Showing 108001 words to 111000 words out of 218311 words
Chapter 37 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣3️⃣
______________
.........Yau daya kasance cikar kwanaki uku tana zaune shiru abin duniya ya isheta. Kiran Amrah ne ya shigo mata. Tai shiru tana kallon wayar kamar mai tsoron ɗauka. Har kiran ya katse sai ga na Basira. Shima bata ɗaga ɗin ba ya tsinke, kamar haɗin baki Nusaiba ma ta kira, yanzu kam zuciyarta sai da ta jijjiga. Hannunta na rawa ta ɗauka wayar takai kunneta bayan ta ɗaga. Kukan Nusaiba ya daki cikin kunenta sai da ta runtse ido. Kafin ma tayi magana Nusaiban ta fara mata bayani cikin kuka.
“Mammah dan ALLAH ki dawo, Yaya Yazeed zai kashe Aunty Nasiba. Gata can ya rufeta a ɗaki sai duka yake wai ta zagi Nazeefa. Gashi su Daddy basa gida sai mu kaɗai”.
Wani irin rawa jikin Hajiya Yaya ya shiga yi, ai bama tasan ta miƙe ta figi hijjab ba tai waje. A ɗimauce ta fice a ƙafa daga gidan cikin sa'a ta samu napep zai wuce ƙofar gida ya ajiye wasu ta shige tana faɗa masa inda zai kaita. Yanda ta azalzala masa gudu ya dinga zubawa bana wasa ba, cikin ƙanƙanin lokaci suka iso ƙofar gidan Chalawa. Sai lokacin ta fahimci ma babu kuɗi a jikinta. Mai napep daya fahimci hankalinta a tashe yake sai yace taje kawai ya zata mutuwa ce, dan duk wanda yaga Hajiya Yaya kam yasan babu lafiya, sannan gidan Chalawa ba ɓoyayyen gida bane, Napep ɗin ma sai suyi ƙyauta da su balle kuɗin hawanta. Burum ta buɗe kofar gate ta shige, maigadi daya zabura yana ganin itace ta shiga ya sauke ajiyar zuciya. Dan shima hankalinsa a tashe yake da irin dukan da Yazeed kema Nasiba tun daga sashensa har sashen Hajiya Yaya. Yarinyar kam yau ta daku sosai, koma yace sun daku, dan daga ƙarshe haɗawa yay har sauran yaran ya cigaba da jibga. Sai yanzu ne babu jimawa ya fito yana huci ya shige sashensa kaman wani bahagon zaki...
Wani irin bugawa kan Hajiya Yaya ya kusan yi lokacin data shiga sashenta ta samu yaranta kwance a ƙasa kowa na kuka jikinsu duk sayin bulala Nasiba kam ma harda jini a goshinta da bakinta. Suna ganinta suka taso a guje suna kuka da nuna mata jikinsu. Jagwab Hajiya Yaya takai zaune a kujera, wani irin jiri-jiri take gani ma ita kam. Tafi minti biyu kafin da ƙyar ta iya furta, “Mi kukai masa?”.
Cikin kuka Nusaiba tace, “Wlhy babu komai Mammah. Daga Nasiba taje sashen kiranshi dan muna son muyi magana da shi akan tunda ya dawo bai ko kallemu ba mi mukai masa, sannan kema baije inda kike ba, shine kawai ya hau jibgar Nasiba tun daga can wai dammi zatazo tace yazo muna nemansa shi sa'anmu ne.”
Zuciyar Hajiya Yaya har kumfa take, ta ce, “Ina Daddyn ku?”.
“Sun fita shi da matar can”.
Cewar Umaimah......
