Showing 39001 words to 42000 words out of 218311 words
Chapter 14 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S COLLECTION AND MORE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko
08169307477
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
***********
________________
......Su babban Yaya na dariyar Maanal AA ya shigo. Duk kallonsa sukai, musamman Mamy dake masa kallon ƙurulla, hakama Nibras ji take kamar taje ta rungumeshi ta fashe da kuka saboda kishin Maanal dake ruruwa a zuciyarta. Gashi yanda lips ɗinsa suka wani ƙara zama pink duk sai taji ta tsargu, zuciyarta ta shiga wassafa mata abinda ya faru. Cike da basarwa AA ya kai zaune. A nutsensa kamar bashi ya gama yima Abah shagwaɓa ba ya ce, “Ikon rabbu, miya saku nishaɗi haka?”.
“Bestynka mana” cewar Fawzan, sai kuma ya shiga bashi labarin abinda tayi. Wani ɗan murmushi ya saki tare da girgiza kansa. Ba ƙaramin dukan zuciyar Mamy da Nibras murmushin nasa yayi ba. Amma sai ya katse yanayin nasu da faɗin, “Mamy mun kai”. Batare daya kalleta ba. Dan yasan tana nan tana tuhumarsa da ido.
Kafin ta amsa masa Fawzan ya dawo kusa da shi neman tsokana, sai dai yana zama ƙamshin sassanyan turaren Maanal daya manne a jikin AA ya shiga hancinsa, idanu ya waro tare da sake matsawa yana shinshina shi. Cike da raɗa Fawzan ya ce, “Ehem-ehem malam yau dai babu zancen dojewa ALLAH ƙamshin turaren Lilly kake yi?”.
Harararsa AA yayi, shima ƙasa-ƙasa ya ce, “Yaya Fawzan ka rage gulma wlhy, mutum da matarsa dan anji ƙamshinta a jikinsa sai mi?”.
Sosai Fawzan ya saki baki da hanci yana kallonsa, shima AA ɗin kallon nasa yake da wani irin salon ɗage gira sama irin na (Eh ɗin nan). Jinjina kai Fawzan yayi, a hankali yace, “Ashe za'a bajeta a gaban Abah gobe. Dole a ƙara maka kwanaki sai after babbar salla”.
Yanzun ma ƙasa-ƙasa shima AA ya ce, “Yo a bajetan mana, zuwa babbar sallar kun fara jiyyarta dan ta fara laulayi kuwa, kunga sai ku bari sai ta haihu ku bani”. Daga haka ya miƙe cike da basarwa tamkar bashi ya faɗa ba. Fawzan daya saki baki yana kallonsa ya kwashe da dariya da faɗin, “Kai wannan yaro tantiri ne kai, ALLAH sai na tona”.
Gwalo AA daya nufi hanyar fita ya juyo yayma Fawzan, kafin yace, “Oum! Mamy! Babban yaya good night”. Ya fice a binsa. Cikin ɗaga murya Fawzan yace, “Muma da bakace mana good night ɗin ba lafiya lau zamu kwana, kuma gobe sai na fasa ƙwai a gaban Abah”.
Wani kalar ƙululun takaici ne ya kume Mamy, dan kallon da takema Fawzan da AA ta gefen ido tsaf ta fahimci abinda suke tattaunawa da juna ta hanyar motsin bakinsu. Gittawar AA a yanzu kuma sarai ta ji ƙamshin turaren Maanal itama. Hakama Nibras data sanya musu ido. Saheeba dai tsarguwa kawai tayi, shiko babban yaya da Oum dariya ma suke musu dan Fawzan da Ajwaad tamkar tom and jarry haka suke. Komansu irin na asalin sako-da-sako ne basa ragama juna. Ta wani gefen kuma kamar wasu abokai.. Fitar AA ɗin ta saka hirar tashi gaba ɗaya, dan dama dai rashin dawowarsu yasa hirar tsaho haka da sha biyu ta wuce...
Lokacin da Oum ta shiga ɗaki samu tai Maanal harta kwanta. Murmushi kawai tayi itama ta shiga kimtsawa domin tafiya wajen mijinta. Taje zuba kayanta a laundry basket taji ƙamshin turaren AA matuƙa a wajen, kayan cikin basket ɗin ta kalla, kayan Maanal ne data cire yanzu. Kasa daurewa Oum tai ta ɗakko doguwar rigar takai hancinta. Itace kuwa ke ƙamshin na gasken gaske. Kai Oum ta girgiza dariya na suɓuce mata, sai yanzu ta fahimci dalilin gudun Maanal da ƙin tsayawa a wajensu da wannan kwanciyar saurin. Ƙasa-ƙasa ta ce, (Wannan nake jiye maka Abansu, karka bashi matarsa dai a juri zuwa rafi) daga haka ta ajiye rigar ta ƙarasa shirinta ta tafi wajen mijinta...
