Showing 132001 words to 135000 words out of 218311 words

Chapter 45 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

ɗauri dasu ƴan kunne da sarƙa. Ita kanta Maanal jinta take tamkar ba ita ba, kamar wata Maanal ɗin ce aka canja. Takalma kawai ta sanya Hajiya Shuwa tace suje a haka after dress a saka idan zasu shiga hall ɗin. Dan rigar tayi bala'in fidda komai na surar Maanal shiyyasa ma akai after dress da za'a ɗora saman su. Duk da itama after dress ɗin ba wani mai kauri bace ba, telar datai ɗinkin ce ta dinkata itama kuma an bita da adon Material ɗin ne kamar dai kayanta na jiya. Wato Hajiya tasan takan tsiya, ita tasan miyyasa tace Maanal ɗin ta fita a haka..........✍️







*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣5️⃣




______________




........Amaal ce ta kama Maanal ta fita da ita dan Oum ce tai kiranta a waya akan a fito da Maanal ɗin su AA har sun iso. Hakama mutane duk sun shiga motoci dan tafiyar gaba ɗaya ake son yi a jere a tsare kamar yanda aka tsara wajen dinner ɗin.
A karo na farko Maanal taji zuciyarta na dukan tara-tara, tsakanin jiya da yau ɗin wani shakkar kasancewarta waje ɗaya da AA take yi, dan jiya wasu abubuwa masu nauyi ta dinga karanta a cikin ƙwayar idanunsa. Haka dai aka fito da ita babu yanda ta iya. Duk da kanta a ƙasa yake, an kuma rufa mata net har fuska hakan bai hanata jin idanun mutane a kanta ba, ga camaras na wayoyi da aketa binta da su, ji take kamar tai kuka. A dai-dai jikin falleliyar motar da RK ke tsaye ya juya musu baya da alama waya yake Amaal ta tsayar da ita. An riga da an buɗe musu dan haka ta taimaka ma Maanal ɗin da zuciyarta keta harbawa da sauri-sauri ta shiga. A hankali AA dake zaune a cikin motar yana binta da wani kallon ƙasan ido ya wani kalar lumshe idanun nasa daddaɗan ƙamshin turarenta na rige-rigen shige masa hanci. Itama dai nasa ƙamshin ne ya gama gauraye nata hancin tare da sanyin ac da motar ta ɗauka. Itama samun kanta tai da lumshe nata idanun nunfashinta na ɗan rawa. Sam bata yarda ta kallesa ba, har aka motsa da nufin tafiya, amma ta gaisheshi ƙasa-ƙasa, bataji ya amsa ba itama kuma bata sake magana ba. A bazata, matuƙar bazata taji shigar tattausan hannunsa da yay ɗan sanyi saboda acn da yake a ciki cikin nata hannun mai ɗumi da laushi, bata gama dawowa a hanyyacinta da riƙo hannun nata da yay ba taji saukar tausasa lips ɗinsa akan bayan hannun nata ya sumbata. Yanzu kam babu shiri dole ta ɗago ta kallesa, a cikin nasa dake mata narkakken kallo suka shige, sai ya sake shanyesu cike da ƙasaita ya motsa lips ɗinsa a raɗa ya furta, “You look great Mrs AA Darma, sai dai bazan taɓa iya barinki shiga a haka ba ina da matsanancin kishi kinfi kowa sanin hakan. Ke ɗin tawace ni kaɗai har a aljanna in sha ALLAHU”.
Sosai furucin nasa taji ya daki zuciyarta da girman gaske, dan haka ta samu kanta da lumshe nata idanun tana ƙoƙarin janye hannunta dake a cikin nasa har yanzu dan wani yarrrr take jin tsigar jikinta na tashi saboda yanda yake murza shi a wani irin hankali. Lallausan murmushi ya saki a karo na farko, duk da iyakar laɓɓansa yay abinsa hakan bai hanata jin fitar ɗan sautinsa ba. Shi ko sai ya wani ja idannun luuuu kamar zai lumshe yana mai kauda kansa gefe kaɗan har lokacin fuskar tasa da ɗan murmushin. Ita