Showing 141001 words to 144000 words out of 218311 words

Chapter 48 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

mu baza'a gaishemu ba Ajwaad”.
Hararrata yay ya ɗauke kai. Su Nene suka sanya dariya. Oum da itama ke dariya tace, “Gaskiya fa Shahidah ta faɗa Auta, dan yanzu babu batun ƴar gaddamar cewa bata girmeka ba matsayin yaya take dai”.
“Ni banzanyi Auntys da su ba Oum, Aunty Sakina ta isheni”. Yay maganar ƙasa-ƙasa yana hararar Amaal itama. Dariya kowa keyi, Amal ta ce, “Ni dai na haƙura ma Yaya Ajwaad basai kace min Aunty ba, dan nasan bama cewar zakai ba. Kuma nima bazan so kace ba dan kai Yayana ne”.
Oum ta ce, “Amaal yada saurin sallamawa haka”.
“Oum gara na sallama wlhy, dan kozan mutu na dawo Yaya Ajwaad bazai ce min Aunty ba kema kin sani”.
Nan ma sosai suke dariya. Shi ko ya fuske abinsa. Sai ma satar kallon Maanal yake ta ƙasan ido. Itako tayi kamar bata san ma da shigowar tashi ba, rabin fiskarta ma gyalen ya ɗan rufe. Godiya sosai AA yayma Nene, tare da alƙawarin zuwa gaisheta nan kusa in sha ALLAHU ita da su Ammie. Sosai Nene taji daɗin hakan ta kuma sake yaba AA ɗin dan tarbiyyar sa ta birgeta sosai. Leda dake a hannunsa ya miƙama Oum, yace ta basu, bai jira cewar kowa ba ya miƙe bayan Oum ta amsa ledan ta miƙama Nene tana murmushi. Amasar ledar Nene tayi tana faɗin, “Tofa mi muka samu kai ɗan nan.....”
Ta kasa ƙarasa maganar sakamakon tozali da tai da kuɗaɗe ƴan dubu bugun Abuja sabbi fil. Da wani irin sauri ta kalla Oum, sai kuma ta girgiza kai tana miƙa mata ledar. “Bazamu amsa ba ɗiyata. Ai abun ma sai ya zama rashin hankali”.
Roƙonta Oum ta shiga yi itama, amma Nene ta dage akan bazasufa amsa ba. Sai ma ta miƙe tana ficewa tunda su Amaal da Aunty Sakina anan za'a barsu su ƙarasa gyara mata gidan sai zuwa anjima kafin anguna su shigo dan ba'a barta ita kaɗai ba. Shahidah dai zata bisu saboda sai sun koma ta gidanta. Suma su Maanal ɗin fitowa sukai yi musu rakkiya, tuni AA ya haɗa motocin da zasu kaisu can gidan Shahidah su ɗauka sauran kayansu sai su kaisu train station. Haɗa ido yay da Maanal dake sharar hawaye Aunty Sakina riƙe da hannunta. Su su Aneesa nata tsokanarta wai sai sun dawo Abuja suna bata kulasu ba. Suna ma haɗa ido da AA ɗin ta risinar da idannunta ƙasa. Haka suka shishshiga mota Oum ta danƙa ledar a hannun Shahidah, zatai magana ta harareta da mata alamar tai shiru. Dole tai shirun kuwa suka wuce. Ciki su Amaal suka koma da Maanal dake kuka sosai, AA ya girgiza kai kawai ya shiga mota ya fice a gidan dan zaije wajen abokansa dake shirye-shirye tafiya suma. Wasu dama tun safe duk sun wuce sai wanda suka rage da zasubi flight ɗin yamma....


