Showing 90001 words to 93000 words out of 218311 words
Chapter 31 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
ajiyar zuciya tare da cire kaya tayo wanka ta fito tai sallar azhar da taga lokacinta yayi. Sosai take jin kewar su Ammie, dan haka ta jawo wayarta data koma bata da amfani, dan in tace ma tayi magana dasu ta net bata da data. Haƙura tai ta kwanta kawai, sai ko barci mai nauyi yayi awan gaba da ita. Bata farka ba sai la'asar, tana mamakin yanda lokaci ke gudu anan, abu kamar ba azumi akeba. ALLAH musulman ƙasar nan suna cin ɓagas. Tayi Asr ta zauna taita karatun Alkur'ani. Wajen shida saura akai knocking ƙofa, tashi tai da tunanin ko AA ne. Amma koda ta buɗe sai taga Mr Li. Gaisheta yay tare da sanar mata ta shirya zasu fita. Ɗan jimm tai, sai kuma ta tambayesa AA ya sani. Amsa ya bata da ai shine ma yace azo a ɗaukesu su duka. Ajiyar zuciya ta sauke, ta koma ciki ta hau kimtsawa. Abaya ta saka mai laushi da ƙyau fara tas, ta ɗan gyara fiskarta ta ɗauka handbag ta fito. Tana isowa motarsu Yaqub na wucewa, Mr Li ya buɗe mata itama ta shiga yaja suka fice a hotel ɗin. Tafiyar ba wata mai nisa bace sosai suka iso wani waje mai ƙyau. Ko ina tarwai da haske tamkar rana. Tana fitowa a mota idannunta suka sauka akan AA dake tsaye hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan riƙe da waya yana latsawa, shigarsa ce dai ta safe sai dai yanzu akwai coat a sama, har yanzu fuskarsa babu walwala. Koda ya ɗago idanunsa yana kallonta sai taji wani iri dan idanunsa har yanzu basu washe ba. Takowa yay cike da ƙasaitarsa da nutsuwa zuwa gabanta, dan ta tsaya cak ne tana kallonsa. Dab da ita yaja ya tsaya, kallonta kuma yake ƙurr..
Nata idanun ta risinar tare da faɗin, “Ina yini”.
Maimakon amsawa a ƙasan maƙoshi yace mata, “How are you?”.
“Alhamdullah”..
Ta faɗa itama a taƙaice. Bai sake cewa komai ba yay gaba, binsa a baya tayi, sai kuma ya dai-daita tafiyarsu suka shiga a jere. Wani keɓantaccen waje suka shiga, an gyara wajen sosai anyi shimfiɗu an jera abinci da alama na buɗa bakinsu ne. Kallonta yay a karo na biyu sai kuma ya matso dab da ita ya kama haɓarta yana kallon ƙyaƙyawar fuskarta, ƙasa tayi da nata idanun. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, cike da kulawa ya furta, “Mike damun ki? Duk kinyi sukuku ko azumin ne?”.
Kanta ta ɗan girgiza masa alamar a'a, sai kuma a hankali ta motsa lips ɗinta murya cike da sanyi ta ce, “Barci bai isheni ba”.
Sake riƙe fuskarta yay sosai yanzu kam da hannu biyu, shima a maƙoshi ya ce, “Sorry my Babie. Ba zamu jimaba ai, muna yin salla sai na maidaki ki kwanta okay”.
Kanta ta jinjina masa fuskarta na wani shagwaɓewa.
Yanda tai ɗin sai ya sashi sauke ajiyar zuciya, cike da tsokana sai dai fuskarsa babu wani alamar wasa ya ce, “Karfa a dinga fakar idona ana karya azumin nan”.
Karan farko Maanal ta waro idannunta sosai a kansa kamar yanda yara keyi idan abun ya basu mamaki, da ɗan karsashi ta ce, “Lah nice kuma zan karya azumi? Nafa girma”.
Shima idanun ya ɗan waro waje kamar yanda tayi, sai kuma cikin raɗa ya furta, “Lah na manta ashe half ɗin Ajwaad ta girma ta zama ammatansa yanzu. Na fara shirin zama ango kenan?”.
