Showing 18001 words to 21000 words out of 218311 words

Chapter 7 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

shirin aiki, da alama ta makara ne. Idonta akan AA ta gaida Oum cike da ladabi, hakama babban Yaya sannan ta juya tana gaida AA ɗin daya juya yana magana da Naufal. A taƙaice ya amsa mata batare daya juyo ba. Maanal dake karantar yanayin kowa musamman Saheeba da tunda suka shigo taga ta mata wani irin kallo ta ɗauke kai a taƙaice ta ce, “Auntys barkanku da safiya”.
Babu yanda suka iya daga Saheebar har Nibras ɗin dole suka amsa. Sai dai kowanne da kalar zafin da yake jin Maanal ɗin a ransa. Yayinda shigar tata ta saka zuciyarsu sosuwa. Duk da bawani kwalliya tayi ba, babu kuma wani ƙyale-ƙyale a tare da ita kamar nasu. Amma tayi matuƙar yin ƙyau mai sanyi. Ga ƙamshinta na fita a nutse babu wata hayaniya. Tunda kuma tai musu kallo ɗaya ta watsar da su a tasu fahimtar. Yanzu kuma ta jefesu da gaisuwar raini. Oho ita bama tasan sunayi ba. Tama maida hankalinta ga babban yaya suna magana...
Shigowar Abah ta saka kowa maida hankalinsa kansa. Sai Mamy dake biye da shi riƙe da briefcase ɗinsa. Sosai Abah dake kallon zuria'ar tasa farin cikin ya mamaye ransa. A ransa rayawa yake (Nanfa duk mallakina ne, zuri'ata ce. Idan kuma ALLAH yaba Fawzan haihuwa da Ajwaad shima Fadeel aka ƙaro masa sai mu sake yawa). Mamy kam zuciyarta ce ta sosu da ganin wahalarta zagaye da kishiyarta. Tayi-tayi ta hana wannan zaman safen a sashen Oum tarasa yanda zatayi. Dan ita inma sun shiga gaisheta sama-sama ne, amma Oum kuwa anan ma suke breakfast wasu ranakun koda matansu sun girka sai su ƙi cin nasu sai sun zo nan musamman Fawzan da matarsa ke malalaciya..... Tunaninta ne ya katse saboda gaisuwar da Maanal ke mata. Amsawa tai fiskarta da murmushi, sai kuma ta tsargu da yanayin shigar Maanal ɗin. Ta ɗan saci kallon AA dake tsaye kusa da Maanal gab batare da suma sun farga da yanda suke ba. Dan ya miƙe ne zai amshi number a hannun Babban Yaya, kasancewar Maanal ɗin na tsaye a wajen suna magana da babban Yayan kuma sai tsaiwar tasu ta kasance gab-da-gab. Itama daba kallonsa take ba sam hankalinta bai kai da kasancewar kusancinsu ba duk da mayataccen ƙamshinsa ya addabi hancinta. Hirama Naufal ke mata tanata murmushi. Itama dai Nibras hankalinta akan AA da kasancewar Maanal ɗin a kusa da shi yake. Zuciyarta na mata zafi da jin kishin hakan. Ganin Maanal bata tare a sashenta ba ita kaɗai tasan a farin cikin da take ciki. Dan yanda take farin cikin har sai da Fawzan yay mamaki ma ya tambayeta. Amma sai tace da shi babu komai...


