Showing 129001 words to 132000 words out of 218311 words

Chapter 44 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

ta murmusa tana tashi. Sosai Maanal ke jin idanu sun mata yawa, sam bata ƙaunar kallo, takurata yake yi. Tana ɗan bin mutane da kallo ƙasa-ƙasa itama ta hango wani kallon tsana da Mamy ke mata ita da danginta. Sai kawai yanayin nasu ya bata ƙarfin gwiwa taji wata dakewa ta musamman ta risketa. Aiko sai ta ƙara dakewa ta ƙawata fiskarta da murmushin da ya tsaya musu kuwa a ƙahon zuciya. An fara buɗe taro da addu'a, sai ɗan abinda ba'a rasa ba aka sanar da isowar tawagar ƴan discussion house. Hauwa'u Jidda, Ummul-Adnan. Ummu Fharuk. Oum Zarah. Maman afrah. Hafsy gayu (Mmn Ajmaal) (ر قية موس). Daddy's girl (Aysha). Hafsy Gayu. Leila. Mrs lawal. Mrs Bash. Fiddausi sani. Aunty Saliha. Aunty maryam. Maman faruk. Saraunia. Sharifa Ahmed. Maman meema .Oum shuraim. Mrs Affan. Maman Fa'izz. Meeno. Oummu nawal. Zubaida chiroma. Oum zarah & muhd. Fattu. Maman Hameeda, Aminatu, INDOBATIK NG. (Kai kuna da yawa, amma dole a dinner na antayo sauran😄👍🤏.)
Ohhh ohhh zokaga mutanen nawa yanda suke shigowa cikin nutsuwa da ƙasaita, ƙyau iya ƙyau wanka iya wanka. Su ɗin na musamman ne, dan haka wajen zamansu ma ya kasance na musamman dan dama an tanada musu shi. Kamar jira suna gama zama ango ma ya iso da tawagar abokansa. Tuni kallo ya sake komawa sama wai shaho ya ɗau giya. Uhhhm uhhmm inji mai ciwon haƙori, kunga angonku kuwa, nace kunga ango AA Darma kuwa? Ya subahannallah, tabbas ranar aure daban take ga kowanne mata da miji. A yanda tsarin yake amarya ce zata je da kanta ta taro ango. Dan haka AA da tawagarsa suka tsaya a waje, Shahidah ce ta kama hannun Maanal suka iso har wajen ƙofa, sai da aka tsayar da Maanal MC ta gyara mata zaman rigarta sannan akace da ango bismillah ya shigo.
Fin minti ɗaya bashi da niyyar motsawa, sai da RK ya tsungunesa. Hararrasa yayi kaɗan, kafin ya motsa a nutse ya shigo cikin hall ɗin. Wani irin shaaaaaah zuciyarsa tayi sakamakon saukar mayan oily fararen idanunsa masu kamar an watsa madara akan Maanal dake tsaye kanta a ƙasa. Tuni wani kirari da mc ta jeroma AA ɗin ya saka Maanal ɗaga idanunta slowly ta sauke a kansa itama, shima dai kallonta yake, zuciyarsa na ambaton sunan ALLAH maƙagi gagara misali daya mallaka masa wannan ƙyaƙyƙyawar halitta matsayin iyalinsa, lambunsa na hutawa. Mc ta kama hannun Maanal suka tafi a hankali har inda AA ke tsaye, wani irin lumshe idanu Maanal tayi, ta sake buɗewa a lokaci guda tare da motsa lips ɗinta kaɗan ta ce, “Barka da isowa mijin Maanal”.
Shima cike da tasa ƙasaitar ya motsa nashi lips ɗin ya furta, “ALLAH yay miki albarka matar Ajwaad”.
“Auuuwwwww!!”.
Mc ta faɗa cike da salon iskanci daya saka hall ɗin ɗaukar hayaniyar ƙananun dariya. Mc ɗin kaɗai taji abinda suka faɗa, amma yanda tai ɗin sai mutane sukai tunanin wasu manyan magana ne daban. Cike da nutsuwa Maanal ta buɗe masa hannayenta kaɗan alamar yazo gareta ta rungume shi tana wani irin murmushi mai sanyi, AA da gaba ɗaya yaji yana narkewa ya shiga takowa a hankali garetan, yana gab da isowa ta wani juya masa baya da sauri tana sake ƙawata murmushinta, sai kuma tasa duka hannayenta ta rufe fuskarta. Miza'ai in ba dariya ba. AA ko ya wani kalar basarwa yana cije lips, batare da yace komai ba ya ƙaraso kusa da ita suka jera. Batare da ya riƙe ko hannunta ba suka shiga takawa a hankali har mazauninsu, sai lokacin ya taimaka mata ta zauna tare da gyara mata rigarta sannan shima ya zauna. Hannunta ya kamo a hankali cikin nasa ya rumtse. A tare suka saki ɓoyayyar ajiyar zuciya. Ƙasa-ƙasa ya ce, “I miss you my half. Irin wannan ƙyau haka ai sai kisa na hana bikin”.
Maimakon ta bashi amsa sai tai murmushi kawai tana risinar da idannunta ƙasa. Dan wani annakirin kallo yake mata mai matuƙar ratsa ɓargon jiki. An cigaba da gudanar da abinda ya tara mutane. Matuƙar ƙawatarwa taron yayi, komai ya ƙayatar yanda ya kamata. Anci ansha amarya tasha kyaututtuka wajen iyaye su Umma matar babba Sardauna, su Mah-mah, su Gwaggo Khadijah, su Mom mahaifiyar Abah kenan. Mamy ma ta daure ta bayar😜 bisa shawarar babbar yayarsu. Sannan aka dawo kan ƴaƴa su Hajiya Majdiya, kai harda ƴammata da ƴaƴaye abin masha ALLAH. Daga ƙarshe Oum uwa maba da mama data saka nata sai da zukata suka girgiza. Gab da magrib taro ya tashi lafiya.
Yanzu ma dai Babban Yaya da kansa ya maida Maanal, wannan tsari ya taimaki Maanal inji AA a zuciya, dan yanda yake jinsa ALLAH daga hall ɗin bikin zai iya wucewa da ita ya sauke matsalarsa, bai taɓa jin bazai iya jurewa ba irin yau, yanda Maanal tayi masifar ƙyau, ga wani irin ƙamshi mai marmasa gaɓɓai da ɓargon jiki. Ko a wannan zaman harga ALLAH girmama iyayensa dake cike da wajen da yayye ya sashi tsayawa a riƙe hannun kawai, shima a ɓoye yayi. Ya rabba! In ko haka wannan gyaran jiki yake to yata buɗe bakin aljihu kenan duk bayan sati biyu anama Maanal ɗinsa. Shi yasan Maanal kyakkyawa ce, sannan akwai tsafta da son gayu, amma a yau ta sake komawa wata ta musamman a cikin idanunsa. Ƙamshin da take kawai ji yake kamar zai suma. ALLAH ya dinga roƙo ya bashi ikon juriya yay kawaici. Dan yayi alƙawarin duk yanda suka tsara bikinsu shi mai biyayya ne..........✍️


