Showing 99001 words to 102000 words out of 218311 words

Chapter 34 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

kamasu. Abah ya shiga yima AA faɗan miyyasa ya barta ta ɗakko azumi tunda yasan awannin zasuyi tsaho.
Cike da tausasasawa AA ya ce, “Abah ba laifina bane fa, kasanta tana da rigima”.
Baki Maanal ta tura gaba kaɗan da faɗin, “Kaima kana da ita ai”.
Dariya duk akayi, banda AA daya ɗan murmusa kaɗan yana wani kallonta ƙasan ido. Babban Yaya da Abah ma dai murmushin kawai sukayi. Hakama Oum dake fitowa. Miƙewa Nuratu tayi idannunta cike da hawaye, dan bata jin har yanzu AA yako kalleta. Oum ta tsaidata da faɗin, “A'a Nuratu ina zuwa? Ai ku wuce muje kitchen lokaci naja kada a makara yau. Muneer jeka sanarma Maman Naufal da Mamy suma dasu Haule”.
Amsawa Muneer yay yana miƙewa, su kuma ƴammatan suka shiga tashi suna nufar kitchen. Miƙewa Maanal itama tai shirin yi AA ya maidata ya zaunar batare da kowa ya lura ba, sai kuma ma dai-dai hakan Oum ta ce, “Baby banda ke kekam zauna ki huta”.
A marairaice Maanal ta ce, “Oum zan iya, zammafi ganin saurin lokacin fa”.
“A'a bazakiyi komai ba, sai dai ki zauna kina tayamu hira”.
Da sauri tace eh ta yarda. Tashi tai tabi Oum, sai AA ya koma ya zauna inda ta tashi ɗin yana amsa wayarsa da ake kira. Yanda kitchen ɗin ya cika kowa na ƙoƙarin fara aikin da aka basa sai abin ya burge Maanal. Tana matuƙar ƙaunar rayuwa family house musamman mai haɗin kai da ƙaunar juna irin haka. Sai taji tana ma Mamy addu'ar shiriya da nata halin, dan tabbas da itace babba a matsayin Oum lallai gidan nan da tuni ya tarwatse, irinsu Mamy basa iya haɗa kan iyali koda nasu kaɗai ne. Shigowar Mamyn ta katse mata tunani, cike da girmamawa ta gaisheta, amma sai Mamyn ta amsa sama-sama cike da gatse kuma ta furta, “Sai yanzu ake ganinki ƴan chaina”..
Gaban Maanal ne ya faɗi, tai saurin kallon sashen da Oum take sai taga hankalinta sam baya anan. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, dan duk wanda yaji a yanda Mamy tai maganar ALLAH sai ya tsargu, saboda kalamai ne a kaikaice amma masu tsauri. Cikin son kare kai ganin murmushin da Saheeba tayi Maanal ta ce, “Ayya Mamy yanzu nake shirin tafiya sashen ki sai Oum tace a kiraku”.
Wani kalar tsaii Mamy tayi tana kallon Maanal ɗin, ita ko tayi fuska abinta tama maida hankali kan Batool da Maimoon dake zaman gyara fruits ta shiga nuna musu yanda zasu yanka kankana a sharp mai ƙyau. Suna a haka akai kiran la'asar, Oum da Mamy suka fita salla, sai Oum tace suma su rabu biyu idan sun dawo sai wasu suje. Maanal da taga ba aikin komai take ba sai itama ta miƙe kawai. Lokacin suma mazan sun fice sallar, daga can zasu zauna jin tafsir ne. Kowa yana dawowa daga salla aiki ya ɗora, zuwa shida an fara fidda komai waje, Maanal dai tuni ta dawo falo dan ƙamshin abincin sai suka fara hawa mata kai, ga ƙarfin jikinta ya sake raunana matuƙa har tana neman fara galabaita dauriyace kawai dan karta tayarma kowa hankali yasa ta dake. Amma duk wanda ya kalla idonta da yay zuru-zuru zai fahimci ƙarfinta ya fara ƙarewa. Aiko da ƙyar ta iya tashi tai alwala kamar kowa duk suka koma waje inda aka shirya abincin da wajen salla. Tana daga kwance aka kira salla, kowa ya fara ƙoƙarin cin dabino ita ruwa ta ɗauka mai sanyi sosai ta shiga sha. Saida ta shanye roba ɗaya tas, ta sake ɗaukar wata ta ɗora, ta sha rabi Najma ta amshe tana faɗin, “Easy mana Aunty Maanal”.
