Showing 33001 words to 36000 words out of 218311 words
Chapter 12 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
ne azababbe na bugawa a kalanda, ga tsauri dan komai na gidansa da doka akeyinsa. Kuka sosai taci, daga ƙarshe ta yanke shawarar yin asubanci ta gudu. ALLAH gara ta koma gidan mijinta duk ma bala'in da za'ai ayi bazata fito ba koda Daddy zai daketa kuwa. Kayanta ta shiga haɗawa, tsaf ta kammala ta ajiye komai a ƙofar ɗakin, sauran kuma ta ajiyesu akan daga baya zata turo su Madeena yaranta su ɗaukar mata. Ko barcin kirki kuwa batayi ba, huɗu na bugawa zabar ta miƙe dama ba wani barcin kirki tai ba, a gurguje ta shiga bayi ta kimtsa ta fito, ta saɓi jakarta tana murmushin nasara, sai dai tana murɗa handle ɗin ƙofar taji gam, hakan na nufin an kulleta ta baya kenan. Ai jitai gaba ɗaya ta wani irin gigicewa, bama tasan ta zube a wajen ba ta fashe da kukan takaici, dan ta tabbatar yayanta ne ya rufeta tun fitar jiyan da yayi.......
🤣🥱Ba abun faɗa
_________★
Sun fito a jere Maanal na faɗin, “Kai dai ka canja hali ALLAH”. Cikin ƙunƙuni take maganar, amma hakan bai hana AA ɗin jinta ba saboda ƙarfin ji da ALLAH ya bashi. Murmushi yay kawai, sai kuma ƙasa-ƙasa shima yace, “Inba tsoro ba a fito fili a faɗa mana”. Sarai itama Maanal ɗin ta jishi, sai dai bata tanka ba saboda isowarsu wajen motarsa. A dai-dai nan kuma Saheeba ta fito daga sashen Mamy, taje wajenta su Haule suka sanar mata tana sashen Oum. Sai ga Nibras itama ta fito daga sashenta, taci kwalliya abinta sai baza ƙamshi take kamar wadda zata fita. Itama dai sashen Oum zataje, kuma wannan kwalliya duk ta AA ce. A tare duk suka tsaya cak suna binsu da kallo, har Maanal ta shiga mota AA daya buɗe mata ya maida ya rufe sannan ya zaga mazauninsa, sai dai shima kafin ya buɗe da kansa Maanal ta buɗe masa ta ciki kamar yanda suke yi a da. Kallonta yay fuskarsa da murmushi mai sanyi, itama ta masa murmushin tana kauda kanta dan su duka zukatansu suna tariyo musu baya ne. A hankali ya baya mai gadi ya buɗe masa gate suka fice.
Daga zuciyar Nibras har ta Saheeba tamkar zata kama da wuta ne. Cikin takaici da wani irin zazzafan kishi Nibras ta ce, “Wannan mayyar yarinyar sai nayi maganinta”.
“Haɗa dani nan Nibras dan na tsaneta”. Saheeba ta faɗa itama a zafafe. Da sauri Nibras ta kalleta dan ita bata san nata zancen ya fito fili bane ba. Kai Saheeba ta jinjina mata batare da sanin manufar Nibras ɗin na tsanar Maanal ɗin ba. Ita kuma Nibras tasan dalilin Saheeban bazai wuce taya ƙanwarta kishi ba. Amma saboda takaicin da take ciki sai ta cigaba da faɗin, “To wai ina zasuje a wannan daren? Nine fa?”.
Wata ƴar dariyar takaici Saheeba tayi, “Kin san tunda tarewa ta gagareta zatabi duk wata hanya ne yanzu na son ganin taja ra'ayinsa, balle an saba da bin maza a waje”.
“Tabbas kumafa hakane. Shegiya mai zuciyar karnuka, mutum yace baya sonki amma ina, inba shashashar amarya ba mara muhimmanci wa ake kawowa a ajiye sashen surukai gana miji”. Nibras ta faɗa zuciyarta na mata raɗaɗi.
