Maanal sallama tai musu ta koma sashen Oum. Bayan ta zauna ta gama breakfast kitchen ta nufa domin shirya lunch. Wayarta dake kashe ta kunna, sai ko sakwanni suka fara rige-rigen shigowa. YouTube take ƙoƙarin shiga domin duba girki ko zataga wani tai sha'awa, sai kawai taci karo da numbern AA ta notification alamar ya tura mata saƙo. Duk yanda taso ta share hakan ta gagara, dole ta shiga WhatsApp ɗin domin duba saƙonsa.
“Your hand is soft😋, and it reminded me why you're the one I want to hold on to forever”.
Iya abinda ya tura kenan da emojin lasar baki. Da alama kuma tun daren jiya ya tura saƙon. Bayan gama cin abincinsu kenan koma tace bayan tashin ta. Samun kanta tayi da sakin murmushi, batare da bashi amsa ba ta fito abinta ta shiga YouTube ɗin datai niyya. Girki tayi masu daɗi, tana ƙoƙarin kammalawa Oum ta shigo. Tako ji daɗin ganin Maanal ɗin a kitchen. Albarka ta sanya mata, sannan tace ta haɗa wanda za'a kaima AA office ya kirata zai aiko driver shiyyasa ma ta taso nema masa abincin, ashema Maanal ɗin ta hutacceta. Da to Maanal ta amsa mata, ta shiga haɗawa kuma komai yanda ya kamata cike da tsari. Har zata rufe ƙular saita tsaya, cokali ta ɗauka ta rubuta (ACICI) a kan abincin sannan ta rufe..
Bayan an wuce da abincin tai salla ta nufi sashen nashi tare da su Inte domin su tayata gyaran da Oum tace taje tayi masa...
________★
Yau ɗin nan sosai aiki yay masa yawa, sai dai hakan bi hanashi yawan duba wayarsa ba kuma WhatsApp, shi kansa ya kasa fahimtar abinda yake jiran gani, sai dai wani sashi na zuciyarsa na tabbatar masa reply ɗin Maanal yake jira. Kuma yaga ta buɗe saƙon awa biyu data shige amma babu amsa. Haka dole ya haƙura lokacin sallah ya wuce massallaci. Bayan ya koma office babu jimawa drivernsa yazo masa da abincin da yay kiran Oum. Zama sosai ya gyara domin cin abincin dan yunwa yake ji. Yana buɗe kula ta biyu yaci karo da rubutun da tayi, shi da farko ma baiyi zaton abu aka rubuta a kan abincin ba ta hanyar zanawa sai da ya saka ido sosai da tunanin ko wani ne ya saka hannu ya jagwalgwala masa. Sai kawai yaci karo da (ACI-CI). Shiru kawai yayi yana kallon rubutun, zuciyarsa na faman masa kai-kawo. Shi dai yayi imani wannan ba aikin Oum bane ai. Amma duk da haka sai ya ɗaga waya yay kiran Oun ɗin. Sannu da aiki yay mata kamar yanda ya saba a duk lokacin data aiko masa da abincin.
Daga can tace, “Ai Bestyn ka ce ma ta girka bani ba. Sanda ka kira waya naje dan nema maka na samu harta kammala girkin”.
Godiyar dai ya sake ma Oum sukai sallama. Yana ajiye wayar ya sauke ajiyar zuciya, sai kuma yayi murmushi mai sanyi. Samun kansa yay da tsayawa yana kallon rubutun kawai, daga ƙarshe ya ɗauka wayarsa yay hoto sannan ya fara zubawa. Sai da ya gama haɗa komai sannan ya sake ɗaukar wayar, hoton ya tura mata, a kasanshi ya rubuta.
“Meaning”.
Kawai....
Maanal na zaune a bakin kadon ɗakinsa data gyara tsaf bayan ta canja bedsheet dan ita kaɗai ta shigo nan su Inte na ƙasa suna gyarawa waya a hannunta suna charting da Waleed saƙon ya shigo. Yanzu kam bata buɗe ba, ta notification ɗin taga abinda ya turo da wanda ya rubuta. Murmushi kawai tayi tana sake maimaita kalmar (meaning) ɗin daya turo a zuciyarta. Daga haka ta cigaba da hirarta da Waleed ɗin kawai. Tabar AA acan da kallon waya. Dan ko da ya kammala cin abinci ya koma kan kujerar aikinsa kaɗan-kaɗan sai ya dauka wayar ya duba kamar ɗazun. Amma har lokacin bata buɗe ba kuma tana a online. Ransa ya sosu amma ya danne, daga ƙarshe ma ya kashe wayar ya ajiye tunda dama iyakar mutanensa ne masu muhimmanci koma yace family ɗinsu kawai keda no ɗin...