Komawa tai ta kwanta tana lumshe idanun da sauke numfashi. Ta jima a haka kafin tai dauriyar tashi yin sallar itama, tana idarwa ta sake komawa ta kwanta. A haka su AA suka shigo suka sameta. Sosai hankalinsa a kanta yake, dan shi kansa a jigace yake balle ita, amma ganin Oum na ƙoƙarin kamata ta tashi ta jinginata a jikinta sai ya sauke ajiyar zuciya ya ɗauke kansa. Kaɗan taci abincin tace ta ƙoshi, Oum zata cigaba da lallashinta Abah yace ta barta haka kawai.
Kwance Maanal takai har sai da aka fara shirin fita salla ta ɗan ƙarfafa kanta, Oum taso ta zauna gida ta huta amma tace zata iya. Haka suka fice hankalin AA a rarrabe. Ana idar da sallar isha'i dole Maanal ta haƙura, dan jiri ma take gani, ga abincin da taci sai juya mata yake kamar zata amayoshi. Ana idar da wutri itace farkon miƙewa. Oum ta bita da kallo, sai kuma ta miƙe ganin kamar Maanal ɗin na layi. Alhamdullah Maimoon na kusa da ita da sauri ta riƙeta.
Cikin rawar murya Maanal ta ce, “Maimoon muje gida amai nake ji”. Babu musu Maimoon ta riƙota sukayo gaba. Sune farkon shigowa gidan. Sai Oum da tun fitowarsu ta biyosu, sai akai sa'a RK da AA sun fito suma suke tambayar Oum ɗin lafiya dan ganinta a ruɗe. Sama-sama ta ce, “Baby! Ina ga bata jin daɗi”. Kowa yasan wa take cema Baby, dan haka suka rufa mata baya, AA da kansa shima ke ciwo jiyake kamar ya rufe idanu ya gansa a gaban Maanal. Aiko shigowarsu gidan dai-dai da fara aman Maanal. Dan da wani irin ƙarfi ta fisge jikinta ana Maimoon tai wajen fanfo da akema flowers barruwa jikinta sai rawa yake ta fara aman. Su duka can sukayi kanta, yayinda Maimoon data bita ta riga su isa tana riƙe da ita. Ina AA na zuwa baima san ya janye Maimoon ba ya riƙo Maanal a jikinsa. Ganin yanda take yunƙuri sai kawai ya rungumeta ta cigaba da yi a jikinsa. Aman ma duk ruwa ne tunda ba wani abincin kirki taci ba. A wannan halin su Mamy suka shigo suka samesu. Dukansu sai sukai mutuwar tsaye ganin yanda AA ke rungume da Maanal tana amai a jikinsa. Zuciyar Mamy na rawa tace, “Ciki? Ciki Ajwaad yay ma yarinyar nan?”.
Wannan furuci nata ƙasa-ƙasa karaf sai a kunnen Nuratu, a wani irin rikice ta ce, “Ciki kuma? Na shiga uku na”. A bayyane tayi tata maganar ita, dan haka ta shiga kunnen kowa harda Abah dasu Oum. Hatta AA ɗin ma yaji, amma da yake hankalinsa na kan Maanal ne bai kula ba. Nibras kam jitai kamar zata sume a wajen. Ajwaad ɗinta ne yama wata ciki! Kai ita kam ai itace ta shiga uku ba Nuratu ba. Saheeba ce ta kama hannun Nuratu ta damƙe domin maidota hankalinta....