Dariya sosai Saheeba keyi, ranta fes ta ce, “Ai Abah ne maganin ƴar iska, uwarta na murna bokanta ya iya aiki an mannota gidan da tsiya-tsiya shiko ya harba musu tsiya, Kinga ɗan maganin da aka ɗan cuccusa dan matse can duk ya sane. Ai wlhy sai mun dage munci ubanta a gidan nan ta yanda ko ruwa bazata iya sha ba sai a ɓoye, da ƙafafunta zata gudu ne”.
Hannu Nibras ta bama Saheeba suka tafa, dan a ganinta ai gara su haɗa hannu da Saheebar su kori Maanal ɗin ita kuma sai tai yaƙin hana shigowar ƙanwar Saheebar ta bayan fage. Aiko a take ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari. Sai da suka gama shirya mugunnyarsu sannan suka nufi sashen Oum ɗin. Acewarsu gara suje su zauna suga dawowarsu...
A hankali AA ke murza steering tamkar baya so, yayinda Maanal tai shiru lafe a cikin kujera. Daga gani kasan duniyar tunani duk suka faɗa. Cikin son kauda yanayin AA yay ɗan gyaran murya. Idannunta dake lumshe ta buɗe ta kallesa, shima ɗan kallon nata yay fisha sai kuma ya maida ga hanya. So yake su dawo kamar da, amma yasan yaƙine babba a gareshi, dan haka maimakon zuwa mata kai tsaye zaibi wasu hanyoyin yin hakan. Muryarsa a tausashe ya furta, “Yaushe kika fara karatun novels? Bayan nasan haushi kike ji idan kikaga inayi ma”.
Ɗan jimm Maanal tayi kamar bata jisa ba, har sai da ya ɗan kalleta. Ƙin kallonsa tayi ita, a taƙaice ta ce, “Kawai na tsinta kaina ne a karatun batare da wani dalili ba”.
Murmushi ne yaso suɓuce masa, amma sai baiyi ba a bayyane ya tsaya masa iyakar cikin ƙirji. Zamansa ya ɗan muskuta da sake damƙe steering da ƙyau ya tsaya a danja data tsaida su, sai kuma ya koma ya jingina bayansa da kujerar ya juya yana kallonta. “Zuwa yanzu books nawa kika karanta?”.
Kaɗan ta ɗan kallesa, cikin yin warrr da idannunta ta ce, “Suna da ɗan yawa fa. Damma Ammie na hanani ne”.
“Ammie bata san karatun novels da daɗi bane shiyyasa. Kinga ni akwai wani book da nake nema saboda labarinsa da aka ɗan fara bani amma har yanzu ban samu ba, koda yake busy na ne ya hanani zuwa manyan books store na duba”.
Yanzu kam muryar Maanal a sake ta kuma juyo tana kallonsa da ƙyau ta ce, “wanne ne?”.
Sai da ya tada motar suka cigaba da tafiya saboda danja ta sake su sannan ya bata amsa. Murmushi tayi mai faɗi sosai har haƙwaranta na bayyana ta ce, “Hum'um kaga nikam na jima da karanta shi, dan tun ina shekarar ƙarshe a makaranta. Ina zaton ma kamar ina da copy ɗinsa yayi daɗi kam ba ƙarya”.
“Woow da gaske Besty?”.
“ALLAH kuwa bari zan duba maka, sai dai inaga yana cikin kayana da za'a kawo daga Kaduna”.
Dai-dai nan yay parking gaban wani baƙin gate madaidaici yana bata amsa, gidan dai daga waje ba wani babba bane, dan kamar gidajen street ɗin ma duk sun fishi girma da ƙyau. Anan wajen gate ɗin ya kashe motar bayan yayi horn, wani ƙyamushashen mutum ya leƙo, alama AA ya masa da hannu na yazo. Bayan ya kunna fitilar cikin motar ta yanda zai ganshi da ƙyau kada ya tsorata. Aiko sai da ya leƙo daga nesa yaga wanene sannan ya ƙaraso yana famar washe baki. Cike da girmamawa ya shiga gaida AA ɗin, amsa masa yay shima da kulawa, kafin yace ya ɗan kira masa yarinyar gidan nan. Nanma da girmamawa mutum ya amsa masa, daga gani dai kasan maigadi ne. Maanal dai na jinsu, dan tunda ta amsa gaisuwar da mutumin yay mata ta ɗauke kanta gefe. Fitilar AA ya kashe, sai kuma ya ɗakko tab.. ɗinsa ya shiga dannawa, miƙama Maanal tab ɗin yay yana faɗin, “Kinga list ɗin novels ɗin da nake nema idan na samu lokaci na karanta su”.