_________★
Sille ya jima akan titin bayan wucewar motar AA. Dan abinda ya gani na faruwa daga nesan da bayansu da yake kasancewar gilashin motar a sauke yake kaɗan ya sashi canja shawara. Waya ya fiddo ya shiga yi musu video. Dan wata shegiyar waya ce dashi mai ƙarfin camara ta yanda yake iya zooming abu mai nisa sosai. Yako yi nasarar ɗaukar komai yanda ya kamata, daga ƙarshe ya adana videon a wayar tasa yana murmushin cin nasara. Dan yaci alwashin sai videon nan ya zame masa kadarar tatsar mutane da yawa kuɗaɗe kafin yasa ai masa editing ɗinsa ya bazashi a media ta yanda sai ya kunyata rayuwar AA da Maanal dan zai canjama al'amarin siga ne ta koma matsayin kafin aurensu ne hakan ta faru. Sauran alwashinsa kuma zai biyo baya dan baya yafiya ba kuma ya canja tsarinsa akan maida murtani saboda sabon idea.....
Hummm wannan Sille! Wannan Sille wai mike damunka ne🙄🥺.
________★
Murmushin da Oum keta faman yi ne ya saka Abah dake binta da kallo faɗin, “Wai shi wannan murmushin na miye?”.
“To Gadanga miye a murmushi ko dai ka tsargu ne?”.
“Tsarguwar ma sai nayi, dan nasan halinki sarai”.
Dariya Oum ta sakeyi, sai kuma takai zaune a kusa da shi tana faɗin, “Abansu ka fahimci a yanayin da Ajwaad da Maanal suka shigo kuwa?”.
Kansa ya girgiza alamar (a'a)
Cikin ɗan waro idanu Oum tace, “Gadanga kaji tsoron ALLAH”.
Murmushi kawai yayi baice komai ba. Oum ta ɓata fuska. “To ALLAH ina gaya maka idan baka bama Auta matarsa ba za'a haifi ɗa mara ido, kadai gani da idonka sau biyu”.
“A haifi ma mara kunne, ai nasan dai duk rashin kunyarsa bazaiyi abinda kike tsoron ba. Fateema da kike ganina sarai nasan abinda nake yi, dan haka ki daina damun kanki ina kan ra'ayina. Saboda ni nasan dalilina nayin komai”.
Shiru kawai Oum tai tana kallonsa, sai kuma ta kai kwance cike da haushi. Baki kawai Abah ya taɓe ya cigaba da duba littafin hannunsa daya kasance na addu'oi....
★Washe gari Abah ya tashi da uzirin fita da wuri, dan haka ya bada umarnin driver yakai Maanal wajen aiki. Yauma kamar jiya bayan sun kammala breakfast da Maanal bataci ba tace azumi take kowa ya shiga motarsa. Driver ya buɗema Maanal mota itama. Oum batace komai ba dan a gabanta Abah ya sanarma driver ɗin. AA ma yi yay kamar baiga komai ba ya shiga tashi motar nasa drivern ya jasa. Sai da suka fito ko street ɗin basu gama bari ba ya saka drivern sa tsaida na Abah. Fitowa drivern yay yazo saitin inda AA ɗin yake zaune yana faman duba wasu takardu. Batare daya kalla drivern ba sai gilashin daya ɗan sauke a dakensa ya ce, “Buɗe mata ta dawo nan”.
Daburcewa sosai drivern yayi, dan ba ƙaramin gargaɗi Abah ya masa ba akan hakan kasancewar yasan AA ɗin zai iya aikatawa. Cikin tashin hankali driver yace, “Ranka ya daɗe Alhaji fa yace...”
