Showing 198001 words to 201000 words out of 218311 words
Chapter 67 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
Amsawa tai tare da tashi zaune.
“Tashi kibi mijinki kinji, sai da safe”.
Ji Maanal tai kamar ta fashe da kuka. Amma bazata iya ma Babban Yaya musu ba. Haka ta miƙe tai musu sallama ta tafi. Babban Yaya ya bita da kallon tausayi. Dan a ransa kawai yaji cewa ga abinda takema gudun. Cike da shaƙiyanci Yaya Fawzan da baya iya shiru shi ya kai bakinsa saitin kunnen Babban Yaya ya ce, “Idan baka saita fitinannen ƙaninka ɗin nan ba watarana ma nan Lilly zata dawo gaba ɗaya dan zugeta sanyi da kaina”.
Fillo Babban Yaya ya ɗauka zai buga masa. Da gudu ya tashi ya fice yana dariya da faɗin, “Oum goodnight ”.
Oum ta ce, “ALLAH ya tashemu lafiya.”
Shima Babban Yaya miƙewa yay ya mata sallama. Oum ta amsa masa da kulawa shima, ta musu addu'a da sanya albarka.
Koda ya fito sai yaci karo da Saheeba tsaye a ƙofar sashensu tana jiransa. Tamkar bai ganta ba ya ɗauke kansa. Da sauri tasha gabansa ta durƙusa. Tare da fashewa da kuma tana roƙonsa yayi haƙuri ya yafe mata koma wane laifi ne yake ganin tayi, wlhy bazata sake ba dan ALLAH yayi haƙuri ya barta ta dawo sashenta. A daƙile ya kalleta ya watsar, sai kuma yay wucewarsa batare dako tanka mata yayi ba ya shige ciki ya maida ƙofa ya kulle...
Kuka mai tsuma zuciya da ruhi Saheeba ta saki. Wlhy ta gaji da zaman sashen Mamy bazata iya ba. Dan duk daɗin wani waje naka wajen daban ne. Ga Mamy da saka aikin tsiya. Haka zatai zaune saboda ƙafarta ba gama ƙwari tai ba taita sakata Safa da marwa tsakanin upstairs da downstairs. Wai sai tace bata gamsuwa da aikin su Haule ita tai mata da kanta, Nuratu kuwa lafkewa take ita adole bata da lafiya. Gaba ɗaya ta maidata wata ƴar aikinta ma. Ga kewar mijinta da buƙatarsa ya riga ya saba mata da fitinarsa. Ga kewar ƴaƴanta dako kallonta basayi gaba ɗaya sun koma sashen Oum ko tunawa da zamanta a gidan basayi. Ga jiya mamanta tace mata ta sanya ido akan Babban Yaya dan tasan mike faruwa tsakaninsa da ƴar Hajiya Shuwa. Wannan magana ma tafi komai ɗaga mata hankali. Dan a duniyar nan babu abinda ta tsana irin kishiya. Kai itafa ko ƙawarta akama kishiya ta daina ƙawance da ƙawar kenan. Shiyyasa ta shirya zuwa ta bashi haƙuri dan gara ta dawo kusa da mijinta in ma nesa da shi da take ne ya sashi fara kallon wasu matan. Tun ɗazun take dakon fitowarsa daga sashen Oum. Dan ita Nuratu yau taje gida amso musu wasu kayayyaki da mamansu ta aiko da su..
Ta jima a wajen tana kuka. Kafin ta tashi ta koma sashe Mamy. Ta buɗe ɗakin da take zaune ta shiga, waya ta ɗauka tai kiran Mamanta tana mata kuka ta zayyane mata komai daya faru. Ran Maman ya sake ɓaci, amma ta kwantar mata da hankali akan ta ƙyalesa indai sukai amfani da wannan kayan data turo duk wani girman kansa zai saukane. Wannan ya sake Saheeba jin sanyi a ranta, har tai shirin barci ta kwanta....