Gaba ɗayansu abin sha'awa a tare suka fito wajen da gwarazan motocin mazajen gidan suke duk a wanke. Dan tun jiya Bola ya wanke su fes kasancewar aikinsa kenan. Yara aka fara sakawa a motar su ta makaranta, sannan Baban yaya ya shiga tasa. Abah ya shiga shima tasa driver a gaba yace Maanal ta shigo kusa da shi. Murmushi AA yay a kaikaice kawai ya shiga shima inda nasa drivern ya buɗe masa. Shima Fawzan ya shige tasa hakama Nibras da taji wani kalar daɗi ganin Maanal tare da Abah zata tafi ba AA ba. Cike da mamaki Mamy take kallon motar Abah, dan bata san da komawar Maanal office ba. Sai da duk motocin suka gama ficewa maigadi ya maida gate ya rufe sannan Mamy ta kalla Oum dake murmushi.
“Wai nikam ƴarki badai aiki aka koma ba?”.
Ƴar dariya Oum tayi, ta ce, “Ai na manta muyi maganar jiya. Da ƙyar muka samu mijinki ya yarda, shine aka kafa mana dokar bazata bi Auta ba nace munji”.
Dariyar yaƙe Mamy tayi, a ƙasan ranta tana faɗin (munafuka abinda kika ƙullo kenan jiya dama. Ba komai zan yi maganinku) a fili kam sai cewa tai, “Ai ina bayansa yay maganinku keda ɗan naki”.
“Oh na manta ƴar adawa ce kefa. Nayi nan”. Cewar Oum tana barin wajen. Dariya Mamy tayi kawai, sai da Oum tai nisa da wajen ta gimtse fuska da rakata da harara. Sai kuma suka kalla juna ita da Saheeba dake cike fam da takaici itama. Dan ita sai yau da taga Maanal da ƙyau fiye da ko yaushe taji zuciyarta ta sake girgizuwa. Maanal ba fara bace ba, amma irin Black beauty ɗin nan ce da ALLAH yayma wani kalar sassanyan ƙyawun fuska dana jiki dana fata. Ga idanu masha ALLAH. Ba namiji ba ko mata da yawa sun sha yaba ƙyawun halittar Maanal, a hakanma tana da ƙoƙarin sututurta jikinta ne. Dan bata shigar banza, ko ɗinki bazaka taɓa ganinta da matsatstse ba sam. Gata ƴar ƙwalisa dan tasan sirrin kula da jiki matuƙa. Rashin yawan fara'arta a yanzu kansa irinsu Saheebar shakkarta, dan sai suga kamar ta cika girman kai ne, ita kuma sam a gareta ba haka bane. Maganar ce kawai yanzu bata cika son yi ba ne.....