Kifa kanta tai a ƙirjinsa dan maganar ta bata kunya, musamman a yanda ya furta yana wani ƙanƙance idanu. Shima sai ya murmusa zuciyarsa cike da shauƙi. Fin minti ɗaya suna a haka kafin ya ɗagota tare da furta, “Kina da alwala ne?”.
Kanta ta jinjina masa alamar eh. Shima sai bai sake cewa komai ba ya nufi wajen da kayan abincin suke ya ɗakko goran ruwa da ɗan bowl dake cike da dabino ya dawo wajan. Handbag ɗinta ya amsa ya ajiye a table ɗin kusa da su, sannan yay mata nuni da kujerar gaban table ɗin. Babu musu ta kai zaune, shima ya zauna a wadda take facing nata. Ruwan ya ɗauka ya kuskure baki itama ya bata, ya ɗauka dabino ya gutsira rabi ya kai rabin bakinta.
“Wai ansha ruwa ne?”.
“A'a zamu karya namu ne”.
Ya faɗa cikin yanayin tsokana yana tsareta da idanunsa masu laushi. Sai baƙar maganar ta bata dariya. A cikin maƙoshi tayi murmushi sannan ta riƙe hannunsa suka saka dabinon a bakinta tare, itama ɗauka tayi ta kai bakinsa.
“Fara ci”.
Ya faɗa a sauƙaƙe.
Kanta ta ɗan girgiza, “Kai ne babba ai”.
Har cikin ransa yaji daɗin abinda ta faɗa, dan haka ya murmusa kaɗan yana kamo hannun nata shima ya gutsira rabin dabinon, cike da kulawa yace, “ALLAH yaya miki albarka! Barka da shan ruwa”.
A saman lips ta amsa da amin tana ɗan murmushi da saka sauran dabinon a bakinta. Irin wannan yanayin kan karya mata zuciya matuƙa, takan ji abin da girma ta yanda har zuciyarta ke raunana taji anya zata iya aiwatar da shawarar su Didi a kansa. Sai dai wani gefe na zuciyarta kan kwaɓeta da gargaɗarta da tuna mata rayuwar da suka tsinta kansu a ciki bayan faruwar komai sai yaji ina.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣4️⃣
______________
.......Miƙa mata ruwa da yay ne ya katse mata tunaninta, sai ta sauke ɓoyayyan nunfashi kawai ta amsa. Sun sha ruwa sannan ya miƙe yana faɗin, “Muje yin salla suna jiranmu”.
A mamakin Maanal ta wata hanyar daban suka fito, sai taga masallaci madaidaici a wajen. A ranta tace wai ina yake samo irin wajajen nan? Dama akwai musulmai a Chaina kamar haka. A ƙarshen bango taga CFO, dan haka ta nufi inda take, ba'a kiran salla a massalacin, sannan ba'a salla da mic. Sai suka bata tausayi, amma koma miye UBANGIJIN da suke ibadar dan shi mai ji ne da ganine a kowane irin yanayi. Basu da yawa sosai, kusan ma zatace sune suka cika massalacin. Sunyi sallar magrib sannan suka fito. Wajen nan da AA ya fara kaita suka koma. Ganin yanda CFO keta shareta cikin kame kai itama sai ta watsar da ita, an gaggaisa da yima juna barka da shan ruwa suka zazauna. AA na kusa da ita, da kuma kansa ya zuba musu abinci ita da shi, ita dai duk sai ta jita a takure, shima ɗin bada wani sakewa yake cin abincin ba. Suko su AS kwasar girki suke hankali kwance duk da suna jin nauyin AA ɗin. Ita da shine suka fara tashi, dan haka sai ya jata kawai suka fito a wajen. Waje suka samu suka zauna, ya ɗan tsareta da idanu.
“Mike damunki? Ko har yanzu barci ne?”.
Kanta ta girgiza masa, sai kuma cike da shagwaɓa ta ce, “Ina jin kewar su Ammie, tunda muka zo banyi waya da su ba. Ko barka da shan ruwa ban musu ba”.
Nauyinta yaji akan hakan. Dan shima ya fahimci bai kyauta ba, shi ya kira iyayensa sun gaisa amma ita bai kira nata ba. Duk da har ga ALLAH yayi niyyar yin hakan shafa'a yayi. Ƙasa-ƙasa ya ce, “I'm sorry”.