_______★
A ɓangaren Maanal kuwa koda ta shigo sashen nasu ta samu AA ya haye sama abinsa, har yama kashe wutar ko'ina sai amfani tai da fitilar wayarta. Tana shigowa bedroom ɗin yana fitowa daga bathroom, bathrobe ce a jikinsa alamar wanka yayo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan harga ALLAH yaji haushi. Itama sai ta ɗauke nata tare da ɗan murguɗa baki ta wuce closet tana ƙunƙuni. (Haka kawai sai na zauna ka kashe ni. Sam babu tausayi a al'amarin ka. Yo in haka auren yake banga abin cewa akwai daɗi ba. Tsabar jaraba sam bana son naga mun kasance mu biyu kawai a waje tunda nasan ƙarshen zancen. ALLAH in zan dawo sashen nan gabana gabana har faɗuwa yake yi. Abu dare da safiya, yammaci da rana idan kana gida ma ba hutu.....) Haka dai taketa masifarta a rai idonta har yana cika da ƙwalla. Wai a hakan ma maganin nan na sit bath da Hajiya Shuwa ta bata yana matuƙar taimaka mata ne. Koda ta fito har ya gama nashi shirin yana zaune a cikin sofa ya ɗakko laptop yana kunnawa. Gefe ɗaya takardu ne sai kwalin fresh milk da kofi. Ɗauke kanta tai tayi shirinta. Tana gamawa tai shafa'i da wutri ta haye gado ya kwanta. Idanu AA ya ɗan ɗaga ya kalleta, sai kuma ya cije lips ya cigaba da aikinsa.
Tun fa yana aikin da marmari har yaji ina bashi yiwuwa. Tattare komai yay ya ajiye, ya tashi ya kashe fitilar ɗakin ma gaba ɗaya dan dama mara haske sosai ce ke a kunne. Maanal datai barci cike da farin cikin fushin nasa dan tasan ko dai yaya ne ta samu sauƙi kawai ta farka a rikice jin ya nutsata cikin jikinsa. Muryarta na rawa ta buɗe baki zatai magana, ai bai bari a ta gama fita ba ya rufe shi ruff da nashi. Bore taso fara masa ya nuna mata ƙarfin ba ɗaya bane, wayon ma kuma ba ɗaya ba, dan sai da yasan duk hanyar da ya bi wajen lankwasar mata da jiki ta fara amsar saƙonsa. Sai da tafiya taje gaɓar tayar mata da hankali ta sanya masa kuka. Baiko saurareta ba sai da ya samu yanda yake so. Daga ƙarshe ya koma lallashinta da mata wayon daya saba. Sai ga hajjajunku an lafe a jikin AA ana sauke ajiyar zuciya.....
Na gabannin asuba kam da ya zame masa jiki kuka ta saka masa bana wasa ba, dole ya haƙura ya ƙyaleta. Koda ya fita salla kafin su dawo haka ta daure ta tashi ta hau gyaran gidan, harta sakko kitchen ta fara ƙoƙarin haɗa breakfast sai gashi ya shigo. Ƙin yarda tai ta kallesa, a haka ta gaishesa ita a dole tana fushi. Shi sai ma ta bashi dariya. Ya rungumeta yana murmushi da faɗin, “Haba Besty munyi faɗa ne wai?”.
Baki ta tura gaba, idannunta na tara ƙwalla ta ce, “Eh munyi, kuma kada ka sake kulani tunda baka tausayi na. Ni wlhy sashen Oum zan koma kafin ka kasheni.”
Sosai dariya tazoma AA wuya. Amma ya danne da ƙyar, a ransa ko ayyanawa yake (Inda ana mutuwa Besty da ba'a haifomu ba ai. Kedai kin cika raki ne kawai da tsoro. Sai kuma yanayin jikinki da sai dai nace Alhmdllh) a fili kam rungumeta yay yana lallashi, sai da tace masa ta haƙura sannan ya fara tayata sukai komai a tare, su Inte ta kira a waya suka kwashi abincin zuwa sashen Oum, dan haka take yi, a sashenta take musu breakfast gaba ɗaya, sai akai can sashen Oum, da rana kuma taje can tayi, hakama na dare. Yau da tasan zata koma aiki saita haɗama Oum harda abincin ranar ta, suma tai musu nasu ta na lunch. Tare sukai wanka suka shirya.