__________★


ZARIA


“Mom please ki barni naje. ALLAH acan nake son yin azumi nidai”.
Harara Hajiya Majdiya ta wurga mata. “Ni kinji nace karkije ne Najma? Ni nace ki kira Mah-mah ki sanar mata, tunda ita tace kije mata azumi kika kuma amsa. Sai yanzu ne zakice kin fasa Abuja zakije. Kina gani kuma tunda muka dawo Rufaidah kullum cikin kira take akan yaushe zaki koma. Ita kanta Mah-mah ɗin jiya muna waya sai da tace yaushe zaki taho.”
Sosai hawaye suka cika idanun Najma. Haushin kanta ya kamata. Miyasa ma ta amsa ma kakar tata zataje can ne. Wayar da sukai ɗazun da Yaya Fawzan ta sake dawo mata. Yanda yake roƙonta akan tazo Abuja tai azumi inba haka ba kullum zai kasance a hanyar Zaria ne. Kuma tasan sunyi alƙawarin ɓoye komai har sai nan da bayan salla Babba ta kammala exam ɗinta... Kamar wadda tunanin nata ya zaburar da ita tai saurin kallon Mom ɗinta.
“Mom na yarda zan kira Mah-mah ɗin, har ma da Aunty Rufaidah ɗin”.
“Sai ki haɗa da Babanki ma. Tunda shima kin san Kano kika gaya masa, kuma ya tsani magana biyu.”
“Mom dan ALLAH ki taimaka min ke ki sanar masa”.
“Wa? Ni? A'a kema kin san ganganne wlhy. Babu abinda ya shafeni. Kinga tashi ki ƙarasa min aiki malama kafin yarana su dawo school da yunwa”.
Sosai Najma ta zunɓura baki tana miƙewa. Kitchen ta nufa dan ɗaura girki. Tana girkin tana neman mafita. Dan bata san yanda zata tunkari babansu ba kasancewarsa mutum mai zafi. Dama da gyar ta samu ya barta zuwa Kanon dan shi kam bai son yaransa suyi nesa da shi ko yaya. Harta kammala tana faman ƙullawa da kwancenwa. Sai da ta fara zuwa ta sanar da Mom ta gama sannan ta nufi ɗakinsu. Miss call har biyu ta samu daga Ya Fawzan. Ta ɗan waro idannunta waje. Kiransa ta shiga yi, sai dai harta tsinke bai ɗaga ba. Tana ƙoƙarin yin na biyu kiransa ya shigo mata. Cike da shauƙi tai masa sallama. Daga can yay ɗan murmushi da faɗin, “Uhm-uhm wannan ƙanwa tawa dai bata jin magana”.
Sosai ta sake kwantar da murya, “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri, ina kitchen ne Mom ta sani girki”.
“Ba damuwa na haƙura ai Mom ce”.
“Yauwa Yayana. Dama fa yanzu zan kiraka. ALLAH akwai matsala......” tsaf ta zayyane masa yanda sukai da mamanta. Murmushi yayi kawai, “Kinga karki damu, ni zan kira Grandma ɗin da kaina. Sannan ki shirya zanzo Zarian na ɗaukeki in sha ALLAHU ”.
Cikin waro idanu kamar yana gabanta ta ce, “Baba fa?”.
“Shima ki barni da shi”.
“Yauwa yaya Fawzan shiyyasa nake sonka”.
“Da gaske?”.
Ya faɗa da wani irin shauƙi. Ai da sauri ta yanke kiran fahimtar katoɓarar da tayi. Ita kuma kawai irin tayi maganar normal ne bada wata manufa ba. Duk kiran da yay mata ƙin sake ɗauka tayi kuwa. Shi kuma daga can yayta murmushi. Tabbas kasancewarsa da Najma na bashi farin ciki, duk da kulawar da yake samu a gareta iya ta kalaman baki ce ta ɗara masa Nibras. Shi kaɗai yasan irin haƙurin da yake akan rayuwa da Nibras. Amma yana addu'ar Najma ta zama sanadin sharuwar hawayensa......


Itama dai Najma cike take da wani irin shauƙi, dan har tsakkiyar rai jin son Fawzan take yi. Kafin yanzu soyayya take masa na ƴan uwantaka kawai, amma lokaci ɗaya da bayyana mata manufarsa sai taji al'amarin ya zarce hakan. Yaya Fawzan shine irin mijin da take ma kanta fata. Wato mutum mai sauƙin kai. Gashi ƙyaƙyƙyawa ga nutsuwa da dattako. Sai dai kuma wani gefe na zuciyarta na jin shakkar matarsa. Duk da a zahiri Nibras ɗin ba wata masifaffiya bace, sai dai irin matan nan ne marasa sakewa da mutane.... Shigowar kira a wayarta ne ya katse mata tunani, a zatonta Ya Fawzan ɗin ne ya sake kira, amma sai taga Uncle Rafeeq. Idanu ta waro sosai, tare da ɗagawa da sauri.
“Lah Uncle R kai ne?”.
“A'a bani bane”.
Rafeeq ya bata amsa cikin gatse. Da sauri tace, “I'm sorry Uncle mamaki nayi ne. Ina yini? Ya Aunty Nuwaira”.
“Lafiya Lau muke. Miya samu wayar Aunty inata kira a kashe?”.
“Nah-nah ce ya shiga da ita bayi ɗazun da safe ta tsunbula a ruwa, shine aka sakata cikin shinkafa”.
“Tofa ALLAH ya kiyaye to, jeki kai mata taki”.
“Okay Uncle. Amma dan ALLAH kafin na kai mata na roƙeka wani abu”.
“Banda kuɗi nayi brock”.
“Kai Uncle nifa ba kuɗi nake nufi ba”.
“To ina jinki”.
“Uncle kaga so nake naje Abuja nai azumi, sai aka samu matsala nariga na faɗama Baba Kano zanzo tun kwanaki, yanzu idan nace masa na canja bazai yarda ba, zai ma iya cewa duka a fasa......”.......✍️





