Showing 6001 words to 9000 words out of 218311 words
Chapter 3 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
shaƙata”.
Dariya sosai Fawzan yake yi, ya kai zaune kusa da Oum ɗin yana gaisheta, itama Maanal ɗin sai ta gaisheshi. Oum ce kawai ta tambayi yaya jikin Autan nata, Maanal kam kunya ta hanata yin hakan. Fawzan ya ce, “Da sauƙi sosai Oum, dan tare mukaje massallaci ma da asuba yau. Ku shiga mana ai ya tashi”.
Murmushi Oum tai da faɗin, “Alhamdullahi”. Sai kuma ta juya ta kalla Maanal da kanta ke'a ƙasa. Cike da kulawa ta ce, “Auta tashi ki shiga masa da abincin gamu nan zuwa”. Kai kawai Maanal ta iya ɗaga mata, sai dai ji take kamar tace ma Oum ɗin a'a amma babu dama. Haka ta ɗauka basket ɗin kanta a ƙasa, Fawzan ne yay mata nuni da ɗakin yana tsokanarta, ita dai yau babu bakin maida murtani sai Oum ke kare mata. Sai da tai ɗan jimm a tsaye kafin tai knocking da yatsanta ɗaya kamar mai jin tsoro, tabbas badan bazata taɓa iya musu da Oum ba komi za'ai bazata je inda yake ba, duk da kuwa har cikin ranta tana jin damuwa da rashin lafiyar tasa. Jin shiru ta sake yin knocking ɗin, sai kawai jitai daga falo Fawzan nace mata ai ta shiga kawai ba lallai yajita ba. Nan ma jitai kamar ta saki hawaye, amma haka ta danne kamar mai tsoron shiga wuta ta tura ƙofar ɗakin a hankali. Sai da ta ɗan rumtse idannunta taja numfashi kafin ta saka ƙafarta a hankali lips ɗinta na motsawa alamar sallama. Bata kalla cikin ɗakin ba ta maida ƙofar ta rufe, yayinda wani sassanyan ƙamshi ya daki hancinta, ɗan sanyin acn da aka saka kaɗan yay wani shiga jikinta. Sosai ta saki ajiyar zuciya a cikin ƙirjinta. Sai kuma ta shiga bin ɗakin da kallo jin alamar kamar babu mutum, babu kowa kam, sai dai gadon babu gyara alamar yanzu aka tashi a kansa, ɗakin ya tsaru matuƙa, ga komai dai-dai misali babu wani tarkace, duk da safiya ce babu yawan haske a ɗakin, dan labulayen duk a sake suke, fitulun kuma a kashe sai mara haske sosai kalar blue. Hakan ya saka launin ɗakin sake zama mai ɗaukar hankali. Nanma ajiyar zuciya ta sauke, sai kuma ta cigaba da takawa a hankali kamar mai sanɗa da nufin ajiyewa ta fice abinta tunda ALLAH tasota baya ɗakin, sai dai kuma da'alama shirin nata zai bi ruwa, dan tana gab da isa tsakkiyar ƙaton bedroom ɗin ƙofar bathroom dake daga can cikin closet ɗinsa da zaka iya hangowa ta cikin ɗakin ta buɗe, harga ALLAH da farko tsorata tayi dan haka ta kalla wajen, sai dai kuma da gudu ta ɗauke idanun nata zuciyarta na wani kalar bugawa saboda saukarsu a kansa. Ba ƙaramin jin ta gama rikicewa tayi ba, dan daga shi sai ƙaramin towel daya ɗaura a ƙugunsa, buɗaɗɗen jikinsa jiƙe da raɓar ruwa alamar wanka yayi, dan hatta sumar kansa a jiƙe take itama dai da alama wanketan yayi. Shima dai cak ɗin ta tsaya, dan ganin nata ya saka shi jin shock na rashin zato dan tunda suka dawo bai gata ba, duk ciwon nan bata shigo dubashi ba. Kamar zai ɗauke kai dan jin haushi. Sai dai ganin yanda tai tsammm kanta a ƙasa ya sakashi sakin wani shegen murmushin gefen baki yana ɗan yin luuu da idanun nasa kamar zai lumshesu. Ƙaramin towel ya cira dake rataye a jikin wani ƙyaƙyƙyawan hanger dake gab da ƙofar bayin, dan an tsara su ne a wajen kala-kala ta cikin closet ɗin gwanin birgewa. Saman kansa ya kai towel ɗin kafin ya fara takowa harya fito daga closet ɗin gaba ɗaya.