dai hannunta ta janye daga cikin nasa, bai kuma hanata ba. Jikinsa cike da kasala ya koma jikin kujerar ya kwantar da bayansa tare da gyara zamansa. Daga haka bai sake magana ba har suka iso hall ɗin da akai matuƙar ƙawatawa, dan tun daga farkon shigowa street ɗin zai baka tabbacin ana wani babban taro na manya. Dan kuwa duk wani ɗan tara dake ji da kansa a cikin Abuja musamman ƴan siyasa da ma'aikatun gwamnati dama abokan kasuwa sun halarci wannan dinner, hatta da shugaban ƙasa ana saka ran zuwansa (saura wani yace Tinbunu nake nufi🙄 to Shugaban kasar Naya Ramadhan B. Hameed Taura😏).
Cike da tsari da nagarta motocin suka kayantu a ƙofar hall ɗin, mutane suka fara fita a nutse suna shiga ciki, ango da amarya dai sai kowa ya gama shiga. Babu zato a karo na biyu Maanal taji AA na zame mata ɗan net ɗin da aka yana mata a kanta zuwa fuska, idannunta kawai ta lumshe zuciyarta na luguden daka, musamman saukar hannunsa a haɓarta dole ta sake matse idanun tsam. Babu zato ko tsammani taji saukar lips ɗinsa a saman nata lips ɗin. Ba gigicewa kawai ba jitai ita kanta motar da suke ciki kamar tana nutsewa a cikin ƙasa ne. Dole ta buɗe idannunta da sauri tana ƙoƙarin tureshi. Sai aka samu akasi hannun nata ya sauka a saman ƙirjinsa, ya kuma saka nashi ya riƙe ya hanata janyewar datai saurin son yi. Ɗayan kuma ya riƙe mata fuska ta yanda ta gagara janye lips ɗin nata. Sai da ya shanye lipstick ɗin da aka sanya mata yay mata masifar ƙyau kuma sannan ya janye nasa baya a hankali, sai dai har lokacin fuskokin nasu na'a gab-gab da juna kowa na busama ɗan uwansa numfashinsa. Ita dai idannunta dake cika da hawaye a rufe suke, wata irin kunyarsa take ji mai tsanani, ga tsoron yanda take ganin idanunsa a juye kuma a ƙanƙance alamar yana cikin wani yanayi mai girman gaske. Shi ko fuskar tata yake kallo kai kace yau ne ya fara ganinta, shi kaɗai yasan mi yake ji. Amma da yake gwani ne a kamewa ya fuske a binsa sam babu ko ɗigon zaƙuwar a kan fuskarsa da idanunsa a zahiri. Maimakon ma barin kunyar tata ta cigaba da tasiri a kofa zuciyar tasa sai yay yunƙurin ɓadda sawu ta hanyar kauda yanayin nasu gaba ɗaya.
“Miyasa kika bari suka sanya miki bayan kin san bana son kina sakawa a duk sanda zaki fita?”.
Ya faɗa da wata irin murya mai sanyi da zurfi ta yanda ita kaɗai ta iya jinsa. Dan koda ace da wani a kusa da su bazai ji abinda yace ɗin ba. Kauda fuska kawai Maanal tai ƙoƙarin yi gefe tana haɗiye hawayen dake neman zubowa daga idannunta na matsanancin haushi da firgici. Amma sai tayi jarumtar hanasu. Eh tabbas ta sani, dan sun sha yin faɗa a shekarun ma ƙuruciya idan ta saka janbaki idan zasu fita, yata takura mata kenan har sai ta goge, a wasu lokutan ma sai dai taji kawai yasa tissue ya kwashe mata shi da kansa, suyita faɗa dan ita harga ALLAH tana son jambaki, gata kuma dama ma'abociyar son kwalliya. Idan kuma ta saka shegen ƙyau yake mata musamman na yau ma dan ALLAH ya bata wasu kalar lips masu ƙyau da fitattacen shaf tamkar an zana mata shi. Gasu da zagayayyen baƙi kafin pink a tsakkiya, dan ko bata saka jan bakin ba sai kaga kamar ta saka ɗin ma a haka. Yanzun ma duk da ya shanye sai lips ɗin na nan da ƙyanzu kamar ma da lipstick ɗin har yanzu.