A gurguje, zamuyi shagalin bikin kawai idan an kammala sai mu koma sauran ɓangarorin yanda abin zaifi tsari🏃🏃








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣4️⃣




______________






.........Washe gari asabar ɗunbin al'umma suka shaida ɗaurin auren Fawzan Aliyu Abubakar Darma. Da amaryarsa Najma akan sadaki 1mil cass da AA ya biya. A lallai su Baba Sardauna sun girgiza zukata da yawa. Abune a bazata, bazata mai ban mamaki da wani bai taɓa hasasowa zai yiwu a family ɗin ba. Musamman ta yanda babu wata alaƙa makamanciyar haka a tsakanin Fawzan ɗin da Najma.
Su Mamy na bedroom suna tattaunawa ana ƙara tausar Maman Saheeba da tun jiya take ƙananun magana da ita kanta Mamy ɗin kawai Saheeban ta faɗo musu kamar wadda aka jeho. A tare suka juyo suna kallonta. Babbar yayar su Mamy ta ce, “Haba Saheeba miyyasa baƙya sanin kin girma ne. Wane gudu kenan keda ke da ƙaramin ciki”.
Cikin hakki Saheeba ta ce, “Gwaggo bazaki gane ba, kuna nan ciki baku san mike faruwa ba. Aure aka ɗaurama Yaya Fawzan”.
A tare suka miƙe, Mamy ta ce, “Fawzan kuma? Wanne kenan? Ba dai nawa ba?”.
“Tabbas shi kuwa Mamy, kuma da Najma”.
“Wacece Najma?”.
Mamy ta sake tambaya dan duk ta ma rikice. Kai tsaye Saheeba tace, “Ƴar Aunty Majdiya dake gidan nan mana”.
Yuuu-yuuu Mamy ta dinga gani a cikin idannunta, lips ɗinta na rawa tama kasa fusta abinda take son fustawa. Babu zato sai gata a ƙasa wanwar ta baje.....


