Showing 78001 words to 81000 words out of 218311 words
Chapter 27 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
ta miƙe ta nufi inda yaken. Kusa da shi ya nuna mata, zama tayi tana satar kallon fuskarsa, batare da yay magana ba ya fara ɗibar abincin yakai bakinta. Fuska ta ɓata, shi kuma ya ɗan harareta. Dole ta buɗe baki ya fara bata, kusan lauma huɗu taga shi baici ko ɗaya ba. Sai ta dauka wani spoon ɗin itama ta fara ɗibowa cike da jin nauyi takai bakinsa. Baiyi musu ba kuwa ya amsa, sai suka cigaba da bama juna har ta fara cewa ta ƙoshi. Bai matsa mata ba shima kuma bai cigaba da ci ba, taje ta ɗakko ledar magungunansa ta dawo, duk yanda suka rubuta ya mata bayani dan da Chaines sukayi, ɗaya bayan ɗaya ta bashi yasha. Yana gamawa yace mata zai kwanta. A marairaice ta ce, “Yanzu babu yanda zamuji ƴan gida su san mun sauka lafiya?”.
Kallonta ya ɗan juyo yayi, sai kuma ya kai kwance. “Zamu kira su amma sai zuwa anjima dan su yanzu dare ne can suna gab da yin sahur”.
“Lah anga wata ne?”.
Ta faɗa fuskanta na washe wa da murmushi. Kansa ya jinjina mata murmushin nata na tasirantuwa a garesa. A cikin maƙoshi ya ce, “Na gani yanzu a net...”
“Masha ALLAH”..
Maanal ta faɗa zuciyarta na wani irin sanyi. Wannan normal ne ga dukkan musulmi, muna jin wani irin farin ciki da nishaɗi da annashuwa ta musamman a cikin jininmu a duk lokacin da watan Ramadan ya zagayo mana. Muna jin kamar mun shiga wata sabuwar duniya ne, muna jin nutsuwa da ƙarfin zuciya mai cike da harsashi. Muna jin kamar a ranar muka fara riskar watan ne. (Ya rabbi kasa muyita ganin watan Ramadan cike da yalwar rayuwa mai tsaho da lafiyar jiki da tsarkin zukata. Ka gafarta mana kurakuranmu ka amshi ayyukanmu a bisa rahamarka da yardar ka, ka gafartama iyayenmu da al'ummar Musulmi baki ɗaya da suka rigamu kwanta dama🙏😭)...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣8️⃣
______________
........A yau ɗaukacin musulman Najeriya suka tashi da azumin watan Ramadan a wasu yankuna na ciki dama sauran ƙasashen Afrika. Sai kuma wasu tsirarun ƙasashe da basu da tazarar lokaci mai yawa da ƙasan ta Nigeria. Yayinda sauran ƙasashen duniya da lokacin ɗaukar bai kai ga ƙarasa musu ba suketa shirye-shiryen hakan suma.
