Showing 189001 words to 192000 words out of 218311 words
Chapter 64 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
shekarun da yawa ne Aunty, kuma kinga yana gama aikinsa ai bamu sake ganinsa ba. Amma muga hoton nan ALLAH kamar shi fa a nan”. Ta jima tana kallon hoton, sai kuma ta ɗago da sauri ya kalla Mamy. “Kai wlhy aunty yaron nan shine. Ina kika samo hotonsa?”.
“Kin tabbatar shine?”.
“ALLAH babu kokwanto shine, kuma a kira Yaya Turai, ai ita dai bazata manta ba tunda ita ta kawo mana shi. Amma tabbas yaron nan shine Ra'iz”.
Sosai zuciyar Mamy ta shiga karkaɗawa, amma sai ta ce, “Bari dai a sake turama Hajiya Turai ɗin mu sake tabbatar wa”. Tai maganar tana ɗaukar waya ta ɗauki hoton, ta WhatsApp ta turama Hajiya Turai, kafin tai kiranta a waya. Sai dai harta tsinke bata ɗaga ba. Sake kira tayi, nan ma ba'a ɗaga ba. Sai ta ajiye wayar yana faɗin, “Maybe bata kusa, nasan in ta gani zata kira”.
Maman Saheeba ta ce, “Hakane, amma Aunty miya kawo kuma zancen yaron yanzu? Kodan ance yarinyar nan virgin ce? Ke baƙya ganin duk shiri ne kawai dan su wanke yarinyar. Ko bayan wancan maganar kin sake jin sun tada maganar. Washe gari ma dangin nasu ba tafiya sukai ba kuma basu zauna da Ajwaad ɗin ba kamar yanda suka ce zasuyi”.
Kai Mamy dake kallonta ta jinina, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Hakane dukkan zancenki Nana. Amma akwai abinda na sani game da mutanen wannan family ɗin dake baki sanshi ba. Dama kai tsaye bazasu zaunar da shi su tambayesa ba a lokacin dake kike zato, sai sun gama munafunce-munafuncensu ke kin ma manta da al'amarin sannan su dawo da shi. Haka kawai kuma nake ji a jikina bincike sukeyi, dan haka dole muma mu dawo da tunanin mu baya akan duk wanda keda alaƙa da aikin nan a wancan karon mu binciko shi musan ina yake a yanzu? Mi yake yi? Musamman shi yaron nan da yay aikin da kuma Doctor. Sai maƙwafciyarmu”.
Cikin gamsuwa Maman Saheeba ta ce, “Kuma tabbas hakane, ai sai yanzu na dawo hankalina. Wlhy duk zatona sun bar zancen ne. Amma abin na matuƙar damina a zuciya. Taya za'ace ba'ama yarinyar fyaɗe ba bayan shi Ra'iz ya tabbatar yayi, shiyyasa ma shi Ajwaad ɗin ya ari laifin ya ɗaurama kansa dan a barshi ya aureta”.
“Nana zuciyata ta fara bani akwai abinda ya kamata mu sani. Ni na haifi Ajwaad na sanshi nasan halin wannan yaron. Wlhy hatsabibi ne na gaske, babu abinda ya baro na ubansu. Shiyyasa kikaga ina kaffa-kaffa da al'amarinsa, na kuma fito na bayyana masa wacece ni kai tsaye bakamar sauran ba. Idan kin san kalmar bahaushe ta KAMAR KAYI KAKI KA AJIYE to haka ne tsakanin Ajwaad da ubansu, tamkar yayi kakin ne ya ajiye. Da da ban bayyana masa wacece ni ba akan waccan banzar matar shi zai fara ganoni, amma yanzu hakan da nayi kamar na kama lagonsa ne. Tsohon shekaru bai iya faɗa ba, duk kuma wata hanyar da wani zai fahimci ni ɗin wacece hatta da sauran ƴan uwansa cikin tosheta yake. Wannan shine dalilina nayin garkuwa da shi.”