Maanal dai data gama yin lagab idannunta na lumshewa ta kwantar da kanta a ƙirjin AA dake rungume da ita. Bawan ALLAH idanunsa sun kaɗa sosai damuwa ta bayyana matuƙa a fuskarsa. Kan nata ya dafe da hannunsa yana shafawa, sai kuma a hankali cike da raɗa dan babu wanda zaice a wajen yaji mi yake faɗa ya ce, “Sannu. Kin gama?”.
Luuuu Maanal ɗin ta buɗe idannunta ta ɗan kallesa, sai kuma ta maida ta lumshe a hankali. Abah ne ya matso inda suken cike da kulawa yana mata sannu, sai kuma yace, “Ajwaad ɗagata a damshin ruwan nan kuje ciki ka gyara mata jiki kaima ka gyara naka sai Rafeeq ya duba ta?”.
Kai kawai AA ɗin ya jinjina. Sai kuma ya miƙe ɗauke da ita camak abinka da dogon mutum da ya wadatu da ƙarfin jiki. Duk da kallo suka bishi, su Maimoon kuma suka shiga gyara wajen. Kansa tsaye sashen Oum ya nufa da ita, Oum na bayansu hakama Abah, can ɗin kuma kowa ya nufa dan Maanal ta basu tausayi, sai RK ne ya shiga mota yana faɗin bara yaje ya ɗakko kayan aiki. Ya Fawzan ne ya bisa domin masa rakkiya........✍️






*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣9️⃣




______________




........AA bai dire Maanal ko ina ba sai bedroom ɗin Oum, yana riƙe da ita ya daidaita ɗumin ruwan sannan ya buɗe shower kawai tana sauka a kansu. A tare suka saki ajiyar zuciya, ita kuma ya sake lafe masa a jiki dan bata cika son ruwa na sauka mata haka a jiki ba shima ya sani tun suna yara. Sai da ruwan ya dakesu da ƙyau sannan AA ya zaunar da ita cikin jacuzzi a hankali. Hular kanta ya fara zamewa, gashin ya jike shima jalab dan Oum ce tace ya saka mata ruwa sosai a cikin kai amma na ɗumi, shiyyasa ma ya tsaya a ƙarƙashin shower ɗin dan yasan bata son ruwa na zuba mata haka a saman kai. Idanunta a rufe suke, amma tana jin yanda yake warware mata gashi daga cikin ribbons ɗin data saka. Saukar hannunsa a saman ƙirjinta kasancewar rigar a manne take da jikin saboda jiƙar ruwa ta sata buɗe ido da sauri, bawan ALLAH ba abinta take tunani yake yi ba, botiran rigarta yake cirewa. Dai-dai ya kama wanda ke a saitin inda bata son a gani ɗin takai nata hannun cike da kasala da rashin ƙarfin jiki ta dafe hannunsa, dan waccan ranar ce ta shiga dawo mata a Chaina. Sai a lokacin ya ɗago shanyayyun idanunsa ya zuba mata. Baki ta taɓe kamar zatai kuka, sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Ni dai ka bari zan cire, kaje waje”.
Hannunsa ɗaya ya shiga janyewa kamar wanda yaji maganarta, harta fara murna a mamakinta sai gani tai ya cire hannun nata ne a wajen ya riƙe da ɗayan hannun nasa ya cigaba da cire maɓallin da ɗayan. Ya ILAHI, Maanal taji kamar tai ihu dan kunya, ga ciyo jitake kamar zata faɗi, amma bawan ALLAHn nan brozan su o'e ko'a jikinsa ya sauke su tsaf sannan ya saki hannun nata ya maida saman kafarta, ita tana ƙoƙarin rufe ƙirjin duk da akwai b a ciki shi kuma ya zame rigar gaba ɗaya ya sauketa ƙasa, ai sai kawai ta kife jikinta kan ƙafafunta tsabar kunya. Bai wani nuna ya damu ba ya shiga ɓalle hook ɗik b ɗinta shima. Ya ARRAHAMAN da sauri nan ma ta ɗago. Hakan ya bashi damar zame b ɗin itama. Bai kula yanda ta saka hannu ta rufe ƙirjin ba gaba ɗaya tama ƙi barin b ɗin ta fita duka. Tasa rigar ya miƙe ya zame, ya shiga zame wandon shima, dai-dai lokacin Maanal ta ɗan leƙo kanta a tunaninta ya ƙyaletane sai taga abinda yake yi.