Hajiya Yaya yanzu fa za'a fara wasan🤣😜🏃
________★
Yau kam dai zaman buɗa baki bazai yiwu a tsakar gidan ba. Dan wani irin hadari ne mai nuna alamar cike yake da iska ya harɗe garin na Abuja musamman ta yankin su AA tunda nan ɗin suke gani. Dole anan sashen Oum aka gyara falo aka shirya komai. Sannan kowa ya fara ƙoƙarin zuwa yay alwala harma da masu son yin wanka dan ƴan mintuna ya rage a kira salla. Yau su kaɗai sukai aiki babu Mamy, tana sashenta wai kanta ke ciwo. Oum dai taje ta mata sannu tare da Maanal. Suma sauran yaran duk sunje. An dawo domin zaman buɗa baki mazan suma sun shigo kamar jira aka fara iska. A kuma dai-dai lokacin Maanal ta fito hannunta ɗauke da bowl da aka saka akan tray an juyo farfesun naman kai a ciki. Ga naman da zafinsa, gashi a kwanon glass. Wani irin murmushin mugunta Nuratu dake bayanta ta saki saboda abinda take shirya ma zuciyarta. Maanal na daga ƙafarta data rage a cikin kitchen ɗin ɗaya na a waje zata ƙarasa fita kawai Nurry ta take takalmin, gaba ɗaya Maanal ta tafi ita da tray ɗin aiko ta fasa ƙarar tsorata tana ambaton sunan ALLAH da runtse idannunta dan ta gama fidda rai kawai sai taje ƙasa kuma sai ta ƙone maybe ma harda raunuka....
Sai dai kuma mi, cikin ikon ALLAH da rahamarsa taji ta tsaya cak ita bata kife ba tray ɗin na a hannunta. Sai dai yanda jikin nata ke rawa romon farfesun ya hankaɗa mata akan hannun. Babban Yaya daya iso wajen cikin zafin nama ne ya amshe tray ɗin, shi kuma AA daya riƙeta ya ɗagota gaba ɗaya ya saka a jikinsa dan jikinta wani irin rawa take na tsorata tama ƙi buɗe idanun sai hawaye dake rige-rigen sakkowa.
Tuni kowa ya miƙe cirko-cirko an zagayesu. Muryar Abah cike da damuwa ya ce, “Amma ya akai ma ta fito haka kamar wadda aka hankaɗo?”.
“Nima dai abinda zance kenan Aban su, yanda ta taho gaba ɗaya sai kace an hankaɗota ai”. Cewar Oum itama. Caraf Menoo dake kitchen ɗin ta fito tana faɗin, “Aunty Nuratu ce ta taka mata takalmi, kuma tana sane dan sai da tayi dariya ma sannan. Dama tunda ta shigo muna kwashe naman ni da Aunty Maanal sai take faɗin__“Yau zatayi maganin rashin kunyar wata mayyar namiji da cikin jikinta na asiri a gidan nan”___ mu bamu kulata ba Aunty ta gama zubawa tace na ɗakko mata cornflakes a store shi zata sha, na fito sai naga Aunty Nuratun a bayanta ta taka mata takalmi”.
Gaban Nuratu dake maƙale a kitchen ya faɗi, jitai kamar ta jawo yarinyar taita jibga, shegiya ƴar ƙarama da ita sai bakin magana, jin falon yay shiru tai saurin juyawa zatabi back door, amma a mamakin kowa cikin wata irin tsawa AA ya furta, “Idan kika fita sai na baki mamaki yau a gidan nan!!”.
Sosai tsawar tasa ta saka yaran nan razana, kowa ya ƙara maƙalewa jikin ɗan uwansa. Manyan kuwa a tsorace sosai suke kallon AA ɗin dan sun san halinsa sarai, asu yaran family ɗin idan suna gulmar yayun nasu sukan ce kaji tsoron ALLAH kaji tsoron marin Yaya AA, dan marin tsoffin sojoji yake yi. Abah zai yi magana ya Fawzan da yaga inda AA ke kallo sai ya leƙa kitchen ɗin, Nuratu data tsaya cak saboda tsawar AA har fitsari ta nema sakata shima cikin ɓacin rai ya furta, “Oh dama kina a kitchen ɗin. To fito nan”.