_________★


Mamy dai ciwon kai ya hanata sukuni, gashi tasha magani babu wani canji, dole Hajiya Turai ta ƙara turo musu Nurse ɗin nan ta dubata. Cikin damuwa ta ce, “Hajiya akwai matsala fa gaskiya, in dai bazaki rage wannan damuwar ba bp ɗinki fa bazai taɓa ya sauka ba. Gashi zuwa yanzu hatta bugun zuciyarki ya canja. Jininki kuwa ba'a magana wlhy, shiyyasa ma kike ganin dishi-dishi ciwon kan kuma yaƙi sauka. Dole zan sake miki allurar barci mai ƙarfi sosai dan ki samu barci, amma ki sani allurarnan barci kawai zata sanya ki, kwanciyar hankalinki shine maganin matsalar ”.
Ita dai Mamy komai tama kasa cewa, dan abun duniya ne ya taru yama zuciyarta rubdugu. Haka Nurse ta mata allurar barci. Tun tana kallonsu da saurarensu har barci yay awon gaba da ita.....


Oum bata san wainar ba ake toyawa ba, tana a tsakkiyar ƴan uwanta dan duk dai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce su kuma. Itama Oum ɗin bata kawo komai a ranta ba tunda taga Mamyn na zagaye da nata ƴan uwan ne. Duk da dai duk yau bazatace tama ga giccin Mamy ba, koda yake ko Abah ba bi take takansa ba tanata hidimarta.


★ Bayan sallar isha'i su RK da ire-irensa dake sa'oin su AA a family ɗin na Darma suka iso gidan domin masa rakkiya. A dai-dai lokacin ne su Amaal ke fitowa cikin shirin tafiya ita da aunty Sakina. Sun sake gyara ko'ina na sashen sun baza uban ƙamshin da har a compound ana jinsa masha ALLAH. Sai da suka shirya Maanal ɗin itama da taimakon Hajiya Shuwa. An mata wanka da turare iya wanka fiye da yanda ake mata shi tun fara gyaran jikin nan. Kafin Hajiya Shuwa ta naɗeta a cikin sabuwar wata lafayar ƴar ubansu mai shegen ƙyau kalar peach da ɗan fari-fari, sai uban stones saketa walƙiya a jiki, an mata kwalliya ƴar dai-dai a fuska aka sake mata turaren turare. Sai ɗauri daya zauna mata akai sannan aka rufeta da lafaya ɗin. Suka saka mata ac dai-dai misali aka zaunar da ita a tsakkiyar kadon ɗakin nan ƙasa ɗin, Hajiya Shuwa tace su barta anan idan AA ɗin yazo da kansa sai ya mata jagora Upstairs ɗin idan ƴar rakiyar tasa sun tafi. Suna jin shigowar motocin su AA suka fito dan dama su suke jira. Suka ma Maanal wayon cewa bara suje wajen Oum kafin su AA ɗin su gama. Dan tun ɗazun take roƙonsu su kwana anan, ganin zata botsare musu da kuka sukace sunji zasu kwana. Shine suka mata wannan wayon suka gudu. Dan ko sashen su Oum ɗin basu koma ba ganin can su AA suka shiga....


★Su AA sun shiga falon Oum a dai-dai lokacin da dukkan mayan matan family ɗin ke zaune zaman jiran su, dan dama ƙa'ida kenan ga duk wani angon family ɗin a lokacin masa rakkiya ɗakin amarya. Kuma abinda zai birgeka isu-isu sukema juna rakkiya ba abokai ba. Su duka su a ƙasan carpet suka zauna dan duk iyayene. Yayinda AA yaje gaban Oum ya zauna, cike da sanyi ya ɗaura kansa a saman gwiwoyinta ya wani lumshe idanu. Abin mamaki sai ga hawaye. Murmushi sosai Oum tai saboda jin saukar hawayen nasa a saman ƙafarta, cike da kulawa da tsantsar so irin na uwa ga ɗa ta duƙo ta leƙa fuskar tasa. Kukan kuwa yake yi da gaske, itama sai taji hawaye sun cika mata ido. Ta dai daure tasa bakin mayafinta ta share masa su. Kafin a hankali cike da kulawa ta ce, “Haba Auta na yau ai ba ranar kuka bace, ranar farin ciki ce mun mallaki Maanal na har abada in sha ALLAHU. Dan haka bana son ganin hawayen nan kaji Babyna, addu'a zamuyi mu godema UBANGIJI daya nuna mana wannan rana bayan jarabawoyin da muka tsallake Abaya. Harma mu haɗa da sadaka domin nuna farin cikin mu ga ALLAH okay”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya buɗe idonsa yana kallonta, tare da kamo hannunta ya sumbata...........✍️










