Showing 168001 words to 171000 words out of 218311 words
Chapter 57 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
da oil a cikinsu. Sai da ya ɗan tsaya a kanta ya gama ƙare mata kallo sannan gently yakai zaune a kusa da ita. Ƙoƙarin matsawa tai da sauri, shi kuma slowly ya riƙota ya hana ta. Sai ta kauda fuska gefe. Wani lallatacen murmushi ya saki a karo na farko. Sai kuma ya ɗan leƙa fuskar tata, nan ma da sauri ta sake juyawa, ya sake leƙota ta can, sai kawai taja pillow ta ɗaura a fuskar. Yanzu kam dariya yayi mai sanyi. Sai kuma ya ɗan rufu a kanta ya janye pillow ɗin. Veil ɗin abayarta ta sake ja ta rufe fuskar. Nan ma ya sake murmusawa, tare da ɗaga veil ɗin ya shiga da fuskarsa ciki shima. Hancinsu na gogar na juna lumsassun idanunsa na kallon nata dake rufe. Sai kuma ya shiga matsar da bakinsa a hankali zuwa saitin idanunta. Iska ya shiga hura mata akan idanun. Murmushi ke son suɓuce mata amma tana danneshi da tsiya-tsiya.
Murya can ciki a yanayin raɗa ya ce, “Bazan tambayeki komai ba sai lafiyar ki Besty. Idan kina dariya, ZUCIYATA tana hutawa, farin cikin ki na mantar dani duk wani tarnaƙi da rikicin dake cikin duniyar nan. Your smile lights up my world, please let me see it again ZUCIYATA”.
A hankali Maanal ta saki murmushin da batai niyya ba. Ji AA yay kamar ana narkar masa da zuciya da wannan murmushi, dan haka ya lumshe idanunsa a wani irin hankali ya sake buɗewa a kanta. Cikin sake maida muryarsa ƙurya matuƙa ya ce, “Open your eyes dan naga hasken da nake so, ki kalla mijinki, kiga lallashi da tarin ban haƙuri dake cikin nasa idanun.”
Tamkar wadda yake control da remote nan ma ta shiga buɗe idanun sannu a hankali. Zubama juna kallo sukai irin mai ratsa zuciya da ƙashi ɗin nan ya marmasar da ɓargo. Sai idanun Maanal suka shiga tara ƙwalla. “I'm sorry! Na tuba bazan sake ba Besty, na tuba! Na tuba. Please for give me zuciyata cike take da nadama. Ki hukunta ni da kowanne irin hukunci da zai sa ki yarda shine dai-dai da abinda na aikata a daren jiya. Ki.....”
“Shhhhhiiii!!!”. Manaal ta faɗa a hankali tana ɗaura yatsarta a saman tausasan lips ɗinsa idanunsu na cikin na juna. Har yanzu fuskokinsu na cikin veil ɗin. Shirun kuwa yay yana kallonta kamar yanda itama take kallonsa da kumburarrun idannunta, sai dai cike suke da laushi da sanyin yanayi, kamar yanda nashi ke cike da lallashi da damuwar halin daya jefata a ciki, dan RK ya masa bayanin komai. Muryarta data sha kuka har yanzu take a dusashe ta sake marairaicewa kamar zata saki kukan yanzu ma ta ce. “Besty! kafin yau ina kallon kai tamkar rubutaccen littafi ne daga kundin rubutacciyar ƙaddarata, amma a yau na fahimci kai ɗin ne da kanka gaba ɗaya kundin ƙaddarar tawa. Kai tamkar wani darene da ake bege da buƙata da fatan gani a shekara ɗaya tak na cikin rayuwa.....”
Cikin narkewa AA ya ce, “Wane dare ne haka Besty na?”.