Tofa Mamy ta baje a ƙar ku kawo ɗauki😮‍💨🏃🏃😌


_______★


A ɓangaren su Oum kuwa wani irin farin ciki ne mara misali zagaye da su. Dai dai Oum na share hawayen farin ciki, lokacin su Fawzan suka shigo shima idanunsa sun kaɗa sosai dan ana ambata ɗaurin auren da sunansa bai san hawaye sun zubo masa ba. Abu ne na bazata, bazata irin wadda ba'a taɓa masa ba a rayuwarsa. Dan koda AA yace zaima Abah magana a haɗa da bikinsa a waccan ranar bai wani ɗauki abin serious ba. Yau kuma Babban Yaya cayay masa wani ɗaurin aure zasuje na ƴar abokin Abah ya bashi kayan jikinsa yace ya saka, duk da yayi mamakin ganin ahalinsu da abokansa da yawa a wajen bai samu damar tambaya ba. Yana zuwa ya rungume Oum ya sakar mata kuka, ALLAH yaso ma daga ita sai shi da AA da RK sai Babban Yaya ne a ɗakin. Itama Oum hawayen take, a haka ta daure ta goge nata tas sannan ta ɗago Fawzan ɗin ta zaunar, shima goge masa nasa hawayen tayi tana murmushi. Albarka ta dinga saka musu, tare da addu'oi masu nauyi akan wannan aure. A haka Abah ya shigo ya samesu. Cike da tsokana ya ce, “Ja'iri, har yanzu kukan farin cikin bai ƙare ba kazo ka tasa uwaka kana cigaba da yi”.
Dariya Oum tayi, su Babban Yaya na murmushi. Zama Abah shima yay, ya sanya musu albarka sosai dan shi kansa shi kaɗai yasan irin farin cikin da yake ciki a yau. A nutse yayma Oum bayanin ai Babban Yaya, RK, da AA ne suka shirya komai suka kuma roƙi alfarmar ɓoye zancen har sai an ɗaura. Tariya kuma sai nan da sati huɗu Najma ta kammala jarabawarta. Albarka itama Oum ta dinga saka musu.
A falo ma dai da tsakar gida duk wani ahalin Darma yayi farin ciki da wannan aure. Hajiya Majdiya kanta sai da tai hawaye. Sai da su Mah-mah sukaita lallashinta dan harga ALLAH abin yazo mata a bazata kamar yanda ya zoma kowa ma....


★Babu wanda zai ce ga halin da Nibras take ciki game da wannan aure, an daiga uwarta ta iso da wasu danginta sun shige sashen. Fawzan kam baima tuna da wata ita Nibras ba balle ya leƙata yasan yaya take...
Sai dai abinda kowa bai sani ba koda Nibras ɗin taji wai an ɗaura auren Fawzan shiru kawai tai na ɗan lokaci, sai kuma ta ɗan taɓe baki batace komai ba dan hankalinta sam a nan ɗin yake ba duk da ƙirjinta sai da ta buga. Amma sai huɗubar da sheɗaniyar zuciyarta ke kissima mata tafi rinjaya a can. Sai da mamanta tazo ne su ransu a ɓace sannan ta sakar mata kuka da faɗin ita bazata zauna da Fawzan ba tunda ya ƙara aure miye-miye....


