Showing 84001 words to 87000 words out of 218311 words

Chapter 29 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

iskanci. Dama kuma an cika anguwa da labarin Huznah bata da mutunci idan aka shigo gidan taga talakawa ne tata musu yatsine-yatsine. Fitsari ta buƙaci Huznah zuwa tayi, kamar bazata tashi ba sai da Sageer yay mata magana. Koda taje tayo sai ta canja wajan kwanciya. Ita dai yarinya batare komai ba ta bama Sageer tsinken gwajin ciki ta faɗa masa yanda za'ai. Bai wani je ko'ina ba anan gabanta yayi komai. Aiko a farko ma ya nuna akwai ciki. Wani ta ƙara bashi, shima dai haka, ta bashi na uku still shima haka.
Ta ce, “Congratuletion Yaya Sageer Auntynmu na da ciki, ya kamata kuje asibiti gobe dan asan kwanakinsa, ga wannan tasha zai taimaka mata daina jin aman. Idan da hali kuma a daina dafa kifin da bata son”.
Sosai Sageer da fuskarsa tai matuƙar washewa tun ambatawar Zubaidah cewar Huznah nada ciki murmushinsa ya sake faɗaɗa. Godiya ya shiga yima UBANGIJI, sai kuma ya shiga sanyama Zubaidah albarka itama. Yarinyar nada hankali da nutsuwa gata bata da yawan magana. Sosai ake yabama tarbiyyar yaran gidansu a anguwar, ga girmama na gaba dan duk wanda ya girmesu a Yaya yake ko Aunty a anguwa ko Baba ko Uncle. Koda ya bata kuɗi ƙin amsa tayi...
Huznah kam tunda Zubaidah ta ambata kalmar ciki tai sumar kwance, so take brain nata ta banbance mata wake da ciki amma kamar bata wani fahimta da ƙyau saboda ruɗani da shiga gigita na bazata. A haka Sageer ya dawo ya wani rungumeta yana sake jera godiya ga UBANGIJI. Hakama Khadijah da Zubaidah ta sanar mata kamar an jehota ta shigo ɗakin, dole Sageer ya saki Huznah. Farin ciki suke shi da ƙanwarsa, yayinda ita kuma ta shiga halin ɗimuwa da gigita. Ina itace za'ace ma tana da ciki, cikin ma na Sageer ba AA ba. Wannan abune da bazai taɓa yiwuwa ba, dole wannan cikin yabi rariya kuwa. Hakan alwashinta ne dan bazata taɓa yarda ta haihu da Sageer ba koma mizai faru sai dai ya faru.......


Tofa babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja🏃🏃🤣


_________★


Tsaf Manaal da AA sukai shirin fita. Duk da Maanal bata so tashi a barcin data koma bayan sallar asuba ba dan ya mata daɗi sosai. Suna fitowa suka ci karo da su AS da rabon su dasu tun randa suka zo. Gaba ɗayansu sun shiga gaishesu da girmamawa ne da tambayar jikin AA dan jiya Mr Li ke sanar musu dalilin fara fita abinda ya kawo su. Da yake anan ba kamar Nigeria ba haka suka haƙura basu je dubashi ba duk da sun so hakan. Maanal nason yima Yaqub magana tana tsoron fushin AA. Sai kuma yanda CFO Faseelat take dama-dama da AA ya ɗan tsayama Maanal a rai. Duk da tun a gida kai tun ma farkon zuwanta MAWAAD ta so fahimtar wani yanayi daga CFO ɗin game da AA. Sai kuma dai ta ƙaryata zuciyarta dan CFO Faseelat A Zakaria ba yarinya bace ba, a ƙalla zatai sa'ar Fawzan koma ta ɗan girmesa kaɗan. A tsakanin Fawzan da AA ma kuwa akwai ƴar tazarar haihuwa kamar yanda Oum take faɗa. Kawai sai Maanal taji ita abun ma ya bata dariya, batare data maida hankali ba ta taɓe baki kawai ta cigaba da istigafarinta a zuciya dan shine mai fishsheta da azuminta a baki.