Yanda ta kauda kai sai shima bai sake magana ba, sai ma ƙoƙarin warware after dress da Hajiya Shuwa ta bashi yayi tare da warware ta. Sosai rigar ke wani irin ƙamshi mai daɗin gaske. Kaɗan ya ɗaga daga zaunen da yake ya ɗan ranƙwafo kanta. A wannan gaɓar kam numfashinta neman ɗaukewa yay, dan kusancin nasu mai girman gaske ne ta yanda wanda ke a nesa dasu ma zai iya ɗauka rungumeta yayi. Shi ko ko'a jikinsa ya yafa rigar a jikinta sannan ya koma mazauninsa ya zauna. Dai-dai nan kuma aka basu damar fitowa. Shine ya fara sauka, sannan ya zagaya ta inda take ya buɗe murfin. Hannu kawai ya miƙa mata batare da yayi magana ba, ita kuma tai shiru taƙi motsi balle ma ta bashi hannun nata, hasalima kanta a ƙasa yake har yanzu.
Hannun nata kawai ya kamo cikin nasa, dole ta ɗago sai dai babu alamar zata fito. Dan tana ma kallonsa tai saurin kauda idonta. Bakinsa ya ɗan taɓe tare da sake matsawa jikinta kaɗan, ta yanda ita kaɗai zata ji ya furta, “Goyo ki ke so ne?”.
Batama bari ya kai ƙarshen zancen nasa ba ta yunƙuro domin fita, dama ta dakata ne saboda mararta data ƙulle taɗan saki, (Bafa ƙaramin gyara Hajiya Shuwa tama Maanal ba, sakamakon sanin Maanal ɗin ba cikakkiyar budurwa bace. Komai baice ba ya taimaka mata ta karasa sakkowar sannan ya gyara mata alƙyabbar yanda yake buƙata. Dan neman magana abokansa sai video suke musu kuwa. Dai-dai nan Oum ta ƙaraso, fuskarta cike da murmushin farin ciki ta haɗasu ta rungume hawaye na cika mata ido. Kafin ta ɗago su batare da tayi magana ba ta shiga tsakkiyarsu hannayensu a cikin nata su duka. Itace ta shiga da su har cikin hall ɗin abokan ango biye da su. Shigowarsu cikin hall ɗin hasken camaras duka ƙaru a kansu, sai Maanal taji daɗin after dress ɗin daya saka matan, dan daba dan yayi hakan ba gaskiya akwai damuwa, zata ji matuƙar takurar shigowa wajen da rigar jikin nata, ita kanta Oum taji nutsuwar ganin Maanal ɗin a haka, dan dama yanayin da taga rigar tayi mata a jiki sanda zata shiga mota ya tsaya mata a rai.
Har inda aka tanada dominsu Oum ta kaisu, koda ta zaunar da su duk sai suka ƙi sakar mata hannaye. Musamman Maanal ma data riƙe da hannu biyu. Dariya ma suka bama Oum, da ƙyar ta danne ta saki murmushi kawai. Tare da ɗaura hannun AA a saman na Maanal ɗin ta rumtse sannan ta zame nata a hankali. Cike da tsokana da murmushi a fuskarta ta ce, “Banda faɗa, in ba haka ba asha bulalar Oum”.
Murmushi sosai AA ya saki mai ƙayatarwa, haka itama Maanal ɗin ƙasa ta sake yi da kanta sosai. Ita dai Oum dake ƴar dariya ta bar musu wajen. Hannunta dake cikin nashi ya ɗan matsa ta yanda dole ta ɗago fuska a yamutse ta dubesa dan taji zafi. Shima kallon nata yake, dan haka ya ɗan ɗage mata gira irin na (kallon fa?) harararsa tayi kaɗan ta sake ɓata fuska tare da ƙoƙarin janye hannun nata amma yaƙi bata dama, sai ma sake damƙesa da yay da ƙyau.
Duk abinda suke idanun mutane da yawa a kansu ne musamman ƴan ɗauka a waya, dan yanzu waya ta zamewa kowa jarabawa, ta bakin wani malami yace yanzu da wayarka kawai aka barka a yayin hisabi ka shiga uku, dan yanda muke ɗaukarta kawai abar muyi nishaɗi ko amfani mu ajiye abin ba haka bane ba, inma bamu sani ba mu sani, akwai hisabi tsakaninmu da abinda muka aikata da su waɗan nan dai wayoyin. Dan haka sai mu shirya, aikata alkairi ko sharri duk UBANGIJI na sane da motsin mu.........✍️