“Daren lailatul ƙadri. Shi ya kasance ɗaya tak da kowanne bawa ke fata da zalamar riska, da yin aiki tuƙuru domin samuwar kodan rabauta ne a duniya, balle ma har lahirar muna fata. To kai a tawa duniyar tamkar wannan daren ne. Da ace za'a bama mata damar zaɓen Namiji sau dubu a rayuwarsu lallai kai zan zaɓa sau biliyan cikin biliyan matsayin aboki, yaya, kuma MIJI. Daga daren jiya zuwa yau ka sauya ni gaba ɗayana da martaba da mutuncin dana gama sallamawa da samuwarsa ga irinka namiji. Dan na jima ina tsoron dare irin na jiya dana san dole zan riska in dai ina a raye koda a bigiren tilas ne, na jima ina tunanin yanda ranar farko zata kasance mai ɗaci da zafi da ƙuna a gareni koda banga canji daga mijin aurena ba, amma ka sauya min ita, ka maida min ita inuwa mai ƘAMSHI mai TSARKI. Mai TSARO. Mai DARAJA. Mai RAHAMA. Mai cikakkiyar SALAMA. Nagode Besty! Nagode da wannan ƙyauta, AJIYA A DUHU ta zame min AJIYA MAI HASKE.....”
Kuka ya ƙwace mata mai ƙarfi, ta rungumesa gaba ɗaya tanayi kamar zata shiɗe. Dan tamkar tana kukan tsahon shekaru ne dake danƙare a cikin ƙirjinta daskare. Tana a jiye da wannan kukan tamkar dama ƙirjinsa take buƙatar samu ta kwanta domin yinsa. Tana kukan da tuna rayuwar azabar da suka sha a Giro ita da ƴan uwanta da Ammie saboda wannan kalma ta fyaɗe ɗaya tak...
Kuce min me AA keyi. Bari na baku amsa, HAWAYE yake yi, KUKA yake yi shima tamkar ita, abinda a rayuwa zaka jima baka gani a cikin idanunsa ba. Duk abinda kaga ya saka Ajwaad Aliyu Abubakar Darma kuka to lallai wannan abu ya kai a kira shi mai daraja da kima. Oum kaɗai AA kema hawaye, ita kaɗai tak. Dan ko ita Maanal ɗin zata iya rantsuwar bata taɓa ganin Ajwaad na kuka ba, tun ma suna yara sai dai kaga idanunsa sun sauya launi amma ba hawaye ba. Hatta uwar data haifesa Mamy tunda yay wayo bata taɓa ganin hawayensa ba. Amma yau kuka yake, hawaye na zuba masa. Kalmomin Maanal na kekketa masa zuciya. Yana jin shine ya cancanta yay mata godiya, ya durƙusa a gabanta ya nema gafararta, ya ɗauketa ya riritata, ya goyata ya zagaya duniya da ita, ya shelantama kowa ita ɗin RAYUWARSA ce. Ta masa hallaci, zuri'arta sun musu hallaci musamman mahaifiyarta da ƴan uwanta guda biyu. Ba Maanal kaɗai yake ƙauna ba, wlhy har Ammie ƙaunarta yake irin kwatankwacin ƙaunar da ɗa kema uwa. Har Shahidah da Amaal ƙaunarsu yake irin kwatankwacin ƙaunar da yake ma Babban Yaya da Fawzan. Jinsu yake a jinin jikinsa saboda bashi da abinda a duniya zai kwatantama wannan zuri'ar da shi.
Sun jima a wannan yanayin mai taɓa zuciya. Kafin ya ɗago yana share mata hawaye. Idannunta dake rufe ta buɗe a hankali, ganin hawaye a fuskarsa shima ta wani waro nata tare da ɗaura hannunta a baki. Cikin muryarta ta kuka ta ce, “Lah kuka kake yi?”.
Dariya ta bashi dan yanda tai ɗin sosai cikin nuna shock ne. Murmushi ya saki mai faɗin gaske da har haƙwaransa na bayyana sai kuma ya kauda kansa gefe ya sharesu tas. Kafin ya juyo yana kallonta, ya ja hancinta kaɗan cike da raɗa ya ce, “Bafa kuka nake ba hawayen amarya ne suka shafeni. Kin san ita amarya ita komai nata daban yake”.