Da yamma koda ya dawo gidan ya samu sun fita ita fa Oum. Bai san ina sukaje ba bai kuma tambaya ba. Dan sashen Mamy ma ƙin shiga yayi kasancewar yasan tana tare da Abah daya yini a gida. Sai da Fawzan ya dawo sannan suka nufi sashen Oum ɗin a tare. Sai dai kuma Nuratun da yake gudun su haɗu a sashen Mamy sai suka sameta a sashen Oum ɗin kwance tana kallo. Yi yay kamar ya fasa zaman, sai kuma akai sa'a su Oum suka shigo.
Tunda ya kalla Maanal sau ɗaya ya fahimci gyaran kai sukaje, dan idanun mutuniyar sunyi ja alamar tayi kuka. Kansa kawai ya girgiza yana kallon Oum. Sai kuma yakai zaune a kusa da ita murya a ƙasa ya ce, “Oum daga ina haka?”..
“Wankin kai nakai Baby dan nasan sanda zaka dawo ka gaji balle ka kaita. Aiko ansha daru, ashe har yanzu bata daina kukan wanke kai da kitso ba. Tamaƙi yarda ayi kitson sam”.
Lumsassun idanunsa ya zubama Maanal daketa ɓata fuska, itako taƙi yarda ta kalla kowa sai ma Fawzan dake lallashinta ta kula. Idanun ya ɗauke a hankali. “Ai inaga sai randa aljanun kan nata suka barta zata daina wannan halin”. Yaba ma Oum amsa cikin sanyin yanayi. Murmushi Oum ɗin tayi, yayinda Maanal da taji abinda ya faɗa ta dallo masa harara. Sai kuma ta miƙe fuuu tai ɗaki.
Oum tace, “Kaga ka Koreta auta”.
“Oum dama mai son yin kuka ne aka jefesa da kashin awaki kawai”. Daga haka ya maida kansa ya kwantar a kujerar. Iya wuya Nuratu takai da iskancin Maanal a gidan, shegiyar yarinya gansamemiya ta zauna tana ma mutane taɓara su kuma suna biye mata kamar wasu makafi. Amma ai ta iya zura hannu a ƙasan table tana taɓa maza ko. Ita kaɗai take surutanta a zuciya, fuskarta kuma na bayyana halin da take ciki...
Da wuri Maanal tayi barci dan kanta ciwo yake mata. Tunda Oum ta bata magani tasha sai barci. Ita dama ƙarshen taɓa mata kai kenan ai. Musamman idan bata so kamar mai aljanun dai tabakin AA ɗin. Washe gari ta kama ranar tafiya, shima AA baije office ba. Amma zuwa goma ya fita a gidan. Bai dawoba sai azhar. Ya samu Maanal harta haɗa kayanta, sai kuma a lokacin ne su Nuratu suka san da tafiyar da Saheeba. Nibras ko dake wajen aiki bata sani ba. Kai tsaye AA daya shigo sashen Oum ya nufa. Daga ita sai Maanal a falon sama. Bayan ya gaida Oum Maanal ta gaisheshi batare data kallesa ba. Shima kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Dan wani irin ƙyau yaga ta masa a bayyane, bai san tun daren jiya Oum kema yarinyar tata gyaran jiki da kayan haɗi na musamman da Hajiya Shuwa ta kawo ba, ta kuma bata abubuwa tasha, ita dai Maanal ta tsargu da abinda Oum ɗin ke bata, dan tasha gani a wajen su Didinta suna sha. Amma sai bata nuna ba ta dake kamar bata gane komai ba.
“Kaya nawa kika ɗiba?”.
AA yay maganar idonsa akan Maanal muryarsa a dake dan ransa a ɓace yake, rashin walwalarsa yau a bayyane take. Mamy ce kuma ta haddasa hakan a gareshi, dan kaca-kaca yau tai masa akan wannan tafiya tasu da Maanal, harda cewa ma da sai dai a fasa da Maanal ɗin ko shi ɗin ya fasa, sai da ya mata alƙawari akan Nuratu data kafa masa sharaɗin kiranta kullum sannan kuma tai masa ALLAH ya isa idan ya mu'amalanci Maanal a shimfiɗa..... Tunanin nasa ya kauda gefe, ya sake maimaita maganar ga Maanal datai kamar bata jisa ba cikin yanayin ɗan tunzura.