_Mu haɗe a Maawad da wanda suka shirya🏃🏃🏃🏃😲_










*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖🔟




______________




........“To ke wace gulmar ta saki canjawar, bayan naji Mah-mah da Aunty Rufaidah na maganar zuwan naki ma”.
Baki taɗan tura gaba, sai kuma cike da shagwaɓa ta ce, “Ni Abuja nake so yanzu Uncle please, idan akai salla su kuma basai nazo musu ba. Kaga nayi ma Ya Fa... Uhm uhm Aunty Maanal alƙawari itama”. Tai saurin waskewa jin katoɓarar da ta nema yi. Jimm Rafeeq yayi yana nazarin sunan data so fara ambata. Sai kuma tunaninsa ya ɗan koma baya akan ganinsu daya dinga yi a bikin nan tare da Fawzan. Tabbas ya zargi akwai wani abu kam, sai dai rashin hujja ya sashi sakin zancen tun a lokaci.....
“Uncle Please mana...”
Ta katse masa tunani. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke. Tare da faɗin, “Ba ruwana, kije ke ki samesa ba babbanki bane”.
Sosai ta sanya masa kukan shagwaɓa. Dan haka yace yaji zai yi tunani ta kaima mamanta wayar....
Badan taso ba ta fita kai wayar, tana addu'a a ranta ALLAH ya ɗaurata akansa, dan tasan yanama Baban nata magana zai amince......