Anan Abuja ahalin Ambassador Aliyu Darma cike suke da farin cikin fara azumin da kuma kewar rashin jin AA da Maanal. Ga Mamy dai fargaba ce da damuwa cike fal a zuciyarta. A cikin ƴaƴan nan uku tafi kasancewar a fargabar al'amarin Ajwaad fiye da kowa. Yaro ne mai biyayya, amma kuma yana da taurin kai, sannan yana biyayya ne a gareta a iya abinda ya tabbatar bai saɓa shari'a ba. Ta wani gefe kuma tana tsoron kaidin mace, tare da masifaffiyar soyayyar da yakema yarinyar nan. Ta tabbatar zai iya mancewada wani gargaɗinta can, shiyyasa tafi kowa matsuwa da ƙagauta a jiran kiransa. Amma gashi har tsawon kwanaki biyu shiru kake ji, bayan duk inda Ajwaad yaje a tafiye-tafiyensa yana sauka baya rufa awanni biyar a ƙasar bai kirasu a waya ko video call ba. Amma a wannan karon sai gashi ba haka bane saboda ya tafi da mace. Macen ma yarinyar data tsana fiye da komai a ɗan tsakanin nan saboda ƙarfin abinda take gani a idanun ɗanta game da ita. Dan duk abinda kaga Ajwaad baya jin nauyin sakawa a gaba ya kalla a gaban kowa, baya shayin tattali da nuna kulawa a kansa, baya iya ɓoye feeling na farin ciki a kansa idan yana waje, baya iya riƙe miskilancin sa a kansa a gaban kowa. To lallai wannan abun ya kai ƙololuwar girma da daraja a garesa. Itafa yaron nan ya duba tsabar idonta ya sanar mata a yanzu Maanal nada power ɗin yin komai da dukiyarsa tunda matar sa ce, dan haka bazai iya cewa tabar kamfaninsa yin aiki ba. Tace ya faɗa mata ma'anar *MAWAAD* yaƙi, ita kuma a tsorace take da fassarawa bisa ga yanda zuciyarta ke hasaso mata. Shiyyasa take son ya faɗa da bakinsa, dan in har ya kasance hakane lallai za'a jisu da Ajwaad fiye ma da gidan nan...
Shigowa Nuratu tana cin indomie tana magana a waya ya katse ma Mamy tunaninta. Binta tai da kallo dai-dai tana miƙo mata wayar. Ganin yanda tai wani getse-tse a gabanta babu ladabi babu risinawa irin na yaro da babba sai abin ya sosa mata rai. Amma batace komai ba ta amsa, Mamansu Nuratun ce, suka gaisa ta tambayeta ya ibadar azumi da aka fara Mamy ta amsa mata. Cike da siyasa Maman Saheeba ta ce, “Yaya ƴan tafiya an sauka lafiya kuwa?”.
Sai da Mamy ta ɗan nisa kafin ta ce, “To zamu iya cewa haka, dan muma bamu jisa ba dai har yanzu bai kira ba”.
Ɗan jimm Maman Saheeba tai, sai kuma daga can tace, “Hummm ke ko Aunty ai ya tafi da mace sai abinda muka gani kam. Kefa da kanki kike sanar min yaron nan duk inda zaije baya rufa awanni zai kiraku yace ya sauka. Amma wannan karon kinji shiru ƴar iskar ta hana shi kenan, koda yake keko ai bata yar a ƙasa ba tunda nn Asiya tasha kuma rainon Fatimah ce. To ALLAH dai ya jishemu alkairi kada a dawo ana ƴan amaye-amaye, tunda ta samu dama yanzu daga ita sai shi ai bazata yarda su raba ɗaki ba, sannan duk yanda zata hillacesa ya bata abinda ta saba samu a titi ai yi zatai”.
Wani irin tiririn zafi ne ya turniƙe zuciyar Mamy, muryarta har rawa take dan fushi wajen faɗin, “Aiko dana tabbatar masa nice na ɗauka cikinsa wata tara nai wahalliyar naƙuda kuma. Ni na rasa yanda zan yi da yaron nan Nana, nafi shan wahala a ɗaukar cikinsa fiye da kowa, ki duba yayin haihuwarsa kamar bazan rayu ba jini ya ɓalle min, inaga tunda cikin Ajwaad ya kai wata biyar a jikina na daina barcin kirki har sai da na haifesa. ALLAH kuma ya ƙwalla fin sonshi a rai fiye da sauran amma sam yaron nan baya dubawa.”