Amsar tab ɗin tayi, ta shiga duba list ɗin, cikin manta dawama take tare ta ɗan karkato tana nuna masa wanda ta karanta a ciki da wanda itama take nema ta karanta. Shima karkarowar yayi sosai har jikinsu na haɗuwa, ta shagala a nuna masa da yimasa bayani har ya ɗaura hannunsa a kafaɗarta ya sake kwantota a jikin nasa da ƙyau batare data farga ba, sai ma sake lafewa tayi sosai abinta tana zuba zance, dama can ta fishi magana, yanayine kawai ya maidata miskilar ƙarfi da yaji. Shi ko idan kaga ya saki jiki kamar haka yana magana to lallai tare yake da ita, dan sai kaga ma kamar ba AA Darma sarkin haɗe fuska da jefa magana ɗaɗɗaya ba da ƙyar. Sun shagala a hirarsu dake fita ƙasa-ƙasa dan ko ita Maanal ɗin da maganarta tafi yawa bawani tanayi zuuu bane ba, koda a cikin motar kake ma ba lallai ace ka jisu yanda ya kamata ba. Balle shi dake bata amsa kamar mai raɗa. Glass ɗin motar tinted ne, dan haka Nuratu data fito cikin matsananciyar kwalliya tana zuba wani shegen ƙamshin mayataccen turaren magani da babarta ta zazzage mata kanta tsaye ta nufi gefen mai zaman banzar fiskarta kamar ta yage dan murmushi. Wai itace yau Ya AA yazo wajenta hira, kai ita kam tafi kowa sa'a a duniya yau ɗin nan. Ta tabbata harta mutu bazata manta da wannan rana ba a tarihin rayuwarta. Sai da taja numfashi ta fesar tare da sake dai-daita kanta da ƙyau, dan babarta taja mata kunne matuƙa akan ta nutsu kada taje tana wannan rawan kan tunda tasan halinsa dai sarai. Sai da ta tabbatar ta samu irin nutsuwar da take buƙata kafin ta ɗaura hannunta a handle ɗin motar ta buɗe tana faɗin, “Assalamu aikum Yayan....” sauran maganar ya maƙale a maƙoshinta sakamakon saukar idannunta akan Maanal dake kwance a kafaɗar AA suna kallon abu a tab...........✍️
_😂😂Ni dai Nurry ƙawata ce bani da damar cewa wani abu anan🥱🤣🤣🏃🏃🏃_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣7️⃣
______________
........Nurry tamkar wadda ta suma haka ta kasance, yayinda AA da maaanal suka ɗago idanu a tare suna kallonta kawai. Ta kuma ƙi tashi daga jikinsa sai ma ƙara gyara kanta da tayi. Jitai zuciyarta ta mata wani irin nauyi da ganin Nurry ɗin, dan tabbas da tasan gidan su yarinyar nan zasu zo da bazata biyo shi ba. Amma a zahiri babu ko ɗigon damuwa a fuskar tata, sai ma wani irin murmushi data sakarma Nuratun a karo na farko ta furta, “Hy” a hankali.