Bedroom slippers ne a ƙafarsa masu taushi, duk da ba ƙara sautin takun nasa ke badawa ba sai take jin sa ita har tsakkiyar kanta, karo na farko a rayuwarta da taji wani mashahurin tsoron kasancewarsu su biyu kacal a waje, da ace zata iya da ɓacewa kawai zatai a ɗakin ta huta. Amma babu damar hakan gareta tunda ita ba aljana bace. Yana isowa gab da ita batama san wani ƙarfi yazo mata ba tai saurin juya masa baya tana sake ƙarfin rumtse idannunta hannayenta biyu data riƙe basket ɗin na ƙara damƙe shi da ƙyau. Cak ya tsaya shima dariya na neman cika masa zuciya, dan yanda ta juya ɗin da saurinta sai ka ɗauka wani kumurcin maciji ta gani ko zaki. Da ƙyar ya iya danne dariyar dake cinsa a rai ya matsa jikinta sosai, tsabar neman magana sai ya zagayo da hannayensa ta gefe da gefenta ya ɗaura akan nata hannayen dake riƙe da basket ɗin, badan ya riƙe hannun nata da ƙyau ba da sai basket ɗin yayi faɗuwar da abincin zai tarwatse a wajen. Yanda ta takure jikinta waje guda ya sake bashi damar manne jikinsa da bayanta sosai tare da duƙo kansa saman kafaɗarta yana busa mata numfashinsa a saman dokin wuya da cikin kunne, sannu a hankali ya sake matsar da fuskarsa jikin tata idanunsa a lumshe, kwantaccen gashin kumatunsa dake da damshin ruwa na gogar gefen fuskar tata. Da sauri ta zame hannunta dake riƙe da basket ya koma nasa hannun gaba ɗaya. Karo na farko ya saki ɗan murmushi mai sautin da har taji, har yanzu kuma idanun nasa a lumshen suke yana shaƙar ni'imtaccen ƙamshinta. Cikin matuƙar raɗar da koda wani ne a kusa da su da wahala yaji miya faɗa a hankali can ƙasan maƙoshi ya furta, “Good morning Bestie”.
Tsabar yanda maganar tashi taima Manaal shigar zuruff bama tasan ta zabura ba tana ƙoƙarin tureshi, dolensa ya bata damar fita a jikin nasa, dan duk ta daburce har tana neman kaɓe basket ɗin abincin hannun nasa. Hanyar fita ta nufa da sassarfa, muryarta na rawa, harshenta na sarƙewa ta furta, “Su Oum na falo”. Kafin yay wani yunƙuri harta fice. Kansa kawai ya girgiza yana mai sakin murmushin da har sai da haƙwaransa suka bayyana, a ransa kam ayyanawa yake (Zamu haɗe ne ai yarinya).
😂Tace maka ita ba yarinya bace yanzu kana sake maidata baya🏃
★ Sarai Oum ta lura da yanda Manaal ta dawo kamar wadda aka biyo, sai dai batai magana ba har sai da Manaal ɗin ta sanar musu cewar ya tashi. A dai-dai nan ma kiransa ya shigo wayar Oum ɗin. Basu ji abinda ya faɗa ba, Oum tadai miƙe tana murmushi tace su shiga.