Wani banzan kallo da AA ɗin ya ɗago ya watsa masa ya saka shi kasa ƙarasa faɗa, sai ma duƙar da kansa da yay ƙasa da sauri. Shi kam dai sun sakashi a tsaka mi wuya. Kusan minti ɗaya AA ya ajiye takardun hannun nasa ya ɓalle murfin motar ya fito. Yayi ƙyau matuƙa cikin baby pink color ɗin suit, fuskar nan babu walwala sai kwarjinin kamala dana ibada ke fita. Maanal da haushin tsayawar tasu ya kumeta taja tsaki tana ƙoƙarin ƙarasa abinda take a laptop ta fito kawai taji an buɗe side ɗin da taken, ɗagowa tai cike da masifa dan son ganin wanene suka haɗa ido da AA da yay kicin-kicin da fuska. Itama dai tayi ƙyau sosai cikin lass da akaima doguwar riga, ta kafa ɗaurin zarah buhari sai veil ɗinta da yay dai-dai da tsarin shigar tata. Tana ƙoƙarin rufe laptop ɗin kawai ya duƙo cikin motar a kanta, kafin ta samu damar magana ya ɗagata cak ya fito da ita. Idan tace al'amarin AA bai fara girgiza tunaninta ba ma ai tayi ƙarya, yanzu banda ikkanci a titin ALLAH zai ɗakkota a mota da safen nan mutane nata kai-kawo. Koma tace a anguwarsu data tabbatar ko wani bai sanshi ba wani ya sanshi duk da ana rayuwa ne irinta ba ruwan wani da wani ɗin nan a anguwar. Da sauri kuwa nasa drivern ya fito ya buɗe masa ɗayan side ɗin da yaga ya zagaya, a ransa kuwa dariyar halin ogan nasa yake, yayinda suka matuƙar birgesa duk da yanata wani sinne kai. Ajiyeta AA ɗin yayi ya gyara mata rigarta ya rufe ƙofar, ita kam ai tamayi sumar zaune ne ko mi zatace oho. Dan sam tama kasa masa magana dan al'ajabi. Shigowarsa wajen da yake zaune hannunsa riƙe da tarkacenta da drivern Abah ya kwaso mata ya sata kallonsa ta gefen ido, sai wani ɓaɓɓata fuska yake kamar ba shine daren jiya ya gama aikata mata abin kunya ba. Aikinsa ya cigaba da yi batare daya sake kallonta ba yana cema drivern sa, “Muje” a daƙile.
Yanda ya basar ya cigaba da aikinsa itama sai ta basar ta cigaba da nata aikin. Har suka iso Company wani magana bai shiga tsakaninsu ba. Kai babu ma wanda ya kula ɗan uwansa. Koda motar ta tsaya kuma kasancewar tana tattara kayanta shine ya fara fita. Tayi zaton zai yi tafiyarsa ne. Amma sai a mamakinta ya zagayo ta inda take ya buɗe mata. Koda ta fito kuma sai ya saka hannu ya amshi kayan hannunta harda handbag ɗin kamar jiya. Ya kuma kama hannunta da ɗayan hannunnsa. Nashi kayan kuwa sai drivern sa daya bisu da kallo yana murmushi ne ya tattara yabi bayansa da su.
Yau ma cike da gulma wanda suka iso ke binsu da kallo suna kuma gaishesu da girmamawa. Yayinda wasu ke gwada son amsar kayan hannun AA ɗin amma sai ya girgiza kai kawai alamar (a'a). Kamar dai jiya harda masu leƙensu ta windows dan gulma. Suna shigowa kuma kowa ya nutsu aka shiga miƙa musu gaisuwa...
Yau dai kai tsaye office ɗinta suka nufa. An gyara komai fes an saka air freshener masu daɗi, shine ya kunna wutar office ɗin dake a kashe, har saman desk ɗinta kuma yaje ya ajiye kayan hannun nasa batare daya kalleta ba ya nufi hanyar fita, ita dai tana tsaye tana kallon ikon ALLAH. Har yaje ƙofar sai kuma ya dawo gabanta yaja ya tsaya. Cike da gargaɗi fuskarsa a tamke murya a dake ya ce, “Daga yau wannan ya zama first and last da zaki bishi in har ba tare da Abah ba. Azumin mi kikeyi kuma”.
Yanzun kam kallonsa tai cike da mamaki, sai kuma ta tura baki gaba ta ce, “Na nafila mana”.
“To sai kisan yanda zakiyi da shi tunda baki sanar min ba.” ya ƙare maganar da dalla mata harara ya juya zai fita..........✍️
_Oh oh AA rigima azumin ne kuma sai an sanar maka munga idi🏃🏃🤣_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣0️⃣
______________
*_LADIES COLLECTION AND MORE_*
08169307477
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S COLLECTION AND MORE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko
08169307477
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
***********
_______________
20
WANNAN SAƘONKU NE😊
LA'ILAHA ILLA-ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAZZALUMIN!!
......A tunzure Maanal data cika tai fam da wannan mulkin mallaka ta ce, “Kamar ya nasan yanda zanyi da shi? Yanzu ibadar ce kuma dan zan yi sai na sanar maka?”.