Ganin yanda Yaya Fawzan yay da fuska ya sake saka gaban Nuratu dukan tara-tara, cikin son nuna pretending ta haɗiye tsoron ta fito a dake. Tana buɗe baki zatai magana a bazata kawai AA ya wani ɗauke fuskarta da mari. Ya ILAHI, wani irin shiru falon yay na sakan irin kamar mutuwa ta ratsa waje ɗin nan da yara kance. Yayinda Nuratu da azaba ta ratsama fuska har zuwa cikin brain ganinta ya shuɗe na wucin gadi kunnenta ya toshe sai wani tsauuuu!!! Take ji a cikinsu like an daki irin ƙarfen nan yay ƙara a ƙarshen dai nawa yay tsaiii!! Ɗin nan. Ta wani kalar tafi taga-taga zata faɗi Mamy ta tareta. Cikin rufewar ido da ɓacin rai AA ya sake yunƙurawa zai mareta Oum ta riƙe masa hannu, dai-dai itama Mamy ta zaburo a tsawace ta kira sunansa, “Ajwaaadd!!!”.
Duk da yanda tsawar Mamy ta ratsa kunnen kowa a wajen a ɓangaren AA ko'a jikinsa. Yabar Nuratu ne kawai saboda riƙe masa hannu da Oum tayi. Ya wani irin watsama Nuratun mummunan kallo... Hannunsa Oum taja ganin zai yi magana tace, “Kaga ya isa zauna a duba mata hannunta koya ƙone”. Wani kallon banzar ya sake watsama Nuratu dake a jikin Mamy ya ɗaga Maanal dake jikinsa cak zuwa saman kujera...
Sai a lokacin Nuratu ta saki kuka. Tsaki Yaya Fawzan yayi yabar wajen zuwa inda AA ke zaune Maanal a jikinsa. Oum na gefensu zaune tana duba hannun Maanal ɗin da yay ja. RK kam tuni dama yabar wajen, inda yasan suna ajiye kit ɗinsu na magunguna ya nufa. A karo na farko Babban Yaya da ransa yay matuƙar ɓaci ya zuba ma Nuratu ido. Sai kuma ya watsa mata harara da faɗin, “Shashasha kawai mai zuciyan banza. Yanzu da ALLAH bai hankaltar da Ajwaad ɗin ba wane irin faɗuwa kike tunanin yarinyar nan zatayi? Zatafa iya rasa rayuwarta kodan abinda take ɗauke da shi tunda da akansa zata faɗi, ga zafi gashi glass. Wato shirinki zubar mata da ciki, to bismillah kada ki fasa dan ALLAH....” shima ya ƙara zabura zai kai mata marin. Hannunsa Abah ya riƙe kawai, batare da yace komai ba yaja Babban yayan suka bar wajen suma. Har lokacin Nuratu na'a jikin Mamy da ranta yay ƙololuwar ɓaci, sai Saheeba dake gefen Mamy ɗin kamar gunki. A kusa da ita Nibras ce. Suko sauran duk suna can zagaye da Maanal, tuni Hashim ya ɗakko ƙanƙara da RK yace ya kawo. A cikin bowl da Meeno ta ɗakko itama aka sanya, AA ya amsa yana saka hannun Maanal a ciki. Baiwar ALLAH idanun yanzu babu hawaye, amma sunyi jazur alamar tana jin zafi sai sauke ajiyar zuciya take jin hannun a ruwan sanyi. Sannu Abah ya mata, ta jinjina kai, hakama Babban Yaya. Ta ɗan ji zafin ya sassauta mata. Sai kuma duk suka bata tausayi ganin kowa baici komai ba sun tare a kanta. Cikin ɗan rawar murya ta kalla AA da idanunsa suka kaɗe tace, “Ya daina zafin ka barshi. Oum muje ayi buɗa baki”.