Sosai Maman Saheeba ta fahimta, ta kuma gamsu da bayanin Mamy ɗin. A ƙasan ranta kuma tana jinjina mata da jin lallai dole itama ta sake shiri kenan. Dan ƴar uwar tata ba kanwar lasa bace ba ashe. Karma ya zamto tana mata kallon kitse ne ita tana mata na rogo. Daga ƙarshe maimakon ita ta ajiyeta a duhu ita sai ta ajiyeta. To itama dai Mamyn kusan kalar tunanin nata kenan. Dan dariya take a cikin ranta da faɗin (Nana kenan, a zatonki ba kallonki nake ba. Duk wani kai-kawonki a tafin hannuna kike wlhy. A tunaninki amfani kike dani wajen cimma burinki akan ƴaƴana da dukiyarsu. Baki san nice nake amfani dake ba wajen cimma nawa burin. Amma muje zuwa dan irin wannan wasan na birgeni, kuma yana min daɗi)
😂Tofa babbar magana, wannan fa shi ake kira da ainahin AJIYA A DUHU. Wayaga kafin biri yaga ayaba, ayaba ta ganshi🤣. Kumuje zuwa mutanena yanzu ne zamu warware ainahin ma'anar AJIYA A DUHU 😄👍.
_______★
A nan kuwa Babban Yaya ne ya samu Oum da batun Ameerah dai yau kai tsaye. Matuƙar mamaki ya kama Oum, farin ciki kuma ya mamayeta har idannunta na tara ƙwalla. Ta kamo hannun Babban Yaya cikin nata. “Fadeel da gaske kake wannan maganar?”.
Murmushi Babban Yaya yayi, cike da kulawa ya ce, “Oum girmanki da kimarki ya wuce nazo miki da kalmar wasa a wannan bigiren. Nace zan rabu da Saheeba kun hanani ke da Abah, ni kuma na gaji da banzayen halayen yarinyar gaba ɗaya. Shiyyasa naga kawai gara nayi irin na Fawzan na ƙara auren. Ɗari bisa ɗari kuma na gamsu da tarbiyyar Ameerah, na kuma tabbatar zan samu yanda nake so. Hakan kuma dazan ma Saheeba shine zai zama hukuncin laifinta har naji na huce”.
“Alhamdullahi, Fadeel ALLAH yay maka albarka. Na kuma baka goyon baya ɗari bisa ɗari.”
“Nagode Oum, ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka. ALLAH ya cigaba da tsare mana ke, ALLAH ya cigaba da baibayeki da farin ciki da kwanciyar hankali”.
“Tare daku baki ɗaya Fadeel. ALLAH yay muku albarka. Yasa kuma ace gwara da aikai. Yanda Auta ya samu farin ciki haka nake fatan kuma na ganku kai da Fawzan”.
Ƴar dariya Babban Yaya yayi, ya ce, “A Oum autanki kam sai dai muce Alhamdullah. Kina ganin wata ƙiba ma da yake yi sati uku kacal da tarewa. Idan naga yana murmushi sai naita kallonsa”.
Dariya itama Oum ɗin tayi. Ta ce, “Kaima haka nake fatan naita ganin wannan murmushin a fuskarka. Dan haka ma ni bazan iya haƙuri ba yanzu zan je na samu Hajiya Shuwa. Idan zai yiwu ma wlhy a haɗe dana Fawzan nan da sati biyu kenan. Dama itama Hajiya Shuwan ta sameni akan Maimoon, Ameer ya sameta da batun yana son Maimoon kasan abin nasa ya fara sauka kwana biyu jiya ma matar ta tafi gida wai tayi yaji”.