Sai da ya buɗe ƙofar sannan ya waiwayo ya kalleta, cike da izza ya furta, “Ya rage naki”. Daga haka yay ficewarsa. Harara ta rakashi da ita. Sai kuma tama ƙofar gwalo dan shi dai ai ya riga ya fice abinsa. Kujerar zamanta ta nufa ta zauna tana ƴar dariyar ƙeta. Dama babu wani azumi da takeyi, tayi hakan ne dan gujema halinsa na salon tattaɓata daya ɗauka. Handbag ɗinta ta buɗe ta ciro ƙyaƙyawan bottle mai kama da cup ɗin nan na zamani dake cike da tea, sai gasashshen bread a ƴar bowl data sanyo batare da ko sanin Oum ba. Dan Inte tasa ta haɗa mata su. Hankalinta kwance ta fara aikinta tana karyawa. Sai zabga murmushi take da bata san na miye ba itama. Kawai dai ta tsinta kanta a cikin nishaɗin yin hakanne....
Kusan ƙarfe goma takarda ta iso mata daga office ɗin HOD. Bata komai bace sai ta tafiyarsu. Komai an kammala, sannan iya su da zasuyi tafiyar an basu hutun zuwa aiki gobe, idan ma daga yau mutum zai wuce gidan duk an basu dama amma sai zuwa break bayan anyi zama da su, suyi shiri kawai dan jibi in sha ALLAHU ƙarfe biyar na yamma jirginsu zai ɗaga. Ajiyar zuciya kawai ta sauke a hankali, zata ƙarasa ayyukanta kawai yau ɗin ita kam bazata tafi yau ba. Ƙarfe sha biyu suka shiga meeting. Sai a lokacin taga sauran wanda zasu yi tafiyar da su. Ashe harda cikin manyan ma. Dan akwai CFO, sai CMO, WCD da sauransu..... Sunyi nisa a meeting ɗin kafin CEO ya shigo shida Assistant ɗinsa. Bayan sun zauna ya nema afuwar jikinrinsa, acewarsa yana da baƙi ne. Maanal na ɗagowa suka haɗa ido. Da sauri ta janye nata. AS ne yay musu bayanin abinda zasuje yi, dan kowa da fanin sa, tare da karanto musu dokokin tafiyar. Zasu yi kwana goma ne, kenan zasu dawo azumi nada kwanaki takwas, dan yau saura kwana huɗu a fara. Daga ƙarshe yace kowa zaiga alert na kuɗi a cikin account ɗinsa domin shirin tafiyar. Bayan komawa ya zauna AA ya dubesu a dakensa, idonsa ne ya sauka akan Maanal a karo na barkatai, sai dai yanzu ita ba kallonsa take ba, tana magana ne da Yaqub ƙasa-ƙasa, da'alana akwai bayanin da yake mata da bata gane ba a maganar AS. Shima janye nasan yayi yanayinsa na canjawa sannan ya fara musu nasa jawabin mai cike da gargaɗin daya saka Maanal ɗagowa ta dubesa, harara ya sakar mata a kaikaice, wani gefen kuma nasiha ce. Ya rufe da addu'a daga haka meeting ɗin ya tashi. A tare Maanal da Yaqub dake mata sallama suka fito, sai kawai jitai an riƙo hannunta, juyowa tai da sauri, sukayi ido huɗu kuwa da mai gayya da aiki. Wani banzan kallo yay mata, sannan ya zubama Yaqub wani kallon gargaɗi daya sakashi barin wajen da sauri.......
__________★
اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ.
Allahummak finihim bima shi'ita.
_Ya ALLAH! Ka isar mini su da abin da Ka so._
_________★
AIRPORT
Cike da farin cikin dawowarsa ƙasar haihuwarsa bayan dogon hutun daya sha na watanni uku yake fitowa a jirgin. Yayi fresh da shi dan ma tsufa ya cinye komai. Ƙarfarsa na gama sauka bisa ƙasa idonsa ya sauka kan amaryarsa, gefe kaɗan Oler ne da Rabilu sai sauran yaransa dai na siyasa. Sen... Bukar Kaugama yay wani murmushin jin daɗi mai cike da ma'anoni. Dan kuwa abu biyu ke ɗawainiya da shi, farin cikin dawowa ƙasarsa a gaɓar da zai mallaki ƴar shilar amaryarsa Maanal, da kuma kewar ƙasarsa ta haihuwa. Babu kunya amaryarsa tazo ta rungumesa tana masa barka da dawowa cike da farin ciki.