Fawzan ne ya fara shiga, Oum biye da shi, itace ƙarshen shiga dan maƙalewa tayi a bayan Oum. Sosai Oum ta nuna farin cikin ganin yanda jikinsa yay sauƙi yau sosai fiye da kullum, shima ganin fara'a a fuskarta sai zuciyarsa ta masa sanyi. Fawzan kam ya tasashi gaba da tsokana shi da Maanal data zauna a cikin yanayin takura, dan tun haɗa idon farko da tayi da AA ta ɗauke kanta bata sake kallon sashen da yake ba. Yanzu ma da Fawzan ɗin ke tsokanarsu kanta a ƙasa sai Oum ke kare musu. A dai-dai nan Saheeba da Nibras sukai sallama. Kafin a basu iznin shigowa Naufal da Anum sun shigo. Kai tsaye yaran inda AA yake suka nufa cike da farin cikin ganinsa a zaune, shima fuskarsa da ɗan sakewa ya ɗaga Anum ya zaunar a jikinsa, Naufal kuma ya zauna a kusa da shi.
Da kai kawai ya amsa gaisuwar da Saheeba da Nibras sukai masa. Ba haka Nibras taso ba, amma har ranta taji daɗin ganin jikinsa da sauƙi sosai yau ɗin. Wani gefe na zuciyarta kuma najin zafin ganin Maanal a tare da shi, gashi data kallesa sai taga idanunsa akan Maanal ɗin suke, ita kuma ƴar ranin hankalin sai wani latse-latsen waya take yi ita adole ga mai aji. Oho ita Maanal bama tasan tanai ba, hasali ma jinta take duk a takure, da Oum zata barta ma da tuni ta wuce abinta ta koma sashenta ita kam.....
________★
A lokacin da anan ahalin gidan ke sashen AA a ɓangaren Mamy tana can tana waya da babbar yayarsu akan batun auren AA ɗin da Nuratu da sukaji su Abah sunyi shiru sunƙi cewa komai ga shi har yau laraba, a yanda tsarin nasu yake kuma daga gobe alhamis ya kamata ace biki ya fara musamman tasu ɓangarensu, amma sunji ɗif babu wani bayani. Shine tai kiran Mamy ɗin dan jin mike faruwa. Bayanin da Mamyn ke mata rai ɓace yasa tace yau zatazo Abujan dan tana Kano. Da wannan sukai sallama.
Zama Mamy tai tana mai dafe kanta. Eh lallai taci nasara akan Abah na hana Maanal tarewa a sashen AA, sai dai tana jin fargaba akan tunkararsa da batun bikin nan kuma. Musamman idan akai dubi da halin da AA ɗin ke'a ciki na ciwo. To amma kuma itama fatanta ai ayi bikin ne. Numfashi mai nauyi ta sauke sosai, tana mai tattara batun gefe ta jingine har isowar yayar tata dai, dan gara su tunkari Abahn tare zatafi samun ƙwarin gwiwa....
Kusan ƙarfe uku na rana kuwa yayar Mamy ta iso gidan. A lokacin kusan kowa yana a sashensa, dan hatta AA yana sashen Oum, daga sallar azhar daya samu iya fita yau shi da sauran yan uwansa suka wuce sashen Oum ɗin. Manaal dai na ɗakin tunda taji motsinsu taƙi fitowa, sai ma tayi kwanciyarta barcin dole, daga baya na gaskiyar ya ɗauketa.