“Ta ina zai duba kuwa Aunty, gashi nan yanda kika sha wahalar ɗaukar cikin nashi da haihuwa haka kike shan wahalarsa a yanzu, ai ke dai bar hatsabibin yaro kinji. Irinsu ai sune zakka a cikin ƴaƴan da ake cewa. Dan basai yaro na rashin jin shaye-shaye ko makamancin hakan yake zama zakka ba a cikin ƴaƴa. Amma koni taƙadarancin Ajwaad na ban tsoro, kuma ba komai ya kawo hakan ba sai shegiyar matar nan ta gefenki data ƙara busar masa da zuciya baya kallon kowa sai ita, baya jin maganar kowa sai ita. Ko tafiyar nan bana raba ɗayan biyu itace ta shirya musu ita tunda Yaya ya hana ƴar gwal ɗinta ta tare, kinga in akai haka ai za'a samu abinda ake so. Shima Yayan da yake a ƙarƙashin umarninta yake ya kasa duba gaskiya ya hana. Ai wlhy shi zaki takurawa ya dame su da waya da gargaɗi, idan ma ta kama kwana huɗu su dawo gida”.
Sosai maganganun Maman Saheeba ke shigar Mamy, jin abinda tace akan Abah kuma sai ta nisa, muryarta cike da damuwa tace, “Nana maganar Abansu ma a barta, kin dai san halinsa ba'a cika masa gari kamar tuwon gero yake sai yay nauyi. Tsartar jaraba ce da shi, dan halinsa kaf sune a jikin Ajwaad, sauran ƴan uwansa wasu abubuwa kawai suka ɗakko. Amma wlhy Ajwaad bai bar komai na mahaifinsu ba. Da haka cire ma batun shi na sashi a azalzala musu zai harbo jirgina ne da wuri, duk abubuwan dake faruwa badan na kasance mai takatsantsan ba da tuni ba wannan maganar akeyi ba ai. Ki dai bari muyi wani tunanin daban, sannan yanzu dakonsa nake ya kira waya na samu number ɗin komai mai sauƙi ne ai”.
Badan Maman Saheeba taso ba ta ce, “Hakane kuma Aunty. Mu barsa to ya kira a samu number ɗib sai musan hanyar kamawar. Bara naje na ɗan kwanta naji azumin farkon kamar zai ɗan yi duka”.
Ƙaramar dariya Mamy tayi, tare da faɗin, “Ke dai raguwa ce dai”. A tare yanzu sukai dariyar, Maman Saheeba tai mata sallama suka yanke wayar. Kallonta ta maida ga Nuratu, sai kuma ta ɗauke kanta tana mai girgiza kai kawai. Tunda asuba data tasheta yin sahur tace ita bazatai azumi ba jini yazo mata......
★A ɓangaren Oum kam kewar su Autanta ta isheta, amma kasancewar Najma na rage mata. Dan barcinsu ma su suka sha sai kusan sha ɗaya suka tashi. Sannan ne suka fito falo Najma ta saka musu *SUNNAH TV* sukai zaman kallon tafsir, dan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zasu fara fita nan cikin anguwar inda malam keyin na mata da safe, na maza da yamma. Sallar azhar ce ta tashe su, bayan sunyi suka ɗan kwanta, kusan ƙarfe uku Najma ta tashi ta fito saboda kiran wayarta da Fawzan yayi cewar ya dawo gida tun azhar, gashi a falon Oum tun ɗazu baiji motsinsu ba. Koda ta fito ta gaisheshi zama tayi suna kallon tafsir, sai hira jefi-jefi da bata shafi komai ba. A haka Babban Yaya ya shigo shima, da'alama kuma ya ɗan jima da dawo gida, dama lokacin azumi basa daɗewa a wajen aiki. AA ne kawai idan bai gadama ba sai gab da shan ruwa zakaga ya shigo. Itama dai Oum fitowa tayi. Tana zama babu jimawa su Inte suna shigo dan tambayar miya kamata a rage na aiki, dan duk azumi gaba ɗaya nan sashen Oum kowa ke zuwa ai aiki, a kuma shirya komai a rumfar bunu dake can compound anan ake buɗa baki ko a tsakiyar gida, ana kammalawa su fice sallar asham anan masallacin kusa da su, inda harda AA a masu jan sallar, dan kuwa babban ɗalibi ne na imam ɗin massalacin. AA akwai ilimin addini, kuma har yanzu akan nema yake bai zauna ba. Kawai dai idan ka gansa a harkar neman kuɗi saika ɗauka bokon kawai aka sani. Amma Alhamdullah anan wajen dukansu Oum batai wasa ba a kansu, kowa kansa cike yake da ilimin addini tunda hatta babban yaya har yanzu bai daina zama gaban malamai ɗaukar karatu ba shiyyasa suke a nushe (KU SAN BOKO BA ILIMIN ADDINI TAMKAR NAMAN KAZA NE A DAFE BA'A WANKE ƘARNI BA🥱) ...