Kallonsa Maanal tayi dan harga ALLAH sai yanzu taji abinda yace, da farko hankalinta nakan charting da take da su Didinta ne, ganin yanda ya tsatstsareta da nashi kaifafan idanun a gaban Oum kuma ko kunya babu sai ta ɗauke nata da sauri. A sanyaye ta ce, “goma”. Komai bai sake cewa ba, sai miƙewa da yay ya fita. Da kallo duk suka bishi, Oum kuma ta fahimci ransa a ɓace yake, amma sai tai tunanin ko daga waje aka tunzuro shin.
Babu jimawa ya dawo da madaidaicin traveling bag na trolling mai shegen ƙyau. Baice komai ba ya wuce ɗakin Oum da shi, fin mintuna goma sai gashi ya sake fitowa da shi. A falon ya ajiye sannan ya ɗan kalla Maanal ɗin ya ɗauke ido yana ƙoƙarin ficewa. Ciki-ciki ya furta, “Ki bar wancan”. Daga haka yay ficewarsa. Kallon juna Oum da Maanal sukai. Fuskar Oum da damuwa ta ce, “Akwai abinda ke damunsa”.
Ƙasa Maanal tai da kanta, dan ita kam bata san mi zatace ba. Itama ta fahimci akwai damuwa a tare da shi, duk da tasan wannan normal ne a halinsa, dama idan kaga sakewa a tare da shi to lallai suna tare ne, dan ita sam bata son yanayin baƙin miskilancin nashi, shiyyasa duk yanda zata sakashi magana ta sani.
_________★
4:30pm
Su AS suka iso domin ɗaukarsu. Shine ya fara fitowa daga sashensa. Sanye yake cikin ƙananun kaya normal wandon jeans black da t-shirt black data kwanta masa a jiki sosai, dan irin mai santsin nan ce da laushi jiki. Yaci zanzaro brawn belt daya fidda ainahinsa na dogon mutum dake tsaye sosai a suffarsa ta zakin. Sai jacket da itama ta kasance brawn color a hannunsa ya saƙale batare daya saka ba. Sosai fuskarsa data sha gyara gashin sajensa ya kwanta luff-luff ke'a ɗaure, kamar ko yaushe idanunsa manne da sirrin fari tas ɗin gilashinsa dake sake ƙawata shi. Tafiya yake ɗai-ɗai a kuma nutse cike da ƙasaita yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa takalmansa masu matuƙar ƙyawu sau ciki na bada ƙarar sauti kaɗan-kaɗan.
Sosai Nuratu ta shagaltu da kallonsa, ji take kamar ta haɗiyesa ta huta. Dan daya ɗan gittata zuwa gaban Mamy mayataccen ƙamshinsa ya daki hancinta jitai illahirin jikinta na rawa. AA da bai san ma tana yi ba dan shi ko lura da ita baiyi ba a wajen ya ɗan zubama Mamy ido kafin ya risinar cike da girmamawa ya furta, “Zamu wuce Mamy”.
Ƙin yarda Mamyn tai ta kallesa, kasancewar su Oum a wajen kuma yasa tai masa addu'a cike da nuna rashin kulawa kamar yanda take musu. Muryarsa a sauƙaƙe ya furta, “Thanks you” a hankali. Sai kuma ya matsa gaban Abah. Murmushi Abah yay masa, tare da ɗaura hannunsa a kafaɗarsa. Sai kuma ya matsar da bakinsa kusa da kunnen AA ɗin ƙasa-ƙasa ya furta, “A rufan asiri a dawo min da yarinyata lafiya Oum's boy, kaga dai gudun rigimar uwar taka yasa na baka salin-alin”.
Idanu AA ya lumshe tare da sakin guntun murmushi kansa a duƙe. Batare da ya yarda ya kalla Aban ba ya gyaɗa masa kai, muryarsa a sanyaye yace, “In sha ALLAHU Abah zan cika alƙawari”.
“ALLAH yay muku albarka”.
Abah ya faɗa yana murmushi da ɗan bubbuga kafaɗar tasa. Gaban Oum AA ya ƙarasa..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣7️⃣
______________
........Gaban Oum AA ya ƙarasa, Maanal na gefenta sanye cikin Abaya red color datai mata matuƙar ƙyau, tai rolling kanta da mayafin, sai mitsitsiyar handbag a hannunta. Suna haɗa ido ta kauda nata, shima nashin ya maida akan Oum, cike da kulawa ya rungumeta, “Oumna zan yi missing ɗinki”.