Dariya sosai ta kuɓucema Maanal. Taja hancinsa itama da faɗin, “Ai shima ango komai nasa daban yake”.
Cikin ɗan taɓe baki da waro idanu ya ce, “Uhhhyim!! Kamar mi da mi kenan?”.
Itama bakin ta ɗan taɓe kamar yanda yayin ta ce, “Bazan faɗa ba sai ka biya”.
Kafin ma ta rufe baki ya sumbaci lips ɗinta, hancinta, da idannunta ya ce, “Wannan yayi?”.
“Uhm-uhm yayi kaɗan gaskiya”.
Lips ya wani kalar ciza, yana ɗage mata gira, ita kuma ta juyar da kai tana dariya. Fuskar ya taro ya maidota, sai kawai ya manne lips ɗinsu ya fara kissing nata. A mamakinsa itama sai ta shiga bashi haɗin kai harda maida murtani. Ai ko brain ɗin AA neman tarwatsewa yayi, tuni ƴan maza suka fara ƙwacewa daga sunansu na Maza........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖8️⃣3️⃣
______________
........Maanal da itama ta lula gaba ɗaya sai da taji salon ya fara canjawa da shiga bubbuga masa baya ta maidosa a hayyacinsa. Yana sakin mata baki ta juya masa baya. Baice komai ba ya rungumeta kawai sukai shiru. Fin mintuna biyar suna a haka shiru kafin ya raɗa mata “I'm sorry” a cikin kunne. Murmushi tayi kaɗan, wani shauƙi na ɗawainiya da ita. Sai ta kawo hannu kawai ta shafi fuskarsa a haka batare data juyo ba. Hannun ya kama ya sumbata. Shima wani iri yake jinsa, Wlh ji yake tamkar zuciyarsa zata fashe, bai taɓa jin abu a ransa irin yarinyar nan ba. Idan yace zai zaman furta abinda yake ji akan Maanal da baki ɗauka za'ai ya haukace ne ma.
Kiran sallar la'asar ne ya sashi tashi zaune. Ya kamata dan ta tashi itama ta saki ƴar ƙara saboda zafin da taji. Da sauri ya maidata ya kwantar, zuciyarsa na raunana ya ce, “Miya faru?”.
Baki ta ɗan tura masa, cike da shagwaɓa tace, “Zafi fa, wajen na zafi bana iya zama”.
Sosai yaji wani irin tausayinta, dan har ƙwayoyin idanunsa sun nuna haka. A tausashe ya ce, “For give me”.
Kanta ta jinjina masa kawai, ya ɗan rungumeta a jikinsa, sai kuma ya sake raɗa mata, “In duba in gani?”.
Fuskarta ta ɗan ɓoye a ƙirjinsa ta ce, “Ina jin kunyarka fa”.
Murmushi ya ɗan yi yana cije gefen lips ɗinsa, yace, “Kunya kuma ta ƙare ai Babyn Oum, Besty Besty kuma Lillyn Yaya F da babban Yaya, sannan shalelen Abanta mai hana mijin ƴarsa matarsa”.
Dariya sosai kirarin ya sanya Maanal. Ta ja masa ɗan gashin gemunsa dake dan kaɗan dan baya barin yay tsaho tana faɗin, “Kai dai ka cika wayo ALLAH Besty”.