*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣6️⃣




______________




......Nibras da dole ta sakata zuwa wajen dinner ɗin dan tangazo ƙeyarta Fawzan yayi sai taji kawai hawaye na cika mata idanu, ita kaɗai tasan irin baƙin kishin Maanal da take ji a zuciyarta, ga maganar Najma ɗin nan, duk da bata zafafa ba sosai abun fa na damunta ta ƙasan rai. A kwanaki biyun nan ji take kamar ta ɗauka wuƙa ta kashe kowa daga ita sai AA su rayu a wannan duniyar. Tayi kuka har bata san adadin hawayen data zubar ba ma. Ita da Fawzan kam sam babu zaman lafiya tace sai ya saketa, shi kuma yace aurensu auren zobe ne ai ba saki ba yaji, sai ma ya tattarata ya watsar ya maida hankalinsa ga hidimar bikin kawai, gefe kuma ga Najma na girmama farin cikinsa, dan ma tana noƙewa wai tana jin kunya. Ba Nibras ke cikin irin wannan halin ba kawai, dan halin da Saheeba ke a ciki zamu iya cewama yafi na Nibras ɗin, dan abu goma da goma ne ita ya haɗe mata, sosai take taya ƴar uwarta kishi, gefe ga hassada da baƙin kishin nan na facalanci dake da tasiri a duniyar malam bahaushe. Na farko dai bama su dake kwana suna tashi da AA a gida ɗaya ba mutanen dake waje ma sun san AA yafi sauran ƴan uwansa arziƙi na dukiya duk da suma suna da gwargwadon nasu, yana da connection da manyan mutane a duniya ma ba Nigeria kawai ba a dalilin business ɗin nashi musamman na agogo. A gidan kaf kowa sonshi yake soyayya irin wadda bata ɓoyuwa, dan a zahirance da baɗini AA ɗan gata ne a wajen iyayensa da ƴan uwansa, kusan shine ZUCIYAR zuri'ar Aliyu Darma. Bazaka fahimci hakan ba sai wani abu ya taɓa rayuwarsa ko mai ƙanƙantarsa zakaga illahirin hankalinsu ya koma kacokan garesa ne. Yan uwansa sun fisa hasken fata, amma shi kuma ya fisu ƙyau ta yanda ko baka san ƙyau ba sai ka iya banbancewa. Shiyyasa tun farko takema ƴar uwarta fatan samunsa. A wani gefen kuma tana taya Mamy faɗa ne da kishin Oum da faɗa akan su AA. Ga ita kanta shegiyar Maanal ɗin wata irin ƙauna Darma Family ɗin ke mata bama iya su zuri'ar Aba kawai ba dan son AA ɗin ya shafeta ga kowa. Koda yake sun san aikin asirine wannan, lokaci suka bata komai sai ya rushe ta zama mujiya a dangin dan ubanta. Bari dai a gama bikin za'asha kallo dan sabon wasa ne zai tashi a gidan Aliyu Darma kamar yanda suka shirya...