Sai a lokacin Nuratu ta farfaɗo, a hankali ta zame hannunta dake ɗan rawa daga jikin murfin ta miƙe tsaye gaba ɗaya. Cikin kaushin murya AA ya ce, “K! Baki iya gaisuwa bane?”. Sosai muryar tasa ta ratsa mata zuciya, sanin halinsa na rashin ɗaukar raini ya sakata sake duƙowa dole batare data yarda ta sake kallonsu ba muryarta na ɗan rawa kamar mai shirin fashewa da kuka saboda kishi ta furta, “Kayi hari Yaya ina yini”. Maimakon amsawa sai yaja siririn tsaki kawai. Maanal dai tama maida hankalinta ga tab ɗin gaba ɗaya tamkar bata san mi sukeyi ba. Maanal ɗin ya nuna mata, cikin harara ya ce, “Ita kin gaisheta ne”. Sosai hawayen baƙin ciki suka ciko idanun Nuratu, cikin matuƙar raɗaɗi da jin ƙunar zuciya ta ɗan kalla Maanal ɗin ta ce, “Ina yini”.
Tsabar wulaƙanci yatsu biyu Maanal ta ɗaga mata, batare data kalleta ba ta ce, “Kina lafiya?”. Wata shegiyar ashariya Nuratu ta shiga mulmulawa Maanal ɗin a zuciya, a zahiri kam dole ta amsa. AA da bai sake ko kallonta ba juyawa yay sit ɗin baya ya ɗakko ledar da Mamy ta bashi. Ɗan kwantowa yay ta jikin Maanal sosai ya mika mata ledar yana faɗin, “Kiba mamanku inji Mamy”.
Sake sumewar takaici Nuratu tayi yanzu ma, har sai da AA ɗin ya mata ƴar tsawa da faɗin, “Wai tunanin uwar mi kike”. Firgigit ta amshi ledar zuciyarta na hautsinawa. Da kansa ya jawo murfin ƙofar kamar a fusace ya rufe. Dole taja da baya da sauri gudun bugeta da murfin. Shi ko ko'a kwalar rigarsa yayma motar key yay reverse batare daya ko sake kallon inda take ba ya bar wajen...
Gaba ɗaya Nuratu ta zube a wajen ita da ledar, wani irin kukan baƙin ciki irin mai babbake zuciyar nan a lokaci guda ta saki da iya ƙarfinta. Aiko da gudu mai gadinsu dana maƙwaftansu suka fito suna tambayarta lafiya. Amma bata ko kallesu ba. Maigadin maƙwaftansu yace, “Kodai mugu ne yazo wajenta a sanar da securitys ɗin shigowa?”. Kai maigadinsu ya girgiza masa, “A'a nasanshi, ɗan uwansu ne ma sai dai idan wani abunne ya faru. Kaga tsaya min a wajenta bara na sanarma su Hajiya.” baima jira amsar shi ba ya shige gidan. Babu jimawa kuwa suka dawo da Hajiya, basu kowa bane face Maman Nuratun da mariƙiyarta, dan jiya Maman nasu tazo daga Kano batare da ko sanin Mamyn ba. Rufuwa sukai a kanta da tambaya cikin tashin hankali. Ganin bazata basu amsa ba suka kamata zuwa ciki, maigadi ya bisu da ledar (Ramadan basket🤣).
Tambayar duniya su Hajiya Turai sunma Nuratu dake kuka kamar wadda ake yankawa amma taƙi basu amsa. Sai da mamanta ta balbaleta da masifa sannan cikin kuka ta sanar musu komai. Suma duk shiru sukayi cikin tsananin ɓacin rai. Musamman ma mamansu. Hajiya Turai ta ce, “Amma dai Kamila bata ƙyauta ba, ni da mukai waya kinga ai tace min zaizo ne wajen Nuratun su ɗan zanta ya kuma bata hasaffin azumi da samari ke ɗan bama ƴammata a yanzu. Shine zasu bari ya taho da wata kuma?”.
Ɓacin rai ya hana Maman su Nuratun iya cewa komai. Cikin fushi ta fisga waya da nufin kiran Mamyn Hajiya Turai ta riƙe mata hannu. “Mi zakiyi?”.
Rai ɓace ta ce, “Kiranta mana yaya Turai, banda rainin hankali tasan har yanzu bata da power ɗin tanƙwasa ɗanta zata saka mutane yin asara a banza yazo yana wulaƙanta mana yarinya”.