Cike da kulawa Babban Yaya yace, “Kin tabbatar ya daina?”. Kanta ta jinjina masa alamar eh. Shi dai AA bai gamsu ba. Amma da yake RK ya nuna maganin da zata sha idan taci abincin sai ya barta. Zaman cin abincin sukayi. Azaba ta ishi Maanal dauriya kawai take, gashi hannun dama. Tana tunanin ta yanda zata ci abinci sai kawai taga AA daya zauna a kusa da ita ya zuba ya juyo gareta. Cike da kulawa ya fara bata, duk da tana jin kunya haka ta daure ta dinga amsa. Bata wani ci da yawa ba tace ya isheta. Maganin ya bata ta sha, hankalin Oum dama kowa na'a kansu. Mamy ce kawai ke faman lallaɓa Nuratu taci abinci wai, amma ko sannu bataima Maanal ba. Wannan abu ya bama kowa dake wajen mamaki, sai dai babu wanda yay mata magana itama balle kula Nuratun dake kukan iskanci, fiskarta raɗam da sayin marin AA..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣4️⃣
______________
.........Har lokacin sallah Isha'i yayi ana zabga ruwa. Dan haka aka gyara daga can gefe don yin salla, dan falon ba ƙaramin falo bane ba. Babban Yaya ne yaja sallar isha'i. Bayan an idar ya miƙe ya dawo baya ya tura AA gaba. Kallonsa AA yay zai magana, Babban yaya yace, “Cmon malam yi mana salla”. Sai ya kalla Abah, daƙuwa Abah yay masa. Sai kawai AA ɗin ya murmusa. Yana ɗan kallon gefen matan idonsa ya sauka akan Maanal suka haɗa ido. Baice komai ba ya juya ya kabbara sallan. Shine yay musu asham, karatunsa na fita da wani irin daɗi mai karya zuciya, ga nutsuwa. Daga ƙarshe babban Yaya ya sake rufewa da shafa'i da wutri. Bayan an idar gaba ɗaya Aba ya tashi yay nasiha mai ratsa jiki akan abinda ya faru tsakanin Nuratu da Maanal. Ya kuma bama Nurry umarnin matsawa ta bama Maanal ɗin da AA haƙuri. Jitai ranta ya wani ƙara ɓaci, amma bata isa yin jayayya da Abah ba. Haka ta je har inda Maanal take ta bata haƙuri. A mamakin kowa murmushi Maanal ɗin ta mata tace ba komai ai tsautsayi ne ta yafe mata. AA kuwa ko kallonta baiyi ba ma. Sai da Abah yay masa magana sannan yace yaji. Daga haka yay shiru.
Gaba ɗaya sai abinda ya farun yasa zaman babu armashi. Ga ruwa ana makawa kamar da bakin ƙwarya. Dan ba'a samu tsagaitawarsa ba sai kusan sha ɗaya. Miƙewar Abah tasa kowa ma ya miƙe ya nufi nasa sashen....
____________★
KANO
Tuni Huznah ta ajiye batun azumi a gefe, dan kuwa dai ya gaggareta, kwance take rijib babu lafiya tun azumi na kwana takwas. Zuwa yanzu kuma kowa na gidan su Sageer yasan tana da ciki. Wannan abu na ƙona mata zuciya kullum sai tayi kuka. Gashi zuwa yanzu ta kasa sake samun damar kiran ko Maman Yaseerah ɗin ce ma. Dan kamar Sageer ya fahimceta sam ya daina ajiye wayar da inda take.
Ta rame sosai sai uban haske data ƙara, komai taci sai amai. Yau dai da jikin yay tsamari dole sukaje asibiti bisa ga shawarar Zubaidah da yayarta. Gado aka basu, dan Huznah ta galabaita sosai saboda amai. Maman Sageer ɗin ce da kanta take zaune da ita a asibitin. Tana son ta saci wayarta ta gwada kiran maman Yaseerah tana jin tsoro. Haka dai ta haƙura. Sai da tai kwana biyu aka sallamosu. Mama tace zata wuce da ita can gidansu ta ɗan ƙara murmurewa Sageer yaƙi. Ita ko Huznah harda kukanta dan taso ayi hakan ta samu ƙafar guduwa. Amma mutumin nan yay ƙememe yaƙi aminta da wannan batu. Yadai yarda Khadijah ta koma can ta zauna tana taimaka mata. Hakan kuwa akai, suka koma tare da Khadijah gidansu.
