Showing 87001 words to 90000 words out of 218311 words
Chapter 30 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
sun tsaya gidan abincin ranar ba Mr Li ya fita yay musu takeaway dan yasan zuwa anjima dole zasu buƙaci abinci........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣2️⃣
______________
........Lokacin da suka iso hotel su AS tuni sun shige, AA ya kalla Maanal dake barci sosai, sai yaji ta bashi tausayi. Ita da ya sani da ragwantar azumi, koda yake yanzu an girma maybe ta daina tunda yaga yau batai raki ba, amma a da duk randa aka kai azumin farko tofa Maanal da kuka take kaishi. Murmushi yayi komai na dawo masa a zuciya kamar film. Baya son takurawa Mr Li, da zasu cigaba da zama a motar ne harta tashi, to yakamata shima a bashi nashi Freedom ɗin yaje ga iyalansa. A hankali AA ya kamata ya kwantar kamar wata ƙwai, kafin ya fita a motar, ta side ɗin da take ya zagaya, ya ɗan duƙo cikin dabara ya kamata tare da juya bayansa ya ɗaurata, a duƙen ya miƙe tana a bayansa har tana gyara kwanci ya miƙe tsaye da ƙyau riƙe da ƙafafunta, ita ko ta sake sarƙe hannayenta a wuyansa ta lafe. Da sauri Mr Li ya tattaro musu kayayyakinsu ya biyosu da shi, a haka ya shiga da ita cikin hotel ɗin, rayuwa ce irin ta ba ruwan wani da wani babu wanda suka zamewa abin kallo, kowa harkar gabansa yake. A haka ya shiga elevator da ita. A bazata ya fito daga elevator ɗin yaci karo da CMO da HOD da alama fita zasuyi, kicin-kicin ya sake yi da fuska, suma duk sai sukai ƙasa da kawuna like bama su ganshi ba. Ko kallonsu baiyi ba balle ya nuna ya ma sansu yay wucewarsa Mr Li biye da shi. Aiko suka juya suna kallonsu cike da mamaki. Eh lallai mace dabance, mace sarauniya ce, mace duniya ce. In ba hakana CEO ne goye da mace, kai lallai babbar magana, al'amarin kamar wani film.
Oho AA baima san anai ba, dan yayi gaba kaɗan can ma ya hango CFO tana waya, ɗauke kansa yay dan ta tsaya tsai daga maganar da take kamar wadda ta suma. Shi ko ya saka card ƙofa ta buɗe yay ciki. Mr Li ya saka masa kayan ta ciki yana daga waje ya juya, shi kuma ya saka ƙafa ya rufe ƙofar abinsa sannan ya nufi gadon ya sauke Maanal dake barci bil haƙƙi alamar ta gaji sosai. Takalma ta ya zare mata, ya warware veil ɗin ma ya cire.. Sai ta sauke ajiyar zuciya ta gyara kwanciya. Tsai ya ɗanyi yana kallonta na kusan minti ɗaya, kafin ya sauke ajiyar numfashi ya sake kai hannu ya fara buɗe botiran rigarta, ya ɓalle fin biyar kamar wadda aka ankarar ta farka, wani kalar cafke masa hannu tayi tana buɗe idanu da ƙyau irin na (lafiya kuwa?) shima sai ya zuba mata nasa a wani kalar kasalance, sai kuma ya shiga jansu ƙasa ya sauke akan hannayen nasu, ita kuma sai tai tunanin jikinta yake kallo ta inda ya buɗe botiran, hannun ta saki da sauri ta kama rigar ta cikuykuye a cikin hannunta ta rufe wajen ruf....
Sai kawai ya samu kansa da sakin wani kalar lalataccen murmushi. Baki ta tura irin na jin haushin dan mi zai mata dariya. Fahimtar hakan sai ya sake sakin murmushin tare da matsar da fuskarsa gab da tata suna busama juna numfashi.
“Idan abinda kike tsoron zanyi ai idanuna a cikin naki zanyi ba kina barci ba fa, dan haka karki damu kanki saura ƙiris”.
Fuskarsa ta ɗan ture ta juya masa baya, sai ya sake yin murmushi ya leƙa fuskar ta bayanta. Cike da son ƙureta ya ce, “Please ki tayani wanka mana na gaji sosai My EverBloom!”.
Gaba ɗaya ji Maanal tai tama daburce ta rasa ina zata saka kanta. Yanda tai ɗin ya matuƙar bashi dariya, tsabar son ya sake ƙureta sai ya riƙota yana faɗin, “Okay! Okay shike nan na haƙura har sai randa aka kawo min ke har ɗakin barcina a lulluɓe like kowace sarauniyar amarya, ki kasance cikin shiri dan babu batun ɗaga ƙafa ranar fa, zan zama kurma ne, sannan makaho na haƙiƙa...”