“Ikon ALLAH, Oum dama shi komai lokaci ne, musamman irin wannan sihirce-sihircen. Haba shiyasa naga kwana biyu ya koma fita aiki, sannan zai tsaya mu gaisa yana wani duƙe-duƙen kai. Dan jiya da magrib har gidan nan ya shigo neman Fawzan, to kin san ɗan naki akwai sauƙin kai amma idan ya birkice yafi kowa daru. Sai cayayma maigadi yace baya nan”.
Dariya Oum tai da faɗin, “Oh ni Faɗima wato Fawzan ko. To ka barni da shi zan zauna da shi, ai tunda ya dawo sai yay haƙuri komai ya wuce tunda mun san bayin kasan bane ba”.
“Ato ya dai kamata Oum”....
★Kamar yanda Oum ta faɗa batai ƙasa a gwiwa ba ta samu Hajiya Shuwa da batun babban Yaya. Ya subahannallah farin cikin da baiwar ALLAHr nan ta nuna har sai da Oum tai mamaki. A take tace wlhy ko yau Fadeel ya shirya ta yarda a aɗaura masa aure da Ameera koda Ameera bata so kuwa. Balle dama taga kwana biyu wani mutunci na yawaita tsakanin Ameera da babban Yayan har tanata mamaki, ashe ashe sun san mi suke ƙullawa...
Shima Aba a ranar Oum ta bashi labari a waya. A mamakinta shima farin ciki sosai ya nuna. Harda tabbatar mata washe gari zai dawo gida. Dariya ma abin ya dinga bama Oum, dan ta fahimci Gadanganta ya huce kenan. Yajin da akai musu kuma ya ƙare. Aiko ya ƙare ɗin, dan washe gari sai ga Abah ya dawo. AA ne yaje ya ɗakkosa a airport shi da RK da sassafe. Ita Oum ta zata Abah ya sanarma Mamy, tunda da dare sukai maganar washe gari kuma sai gashi itama bata san da safen zai dawo haka ba sosai. Dan bama tasan AA yaje ɗaukarsa ba shi da RK, tunda RK banan yake kwana ba yana gidansa dake cikin asibitinsa shi da matarsa, sai dai kusan kullum Nuwaira na nan gidan saboda laulayi. AA kuwa yau weekend batai tsammanin ganin idonsa da wuri ba ma sam...
A lokacin da su AA ke shigowa da Abah gidan ne kuma su Mamy ke can suna tattaunawa ita da Maman Saheeba akan batun hoton Ra'iz, suna kuma tsumayen kiran Hajiya Turai amma shiru.. sai kawai ga Saheeba kamar an jehota tana sanar musu ga Abah can ya dawo. Mamaki ya kama Mamy da Nana, amma sai Mamyn batace komai ba tunda tasan mike faruwa tsakaninta da Aban. Koda Maman Saheeba ta ɗakko zancen ma sai ta basar ta hanyar ɗaukar waya tana faɗin, “Bara dai na sake kiran Hajiya Turai ko ina ta shiga haka”.....
__________★
Duk kiran da Mamy kema Hajiya Turai akan idonta ne. Dan lokacin tana jikin Sille kwance ya gama Sille ta tas. Yau kwanansa biyu a gidan tare da ita, shiyyasa dama take son tura Nuratu gidan su Mamyn dan tafi samun isashen lokaci da Sillen. Cikin ɗan yamutse fuska ta nunama Sille fuskar wayar da faɗin, “Mamarka fa ta daman. Kuma bazan ɗauka ba dan nasan sotake tace Nuratu zata dawo gida. Ni kuma bana buƙatar haka ban gaji da kai ba”.
Cike da iskanci Sille yay dariya da faɗin, “Ke dama kina gajiya dani ne. Shekaru sunja amma kina ƙara kangarewa. Ya kamata ki ɗaga kiji minene, kin san daren jiya na tura mata saƙo na san kuma ya risketa zuwa yanzu. A nawa hasashen ta zurfafa tunani akan hotunan dana fara tura mata, tana son sanin miya alaƙanta hoton matar ɗanta da sauran hotunan, anan ne zata fara tuna wanene ɗayan hoton shima”.