________★


Su Maanal dake gidan Shahidah ma labari ya iske su, duk da Maanal tasan da shirin itama sosai taji farin ciki, aiko nan suka zagaye Najma. Kowa da abinda yake faɗa na farin ciki har sai da ta sanya musu kuka dan abin yazo mata a bazatar ne itama. Sai da Didi Shahidah ta ɗauketa a cikinsu ta maidata ɗakinta. Babu ɓata lokaci ta sanyata tai wanka, acewarta bashi yiwuwa amarya ta zauna a haka dole taci gayu duk da ba yanzu ne biki ba. Aiko sai ga kiran Oum ma ya shigowa Shahidah. Tace za'azo ɗaukar Najma ɗin yanzu. Su kuma shirya dan itama Maanal da wuri za'azo ɗaukarsu saboda ana son zuwa dinnar da wuri a tashi da wuri.
Ana wucewa da Najma kuwa itama Maanal aka hau shiryata, dan zuwa lokacin la'asar tayi. Sai kawai ƴar shagwaɓar ta kama musu kuka. Dan wlhy jitake tamkar yanzu ne za'a fara kaita gidan su AA ɗin. Haka dai aka gama shiryata cikin atamfa datai matuƙar ƙyau ta kuma samu ɗinki na nutsuwa. Uncle Sadeeq, Daddy da ya zo ɗaurin auren Najma ya wuto nan, Uncle Ahmad mijin Amaal, sai su Nene sukai mata faɗa da nasiha mai matuƙar ratsa jiki da ɓargo. Daga ƙarshe suka sanya mata albarka da fatan alkairi a rayuwar aurenta. Ƙarfe biyar saura haɗaɗɗun motocin ɗaukar amarya daga manyan yaran Abuja suka iso ƙofar gidan Didi Shahidah. Ya subahannallah tsarin ya matuƙar haɗuwa, motar amarya a tsakkiya tasha flowers. Su Nusaiba dai ai tun jiya sun gama mutuwa a tsaye. Daga uhhm sai uhhm kawai kake ji a tsakaninsu. Haka suma rukunin ƙannen Huznah, abin duniya ya ishesu sai ƙiyastawa suke a ransu da yanzu fa Huznah ake ma wannan hidimar.
A nutse Nene ta saka Maanal dake uban kuka a motar RK dan shine zai ɗauki amarya shi da Fawzan. Surukan Nene sai zabga guɗa suke, masu hotuna nayi masu videos nayi. Har motocin suka iso gidan Darma Maanal dake kwance jikin Nene na hawaye, dan yanzu kam tasan ba wasan yaran da akai a watannin baya bane zaman aure ɗan gaske aka kawowa yi a karo na biyu wannan gida. Har ciki motar amarya ta shiga, su Ummah tsoffi suka fito da kansu suka tarbi amarya. An fara kaita sashen Oum, Oum ta rungume abarta tana share hawayen farin ciki, Babynta ta dawo kusa da ita a karo na biyu matsayin matar ɗanta. ALLAH zai cika mata burinta. Bayan addu'oi aka fito da ita aka nufi sashen Mamy. Anan kam dai cike da bariki su Hajiya Turai suka tarbesu, sai dai Babu Mamy, dan tana can kwance a gado an saka mata ƙarin ruwa. Dan faɗuwar datai ɗazun sume musu tayi, shine Hajiya Turai ta kira wata ƙawarta Nurse tazo kamar ƴan zuwa biki, itace ta duba Mamyn ta tabbatar musu jinjinta yayi masifar hawa, dan haka bayan ta farfaɗo da ita tai mata allura mai ƙarfi aka saka mata drip kuma. Shine suke ɓoyewa dan basu son ko Abah yasan halin da ake ciki. Babu wanda ya tambayi rashin ganinta a wajen tunda ansan yanda takema Oum kara. Su sukai addu'oi duk da basu kai ciki ba. Daga nan aka dawo da Maanal sashenta. Bayan an sakata tayi alwala aka shiga da ita ciki bakinta da addu'a. Anan bedroom ɗin ƙasa suka ajiyeta bisa umarnin Nene...
Gaba ɗaya yaran Hajiya Yaya dana Hajiya Basariyya sun gama sumewa a tsaye. Karo na farko na rayuwarsu suka fahimci ashe ubansu yaron masu arziƙi ne kawai, dan wlhy a dukiya irin ta wannan gidan da ginin kawai suka gani mahaifinsu ba komai bane. Dan wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa. Saka motar 90m ba komai bace a lefe da sukai. Dole Huznah da Hajiya Basariyya ke haukacewa kambuuu...
Basu ƙara raina kansu ba sai da aka fara shigowa da wasu irin haɗaɗɗun manyan bowl glass na abinci, yo in banda kasada irin ta mai kuɗi a ranar biki zaka fito da kayan gilashi matsayin kwanon bada abinci ga ƴan biki. Lemuka kam kala-kala ba'a maganar su coc.. fanta... Da ire-iren su ƴan biyu sha biyar, kai jama'a, ashe jiya da suke jinjina kwalliyar mutanen ƙaramin wasa ne, yau da take ranar dinnar zasu baza ido susha kallo ɗan gaske. Mamaki ya ishesu ta yanda su Ammie suka san waɗan nan mutane haka? Wai harma ace shi AA yama Maanal fyaɗe. Duk da ƴaƴan Ammie kaf ƙyawawa ne matan manya, amma yanda ƙasar nan ta koma ta bani gishiri in baka manda, auren ƙwarya tabi ƙwarya mai kuɗi ya aure ƴar talaka tsananin rabo ne wlhy, indai iskanci ne a sheƙe aya zasu yarda da ƴaƴan malam Shehu, amma a fagen raya sunnar MANZON ALLAH ba wannan maganar, in kikai wasa ma sai dai ki tsinta shagalin bikinsa na yawo a social media. Koki zama cikin ƴan aikin shirya bikin.
Sai da kowa yaci ya ƙoshi dan kayan alatun da aka kawo musu duk ƙoshinka ka gani sai ka ci. Maanal ce kaɗai bata iya taci komai ba. Dan ita yau babban tashin hankalinta ace ita da AA zasu kwana. Addu'a take ALLAH yasa anan su Nene zasu kwana...