Ita dai tuni ta cusa kanta a tsakiyar ƙafafunta ne tana jin kamar gadon ya rabe biyu kawai ta shige ciki ya maida ya rufe da ita. Shima fahimtar ya gama kaita maƙura ya sashi duƙawa ya sumbaci wuyanta ta gefen kunnenta, wani kalar girgiza jikinta yayi dan har tsakiyar kai taji sumbar nan, sai kawai ya miƙewa yana ƴar dariyan shaƙiyanci yabar wajen. Kaya ya fara cirewa dan wanka shi yafi buƙata fiye da komai a yanzu. Ita dai tana rufe a wajen har sai da ya shige sannan ta koma ta buɗe iya fuskarta tabar jikin kawai a rufe, sai dai ta wani ɓata fuska abin dariya.....
___________★
Cikin dauriya da son nuna juriya Huznah ta tashi da azumi, duk da da farko Sageer yace mata idan bazata iya ba ta barshi. Ta dage akan zata iya, jin tace zata iya shima ya sameta yako more da asubar sannan sukai sahur, haushin abinda yay matan ya sata jin sake tsanar cikin. Tana samu ya fita sallar asuba ta saci wayarsa ƙarama ta ɓoye. Koda ya dawo sai ya kwanta a ɗayan ɗakin dan hakan shine samun lafiyarsa. Ba ƙaramin daɗi hakan yayma Huznah ba. Da wannan damar ta saka number Yaseerah cike da fatan samunta, dan bata son kiran ƙannenta wani yaji.
Ɗagawa Yaseerah dake cikin ɓacin ran faɗan da suka sha da Abdull akan cikin data samu tayi. Jin Huznah yasata jin mamaki, tace, “Lallai Huznah, shike nan daga yin aure kin manta kowa”.
“Humm Yaseerah bazaki gane ba, yanzu ba lokacin kace nace bane tura min numban Mama dan ALLAH”.
Da mamaki Yaseerah tace, “Kai kece baki da number ɗin Mama kuma?”.
Cikin rawar murya Huznah ta ce, “Ba rasawa nayi ba Yaseerah ƙwace wayata yayi, ni kuma ina son yin waya da wani a cikinsu ko ita ko Ummi, amma na gwada layin Ummi yafi sau a ƙirga bana samu, shiyyasa nake son kiran Mama dan koma minene nasan zata sani”.
Sosai al'amarin ya daki zuciyar Yaseerah, amma Huznah ta riga tace mata bata son magana mai tsaho, dan haka ta ce, “Okay bara na tura miki. Amma idan kin gama da Maman dan ALLAH kimin ko flashing ne”.
“Ba damuwa”.
Kawai Huznah ta faɗa tana yanke wayar. Ko minti ɗaya kuwa ba'a rufa ba sai ga saƙon Yaseerah, jikin Huznah na rawa ta kwashe number a wani littafi ta goge daga massage sannan tai past ɗin wanda tai copy daga massage tai dailing tana shigewa toilet bayan ta murzama ƙofar ɗakin key. Toilet ɗin ma kullesa tayi. Dai-dai nan Maman Yaseerah ta ɗaga kamar a barci take. Kafin ma ta tambayi waye Huznah ta ce, “Mama nice Huznah”.
Da sauri Maman Yaseerah ta tashi zaune, ta ce, “Huznah ina kika shige inata neman layinki?”.
Kuka Huznah ta sanya mata, kafin ta fara bata labarin komai dake faruwa, tun daga ƙwace wayarta da yayi har zuwa satan tashi da take yi tana kiran Hajiya Basariyya bata samu da maganar ciki daya bayyana jiya. Ba ƙaramar sumar zaune Maman Yaseerah tayi ba, ta ce, “Ciki kuma Huznah yaya akai haka? Sake yarda kikai kika bashi kanki?”.
“Mama ya zanyi? Idan ma ban yarda ba ta ƙarfi yake bina wlhy. Wlhy idan naji ko motsinsa ƴan hanjin cikina har kaɗawa suke. Sageer mugune sosai Maama, bar ganinsa shiru-shiru baida kirki da imani”.
Ajiyar zuciya Maman Yaseerah ta sauke. Cike da lallashi ta ce, “It's okay! Kukan ya isa haka. Ai idan yasan wata bai san wata ba dan ubansa. Mamanki na katsina ne gidan kawunta.....”
Cikin katseta Huznah ta ce, “Na shiga uku Kawu Manu?”.
“Shifa! Yayanta ne ya kaita da tsiya-tsiya, amma ki kwantar da hankalinki jiya ta samu wayar yarinyar maƙwafta ta kirani, ta kuma tabbatar min bazata wuce nan da sati ba zata dawo. Kema ki kwantar da hankalinki irin ƴan iskan yaran nan su Sageer ta siyasa ake musu. Ciki dai bazaki haifesa ba dan uban shi, ki cigaba da kwantar masa da kai har ALLAH ya kaimu ya barki zuwa salla zamu san yanda zamuyi da shi, kema kuma kinzo kenan”.