_________★


Kusan a tare motar Abah data AA suka iso MAWAAD COMPANY. Maanal dake murmushin hirar da Abah ke mata tabi ko'ina da kallo. Komai yana a yanda ta sanshi. Sai da Abah ya ƙara mata nasiha na karta sakarma AA fuska da Addu'a sosai sannan ya barta ta fito. Hango AA tsaye jikin motarsa yana waya yasata tsayawa har sai da motar su Abah ta fita. Numfashi ta sauke a hankali, wata irin ƙauna ta ɗa da mahaifi na sake mamaye zuciyarta akan dattijon arziƙi Abah. Tabbas alkairin Abah a gareta mai yawa ne, da baki bazai iya musaltashi ba ma. Jinsa take a ranta shi da Oum matuƙa gaya a matsayin mutane masu muhimmancin gaske. Wani murmushi mai sanyi ya ɗan suɓuce mata hawaye na taruwa mata a cikin ido tunawa da nasihar Oum ita kuma. Ita fa dariya Abah da Oum ɗin ke bata ma a kwana biyun nan, Abah na nuna mata ta hora AA, Oum na lallashinta ta yafe masa komai ya wuce su koma kamar da can baya da suke.....
Tunaninta ne ya katse jin an riƙo hannunta da wani tattausan abu da ta tabbatar hannu ne shima. Sai kuma ƙamshin turarensa yay mata irin shigar zuruff ɗin nan ya wuce har tsakkiyar brain ɗinta yabar maƙaƙinsa a maƙoshinta. Cikin ɗan motsawar zuciya ta waiwayo, sai ko idanunta a cikin nasa daya wani tsatstsareta da su. Ƙwacewa numfashinta ya nema yi, ta fisgoshi da ƙarfi tana mai saurin juyawa ta kalla harabar Companyn. Sosai ma'aikatansu ke shigowa ciki, wasu a abin hawa wasu a ƙafa. Da yawansu idanunsu a kansu suke, duk da dai sai wani sinne kawuna suke wanda ta tabbatar na munafuncine kawai. Ƙoƙarin sake juyawa garesa ta sakeyi, dai-dai ya kawo ɗayan hannunsa zai zare handbag ɗinta a ɗayan hannunta. Hucin numfashinsa ya wani irin sauka mata a fuska. Gaba ɗaya sai tai mutuwar tsaye kawai, harya gama zare handbag ɗin ya koma tsaye sosai hannunsa a cikin nata. Batare daya kalleta ba can ƙasan maƙoshi ya furta, “Let's go”.
Ƙin motsawa tayi, dan haka ya waiwayo yana kallonta. Da wani salon ƙanƙance idanu tamkar ya manta a inda suke tsaye, muryarsa acan ƙurya ya furta, “Ko goyo kike so?”. Yay maganar da ɗan takowa gabanta kamar zai duƙa ɗin ta hau bayansa. Ai a zabure ta riƙo hannunsa jikinta har yana ɗan rawa. Hakama muryarta na rawa ta ce, “Ya ilahi mi kake yi haka?”.
Karo na farko ya saki wani shegen murmushi da ita kanta sai da zuciyarta ta motsa. Girarsa ɗaya a ɗage yana wani wara mata fararen idanunsa masu ƙyalli a cikin nata. Sai taji tsigar jikinta na tashi. Da sauri ta ɗauke kanta. Shima bai sake magana ba yaja hannun nata. Dole ta bishi yanzu kam suka fara tafiyar a jere. A nutse suke ɗaga ƙafafunsu su ajiye kuma a tare. Hakan yasa ƴan gulma sake nutsuwa a kallon nasu, harda masu ɗaukar hoto a kaikaice. Sarai AA na lure da komai, amma da yake gwani ne a iya basarwa da kama kai yayi tamkar ma bai san da wasu halittu a harabar Companyn ba bayan shi da ita. Ita ko kunya da nadamar ƙin saurin shigewarta tuni duk ta baibayeta.
Securitys ɗin ƙofar kansu sunyi kasare suna kallon abin mamaki, yau boss riƙe da handbag ɗin mace. Macen da kowa yake cikin ɗunbin mamakin aurensu. Dan tunda akai bikin a companyn gulmar kenan. Burin kowa wannan ranar da zasu dawo kan aiki, dan kowa jima yake kamar bai taɓa ganin Maanal ɗin ba. Cikin sauri suka shiga miƙa gaisuwa ganin suna neman gota su. Tare da yi ma boss murnar aure da jajanta masa yaya jiki. A mamakinsu ya amsa harda ɗan murmushinsa. Duk da dama can ba wai yana wulaƙanta kowa bane, amma ganin murmushin boss haka arhar banza ai sai mai rabo.
To a cikin ma suna shiga kowa yay tsit, waɗanda ke leƙensu ta windows da musu video duk sun koma mazauninsu da gudu. Gaba ɗaya Maanal ji take kamar ta zura da gudu, dan gaba ɗaya attention ɗin kowa ya dawo kansu ne. Ta gefe ido take kallon ganin yanda duk suka miƙe a tare cike da girmamawa, shima sai yaja ya tsaya. Da ɗaɗɗaya suka shiga miƙo gaisuwa. Hannu ya dinga ɗaga musu fuskarsa da sakewa amma ba murmushi yake ba. A mamakinta sai itama suka shiga gaisheta. Karo na farko ta ɗan ɗago ta dubesu, ba wani yawane da su ba dan ba'a gama zuwa ba. Nan kuma iya waɗanda ke a ƙasa ne, mafi yawansu ma cleaners. Guntun murmushi kawai tai musu.
Fahimtar a takure take yasa AA ɗan kallonta tare da matsa hannunta dake a cikin nashi. Dubansa ta ɗanyi, a saman lips ya furta mata, “Muje”. Yanzu kam bata musaba ta bishi, dan hakan zaifi mata sauƙi ita kam. Duk da dai a ranta bata son binsa office ɗinsa department ɗinsu take son wucewa. Suna shiga elevator ta wani sauke ajiyar zuciya tare da janye hannunta dake a cikin nasa. Dariya ma shi kam ta bashi, dan haka ya taɓe baki da faɗin, “Matsoraciya, nine kika raina kawai”.
Kallonsa tai baki a tunzure ta ce, “Waye matsoraciyan?”.
Kamar wasu masu faɗan yara ya juyo yana riƙe ƙugu idanunsa ware a kanta ya ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login