Mamy da kanta ta fito ta tarbi ƴar uwarta, kai tsaye kuma sashenta suka wuce, suna dai-dai gifta window ɗin Oum dake kallon sashen Mamy ɗin sautin dariyar su Fawzan ta shiga kunnunwansu, kasa haƙuri sukai sai da suka leƙa. Aiko idanunsu suka gano musu zaratan mazajen ƴaƴan na Oum zagaye da ita tana bama AA abinci a baki, dai-dai kuma lokacin Babban Yaya shima ya buɗe nasa baki wai ta bashi, shine suka saka sanya dariya, shima Fawzan yace bazai yarda ba ya je aka bashi. Kai da kaga fuskar Oum kasan cike take da farin ciki, haka suma su babban Yayan, farin cikin Oum ɗinsu ya saka fuskokinsu bayyana murmushi na musamman, musamman ma shi da AA da ba cika son yin dariya sukai ba sai sun so. Fuuuuu Mamy ta wuce sashenta zuciyarta na tafasa. Koda suka shiga ɗaki saita sakar ma yayarta kuka. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga ƙirjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al'amarin na Oum fa na neman zame musu ɗan zane. Dan tabbas ta rigada ta gama mallake zukatan yaran nan da salon makirci (kamar yanda suke fassara soyayyar Oum ɗin akan su AA. Sai dai kuma wannan nasu mummunan zaton ne kawai, dan ita dai baiwar ALLAH Oum har cikin zuciyarta ne, hasalima takan manta da cewar ba itace ta ɗauka cikin su AA tai naƙudarsu ba saboda yanda ta sakankance matuƙa).........✍️
_Dangin Mamy ina gaisuwa 🙄🥱🏃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣
______________
5
......Sun tattauna sosai kafin su yanke shawarar yayar ta tunkari Abah da batun bikin cikin hikima. Hakan kuwa sukayi, bayan sallar la'asar Abah ya dawo gida Mamyn tai mata rakkiya har sashensa. Bayan sun gaisa cikin mutunta juna dan akwai ƴar kunyar surukuta a tsakaninsu duk da kuwa Abah ya girmeta sosai, amma yana kawaice mata saboda dattako. Cike da kissa tana murmushi take faɗin, “Kukam kamar a kanku aka fara aurar da auta, yanzu bayan shagalin Kanon bazaku barmu mu huta ba wani satin kunce zakuyi wancan kuma?”.
Cikin danne takaici da ƙyar Mamy ta ƙaƙaro murmushi tana ɗan laɓe baki, “Ai jikinsu ne zai gaya musu dan nikam dai nayi na ALLAH da naje muku Kanon ma. Amma da zaku tausayama kanku da kun barshi ku haɗe duka”.
Cikin rashin damuwa Abah yay ƴar dariya shima da faɗin, “Ai ku kwantar da hankalinku bikin ma Saturday ɗin dama da wahala ya yiwu. Dama yau nake son zama daku akan zancen dan yau da safe Baba ya kirani, ya kuma tabbatar min zuwa gobe shima zai samu mutanen gidan naku dan bammayi zaton Aunty Babba zatazo ɗin ba”. Ya ƙare maganar yana kallon Aunty Babba datai wani irin ɗagowa tana kallonsa.
Wani irin harmutsawa zuciyar Mamy tayi, da ƙyar Aunty Babba ta iya saita yanayinta cike da dakiya ta ce, “Lafiya dai ko Aban Fadeel? (Dan haka take kiransa)”.
“No lafiya Lau, Baba ne yace a ɗan dakata Ajwaad ɗin ya ƙara samun lafiya sosai, dan yaron nan ya bugu sosai dan ma ALLAH ya bashi ƙarfin hali ne. Ga kuma mutane sunyi ƙoƙari na zuwa wancan ɗin, ga azumi yana gabato mu kwana goma sha kawai ya rage, sai yace a bari kawai bayan salla idan muna da rabon kaiwa sai ayi. Amma nima naso ayin kawai a huta, damma uwarsa taƙi bani haɗin kai amma ina son horasa akan yarinyar nan ita kanta, idan son samuna ne kada ta tare yanzu har sai bayan sallar itama da kansa ya magantu ya faɗa mana dalilin ƙin amsar aurenta da yay har yana neman kashe kansa, amma nasan da wahala ta bari duk da dai jiya da yau naga ta daure ana son aga gudun ruwana, kuma zasusha mamaki ita da ɗan nata dan na shirya musu sosai....”
Gaba ɗaya takaici ma ya hana Mamy magana, jitake kamar ta falle fuskar Abah ɗin da mari ta huta daga ita har yayar tata. Amma dai suka danne da ƙyar suna ƙawata fuskarsu da murmushi kaɗan. Da ƙyar Aunty Babba ta ce, “Uhhm kaima kasan dai bazata bari ka horashin ba Aban Fadeel, amma kuma hakan shine dai-dai, ya kamata yasan muhimmancin yarinyar, kar yaga an bashi a ɓagas ya ɗauka arha ya samu ”.