Sun isa *Nicolas G. Hayek Watchmaking school* da zasu samu horaswar. Tarba suka samu ta musamman ga matashin professor Zhang Kuma abokin karatu ga AA. Dan cike da tsokana ya ɗan kalla Maanal dake a sashen AA sannan ya ɗan kalla AA ɗin yana masa wani salon tambaya da ido. Ɗan kallon Maanal ɗin shima AA yay, sai kuma yay murmushi...
Prof.... ya ce, “Wow Maanal right?”. Ƙaramar harara AA ya sakar masa, Prof.. ya sanya dariya. Hakama AA ɗin murmushi yake yi. Bayan AA ya gama doguwar jiyyar abinda ta faru da ƙyar su Abah suka samu ya koma makaranta a wancan lokacin, dan likitansa ya tabbatar musu hakan ne zai taimaka ma brain ɗinsa samun daidaito da heart ɗinsa datai breaking. Ga kuma matsanancin depression da yake ciki a lokacin. Haka kuwa akai AA ya zana SSCE ta online abinka da ƴaƴan manya, babu jimawa sakamako ya fita aka shiga nema masa admission, cikin sa'a aka samu kasancewar Abah matsayin ambassador. Sannan takardunsa sunyi ƙyau sosai dan ya samu result mai ƙyau sosai. A jami'ar ya haɗu da Zhang, a lokacin shi yana Masters ɗinsa ne, inda AA ke zuwa ya zauna ya ware kansa nan suka haɗu da Zhang, tun yana tsayawa yayta kallonsa daga nesa dan shi yanayin fatar AA ɗin ke ɗaukar masa hankali har takai ya fara ɗan masa magana.........✍️






*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣1️⃣




______________


.......Da farko AA baya kulashi kamar yanda baya kula kowa a makarantar. Yakan dai shiga aji da an gama lecture zai fito yazo wajen ya zauna har sai lokacin wata kuma. Sai yazo yini guda ya fita baiyi magana da kowa ba a school ɗin. Wani lokacin Babban Yaya da RK ke zuwa ɗaukarsa, wani lokcin kuma Abah da kansa kuma su suke kawosa. Kamanin da suke da juna yasa Zhang fahimtar suna da alaƙa ne, ya kuma ji sunan Maanal ne a bakin AA, dan in yana zaune shi kaɗai ɗin nan yakan rufe idanunsa yay shiru a kujerar wajen kamar mai barci amma zakaji sunan Maanal na fita masa a baki ko yace Besty. Tun Zhang na ɗaukar AA nada matsala ta brain shiyyasa yake sambatun kiran abinda bai san miye ma'anarsa ba har daga baya ya gane AA yana cikin depression ne. Dan yayi course na karantar halayyar ɗan adam. AA ya bashi tausayi, dan haka ya fara zama kusa da shi koda bazai kulashi ba, dan wani lokacin ma tashi yake ya bar masa wajen. Shi kuma bai taɓa ce masa komai ba tsawon lokaci har AA ɗin ya daina tashi a waje idan yaga Zhang yazo ya zauna. Yau da gobe sai yake zama suyi gaisuwa kawai har dai shakara taja. Bayan sanin sunan AA abu na biyu da Zhang yaso sani shine miye ma'anar Maanal, sannan waye Besty da yake jin AA yana yawan ambanta. “Maanal suna ne, kuma itace Besty”. Ya bashi amsa a taƙaice. Ya ce, “Mace ne ko namiji?”. Anan ma AA bai kawai komai ba ya ce, “Mace”. Tun daga nan Zhang ya fahimci matsalar AA. Bai sake masa tambaya akan hakan ba kuma har AA ɗin ya fahimci abinda Zhang ya karanta, sai kawai Maanal tazo masa a rai da zane-zanenta.