Zaman Khadijah baya hana Sageer kasancewa da Huznah duk da dai ba kamar da ba, ga rashin jin daɗi jiki, ga fitinarsa, ga tsanar datai masa. Kullum itace mafarkin AA. Ta gwada amsar wayar Khadijah ta kira number AA amma ba'a ɗagawa, ta mamanta ma bata samu har yanzu. Da Maman Yaseerah kawai take ɗan samu tayi waya. Itako tanata ɗaurata akan shawarwari. Kuma Huznah ɗin na hawa a kansu yanda ya kamata.
Ranar cikin sa'a Sageer ya kamata tana waya da Maman Yaseerah. Bai ce mata komai ba bai kuma nuna mata yaji ba. Washe gari ya amshe wayar Khadijah gaba ɗaya suka koma ɗaya da Huznahr. Wannan abu ya bama Khadijah haushi ta gudu gida. Da yay mata magana tace bata da lafiya. Dama shi haka yake so, dan zamanta a gidan na ɗan takurashi hutawa yanda ya kamata tunda da rana babu dama ana azumi. Kwananta biyu da komawa ya bata wayarta. Aiko data fahimci haka sai ta sake langarewa taƙi takoma Huznah aka koma ƴar gidan jiya. Ga laulayi ga fitinar uban ciki........
___________★
Alhamdullah hannun Maanal bai tashi ba, sai dai wajen yayi ja sosai amma tace bata jin zafi. Haka suka shirya suka fita tafsir, amma banda Mamy, Nuratu, Saheeba. Hakan ya bama Oum mamaki, sai dai batace komai ba a tunaninta ko zasu biyosu a baya. Amma har sukaje suka dawo shiru. Oho su yaran ko'a jikinsu, dan suna ma ajiye hijjabai can inda swimming pool yake suka nufa acewarsu yafi sanyi. Oum bata hanasu ba, dan itama kwanciya tai danta ɗan huta..
Su Maanal sun zo zasu gita ta sashen Mamy Haule ta taresu tace Maanal tazo inji Mamy. Batare da wani damuwa ko kawo wani abu a rai ba Maanal ta bita, su Najma suka wuce abinsu. A falon ƙasa Maanal ta samu Mamy da Saheeba da Nuratu zaune. Batare data kallesu ba ta ƙarasa inda Mamy take, cike da girmamawa tace mata, “Mamy ina kwana”.
Banza Mamy tai mata bata amsa ba. A tunanin Maanal bata jiba ta sake maimaitawa tana ɗan ɗagowa ta kalla Mamy ɗin. Amma nan ma bata amsa ba, sai ma dariya Nuratu da Saheeba suka sanya. Kawai sai abin ya soki Manaal. Wata irin zuciya ta shiga yunƙuro mata a wuya, amma sai ta danneta da ƙyar ta ce, “Mamy gani”.
Ai batama rufe baki ba kawai taji saukar mari, kafin ta gama dawowa a hanyyacinta aka sake sauke mata wani. Cikin wata irin kaushin murya Mamy ta nuna Maanal da kanta ke a ƙasa dafe da kumatunta da duka hannu biyu. “Na farko wanda kika saka yayma Nuratu ne. Na biyu na gargaɗi ne. Wlhy! Wlhy! Daga yau idan kika sake zama sanadin da ko kallon banza Ajwaad yayma Nuratu anan gidan na rantse miki da ALLAH sai na sakashi ya miki saki uku. Banda ma jaraba da baƙin naci irin na yaron yanzu da baka isa ka tankwarashi ba mi Ajwaad zai yi da ke sauran wasu. Koda yake banga