Kayan farko data ɗakko zata saka AA yace bai yarda ba. Shi da kansa ya zaɓo mata wanda zata saka. Data saka ɗin kuma nan ma ya haɗe fuska wai suma ɗin dai tayi ƙyau. Gudun kar ya ja musu makara ta shiga lallashinsa, da ƙyar ya haƙura suka fito.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣8️⃣
______________
.......Sashen Mamy suka fara nufa. Sosai zuciyar Mamy ta wani irin tsargawa. Dan wani irin ƙyau da nutsuwa ta gani a fuskokin yaran. Kodan hankalinta ba a kwance yake ba kwana biyun nan shiyyasa bata luran ba sai yau. Badan kar ace tayi ƙarya ba da tace idannunta kamar suna kallo mata yaron ciki a tare da Maanal. Kai ina abinda ma bazai yiwu ba kenan. Ciki fa, tabbas yarinyar nan akwai ƙaramin ciki a jikinta. Sai maganar wancan cikin ƙaryar ya faɗo mata a rai, a take taga wautarta a wancan lokacin, to yama akai ta zurma da wuri daga ganin yarinyar na amai, yanzu kam gashi babu wani signing na ciwo a tare da ita amma wlhy gaba ɗaya alamomin yarinyar ya mata na mai ciki.....
Gaisuwar da suke mata ta katse mata tunaninta. Da ƙyar ta iya amsawa tana tsare AA da shima yay mata wani fresh da shi da ido. Yaron ya ƙara ƙyau da cikar kamala harda ƙiba. Kaida ka ganshi kasan hankalinsa a kwance yake, yana kuma hutawa da kwasar ganima a jikin mace dai-dai gwargwado. A lallai babbar magana. Ina hankalinta ya tafi har haka ita kuwa. Bata da amsar hakan, dan a yanzun ma dai hankalin nata baya a tare da ita har AA da Maanal ɗin suka fice abinsu. Sai Saheeba da itama jikinta ke mazarin abinda ta hango a tattare da Maanal ɗin ta maidota hankalinta ta hanyar faɗin,
“Kai amma yarinyar nan fa wlhy kamar mai yaron ciki”.
“Taratsatsatsa!!!!!!”. Kake jin sautin tarwatsewar abu a ƙasa. Ba komai bane face kofin shayi da Nuratu ta fito da shi a hannu daga kitchen. Dan ƙamshin turaren AA da tajiyo ne ya sata fitowa da sauri sai furicin Saheeba a kunneta babu kuma AA a falon. Muryarta na rawa ta ce, “Ciki kuma! A jikin wa?”.
Saheeba ta ce, “A jikin wa kuwa in ba tsinanniyar yarinyar nan ba Maanal. Wlhy ko rantsuwa nayi babu kaffara wannan yarinyar ciki ne da ita ko Mamy?”.
Mamy bata iya ta bama Saheeba amsa ba Nuratu dake hawaye ta ce, “Kenan da gaske wancan cikin bana gaskiya bane yarinyar nan is a virgin?”.
Saheeba tace, “Tabbas wancan lokaci mun ruɗa kammu ne kawai yanzu ne yarinyar nan ke ɗauke da ciki na gaske. Maganar budurwa ce kuwa dole shima mu bincika dan akwai ƙamshin gaskiya”.
Saheeba ke bayanin amma zuciyar Mamy ce ke duka da ƙarfi, jikin Nuratu kuwa na rawa.....