Wata wawuyar ajiyar zuciya Huznah ta sauke, ranta fes tace Nagode sosai Mama, ALLAH ya saka miki da alkairi. In sha ALLAHU zan dinga kiranki idan na samu sarari, amma karda ki kira dan zai iya ganewa”.
“Babu damuwa in sha ALLAHU”.
Daga haka sukai sallama Huznah ta sauke wayar tana murmushi. Gaba ɗaya sai taji kamar an zare mata dukkan damuwar ta ne. Bayin ta buɗe ta fito tana goge kiran da tayi, taje ta cire key ɗin data sakama ƙofar sannan ta koma saman gado ta kwanta.......
___________★
Gab da ƙarasawa lokacin sahur AA ya farka cikin matsanancin yanayi, wannan abune daya saba fuskanta a rayuwarsa tun a farkon girma, amma baya masa tsamari mai wahala kamar na tsakanin nan, musamman kwanaki biyun nan da kusancinsa da Maanal ya zama dab, suna kwana gado ɗaya, su yini tare cikin farin ciki, ta ɗan saki jiki da shi kuma duk da ba kamar asalin yanda suke a baya ba. Yasan duk yanda Maanal zata kai ga tsanarsa, da jin zafinsa dole ne shaƙuwarsu ta baya ta dinga yin tasiri a gareta da karya lagonta koda lokaci-lokaci ne. Balle kuma yarinya ce ƙarama ita har yanzu, zuciyarta bata gama ƙwarin iya riƙe abu ba irin da tsauri ɗin nan, ya taɓa ji a wani hasashen masana a shekarun ƙuruciya ɗan adam yana da rangwamen tasirantar da damuwa ko ɓacin rai wajen girmama shi a zuciya, ko ɓatama mutum rai kayi ko cutar da shi a shekarun ƙuruciya irin daga 15years na fara fahimtar kai da kai zuwa irin 26 to 7 haka wasu ma har 30 zakaga yana da sauƙin zafafa al'amarin, wani ma cikin ƙanƙanin lokaci yake hucewa abin ya wuce a ransa, wani kuma daka dawo ƙyautata masa ko lallashinsa shike nan ya bar abin koda zai dinga tunawa lokaci-lokaci ransa ya ɓaci. Ko ga rayuwar aure mafi yawan mata a shekarun farkon aure basu cika girmama wasu ƙuntatawa na miji ba, watama mijin ne zai mata laifi idan taga yayi fushi zata bashi haƙuri harma ta durƙusa. Amma da an shiga shekarun hankali 30+ in sha ALLAHU ita zata tafka masa tsiyar ta juya masa ƙeya a gado ta barshi da kallon bayanta ko'a kwalar rigarta. Sannan a lokacin ne zakaji a hira tana ai lamarin rijalu sai su, ko kuma namiji ba ɗan goyo bane ba. Kumafa kafin lokaci idan taji wasu na faɗa haushi ma take ji, watama kaji tana bada amsa da nata dai ɗan goyo ne, koda kuwa yana ƙuntata mata a lokacin. To ba komai ke jawo hakan ba sai rashin girmama abu irin na shekarun ƙuruciya. Ya tabba wannan shike ɗawainiya da Maanal. Dan da'ace tunda suka rabu basu haɗuba sai da ta shiga 30+ na shekaru wlhy da yaga rashin mutunci, kuma ko sama da ƙasa zata haɗe bazata yarda su sake rayuwa ba. Amma yanzu 21+ take da, shiyyasa yake iya raunana zuciyarta da canja mata tunani harta shagalta da shi duk da wancan yanayin bai gogu a zuciyarta ba.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣3️⃣
______________
........Tunaninsa ya katse saboda wani irin murɗewa da cikinsa ya ƙarayi. Sosai ya dunƙule waje guda yana mai ambaton sunan ALLAH. Wannan yanayin ne ke sashi riƙe kansa da tsiya-tsiya daga taɓata tako wace irin siga, dan ya tabbatar a ƙarshe wahala zai sha, ko kuma ya aikata abinda shi da kansa zai dawo yana ƙalubalantar kansa. Duk fitinarsa bazai iya ƙin biyayya ga iyayensa ba, wlhy koda ace zai cutu ya gwammace hakan. Ya tabbatar Abah bazai hanashi matarsa dan cutarwa ba, idan har zai iya juriya da haƙuri na shekaru, na ƴan kwanki ne zai nuna gazawa....