Dariya AA ya sanya tamkar bashi ba. Ya miƙe kawai da ita jin ana ƙoƙarin tada salla suka shige bayi. Alwala sukayo, ya sake ɗakkota ya dawo da ita. Shi da kansa ya saka musu sallaya yay musu jam'i, suna idarwa ta miƙe dan bata iya zama da ƙyau, gashi in tana tafiya ma tana jin zafi dan haka take yi a hankali. Sosai tausayinta ya cika zuciyarsa. Haka dai ya daure sukai zaman cin abinci. Gaba ɗayansu ma akan naman da akama dahuwa ta musamman suka huce haushin yunwarsu. Sai da sukaci suka ƙoshi yana faman tsokanarta tana ɓoye fuska sannan ya bata magani tasha, shima yasha nashi. Yana son zuwa ya gaida mutane yana jin kunya, gefe kuma baya son barinta ita kaɗai. Sai wajen biyar Amaal da Shahidah da Sakina suka zo gidan. Tana cikin jikinsa yana karanta musu novel Oum ta kira shi ta sanar masa ga su Shahidah tun 4 sunzo gidan zasu zo su duba Maanal. Dama ta zata zai sakko sallar la'asar ne shiyyasa. Sosai kunya ta kamashi, dan wlhy yau kunyar Oum yake ji, kai ko Yaya Fawzan saboda shegen tsokanarsa baya fatan su haɗu, dan Rafeeq sai da ya masa tas ɗazun ƙin kulashi dai yayi. To balle kuma ace Babban Yaya da Abah. Dan shi a zatonsa ma duk baƙin sun tafi zuwa yanzu......
_________★
A ɓangaren Aunty hamshaƙiya Shahidah kuwa tanata dakon dawowar Babban Yaya daya garƙame ƙofa. Amma bawan ALLAH bayan sallar azhar bai shigo gidan ba. Sai da aka idar da la'asar harma da kusan rabin awa sai gashi ya shigo da mota ashe ma fita yayi. A dai-dai lokacin kuma Ameerah ke fitowa daga sashen Mamy ita da su Shahidah sunje sun dubata. Dan sun saba da Ameera yanzu suma tunda akai kai-kawo a hidimar bikin nan tare. Tsai babban Yaya ya tsaya yana kallon Shahidah da Ameerah dake a jere tare. Su dukansu fuskokinsu da murmushi da alama magana suke yi, sai Amaal a bayansu ita da Sakina. Iska ya ɗan furzar yana mai kauda kansa daga kan Shahidah gaba ɗaya ya maida ga Ameerah. Wani shegen murmushi data sake saki sai shima ya samu kansa da sakin makamancinsa. Sai kuma ya kai hannu ya ɗan shafi sajensa ya lumshe idanunsa ya buɗe lokaci guda, a fili ya ce, “Fadeel kana lafiya kuwa?”. Dai-dai nan su Amaal suka nufi sashen Oum, ita kuma Ameerah ta nufo hanyar gate alamar gida zata wuce dan har tana magana cikin taushin mutyarta da ɗan ɗaga sauti ta ce, “Didi ina jiranku fa dan ALLAH”.
“Shahidah ta ce, “Ke dai jeki shirin tarbarmu kawai”.
Dariya Ameera keyi tana tafiya da baya da baya. Sai kawai ya buɗe motar ya fito. Ya ɗan duƙar da kansa yana saka key a aljihu kawai ya jita a jikinsa. Da sauri ta juyo, dai-dai shima ya ɗago idanunsa suka shige cikin na juna. Ido ta ɗan waro waje, sai kuma ta sake matsawa baya kanta a ƙasa ta ce, “I'm sorry Babban Yaya”.
Shiru bai amsa mata ba tsawon sakanni, sai kuma ya taka kaɗan ya ƙara matsawa gabanta. Kan Ameera dai a ƙasa zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. A bazata matuƙar bazata ya ɗan duƙo saitin kunnenta ya furta, “Ranar kin bigeni kince min sorry, yau ma haka, gobe kuma idan mun haɗu ban san miza'a min ba a ƙare da cemin sorry”.
Gaba ɗaya ji Ameerah tai kamar zata narke. Ta wani ɗago da sauri idannunta a ware ta kallesa, cike da suɓutar baki ta ce, “Lah na shiga uku....”
“Ko dai na shiga uku ni da ake ta turewa ba”.
Ya sake faɗa da wani salo mai taushi dai-dai da yanayinta yana wani ɗage mata gira sama. Ai bama tasan ta kwasa da gudu ba tai hanyar gate. Samun kansa yay da sakin dariya yana binta da kallo harta gama ficewa.