Bayan sallar la'asar badan Mamy taso ba ta tattaro su Saheeba zuwa sashen Oum. Dan cike take da jin zafin Oum ɗin. Oho ita baiwar ALLAH bama ta hankalta da yanayin Mamyn ba, kawai abinda ta kawo a ranta azumi ne dai na farko da kowa sai ya ɗanɗana kafin a saba. Su duka sun kasance a kitchen harda masu aiki. Abah da Babban Yaya da Fawzan sai Naufal suna massallaci daga Asr basu dawo ba sukai zaman jin tafsir. Abinci mai rai da motsi suka shirya ana ƴar hira sama-sama. Wajen biyar na yamma sai ga tawagar ƴan hutu daga Kano sun iso. Abah ne kawai yasan da zuwansu. Tuni fuskar Mamy ta sake tsukewa, yayinda ta Oum ta yalwatu da farin cikin ganin ƴaƴan ƴan uwanta. Domin kuwa samarin yara ne biyar, na Uncle Mahmud biyu, sai na Uncle Modibbo ɗaya da mace budurwa ɗaya, sai ɗaya na Uncle Hussain, ɗaya na Uncle Hassan. Sai sauran ƴammata uku, Autar su Nuwaira, sai biyu da suka kasance jikoki suma ta ɓangaren Abbah mahaifin su Oum. Najma ma dai sosai take a farin ciki. Tuni aka buɗe ɗakunan ƙasa na ɓangaren Oum, samarin zasu zauna nan, su dukasu kusan sa'anni ne dan duk bazasu wuce 20, 21, 22, ba, su kuma ƴammatan wasu sun girmi wasu, akwai sa'annin Najma biyu, biyun kuma bazasu wuce 15 ba. A ɗakin Najma su suka haɗe, duk da Oum tace ya musu kaɗan a sake buɗe wani ɗakin sukace a'a. Samarin kuwa biyu suka rabu. Dan sunce akwai Hashim daya rage shima yana zuwa daga Sokoto ɗan ɗan uwan Oum ne shima dai ta ɓangaren Abbah. Shine wanda su AA suka taɓa zuwa gidansa lokacin da zasu je Giro.
ALLAH yaso su Oum da yawa sukai abincin, dan dama Abah nata jaddada musu ayi abinci sosai akwai masu ci. Da suka tambayi su wanene yace sudai su ƙara kawai. Ashe yaran ne a hanya. Gida kam dai Alhmdllh, sai hakan ya sake ragema Oum kewar su Maanal duk da dai sunan manne a zuciyarta a dukkan motsinta.