Wannan shine tushe kuma asalin kafa alaƙarsu, kuma shine ya taimaka masa wajen kafa Maawad Company dan da taimakon Professor Zhang. Ya taɓa zuwa Nigeria lokacin buɗe MAWAAD COMPANY. Hakama zanen dake a companyn yasan na Maanal ne dan anan Chaina AA yasa aka zana shi yana siffanta musu ita. Har zuwa yanzu AA bai taɓa bashi any labari akan Maanal ba, iya abinda ya sani kenan, amma da kansa ya fahimci ita budurwarsa ce, amma basa tare. Sanin AA baya kula mata sam ganinsa da mace a yanzu da kuma kamanin da Maanal tai masa da wani hoto daya taɓa gani a wallet ɗin AA passport ne ma yasa shi saurin ganewa duk da bai tabbatar ba ya dai canka ne kawai....
Rungume AA Prof yay cike da tayashi farin cikin jin ga Maanal a matsayin matarsa, cike da tsokana ya ce, “Wannan karon dai tunda Maanal ta dawo ya kamata nasan labarinta”.
A mamakinsa murmushi AA yayi, bai kuma musa ba, amma bai ce komai ba dai a bayyane. Maanal AA ta zubama ido, tana son fahimtar mi Prof ke son faɗa, sai dai yaƙi yarda ma su haɗa ido har suka isa wani aji bisa jagorancin Prof ɗin. Sun fara gabatar da lecture ta awa ɗaya. AA na kusa da Maanal dan haka ta dinga masa tambaya akan abinda bata gane ba dan anayi suna rubutawa ne. Bayani yake ɗan mata, wasu kuma yace ta bari su koma masauki dan ta samu damar fahimtar Prof ɗin. Daga school ɗin wani companyn Prof ya wace da su. Su AS suna a motar su kamar yanda suka zo, ita da shi a mota Mr Li na jansu, sai Prof a gefen driver. Hira suke da AA da Chaines, dan haka Maanal ba fahimta take ba. Sai ta ma maida hankalinta a bitar abinda suka koya yanzun nan. Wani katafaran companyn agogo sukazo. Sosai wajen ya birge kowannensu, suka cika da fatan suma wataran suga companyn su a haka. AA da Prof ne suka jagoranci zagayawa dasu, Prof na musu bayanin komai yanda zasu fahimta su kuma ƙaru da ilimi. Suna ko ƙaruwar, dan duk sun nutsu yanda ya kamata. Maanal sai take jin kamar ana wanke mata brain ne, wani sabon karsashi take ƙara ji game da zane-zane bama na agogon kawai ba. Anan sukaci lokaci sosai. Bayan sun fito suka maida Prof makaranta, su kuma suka nufi wani wajen. Isowarsu yasa kowa ya fahimci massallaci ne. Sosai nan ma ya birge su Maanal, musamman ma ita da AA ke mata bayanin komai. Hakan ya fahimtar da ita lallai AA yasan Shanghai sosai, kuma da alama yayi zaman garin ma. A karo na farko ta fara kwaɗayin son jin wani abu game dashi bayan rabuwarsu. Lokacin sallar zuhur ne, ita da CFO Faseelat suka nufi sashen mata, su kuma su AA sashen maza. Itama Faseelat ta taɓa zuwa massallacin dan ita wannan shine karo na biyu da akai irin tafiyar nan da ita a ƙarƙashin kamfani, sannan a karan kanta tazo Chaina har cikin Shanghai yawon buɗe ido da tsohon mijinta. Kuma duk ta ziyarci massalacin dan yanada tarihi mai girma a wajen musulman Chaina. Koda aka idar da salla zamansu sukai, dan AA ɗin yace suna nan har magrib. Alkur'ani Maanal ta ɗauka tai karatu, sai Faseelat ta shagala a kallonta, daga ƙarshe ta ɓingire barci itako Maanal nata karatunta har Asr. Ita ta tada Faseelat ɗin ta fita ta canja alwala, sun gabatar da la'asar sai suka fito domin shan iska kamar yanda Faseelat ɗin ta shawarci Maanal. Bata musa mata ba, dan koba komai matar zata iya haihuwar kamarta idan auren wuri tayi.