*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣0️⃣




______________




........Cike da tsokana RK ya ce, “Ikon ALLAH, amarya na kuka idan za'a kaita gidan miji yau ga ango nama mamarsa kuka za'a kaisa wajen matarsa”.
Aiko sosai falon ya kacame da dariya, AA ya ɗauka fillo ya jefa masa. Cafewa RK ɗin yay yana masa gwalo. Aiko sai suma su Mama da Umma da Mamma da Gwaggo Khadijah suka shiga masa tsokana irin ta kakkanni, nan fa su Oum suka shiga karesa suma. Anyi wasa anyi raha kafin a koma nasiha da gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne ga AA ɗin, ta yanda zai zama mai haƙuri akan mace, ta yanda zai ƙyautata mata, ta yanda zai shagwaɓata ya riritata, ya sauke haƙƙokinta da ƙyautatata mata. Ya tattala soyayyarsu kullum taita ƙara danƙo a maimakon rauni da maza da yawa ke saka soyayyarsu yi saboda sakacin sauke haƙƙoƙin da suka dace akan iyalansu. Sun nuna masa muhimmancin sauƙaƙama mace saboda kasancewarmu masu rauni. Suka kuma tunasar da shi zaman aure zaman ibada ne ba zama irin na saurayi da budurwa ba, yanzu maganar ƴakin soyayya da farautarta ya ƙare. Lokacine na tabbatar da ita ta jaddadata domin ta ƙara nauyi a sikeli da danƙo fiye da sufagilu. Haƙuri da kura-kuran mata dan mu a karkace muke, wanda ya dage ko fariyyyar son ganin ya lanƙwasamu mun miƙe to ya tabbata sai dai mu karye ɓas. Dan haka ya kula yasan miya dace ga zaman auren, ya zama mai tausasawa sai yaci ribar zaman har yay nisan zangon kaiwa wasu shekarun da za'a ringa lissafi shekarun aurensu suma. Daga ƙarshe aka rufe da addu'a mai tsaho da ratsa jiki, sannan aka sallame su dan zasuje sashen Abah su masa sallama da su Babban Yaya. Kasa tashi AA yayi, har sai da Oum ta miƙe tana murmushi ta kamasa ta miƙar. Sai kawai ya rungumeta. Harga ALLAH zuciyarsa tai rauni, wai shima yau yayi aure za'a danƙashi ga matarsa ya bar Oum ɗinsa da yake manne da ita akoda yaushe, shike nan zai tashi daga saurayi ya koma magidanci. Da ƙyar su RK da jikinsu yay sanyi suma suka janyesa. Dan soyayyar Oum da yaran nan uku musamman Ajwaad na taɓa zukatan wannan Family ɗin matuƙa. Ɗagosa Oum tayi ta share masa guntun hawayen sannan ta kamo hannun Modibbo ta damƙa na AA a ciki, sai ta koma ta zauna tana riƙe hawayenta itama. Yau finally ta aurar da autanta yaranta sun gama auren fari sai kuma ga masu burin ƙarawa kamar yanda Fawzan yayi.