Bayan sallar Magriba mai kwalliya ta iso tare da Hajiya Shuwa, atake ta saka Manaal tashi ta shiga sabon wanka da wasu irin haɗin turarurruka masu ƙamshin tashin hankali, data fito kuma aka saka wani a wuta aka lulluɓeta da ƙaton bargo ta ƙasa kuma ta zauna a kujerar tsuguno. Tafi mintina talatin aciki dan Hajiya Shuwa tana ɗagawa tana ƙara turaren ne a cikin rushin. Sallar isha'i da ake kira ta bata umarni tashi tayi, Maanal tai sallarta a tsanake sannan ta zauna mai kwalliya ta fara nata aikinta.
Suma dai su Shahidah suna can suna nasu shirin dan Oum da kanta ta samesu, ta kuma tabbatar musu anan zasu kwana baza'a bar Maanal ita kaɗai ba karma suce zasuje gidan Shahidah jiyama tayi shiru ne kawai saboda Maanal zata kwana can
Murmushi Nene tayi, tare da sake jinjina karamcin Oum. Hummm jama'a, nace kunga yanda ake zane muku fuskar amaryarku. Abin ba'a magana dan tayi mahaukacin ƙyau na'a tsaya aita kallo. Su kansu su Amaal sai hotuna suke zuba mata. Sosai tai ƙyau komai ya fita da fitarsa, sai ƙamshi take zabgawa kamar a kamfanin turare. Kora su Amaal waje Hajiya Shuwa ta sake yi, suka fara shirya Maanal ita da mai kwalliya da wadda tai ɗinkin Maaanal ɗin. Wato jama'a, Material ne aka samu akama wani shegen ɗinkin doguwar riga na tada kan maƙiyi, aka bisa da stones masu shegen walƙiya da ƙyalli ta yanda in aka kashe fitila suke wani bada kala. Idan baka da lura ma bazaka taɓa cewa Material bane saboda yanda aka tsara mata ɗinki. Gashi ya wani masifar bin jikin Maanal ɗin tamkar an zanata a takarda. Komai ya fita da tashi fitar. Cikakkiyar ƴar gatan amarya kenan. Hajiya Shuwa ta sake binta da ƙamshi bayan an zuba mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login