A mamakinta suna fitowa sai suka hango AA can cikin wata rumfa zaune tare da wani. Kamar ance ya juyo suka haɗa ido. Wani ɗan sassanyan murmushi yay mata itama sai ta samu kanta da maida masa murtani. Da hannu yay mata alamar tazo. Sai ta ɗan juya ya kalla CFO. Gani tai itama hankalinta akan AA ɗin yake, duk da dai tana kallonsa ne cike da basarwa na manyam matan Abuja. Cikin ɗan kwantar da murya na girmamawa Maanal ta ce, “Bara naje yana kira”.
Kamar wadda ta daburce CFO ta amsa mata a ɗan daburce. Ita dai Maanal batabi takanta ba tai gaba. A zuciyarta ko faɗi take (Tsohuwar kawai ƙwalelenki wannan kayan sai Maanal) tai gaba abinta. Tan a isowa wajen AA ya kamo hannunta ya zaunar a kusa da shi, kafin cikin girmamawa ya kalla dattijon mutumin da sai yanzu Maanal taga fuskarsa ya nuna masa Maanal ɗin da alamu suka tabbatar ya riga ya masa bayani a kanta. Ita kuma ya juya yana sanar mata cewar shi ɗin malaminsa Āhōng Chen a lokacin da yay zaman Chaina na tsawon shekara biyu. Murmushi Maanal tayi, cikin harshen turanci ta rissina ta gaida shi. Shi ko dattijo ƙyaƙyƙyawa cikakken bacine da hasken addinin Islama ke zageye da kwarjininsa ya amsa mata da kulawa shima da harshen Ingilishi. Ya ɗora da addu'a a garesu. Kan Maanal a ƙasa take amsawa, yayinda AA ke amsawa kai tsaye. Āhōng ya shiga yi musu nasiha da bama Maanal ɗin labarin zamantakewarsa da AA, a labarin Maanal ta fahimci Āhōng ya taimaki AA sosai a rayuwa, dan har lokacin da suka haɗu AA na cikin depression, shine ya ringa masa addu'oi da shawarwari ya jashi a jiki har ya bayyana masa damuwarsa, cikin ikon ALLAH kuma kafin yabar garin sai gashi abubuwa sun dai-daita masa. A cikin labarin yake basu shawarwarin gina ƙyaƙyƙyawar alaƙar rayuwar aure mai tsafta da danƙo. Sosai Maanal ta jinjina ilimin wannan bawa, ashe mu baƙaƙe musamman a Nigeria da muke ɗauka kamar mune kawai musulmai ashe namu wasa ne, dan da yawanmu bama ƙoƙarin neman ilimin addini akwai dai son addinin a tare damu wannan ta shaida kam...
Kiran sallar magrib ne ya tashesu a wajen, ita ta koma sashensu na mata su kuma suka nufi na maza. Alwala tayo dan bataga CFO ba. Sai da ta shiga massalacin ta ganta a sahun gabansu, batayi magana ba tasha ruwa da dabinon da aka basu sannan aka gabatar da sallar magrib. Bayan an idar suka fito domin yin buɗa baki anan harabar massallacin da ake shiryawa gwanin birgewa. Ɓangaren mata daban na maza daban. A yanzu sun gaisa da mutane daban-daban dan matan basu da yawa sosai. Daga ita dai CFO ne kuma baƙar fata a wajen, duk da Faseelat farace tas-tas da alamar ma ana ƙarawa da skincare, amma hakan bazai hana a kirata baƙar fata ba. Itako dama baƙar ce, kuma Alhamdullah tana alfahari da fatan ta. Kaɗan ta tsakuri abincin, lokacin isha'i yayi suka koma cikin massallaci. Anyi sallar isha'i akai asham. Sun gaisa da mutane akai sallama kowa ya fito domin kama gabansa. Sosai rayuwa a massalacin taima Maanal daɗi, duk da wani gefe na zuciyarta na missing ƙasarta ta haihuwa da yanda azumi ke kasancewa musamman na farko da ake kaishi cike da ɗoki da buri. Waccan shekarar iyanzu suna a Jos ita da su Zeezah, acan sukai azumin sai da yakai tsakkiya suka dawo Kaduna. Sai ta ƙara jin wani kalar kewar mutanen gida...