Ai a tare maigadi da Bola da drivers dake hira a gate suka saki baki da hanci suna kallon Babban Yaya. Tab ɗin babban Yaya ne da dariya. Babbar magana ɗan sanda yaga gawar soja. Maigadi yace, “Sufa miskilan mutane idan suka faɗa soyayya narkewa suke yi gana ɗaya ba sauƙi”.
Da sauri drivern AA ya ce, “Nizan baka labari dan ni nake ganin ainahin narkewa a wajen ogana da tashi tauraruwar. Eh lallai wato gidan nan bana ƴar aure-aure za'ai, sabon zubi aketa mana. Dama mun gaji da mugun halin ruɓaɓɓun nan Hajiya Saheeba da Hajiya Nibras.”
“Wlhy munfa gaji, mu ƴan jam'iyyar amare ne ALLAH yasa ayi damu”. Cewar drivern Abah.....
Dai-dai nan mai delivery yay knocking gate, tashi mai gadi yay ya leƙa. Mutumin ya gaisheshi da miƙa masa wata ƴar leda yana faɗin, “Saƙone aba Hajiya Kamila”. Sai kuma yaba mai gadi littafin hannunsa alamar ya saka hannu. Amsa yay ya saka hannun ya bashi, ya juya da ledar a hannun yay sashen Mamy yana faɗama su Bola yana zuwa...
Babban Yaya kam da bai san sunayi ba tuni ya nufi sashensa fuskarsa da murmushi, sai dai yana isowa yaga Saheeba da yara alamar shi suke jira ya gimtse fuska. A take tasha jinin jikinta. Amma sai ta dake tana masa sannu da zuwa da faɗin, “Tun ɗazun ai muke jiranka nazo naga ƙofar sashen a rufe”.
Maimakon bata amsa hannun Naufal da Anum dake masa oyoyo ya kama. Yasa key ya buɗe, yaran ya fara turawa ciki ya shiga. Saheeba zata shigo yay tsaye a ƙofar. Cikin watsa mata mummunan kallo ya ce, “Ina zaki?”.
A daburce ta ce, “Ciki mana Daddyn Naufal”.
A dake yace, “Sai dai wani cikin amma ba nan ba, ki koma can sashen Mamyn ki ci gaba da zama har sai na nemeki. Kuma ba gidan nan nace ki bari ba can nace ki zauna, dan ko nan da gate kika taka na rantse sai kinsha mamakin abinda zan miki.”
Bam ya maida ƙofarsa ya rufe kafin ma tace komai. Ai garrrrr jikin Saheeba ya shiga rawar mazari kamar an kunna vibration. Brain dinta kam neman tarwatsewa take saboda yanda kalamansa ke maimaita kansu a cikin kanta.......
____________★
KADUNA
Sosai hawaye suka ciko ma Yazeed idanu ga murmushi shimfiɗe a fuskar tasa duk a lokaci guda. Zuwa yanzu kam ya gama yarda, ya kuma sallama lallai ya rasa, ya rasa Maanal na har abadan. Dan videos na shagalin bikin yake kallo a media. A bazata Nazeefa daketa bayansa batare daya sani ba tai ƴar dariyar data sashi juyowa ya kalleta. Gimtse dariyar tayi tana mai daidaita yanayinta, sai kuma ta zagayo ta zauna a kusa da shi ta ɗora kanta a kan kafaɗarsa kamar bataga yanda ya wani sake haɗe fuska ba.
“Yaya! Ya kamata ka bani no ɗin Maanal na kirata na mata ALLAH ya sanya alkairi ko? Tunda ALLAH baiyi za'ai bikin damu ba”.
Idanunsa ya rufe zuciyarsa na masa wani irin zafi da rainin hankalinta, amma a zahiri sai baice komai ba ya ture hannunta data ɗora a saman ƙirjinsa ya miƙe gaba ɗaya ya bar mata falon. Kallo ta bishi da shi tana wani murmushi, sai dai kuma yana gama ficewa ta haɗiye murmushin, wayarta ta ɗauka ta shiga media, cikin sa'a da videos ɗin data shiga nema ta fara cin karo. Wani irin bugawa taji zuciyarta na mata da tiririn zafi ganin