Mamy kam ji take kamar zuciyarta zata baro ƙirjinta ta fito ne kawai. Taso ƙin zuwa wajen dinner ɗin, Maman Saheeba ta tunzurata akan gara suzo ayi komai akan idonsu ai kamar jiya dan su san ta hanyar da zasu yaƙi Oum. Wannan dalilin ne ya sata zuwan duk da bata da lafiya ƙarfin haline kawai, yanzu haka kamar kanta zai fashe dan ciwo...
Yau ma dai ƴan discussion house cike suke da wannan waje cikin kwalliya ta ƙasaita da aji da halin girma. Can na hango muku su Aisha yuguda. Asiya salihu. Fauzarh collection. Hafsat adam651. Maman khairy2003. Lubabatu miss. Maryam Muhammad. Zuwaira muktar limanci. Shafa'atu limanci. Sadiya Ibrahim merariya. Maman meema. Deryer012
Mrs Suraj. Bilqeesu. Oum moh'd. Sa'adatu ibrahim mua'zu . ام الصديق. Ummu aslan&asala. Fateema Umar.. kai sunada yawa fa masha ALLAH, dan hada ZAFAFANKU ba'a barsu a baya ba...
Babban Yaya ne yay addu'a mai tsayi ga ma'auratan, Fawzan ya bada kaɗan daga tarihin ango da nasarorin daya samu a rayuwa. Ya kuma bada na amarya dan yace itama ƙanwarsu ce. Ya kuma ɗora da taƙaitaccen tarihin rayuwar ƙuruciya ga waɗan nan ma'aurata daya taɓa zukatan jama'ar wajen matuƙa musamman wanda basu san da hakan ba irinsu CFO, su Zaharadeen, su Yaƙub kai kaf ma ma'aikatan MAAWAD COMPANY jikinsu yay sanyi, CFO ta gama mutuwar zaune harda hawaye dan ta fahimci a lallai AA na Maanal ne. Yayinda ake nuna hotunansu a ƙaton magijin dake bango guda. Wani hoton dole mutane ke dariya, dan su kansu basu ma san an ɗaukesu ba a wasu wajajen, kuma ba kowa bane da wannan aikin sai Fawzan a wancan lokacin, dan yayi jarabar ɗauke-ɗauken hotuna da camara ɗinsa kasancewarsa mai son hakan shima, aka ce shi Salim ɗin Uncle Mahmud ya gado, shiyyasa wasu hotunan su kansu su AA ɗin basu san da zamansu ba sai yanzu. Maanal sai faman ɓoye fuska take dan AA sai tsokanar ta yake. Komai ya ƙayatar da mutane kamar yanda Fawzan yay fata, dan haka aka shiga tsakkiyar shagali cike da shauƙi. Komai ya tafi a nutse a kuma ilmance, babu wani rawar kai ko aikata abinda ya zarce Shari'a, hasalima ango da Amarya basu tashi daga wajen zamansu ba ko sau ɗaya balle yin rawa. Duk wanda zai musu liƙi anan wajen zamansu yake samunsu yayi. Aiko doller tayi kuka na gaske, dan abokan AA da manyan mutane sun nuna masa shi ɗin fa shine, yayinda matar shugaban ƙasa Raudha Ramadhan Taura ta danƙarama amarya ƙyauta ta musamman. Mawaƙa sun zuba capacity iya iyawa musamman Halifa sk ɗorayi daya maimaita mana waƙar bazani daina kuka ba, suma sauran mawaƙa irinsu Ado gwanja, Umar m Sharif, breaker, Sarkin waƙa, sun zubar mana galan-galan munsha rawa. Hotuna ba'a magana. Video kam tuni sun karaɗe media kamar ba gobe. Kafin kace mi wannan dinner ta zama on top a wannan dare. Al'amarin sai ya zama abin mamaki da tattaunawa musamman da ba kowa yasan da ɗaurin auren ba dinner ɗin ce kawai tayi girgizar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login