“Ato kema dai ƙya faɗa Aunty, amma bazata yarda ba, shekaran jiya fa kuka ta sanya min ma wai ina son na maida masa ciwo baya. Tunda dai anyi ya wuce a haƙura mana. Kai ban san irin son da Fateema kema yaranta ba wlhy.”
Shiru Aunty Babba tai masa dan maganarsa ta ƙarshe sake sukar mata zuciya take, ita ko Mamy ma sai ta miƙe abinta. Shima kiran wayarsa da akayi ne ya sashi miƙewa ya fita. Da kallo suka bishi, yana fita Mamy ta miƙe a fusace har idannunta na tara ƙwalla tana faɗin, “Ashe da rigima kuwa a gidan nan Aunty......”
Da sauri Aunty Babba ta rufe mata baki, sai kuma ta kama hannunta suka fice ta baya zuwa sashenta.....
__________★
Har dare Oum bata san yayar Mamy na gidan ba. Sai kusan takwas su AA sun dawo massallaci, shi kaɗai ya wuce sashen Oum. Babban Yaya da Fawzan kowa sashensa ya wuce. Abah kuwa sun barsa a waje yana gaisawa da maƙwafcinsu. Kai tsaye upstairs AA ya haura, dan ƙasan masu aiki na gyarawa kasancewar anan suka tashi. Shiru falon babu kowa sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka saka ke tashi. Cikin yanayinsa na wanda yasha faman jiyya ya kai kwance a doguwar kujera, a haka ya jawo remote ɗin tv dana ac ya kunna, yana cikin searching channel Oum ta fito daga bedroom. Zama tayi tana ɗan matse fuska da faɗin, “Auta kun dawo?”.
Remote ɗin tvn ya ajiye tare da juyowa ya kalleta. Maganar da yay yinƙurin yi ya haɗiye tare da tashi zaune idanunsa akanta. Fahimtar kamar ya gane yanayin da take ciki ya sata saurin gyara fuskarta, cikin murmushi ta ce, “Lafiya? Ya naga ka tashi?”.
“Oum muje asibiti”. Ya faɗa cikin sanyi da damuwa maimakon amsa tambayar datai masa. Murmushi ta sake saki tana gyara ƙafafunta, “Asibiti kuma? Ni lafiyata ƙalau”.
Idanunsa da suka ɗan kaɗe ya tsurama ƙafafunta, sai kuma ya zamo ƙasan lallausan carpet ɗin falon ya zauna gab da ita. Ƙafafun nata ya kamo ya ɗora a saman jikinsa. Duk sun ɗanyi fushi kuwa, cikin sauri ya ɗago yana kallonta. “Oum dan ALLAH ki tashi muje asibiti, see your leg! fa”.
Murmushi sosai Oum tayi da faɗin, “Oh oh! Look, there's nothing wrong, my dear. I'm okay fa. Kawai dan kwana biyu ban ɗan motsa bane ba. Sannan yau na manta bansha magani na da yamma ba sai yanzu na tuna nasha bayan idar da salla. Ina mai tabbatar maka zata sauka yanzun nan”.
Sam bawai zuciyarsa ta gamsu bane, amma bazai iya jayayya da ita ba. Sai kawai ya shiga mammatsa mata ƙafafun. Idanu kawai Oum ta zuba masa tana murmushi, dan tasan yayi shiru ne kawai badan ya gamsu ba. Cikin son kwaranye masa damuwar data bayyana akan fuskarsa ta ce, “Auta ya kamata kaci abinci fa, sai kasha maganinka, doctor yace 8 amma gashi har ta shige baka nema ba.”
Fuskarsa a narke sosai ya ce, “Oum bana jin cin komai fa, zan sha maganin a haka kawai”.
“A'a bazai yiwu ba, bara na haɗa maka ko tea to.”
Da sauri ya maida ƙafafunta da take neman janyewa a jikinsa. “No Oum zan