Dai-dai nan tunaninsa ya sake tsayawa, sakamakon kaɗawar alarm. A hankali Maanal ta fara motsawa, sai kuma ta shiga buɗe ido bakinta da addu'ar tashi a barci. Yau ma a kai da ƙafan suka kwanta, ta kuma jera filos a tsakkiya, dan bayan ta farka a barcin daya figeta saboda matsananciyar kunyar da ya sakata a ciki sai taga AA a gefenta har yayi barci, da alama kuma yayi wankan, tashi tai itama saɗaf-saɗaf zuwa bayi tayi wankan ta canja kaya, ta sake dawowa a hankali ta kwanta bayan ta jera filos ɗin, barci kuwa yay awon gaba da ita dan har yanzu jinsa take sosai. Tana ƙoƙarin tashi zaune idonta ya sauka akan AA daya juya mata baya, amma yanda ya ɗan dunƙule jikinsa kamar ranar sai gabanta ya faɗi, a ranta rayawa take kar dai baida lafiya?. Babu mai bata amsa, bata son kuma yin magana, sai kawai tai ƙoƙarin sauka, bayi ta nufa tana ɗan waiwayensa, harta shiga bai motsa ba.
Duk abinda take AA na jinta amma ya daure har sai da ta shiga bayi sannan ya tashi zaune cike da jarumta da juriya. Abin tausayi idanunsa sun wani kaɗe, jijiyiyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Yana zaune a haka cikin ambaton UBANGIJI Maanal ta fito, ganinsa zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya, shima ɗan ɗagowa yay ya kalleta, sai kuma ya janye idanun dan wani irin ji yay kamar an dakar masa kai da hama sakamakon saukar idanunsa akanta. Wani irin ƙyau kayan barcin data saka sukai mata, duk da bawani sun matseta bane kasancewarsu masu santsi sun kwanta mata a jiki luf. Tana zama ya miƙe, batare daya sake kallonta ba ya wuce bayi dan baya so taga halin da yake a ciki. Yafi mintuna goma a bayin sannan ya fito, Maanal bata yarda ta kallesa ba sam, duk da bata kawo a ranta ma wanka zai yi ba. Shima yaji daɗin ƙin kallon nasa da batai ba, jallabiya ya ɗauka ya koma ta bayanta ya saka ya zame bathrobe ɗin. Sai da ya ɗauka maganinsa ya sha yana addu'a a ransa ALLAH ya taimakesa ya samu natsuwa sannan ya juya a karo na farko ya mata magana...
Kallonsa ta ɗanyi itama, dan yanda taji muryarsa kamar mai mura sai da zuciyarta ta tsarga.
“Baka da lafiya ne?”.
“Mi kika gani?”.
Kanta ta girgiza masa kawai, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Ba komai”.
Shima numfashin ya ɗan furzar, cikin son kauda yanayin yace tazo suyi sahur barci yake ji, gashi fitar wuri zasu yau. Komai bata sake cemasa ba tazo ta zauna. Daga ita har shi basu wani ci abin kirki ba, dan kowa da abinda ya damesa. Shine ya fara tashi yaje bayi ya sake yin brush yayo alwala. A mamakinta maimakon kwanciyar da yace zai yi sai taga yayi salla raka'a biyu ya ɗauka Alkur'aninta ya fara karatu, gashi sai wani sauke ajiyar zuciya yake a jajjare. Itama dai gyara wajen tayi taje tai brush ɗin tayo alwalan....
Kamar yanda ya faɗa da wuri suka fita yau, sai dai fa sam baya a cikin walwala. Companyn jiya suka koma, shi baima shiga ba, a mota suka barshi yace mata zaije wani waje ne. Kai kawai ta jinjina masa da masa addu'a dan ta fahimci yau ƴan miskilan ne a ka. Alhamdullah yau ma sun samu ilimi sosai dan komai an musu ne a bayyane practical. A rai Maanal na jinjina mutanen nan da halayyarsu, sam babu mugunta a tare dasu. Baƙar fata ne zai iya abu ya koya maka cikin sauƙi harda wasu sirrika nashi tab ɗin. Duk da ta fahimci AA nada babbar alaƙa da companyn ne amma ta jinjinama halaccinsu. Dan ta fahimci hakkane a lokacin da idannunta ya sauka a hotunan dake manne a wani office da suka shiga na mutane goma harda hoton AA. Al'amarin nata mata kai-kawo a rai amma ta rasa yanda zata tambaya. Yau sunfi jiya daɗewa anan, suna fitowa kuma masauki aka maida su. Ita kaɗai Mr Li ya ɗakko, koda ta tambayesa AA sai ya sanar mata suna meeting ne. Bata tambayesa meeting ɗin mi ba kawai tai shiru. Har ɗakinsu yay mata rakkiya da kayayyakin da bata san na miye ba. Tana shiga ta sauke