Da taimakon yaran aka shinfiɗa manyan carpet da dama ana tanadarsu ne dan irin wannan lokacin ne kawai. A compound aka baza su, sannan aka shiga fitar da nau'o'in abinci da suka shirya abinka da mutane da yawa. Dandanan wajen yay ƙyau daka kalla kasan a lallai Ramadan ya kama. Yaran sunata ɗauka a waya abinka da ƴan ɗore-ɗoren social media. Da farko Nuratu nata ɗauke-ɗauken kai, sai dai fa tasha jinin jikinta dan ita kanta tasan yaran a goge suke da ilimi sannan gidan iyayensu akwai kuɗi suma, dan sanin kanta ne ALLAH yayma zuri'ar Darma arziƙi tun na tushe daga iyaye. Hakama family ɗin su Oum ta ɓangaren Abbah, K. Kura yana ɗaya daga cikin manyan likitoci a ƙasar Najeriya ga shi kuma ɗan kasuwa, mahaifinsa shima dai ya tara ya bar musu. Abinda ya sosa mata zuciya yanda yaran suka wani watsar da ita amma su kansu a haɗe dan kamar su cinye Najma, haka ma sun janye Anum a cikinsu su adole ga ƴan haɗin kan dangi. Humm tasha jin Saheeba da Mamy suna faɗin haɗin kan Darma Family da masifar son juna da suke da shi, bata tabbatar ba sai a yau ganin ƴan yaran nan yanda suke 5&6 matuƙa. Gasu a nutse babu rawar kai sam a tare da su. A haka su Abah suka shigo bayan sallar magriba, lokacin kowa yaci dabino yasha ruwa sanata yin sallar magrib. Wani irin farin ciki a bayyane kowa ya gani a fuskar Aba, Babban Yaya, Fawzan. Dan tuni yaran sun wani zagayesu. Duk rashin fara'a da yawan magana ta Babban Yaya kamar zai cinye yaran a bayyane dan so. Kai wannan abu na kona ran Mamy, har mamakin irin haɗin kan wannan family take yi.....
Abin sha'awa abin birgewa kowa ya nema wajen zama aka fara buɗa baki, maza na nan ɓangaren mata anan ɓangaren abinci a tsakkiya. Kuma duka harda masu aikin gidan ne, harda wanda bama musulman ba duk an jawosu. Wannan itace ainahin ɗabi'ar wannan gida, shiyyasa a cikin masu aikinsu mutum biyu sun taɓa musulunta a bisa jin daɗin wannan yanayin, dan haka suka kyautata rayuwarsu a yanzu haka suna zumunci da su sosai kuma suna zuwa gidan. Bayan an karya da gwargwadon abinda ya sauwaƙa marasa alwala suka tashi suka sabunta, masu ita suka kimtsa aka fice sallar asham anan masallacin dake kusa dasu dan jikin gidan su Hajiya Shuwa yake. Su kansu anan suka iske su Hajiya Shuwa suma sun fito. Massalacin upstairs ne. Ƙasa maza sama mata, kusan ƴan street ɗin duk anan suke salla, musamman da azumi cika yake tab, wani ma sai a lokacin yake tuna wanene makwafcinsa.......✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣9️⃣
______________
........A ɓangaren ƴan chaina kam a yau su kuma zasu ɗauki nasu azumin. Dan kammala yin sahur ɗin Maanal da AA kenan. Yanda ta takura masa da batun kiran ƴan Nigeria ganin da sauran lokacin kammala sahur ma balle ai batun sallar asubahi yay zaman kiransu video call dan yasan a yanzu darene an dawo sallar asham acan. Hakanne kuwa, dan shigowar su Oum ɗin kenan sun sake zama anan compound masu ƙara abinci na shiri masu hira nayi saƙo ya shigoma babban Yaya a waya. Murmushi yayi tare da miƙama Fawzan dake kusa da shi waya. Fawzan na gama karantawa ya wani kwashe da dariya. Duk kallonsa kowa yayi, baima jira kowa ya tambayesa ba ya miƙe yana faɗin, “Oum ki shirya autanki zai kira video call yanzu”.
Aiko tuni fuskar Oum ta washe da sabuwar fara'a, yayinda Mamy tai saurin duban Fawzan. Suko yaran suka shiga ɗoki zasu ga Yaya AA. Dan tunda suka iso suke tambayar yana ina. AA nada farin jiki ga yaran family ɗin, dan duk da bai sakar musu fuska indai suka ce suna buƙatar abu ko bashi suka tambaya ba in dai yaji zai yi musu abin yace wancan ya barsa. Sannan in dai sukai irin wannan zuwa hutun zakaga yana musu saye-saye na abubuwa daban-daban. Ranar salla ko zai sa a kaisu duk inda suke so koma shi ya kaisu. Nuratu kam jikinta har rawa yake, dan tunda Babban Yaya yaje ya ɗakko laptop a