“Innalillahi... Ajwaad kaga mi kake yi kuwa?”.
Ta faɗa muryarta na rawa, tana kuma sake maida kanta ta kife. Sai da ya kammala tsaf yabar boxer kawai sannan ya sake duƙowa gabanta, a cikin kunnenta ya raɗa ma, “A'a Aunty Maanal ban gani ba”. Daga haka ya ɗagata camak ya miƙe tsaye, kafin tai wani yunƙuri ya ƙara sakar musu ruwan shower ɗin ta yanda ta kasa magana. Ta kuma rikice saboda saukar ruwan ta saki hannunta dake rufe da ƙirjinta tana ƙoƙarin rufe fuskarta. To shifa bawan ALLAH AA dama ta samu, kallo-kallo ƙyauta daga ALLAH....


Tabbas badan halin da take ciki ba, ga kuma su Oum yasan duk zaman jiran fitowarsu suke, da yau babu abinda zai hanashi yin abinda ransa yaso. Tunda ga abinda ake hanasa gani da ɓoye masa available. Amma ba komai, idan kere na yazo zabo na yawo ai ya tabbatar za'a haɗe wataran. Maanal kam tunda ta fahimci abinda ke faruwa ta shige jikinsa kawai ta rungumesa duk dan hanasa kallar mata jiki. Hawaye kam sun cika mata idanu. Ga jikin nata babu karfi kona sisi. Da ƙyar ta yarda ya saka mata bathroom, ƙasan zuciyarsa kuma yana tunanin shi ya zai yi da kaya suna a ɗakin Oum ne fa. Karo na farko yaji wata kunya mai girma ya baibayesa, kai ya ilahi shine dayin wanka yau a bayin Oum tare da Mace. Rashin makama ya sashi jan towel ya ɗaura ya ɗakkota suka fito, dan ya tabbatar kowa babu a ɗakin. Aiko babu kowan, sai kayansa da ya gani a saman gado an ajiye. Ajiyar zuciya ya sauke, yasan Babban Yaya ko Ya Fawzan ne da wannan aikin. Bai ɓata lokaci ba ya shirya, itama ganin tana rawar sanyi duk da ruwan zafi ya saka musu sai yay saurin duba mata kaya ya saka masa masu kauri. Dai-dai nan akai knocking, sai kawai ya bada izinin shigowa. Oum ce sai RK biye da ita. Kawai sai ga Mamy ma ta shigo. Aiko dai-dai AA na maida hankali ga RK dake masa magana idonsa ya shiga cikin na Mamy, wani mummunan kallo kuwa ta zuba masa mai kaɗa hanji, haka kawai sai abin ma shi ya bashi dariya. Amma dai baiyi ba ya ɗauke idanun nasa tare da kaiwa zaune kusa da Maanal dan RK yace ya zauna ne ya mata komai da kansa. Oum ma na zaune ne ta ɗaura kan Maanal a cinyarta.
Komai AA ya mata, RK na nuna masa yanda zai yi. Batare da damuwa ba RK ke faɗin, “Ka saka mata iya drip ɗin nan kawai da zai tsaida aman ta kuma samu ƙwarin jikinta. Dan bai kamata tasha kowanne magani ba ko makamancin hakan saboda kar ai ɓarna har sai zuwa safiya anyi gwajin ciki sannan”.
Juyowa AA yay yana kallon RK, shima da yake kallonsa yake sai ya ɗaga masa gira. Ƴar harararsa AA ɗin yayi, shiko ya sanya ƴar dariyar mugunta, ba kuma dan kowa yayita ba sai Mamy, saboda yaga kallon data jefama AA sanda ta shigo. Sannan duk da shi ba likita bane fannin mata yasan babu wani ciki da Maanal keda galabaitar dogon azumin da sukayi ne dana wahalar tafiya, kuma sai ana kai azumin tasha ruwan sanyi maimakon na zafi, ta kuma sha shi da yawa sosai...