“Eh kuma fa hakane, ai bari ma na duba WhatsApp dan ɗazu kuwa naga kamar ta tura min hoto kafin kiran nan ma”. WhatsApp ɗin kuwa ta shiga, sai ko ga hoton Ra'iz. Da mamaki ta ce, “Baby na kaga kuwa hasashenka yayi dai-dai. Wai ya akai kasan matar nan haka da yawa ne?”.
Mintsini mai zafin gaske ya bata cike da baƙar mugunta har sai da tai ƙara. Kafin cikin raɗa ya ce, “Karki manta ita ɗin UWATA ce, sannan irin tunaninta gareni ki kula ita ɗin SURUKARKI ce”.
Hajiya Turai tasan halinsa sarai dan haka tai murmushin yaƙe kawai. Shi kuma ya ɗauka taba yana kunnawa da faɗin, “Kice mata shine wanda take tunanin, idan ta tambayeki yana ina yanzu kice ta tambayi ɗanta Ajwaad”.
Cike da mamaki ta ce, “Amma Baby miyasa zanyi hakan?”.
“Saboda haka na tsara. Dan komai nawa ni ina binsa daki-daki ne kema kin sani”.
Kanta ta jinjina masa da faɗin, “Kayi haƙuri na fahimta”.
Banza ya mata, sai kuma ya ɗaura mata tabar a baki, dole ta zuƙa. Aiko tari ya sarƙeta dan bata iya sha ba. Sai idan yaso mata mugunta ne yake sakata sha dole ko ƙwayoyi. Aiko tari take sosai idannunta sunyi jazur. Yako shiga balbala dariya cike da tsantsar mugunta har kifawa yake..........✍️
😮💨Kai jama'a ALLAH ya rabamu da faɗuwar baƙar tasa. Ga kuma wata sabuwa. Shin miya alaƙanta Hajiya Turai da Sille kuma🤣 AJIYA A DUHUn fa kenan kumuje dai zuwa🏃🏃🏃🏃.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣4️⃣
______________
........Maanal na kitchen AA ya shigo, dan tunda taji yana waya da RK daya kirashi yazo su ɗaukesa Abah a airport ta martaye daga barcin da take yi tunda taji Oum ma bata sani ba. Sosai AA da ƙamshi ya jawoshi kitchen ɗin mamaki ya kamashi, dan yasan shi dai barci ya barta tanayi. Hankalinta yayi nisa a harhaɗa abincin yay gyaran murya, juyowa tai da sauri, sai kuma ta sauke ajiyar numfashi a shagwaɓe ta ce, “ALLAH ka bani tsoro Besty”.
Murmushi yayi, sai kuma ya ƙaraso inda take ya rungumeta ta baya kasancewar ta juya tana kwashe Irish ɗin dake cikin air pryer. Wuyanta ya sumbata tare da raɗa mata, “I'm sorry. Yaushe kika tashi ke da na bari kina barci?”.
Ɗayan hannunta takai ta shafo fuskarsa. “Tunda Uncle R ya kiraka na farka, kawai nayi shiru ne harka fita. Yaya Aban?”.
“Abanki na lafiya gashi can a sashensa. Yanzu wannan kayan daɗin duk na waye?”.
“Na Abah mana”.
Ta faɗa tana juyowa bayan ta zuba wani dankalin.
“Mu baza'a sammana ba kenan?”.
Kaɗan taja hancinsa da faɗin, “Ko ɗan guntu bazaku samu ba”.
“Idan an hanamu wannan ai Ni sai a bani nawa abincin”.
“Oh kana ma da wani abinci kenan?”.
“Eh mana”.
Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya. Sam bata wani fahimci ina ya dosa ba, dan haka ta ɗan taɓe baki. “To maza kuwa kaje kaci, dan nan babu kasonka”.