★★★
Su AA da basu san suna yi ba kuwa tuni sun isa sashen Oum. Itama dai yau kamar hasashen su Saheeban ya buɗe mata idanu akan Manaal ɗin. Dan sai duk kammanin ta suka juye mata na mai yaron ciki. Ko kuwa kwalliyar da tai ne ya canjata zuwa hakan. Duk da bawai Maanal ɗin tayi zane-zane a fuska bane. Hasalima hoda da kwalli sai lips-gloss ne kawai ta saka.
Komai dai Oum batace akan hakan ba, sai ma gaisuwa da sukayi, dai-dai kuma nan Babban Yaya da Yaya Fawzan suka shigo suma a tare cikin shirin fita. Manaal ta gaishesu suka gaisa da Oum da AA sannan sukai zaman yin breakfast. Yau dai Fawzan bai tsokani AA ba. Hakan yasa Oum da sauran ƴan uwansa fuskantar ransa a ɓace yake. Sun tabbatar dai bazai wuce shi da Nibras ba, dan haka cikin hikima irin ta iyayen ƙwarai Oum ta shiga yimasa nasiha, ai ko sai gashi kafin su gama su fito harda ɗan murmushinsa. Su dukansu sukan shiga damuwa a duk lokacin da suka ga babu fara'a a fuskar fawzan, ba komai yasa haka ba kuma sai sanin shi mutum ne mai sauƙi da yawan fara'a, akan jima baka ga damuwa a tare da shi ba, dan ko abu ya ɓata masa rai yakan shanye shi ta yanda da wahala a gane masa kai tsaye.
AA da kansa ya buɗema Maanal mota ta shiga, sannan ya zagaya ɗayan side ɗin da driver ya buɗe masa shima ya zauna. Yana gama zama ta kwanto jikinsa, kanta a kafaɗarsa ta lumshe idanunsa ɗan barci ne a cikinsu. Kallonta ya ɗanyi, sai kuma a hankali ya kamo hannunta cikin nashi ya riƙe. Ɗayan hannunsa kuma wayarsa yake dannawa yana son yay kiran RK.
Tafiyar ƴan mintuna ta kawosu MAWAAD COMPANY. Sai Maanal taji tayi kewar wajen sosai. Yanda take kallon ko'ina yasa AA sakin ɗan murmushi. Ƙasa-ƙasa yace, “Kinyi kewarsa ne?”.
“ALLAH sosai ma Besty”.
Murmushi ya sake yi, sai kuma ya ɗan taɓe baki ya yunƙura ya fita dan har driver ya buɗe masa. Zagayawa yay ya buɗe ma Maanal, ya duƙo ya riƙo hannunta, ɗayan kuma ya ɗauka handbag ɗinta ya riƙe. Tuni masu shigowa suka tsaya kallon gulma, dan haka kawai suka tsargu da boss ɗin yau tare yake da amarya. Aiko sun gane ma idonsu abinda suke jiran, AA kam da baima san sunayi ba ƙoƙarin gyarama Maanal mayafinta yake yana kallon ta da murmushi, ita kuma tana masa magana a shagwaɓe dan yace mata yau a office ɗinsa zatai aiki ne, ita kuma tana cewa a'a bata yarda ba ita dai nata zata zauna sai tafi yin aiki da ƙyau. Uhhm babbar magana boss na murmushi available. Wannan shine taken gulma yau a Maawad.
Lokacin da suke shigowa AS da shima ya iso yanzu suka haɗu a waje na biye dasu sai driver daya kwaso musu kayayyakinsu. Cike da farin ciki da girmamawa kowa kema Maanal barka da dawowa office. Itako tana amsawa kowa da kulawa da fara'a. Hakan kuma sai yayma kowa daɗi dan basuyi zaton haka ba. Jin tarihin alaƙarta da ogansu yasa suka fahimci hotonta ne a ko'ina na companyn, yanda aka ɓoye kamaninta ne yasa basu gane ba. Irinsu Zaharadeen kam kunya ce fal a cikinsu da jin shakkar haɗuwa da Maanal. Yayinda ƴammata masu ɓoyayyar manufa akan boss suke jin kishinta da shakkarta a wani gefen. Dan sun san dai lallai wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa. Saboda muhimmancita ga boss mai girma ne ƙwarai da gaske da yanzu yake a bayyane gare su.