Tsaf AA ya ɗaura mata ruwan, atake kuwa barci yay awan gaba da ita. RK yace a cire towel ɗin da aka naɗe mata kai da shi a busar mata da shi saboda mura. Daga haka ya fita a ɗakin. Su Abah ne da Babban Yaya da Ya Fawzan da sauran matasan yaran suka fara shigowa suka dubata. Ganin tana barci sai suka fita. Suma matan suka shigo, dai-dai lokacin AA ke amsar hand-dryer a hannun Oum yana faɗin ta barshi yayi sunje suci abinci tunda ta samu barci. Oum bata musa ta bashi, haka ya zauna abinsa batare da tuna akwai Mamy a ɗakin ba, balle matan yayunsa da ƙannensa ya ɗaura kan Maanal a cinyarsa ya fara busar mata da gashin a nutse tamkar ba shi ba. Ai sagade Saheeba da sauran sukai suna kallon ikon ALLAH. Zuciyar Nibras kam tamkar zata fashe dan bugun da take yi. Nuratu kuwa ji take kamar ta je ta daɓama Maanal dake barci wuƙa a ƙirji. Suko su Najma abin birgesu yay, Yaya AA sarkin ɗaure fuska da bayama kowa magana ne yau yake busar ma da mace kai. Tab ɗin abin dole ya zama mai ƙayatarwa. Yako zama ɗin, dan sunji sunama kansu addu'ar samun irin hakan daga mazajensu. A haka Oum ta kaɗo kansu duka suka fito domin cin abinci bisa umarnin Abah daya leƙo.
Gaba ɗaya Mamy jitake juwa na ɗibarta, dan haka batai zaman cin abincin ba tace zataje ta ɗan watsa ruwa tukunna. Oum zatai magana Abah ya wani riƙe mata hannu ta yanda duk yaran bazasu gani ba. Da mamaki ta kallesa, sai kawai ya wayance ya ce, “Zarah na kodai mun kusa ganin jinin autanki ne?”.
Murmushi Oum ɗin tayi, cikin raɗa ta ce, “Haka nake fata Gadanga. Shiyyasa ƙaninka yace baza'a bata komai ba sai anyi gwaji an tabbatar”.
Murmushi mai faɗi Abah yayi. Ya sake ɗan matsa mata hannu. Tana ganin Babban Yaya ya juyi zaiyi magana ta zame hannun nata da sauri. Mamy data kasa tafiya tana kallon komai sai hawaye suka wani gangaro mata zuuuu-zuuuu. Wai ita kam yaya zatai da Fateema a rayuwarta ne? Ga kuma wani bala'in da bata taɓa tunanin tsintarsa anan kusa ba saboda yanda tasan Ajwaad na mata biyayya, amma sai gashi yaje ya kwanta da yarinyar nan harda ciki.....
Tana shiga bedroom ɗinta ta zube a gado ta fashe da kuka kaikace mutuwa akayi mata, dan wlhy ta jima a rayuwarta bataji abinda ya nema fasa mata ƙirji a lokaci guda ba irin wannan al'amarin. In har Maanal ciki ne da ita, kuma cikin na Ajwaad ai Oum ta gama cinta wasa a wannan gaɓar, ita kuma abinda bazata yarda da shi ba kenan, dan haka ta rantse da ALLAH sai cikin nan ya zama JINI mai gudana a saman tiales ɗin banɗakin Fateema. Da wannan alwashin ta ɗauka waya tai kiran number Maman Saheeba. Tsaf ta zayyane mata komai, ita kanta Maman Saheeba ɗin sai da zuciyata ta sake wani girgizar tashin hankali, dan dama Nuratu ta kirata tana kuka take faɗa mata, sai dai bata fahimci komai ba saboda kukan da Nuratu ɗin ke yi. Ta kuma kira Saheeba bata ɗaga ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login