“Toke banda abinki keda bata san kina garin ba kuma. Ki barni kawai da ita. Dan ni ba Kamila zanmawa yarinyar zan wulaƙanta. Sai na sakata nadamar dawowa rayuwar ahalin Darma. Shi kansa Ajwaad ɗin zan koya masa hankali, dan banga mai taɓa min Nurry yay barci lafiya ba koda kece da kika haifeta. Dan ni ba yayar uba bace kawai uwa ce”.
Sosai zuciyar Maman su Nuratu tai mata sanyi, shiyyasa take matuƙar son Hajiya Turai. Dan akwai mutunci da ƙaunar juna sosai a tsakaninsu tamkar ba yayar mijinta ba. Kai a kaf dangin uban su Saheeban da Hajiya Turai kawai suke ɗasawa, ba kuma komai ya kawo hakan ba sai halinsu ne da yazo ɗaya. Sannan Nuratun tun daga yaye Hajiya Turai ta ɗauketa ta riƙe kasancewar ita har yanzu ALLAH bai bata haihuwa ba, mijin ma ya jima da rasuwa shiyyasa suka baro Lagos inda suke zaune da suka dawo nan Abuja. Sai dai da yake tana bussines koda yaushe ƙafarta na hanyar lagos ɗin da Dubai da Chaina. Shiyyasa Nuratun ke zuba tsiyarta yanda take so a garin na Abuja, dan ƙazamin gata Hajiya Turai ke mata, sannan duk abinda ta nema saita mata shi. Wannan yasa take jinta a babbar yarinya ɗiyar manyan mata masu kuɗin Abuja. Dan ubansu dai bawani kuɗin arziƙi ne da shi ba, hasalima da bazar Hajiya Turai ɗin yake rawa shima....
Hajiya Turai data raka Nuratu ɗaki tace ta kwanta tana fitowa ta tashi, wayarta ta ɗauka tai kiran Sille. Bugu biyu kuwa ya ɗauka. Kamar yanda ya saba cike da yaudara ya shiga yimata kirari da fasa mata kai. “Kaga Sille yanzu ba lokacin kirari bane ba tsaya kaji”. Nuratu ta faɗa muryarta a shaƙe. Ɗan ɓoyayyen murmushi yayi daga can, a zahiri kam murya a dake kamar bai san komai ba ya ce, “Ina jinki uwar ɗakina mike faruwa? Waya taɓa min ke yaga fushin maza dan walle ina iya tada Abuja harda fadar shugaban ƙasa”.
Murmushi tayi a karo na farko, shi yasa take matuƙar ji da Sille a rayuwarta, take kuma taɓa duk wanda taso hankalinta kwance dan shine garkuwar ta. Tasha sakashi ya nakasta mata duk wanda ya nuna mata yatsa a garin Abuja wallau namiji ko mace. Numfashi ta fesar mai raɗaɗi, kafin ta shiga faɗin, “Aiki nake so ai min akan jakar yarinyar can da tama AA ɗina asiri ta auresa”.
“Angama uwar ɗaki. Ƙafafu za'a cire mata ko hannaye ko fuskar za'aima ɓalli-ɓalli irin wanda kikama Huznah take kowama”.
Dariya Nuratu ta kwashe da shi, dan fuskar Huznah ɗin ce ta faɗo mata arai. Ta ce, “Kai Sille kai duniya ne, daɗina dakai baka da mantuwa sam. Ita wannan ai ta wuce ɓalli-ɓallin yarbawa, dan zunubinta mai yawan gaske ne. Zan turo maka abinda nake so ai mata. Kuma a satin bikina bayan salla zaka mata hakan, dan ina son aci shagalin bikina tana asibiti kwance rai a hannun ALLAH dan uban ubanta”.
“An gama babbar yarinya, kune Abuja kune kuma masu riƙe da ƙasar gaba ɗaya, dan masu mulkinta a tafin hannunku suke tunda kullum tsaye suke a gabanku haihuwar tsoffinsu”.
Sosai Nuratu ta sanya dariya harda kwanciya, cike da jin takaicinta ya ragu ta ce, “Zakaga saƙo a lalitarka Sille”. Daga haka sukai sallama ta yanke kiran.....
Daga can dariya Sille ya kece