Har cikin elevator hannunta na riƙe cikin nasa, amma kasancewar su AS a tare da su ya kama kansa kamar ba shi ba, itama Maanal ɗin a nutsenta take. Sai da suka fito ne ta saka masa rigimar ita dai office ɗinta zata. Dole ya haƙura ya yarda, amma sai taga ya nufi sama inda nashi yake na ƙarshe shi da AS. Zatai magana ya hanata, sai da suka iso taga AS ya buɗe office ɗin jikin na boss ɗin da ada yake kamar ma'ajiyar wasu muhimman abubuwa yasa Maanal a mamaki. Koda suka shiga sai tai tsaye tana kallon ikon ALLAH, sai kuma ta kalla AA ɗin dake kallonta yana murmushi.
“Office ɗin waye?”.
“Matar AA Darma mana. Kina tunanin zan barki ki cigaba da zama can ni ina nan? Sannan kema president ce kuma (Chairwoman) a wannan companyn, kina kuma da damar cigaba da kasancewarki a artist dan bazamuyi sakacin rasa gwarzuwarmu ba a wannan fanin. Barka da zuwa sabon office Bestyna”.
Rasa ma abin cewa Maanal tayi, sai taji kawai ƙwalla ya cika mata idanu. A hankali ta shige jikin AA ta rungumesa tsama ta wani kalar sakar masa kuka. Shima slowly ya lumshe idanunsa tare da rungumeta yana ɗan murmushi. Saɗaf-saɗaf AS ya lallaɓa ya koma tare da ja musu ƙofar gulma da dariya fal cikinsa.
AA cak ya ɗauka Maanal har zuwa office chair ɗinta dake sabuwa fil dan komai na office ɗin sabone irin na office ɗinsa, wancan kuma office ɗin Yaqub aka maida ciki a madadinta. Zama yay a kujerar ya sakata a cinyarsa. Sai da ya ɗiba tissue dake a saman desk ɗin ya share mata hawayen sannan cike da lallashi da soyayya ya ce, “Babyn Oum kwana biyun nan shagwaɓa kike jin yimin da yawa. Komai kuka kina son zama rigimammiya. Minene abin kuka anan, companyn ki ne fa, ko office ɗina kikace na fito na baki ba da gudu zan fito ina faɗin, “An gama Madam ba”.
Dariya yanda yay ya bata, sai ta saki murmushi da ɗan ja masa hanci ta ce, “Daka zama mijin tace”..
Murmushi yayi mai ƙyatarwa, tare da sumbatar lips ɗinta ya ce, “Aini mijin kafin tace ne ma. Idan kuma da abinda yafi ma hakan to gaskiya duk ni ne Besty”.
Dariya sosai yanzun kam Maanal keyi, shima yana tayata da murmushi. Zata fara masa godiya ya rufe mata baki da nashi. Bata hanashi ba, sai da ta tabbatar ta nuna godiyar tata a haka sannan. Ya rungumeta shima yana sanya mata albarka. Jin yanayinsa na ɗaukar sabon salo cike da wayo ya zame jikinsa ya bar office ɗin zuwa nashi shima. Ita ko ya barta da farin ciki tana faman zagaye office ɗin da kallo komai. Daga ƙarshe tai kiran Ammie a waya tana sanar mata. Ita kanta Ammie sai da taji ƙwalla ya taru mata a ido, dan a rayuwa takan ji matsannacin farin ciki idan taji Maanal a farin ciki. Kodan yarinyar ta wahalu a shekarun baya ne fiye da sauran oho. Bayan ta katse kiran su Didi ta kira suma ta gumtsa musu. Suma suka tayata farin ciki sosai....
Aikin dake a companyn sosai yasa babu zama, kowa aiki yake tuƙuru