Ya faɗa cikin maƙoshi. Murmushi Oum tayi, tare da ɗan bubbuga bayansa. Sai kuma ta ɗagoshi cike da kulawa fiskarta da murmushi ta shafa fuskarsa. “Nima haka Auta, amma karka damu kamar yau ne ai zaku dawo. Ga Baby na nan zata kula min da kai”. Tai maganar tana juyawa ta kamo hannun Maanal. A cikin nashi ta sanya, a tare suka saki ɓoyayyar ajiyar zuciya kuwa. Sai dai a zahiri kowa a dake yake, dan Maanal ma kanta a aƙasa yake, shine ma dai ke kallonta ƙasa-ƙasa. Addu'a sosai Oum tai musu, tare da damƙa ma junansu amanar kansu. Daga haka tace suje lokaci na ƙurewa. Gashi jirginsu 5:20 zai tashi.
Sai yanzu ne Saheeba ta buɗe baki da ƙyar tai musu addu'ar dawowa lafiya, hakan ne ya zaburar da Nuratu, itama ta ce, “Ya AA ALLAH ya tsare”.
Hannu kawai ya ɗaga musu, tare da kai ɗayan hannunsa ya amshi trolling ɗinsu da Maanal ta kama zata ja. Ɗan ɗagowa tai ta kallesa, suna haɗa ido ta janye tare da sakar masa akwatin. Shima bai ce komai ba ya turashi yay gaba, ita ko Maanal sai da ta sake rungume Oum sannan ta wuce idannunta cike da hawaye. Ji take kamar zasuyi tafiya ne mai jimawa.
Da sauri AS ya zaburo ya amshi akwatin hannun AA ɗin domin sakawa a booth dake buɗe. Shi ko jikin motar ya nufa ya tsaya har Maanal ta iso, ganinsa tsaye ya sata fahimtar ita yake jira ta shiga. Dan haka ta nufi shigar, hannu yasa ya tare mata saman kai dan karta buge, sai kuma akai rashin sa'a abayarta ta nema taɗeta. Riƙota yay da hannunsa ɗaya bayanta ya jinginu da jikinsa. Muryarsa a ƙasan maƙoshi can ƙasa sosai ya ce, “Are you okay?”.
Kanta ta jinjina masa tana ɗan sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta matsa daga jikinsa ganin su Oum duk suna kallonsu har tana iya hango yanda fuskar Mamy, Nuratu da Saheeba ta canja, shiga tayi sai dai tana ɗan yamutsa fuska dan ƙafarta na ɗan mata zafi. Lurar da AA yayi saboda idonsa a kanta yake ya sashi kaiwa tsugunne irin na yanayin maza ya ɗaga Abayar kaɗan ya kamo ƙafar dake a cikin ƙyaƙyƙyawan baƙin takalmi fes-fes da ita. Takalmin ya zare ya ajiye, batare da damuwa ba ya ɗaura ƙafar a saman jikinsa. Ji Maanal tai kamar tayi kuka dan nauyin Abah da Oum. Amma yaya zatai tunda tasan ba fasawa zai yi ba. Duk da haka sai da tai magana a sanyaye ta ce, “Bafa da yawa bane”.
Bai kulata ba, sai ƙoƙarin ɗan jajjan ƙafar kawai yake yi, sai da yay kusan na minti biyu sannan ya maida mata takalmin ya gyara mata ƙafar a cikin motar tare da rigarta ya miƙe. Da kansa ya rufe mata murfin sannan ya juya ya kalla su Oum dake kallonsu cike da jin daɗi, sai dai banda su Mamy. Dan ji tai wani irin ƙududu ya riƙe mata zuciya katamaumau. Nuratu kam ƙwalla ne suka cika mata ido ma. Hannu ya sake ɗaga ma iyayen nasa sannan ya zagaya ɗayan side ɗin da AS ya buɗe masa ya shiga ya zauna. Suma su AS sukai sallama da su Oum ɗin suka shiga motar ta fice.
Sannu a hankali Maanal ta lumshe idanunta da hawaye suka ciko. Jin suna neman zubo mata ta buɗesu tare da kai yatsarta ta ɗauke su tana kallon waje. Sarai AA na hankalce da ita, dan haka ya kai tattausan hannunsa ya kamo nata dake ajiye a kan cinyarta, saman tashi ƙafar ya dawo dashi yana mai harɗe yatsunsu waje guda. Ta gefen ido ta ɗan dubesa, ganin ba ita yake kallo ba ta shagala sosai a kallon nashi, dan harga ALLAH idan tace bai yi mata ƙyau ba ma tayi ƙarya.