“Mi matar Ajwaad ke tunani? Bayan gashi a gefenta”.
A bazata taji saukar lallausar muryarsa a cikin kunneta, fiskarta da murmushi ta juyo, yana daga bayanta ne ya ɗan duƙo, sai ta samu kanta da kai yatsa ta ɗan dungure masa kai da faɗin, “Miyasa mijin Maanal ya cika sa ido ne?”.
Murmushi yayi mai faɗi da ƙyatarwa, ya miƙa sosai tare da kama yatsar nata cikin hannunsa. Sosai abinda ta faɗa ya wani ratsa masa zuciya da cikata da farin ciki. A hankali ya jawota gabansa, batare da tunanin komai ba balle kunyar mutanen dake ɗan kai-kawo ya rungumeta, dan su AS har sun wuce wajen mota. A hankali ta kumshe idanunta, shima haka, suka saki ajiyar zuciya a tare zukatansu na sauka a kankali daga nauyin da su kayi. Cikin ƙaramin sauti mai marmashe zuciya AA ya furta, “Barka da shan ruwa ZUCIYAR AJWAAD”.
Wani irin zuuu Manaal taji a jikinta. Sosai kalamansa na ƙarshe suka mata nauyi. Akwai shaƙuwa mai girma tsakanin da AA, irin shaƙuwar da zata iya rantsewa bata taɓa yi da wani ba. Ɗaya baya ƙaunar ganin ɗaya a damuwa, hatta da ciwo sun sha yi a tare. Abubuwa da yawan gaske nasu a tare ne. Amma basu taɓa danganta al'amarinsu da wata kalma ta soyayya ba koda ƙanƙanuwa. Sai dai suji a bakin mutane na ambatawa amma basu da kansu ba. Zata iya cewa wannan itace kalma ta biyu a rayuwarta da taji daga bakinsa da zata iya kamantata da hakan bayan kalaman ɗazun da asubahi, amma sai ta basar, kamar yanda suka saba ta ɗago fuskarta da dariya tana kai masa mintsini....
Da sauri ya ce, “Ouch! Besty wai a ina kika koyo muguntar nan ne?”.
Dariya tayi tana ɗan tafiya da baya, girarta a ɗan ɗage ta ce, “Da zafi ne?”.
Hararta yay da ɗan haɗe fuska ya ce, “Kina son sani?”.
Gira ta ɗaga masa.
Ya ce, “Okay bari sai munje makwanci zan banbance miki”..
Duk da gabanta ya faɗi sai ta sanya ƴar dariya, “Besty ai nasan kai bawan ALLAH ne baka faɗa cikin azumi”.
Yanzun kam dariya sosai tazo masa amma ya daure baiyi ba ya saki murmushi tare da takawa ya riƙe hannunta daga ƴar tafiyar da take da bayaya. Tafiya suka fara a tare cike da nutsuwa har zuwa wajen motarsu, Mr Li ya buɗe musu suka shiga. Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya, sai kuma suka kalla juna. Murmushi sukayi a tare, gira a ɗan ɗage AA ya ce, “Yaya kin gaji ne?”.
“Sosai ma, burina kawai nakai kwance yanzu. Gashi kuma ina son duba lecture ɗin yau”.
Kafaɗarsa ya ɗan matso mata alamar ta kwanta. Sai da ta kallesa sukama juna murmushi mai sanyi sannan a hankali takai kwance a kafaɗar tana sauke ajiyar zuciya acan cikin ƙirjinta. Sai kuma ta gyara zamanta tana lumshe ido. Baice komai ba illa ɗan kallonta da yay ya ɗauke idonsa. Cikin ƙanƙanin lokaci Maanal tai barci, har bata san sunzo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login