Fahimtar bata gane ina ya dosa ba ya sakashi sakin murmushi. Cike da son ƙureta ya duƙo ya gwargwaɗa mata a kunne. Ai babu shiri ta kallesa, sai kuma ta shiga turashi cike da bori tana faɗin, “ALLAH ya shiryeka bar kitchen ɗin nan”.
Dariya ya shiga yi, itako ta dage sai turashi take. Gocewa yay kawai ya ɗane kan kitchen cabinets. Ta tsaya tana hararsa hannayenta riƙe da ƙugu. Fuskarsa da murmushi ya haɗe hannayensa waje guda. “Yi haƙuri giwar mata, amaryar AA Darma”.
Dariya ya bata sosai, ta murmusa tana juyawa kan aikinta. Sai kuma ta matsa inda coffee maker yake ta haɗa komai a ciki. Ta sake dawowa tana duba abubuwanta dake kan wuta. AA kuma ya zaro wayarsa datai ƙaramin vibration alamar shigowar saƙo yana dubawa. Coffee ɗin da yay ta juye dama kofi ɗaya ta saka ta ɗako tazo gabansa da shi. Miƙa masa tai, ya amsa tare da sumbatar gefen fuskarta ya ce, “Thanks you, ALLAH yay miki albarka”.
“Amin ya rabbi tare da kai”.
Itama ta faɗa tana komawa kan aikinta. Zuwa can yace. “Besty zo kiga”.
Spoon ɗin hannunta ta ajiye ta nufoshi. Kamota yay ya saka a tsakiyar ƙafafunsa kansa na a kafaɗarta ya shiga nuna mata abu a waya.
“Woow ammafa sunyi ƙyau, amma da za'a ɗan ƙara wani abu da zasu fi haka ƙyau. Waya zana?”.
“Da gaske?”.
“ALLAH kuwa. Musamman ma hannun, ni sai yay min girma gaskiya. ”
“Prof... Ne ya turosu yanzu ta email. Wai ko zamu iya fitar da su amma fa gaggawa ake so kada su wuce 10 days”.
“Da gudu ma za'a iya, musamman idan akwai kayayyakin da agogon ke buƙata a company”.
“Eh to sai dai mu bincika. Mizan tayaki da shi? Faka-faka ki duba zanen zuwa gobe dole muje company”.
“Amma gobe fa muna da baƙi ka manta”.
Gannin yayi jimmm alamar tunani ta ce, “Amma idan dan tattaunawa ne ai nake ga babu damuwa tunda dama wanda ya kamata a tattauna da su ɗin ne sai kawai ayi meeting ɗin anan. Kaga Monday sai kowa ya tashi da shirin aiki”.
“Woww kuma haka ne. Thanks you. Mizan taya ki?”.
“Yi zamanka nama kammala, kashewane kawai. Sai dai zaka taimaka ka kaima Oum kaga banyi wanka ba”.
“Na zama ɗan aike kenan?”.
“Eh mana, bakaji wani mawaƙi yace ku bayin mata bane ba”.
“Ya muka iya mun amsa da hannu biyu. Dan jin daɗin duniyar sai da ku Besty”.
Dariya sosai Maanal ta sanya. Da taimakonsa ta zuba komai a kuloli da bowl masu ƙyau da duk ta fiddo a kwalayensu. Suka jera su a basket har uku sannan. Cike da tsokana tace, “Kafa bi a hankali Besty, dan in ka zubar sai kasha bulala”.
Dariya yayi yana fita ta back door, itama tana dariyar ta shiga fita da nasu saman dining, Dan yau anan sashensu zasu yini itama Oum a barta ta huta da Abah. Babu daɗewa AA ya dawo ya ɗauka ɗayan basket ɗin ya sake fita. Ita kuma ta hau gyaran kitchen ɗin. Koda ya dawo ya sanar mata Aban da Oum nata sanya mata albarka