Da ƙyar su RK suka ja AA dake ta kallon Oum suka fita da shi. Sun wuce sashen Mamy, sai suka samu tana barci, anan ko maimakon AA ya samu faɗa da nasiha kamar a sashen Mamy sai su Maman Saheeba suka ɓige da habaice-habaice. RK ne kawai ya fahimci inda suka dosa, sauran ko basu kawo komai a ransu ba sai shi AA ɗin kansa. Dan haka baici komai ba ya miƙe yay musu sai da safe ya barsu da baƙin cikin sharesun da yay. Haka sukaita zage-zage da aibanta Oum da Maanal dama Darma Family gaba ɗaya har Maanal da danginta basu tsira ba. Sashen Abah shine na uku, daga shi sai Uncle Mahmud da Uncle Hussain da Hassan ɗinsa, anan ma nasiha mai ratsa jiki iyayen sukai masa. Tare da jadadada masa haƙƙoƙinsa na miji akan matarsa. Sai dabaru na kula da mace ta yanda aure ke ƙarko da ikon ALLAH. Daga ƙarshe akai addu'a sannan suka taso, sai sashen Babban Yaya. Sun sameshi shi kaɗai a falo zaune yana shan shayi yana kallon labarai. Kama AA yay ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Kafin ya ɗagosa yana murmushi ya riƙe masa fuska da hannaye biyu. Cike da raɗa Babban Yaya ya ce, “Finally yau Autan Oum ya mallaki Lilly na, zata maidashi babban mutum, nan da wata tara su haifa min ƙyawawan yara masu kama da su”.
Kunya sosai ta kama AA. Sai kawai ya sake rungume Babban Yaya hawaye na cika masa ido. Dariya babban yaya ya sake yi sauran na tayashi sannan ya zaunar da shi kusa da shi. Shima dai yayma AA nasiha da jadadda masa zama miji na gari a wajen Lilly. Ya rufe da addu'a mai ƙarfi. Daga nan sashen Fawzan suka nufa, shi kam sai Nibras kawai suka samu a falo. Duk tayi wani wujiga-wujiga da alama kuma leƙensu take ta window kafin su shigo. Bayan ta gaishesu cikin son danne kanta da ƙyar RK yace ta kira musu Fawzan. Tana miƙewa ma sai gashi yana sakkowa daga sama. Yana zuwa ya rungume AA, cike da raɗa yanda kowa baya ji ya ce, “Oh oh yau fa Autan Oum zai shiga daga ciki. Babu dokar Aba a kansa Lilly zata dinga masa TAWAI”.
Mintsininsa AA yayi, Yaya Fawzan ya ce, “Ouch wane muguntane wanan haka Auta?”.
Cike da shaƙiyanci AA yace, “Ƙanwarka ta koya min”.
Yanda yay maganar a fili ya sanya kowa dariya. Dan saika rantse bama shi yay zancen ba, babu wani fara'a a tare da shi. Yaya Fawzan yakai zaune yana faɗin, “Shike nan na yafe maka kaci albarkacin Lilly, zauna na maka nasiha dan bazan yarda da rashin mutuncin mijin ƙanwa ba lallasaka zanyi idan kai mata ko kallon banza eh”. Babu wanda bai dara ba yanzu ma. Kafin Fawzan yaci serious kamar ba shi ba ya fara ma AA nasiha shima, daga ƙarshe suka rufe da addu'a sannan ya sallamesu. Koda AA yace shi bazai masa rakkiyar ba? Sai Fawzan yay shiru, sai da yaga kamar AA ya ƙwaɓe fuska sannan ya miƙe yace “Muje taɓararre kawai. Yanzu dai zamu huta muma Lilly ta kwasa”.
Lokacin da suke ficewa idon Fawzan ya sauka akan Nibras dake ɓoye ƙarƙashin bene tana kuka sosai. Kansa kawai ya girgiza yay gaba hannunsa riƙe dana AA. Shima AA ɗin sarai yaga Nibras ɗin, amma ya basar kamar bai ganta ba. Sauran ko babu wanda ya lura sam..


Wani irin daddaɗan ƙamshi mai sanyaya zuciya da sauke gajiya ne ya fara musu sallama a falon, musamman ga AA daya fara shiga. Gaba ɗaya falon ya ɗauki wani irin ƙyau mai ƙayatarwa daka kallesa ka san a lallai gidan amarya kazo. Duk zama su RK sukai kowa na sauke numfashi, dan ba ƙaramin daɗi ƙamshin gidan yay musu ba. AA zai zauna Yaya Fawzan ya ce, “A'a ango tashi kaje kazo mana da amarya muna nan”.
Ɗan jimmm AA yayi, sai kuma ya miƙe dan harga ALLAH soyay daga iya nan suyi sallama su koma shi kaɗai yaje ga matarsa. Amma bazai iya ba yana jin nauyin Yaya Fawzan ɗinsa. Tsayawa yay a ƙofar ɗakin ya zubama handle ɗin ido na sakanni, dan Amaal ta tura masa text cewar Maanal ɗin na nan ƙasa. Sai kuma ya sauke numfashi a hankali sannan ya murɗa handle ɗin kamar baya so ya tura kai ciki da sallama ƙasa-ƙasa. Zuwa yanzu Maanal na kwance ne dan ta gaji da zaman, ga tsoro na shigarta haka kawai, ta kira Didi Amaal tace su dawo dan ALLAH tsoro take ji, shine tace mata ta daure na ɗan lokaci ne gasu AA ɗin nan shigowa. Tun tana kallon ƙofa harta zame ta kwanta idanunta a lumshe ta faɗa tunanin duniya da nazarce-nazarcen ruguntsumin cikinta. A wannan yanayin taji an buɗe ƙofa, kafin ma ta nema ba'asin wanene sassanyan ƙamshin turarensa ya shigo mata hanci duk da yanda nata ke tashi da wanda aka sanya ma ɗakin ma. Luff tayi kamar mai barci tana ƙoƙarin saisaita numfashinta har ta fahimci isowarsa inda take ya tsaya cak. Shiru bata buɗe idanun ba, yana daga tsaye shi kuma ya zubama ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yake gani kaɗan raunanan idanunsa. Kallon fin minti guda sannan ya wani fusrzar da iska mai nauyi sakamakon saukar idanunsa akan ƙugunta daya wani bada shep ta hanyar fidda lafaffen cikinta zuwa cikar ƙirji dana ƙugun dan lafayar mai kwantawa ce a jiki. Sannu a hankali kamar wanda baya so ya duƙo yana kai hannu ya yaye fuskarta da ƙyau, cike da raɗa ganin taƙi buɗe idanun ya furta, “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki Madam pretender”.
Baki Manaal ta ɗan cuna a karo na farko, amma still taƙi buɗe idannunta. A karo na farko yay murmushi kaɗan, sai kuma tunawa da ana jiransu yasa shi sake furzar da numfashin ya ce, “I'm sorry drama queen. Ajiye shagwaɓan muje wajen su Yaya Fawzan mu dawo duk sai ki tattaro kiyi min harta shekara 8 da suka wuce da nayi missing duk zan ɗauka a yau ɗin nan koda ina faɗuwa ina tashi ne”.
Shiru nan ma tayi, sai dai ta buɗe idannunta a hankali ta sauke a kansa, suka ɗan zubama juna ido, sai kuma ta janye nata tana tashi zaunen a nutse. Taimaka mata yay batare daya janye nasa idanun ba ya miƙar da ita, sai kawai ya sanyata a jikinsa ya rungume. “Alhamdullahi! Alhamdullahi! Alhamdullahi!” ya jera har suka uku a jere yana sauke ajiyar zuciya. Cikin raɗa ya sake faɗin, “Ya rabba nagode maka daka nuna min wannan rana, kai ne ka bani ita tun tana ƙarama, ka jarabceni da kuɓucewarta a gaɓar dana gama sakankancewa, ka dawo min da ita a lokacin dana gama sallamawa na rasata, ka bani ita a randa na gama yarda tawa rayuwar ta ƙare kenan gaba ɗaya. Yau gashi ka shigo da ita a cikin gaba ɗaya duniyata a gaɓar da nake cikin matsanancin zumuɗi, ƙagare, farin cikin kasancewar tamu. ALLAH kai mata albarka, ya rabbi ka tausasa min ita ta zame min mar'atussaliha. Ya rabbi ka ƙarfafa min ita ta zama uwar ƴaƴana jajurtacciya, ya rabbi kai mata rahama mara yanke wa, ka tsare min ita daga kowanne irin sharri na fili dana ɓoye, ka baibaiyeta da alkairinka da rahamarka, ƙasa ta zama mai koyi da Nana Khadijah, kasa ta zama mai koyi da Nana Ai'sha. Ƙasa ta zama mai koyi da Nana Hafsah. Ƙasa ta zama mai koyi da Nana Saudah, ƙasa ta zama mai koyi da Nana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login