Batace komai ba shima sai yay shiru. Cikar lokaci sallah ya sakasu tashi. Sunyi isha'i da asham. Koda suka fito anan suka bar su AS, shi da ita suka wuce, wani gidan abinci mai shegen ƙyau suka isa, ganin an saka halal ya sata sauke ajiyar zuciya. Abinci aka shirya musu na gani na faɗa, anan kam cike da kulawa ya rinjaye ta sukaci suka ƙoshi. Basu koma hotel nasu ba sai kusan ɗaya na dare. Shi kam a gajiye yake fiye da ita, dan haka yana kwanciya sai barci. Dama haka yake so shiyyasa yaba kansa wahala da zirga-zirga ko zai samu raguwar kusancin zamansu a tare idan sun dawo makwanci. Saboda shi kaɗai yasan abinda yake fuskanta a jikinsa da wannan zaman waje ɗayan nasu. Ya kuma fara fahimtar gangar jikinsa so take taƙi bashi haɗin kai bisa shirinsa......
_________★
9-Ramadhan.
A yau ɗaukacin musulmai suka kai azumi na tara-tara a wasu ƙasashe, wasu kuma na ƙoƙarin ƙarisa kaiwa irinsu Maanal dake a Chaina. Yau gaba ɗaya a busy suke, dan sunata shirin komawa ƙasarsu ta haihuwa. Babu abinda Maanal zatace da UBANGIJI sai godiya a kwanakin nan, domin kuwa ta ƙaru da abubuwa masu yawan gaske. Irin siyayyar da AA yayi mata har tsoro abin ya bata, wai iyaka ma wanda ta gani kenan. Dan bata sani ba ma ya tura wasu kayan Nigeria kusan kwana uku kenan. Duk da daɗi da Chaina tai mata hakan bai hanata jin ɗokin komawarsu gida ba. Dan tayi kewar kowa da Kowa. Duk da zuwa yanzu hatta su Ammie duk tana waya da su...
A ɓangaren AA kuwa a matuƙar takure da azabtuwa yay kwanakin nan. Shi kaɗai yasan ɗunbin yaƙin da yay da kansa wajen kauda ido ga Maanal a tsakanin nan. Sai kuma azumi daya sake taimakawa ya zame masa garkuwa. Rashin walwalarsa a bayyane take, sai dai hakan bai hanashi bama Maanal kulawa mai tsayawa a rai da zuciya ba wadda shi kansa ya fahimci ta sakata ƙara zama mai laushi, shaƙuwarsu kuma nata dawowa kamar da duk da bawai tana sakin jikinta bane kamar da ɗin yanda ya kamata. Dan wataran idan ta miskile masa ma har mamakinta yake. Badan yana kewar iyayensa ba da ita kaɗai zai tura Nigeria shi kam sai bayan salla ya koma dai-dai sanda Abah ɗin ya yarda zai bashi matarsa. Haka dai ya daure yay musu shiri yanda ya kamata. A gajiye sosai suka koma hotel ɗinsu, dan sunje ƙarasa wasu yan abubuwa ne da suka rage. Kasancewar ya tsaya suna magana da CMO a waje ita kaɗai ta shige ɗaki, gudu-gudu ta hau zame kaya da planing ɗin shiga wanka kafin ya shigo. Dan harta fiddo kayan da zata canja a bayin kamar yanda take yi. A bazata kawai ta ɗaga riga zata cire bawan ALLAH ya shigo. Daburcewa tayi gaba ɗaya, ga rigar taƙi fita hasalima ta maƙale mata ɗan kunne dan atamface ga style ɗin ɗinkin wuyan irin ƙaramin nan ne. Faɗin rigar kuma yasa ba'a saka mata zip ba.
Cak AA yaja ya tsaya ƙirjinsa na wani dokawa da sauri-sauri. Ji yay kamar ya juya ya koma, sai dai kuma yanda take kicin-kicin yasan zata iya buguwa da wani abun. Gashi ta gagara cire rigar, jikinta kuwa har rawa yake. Kamar wanda aka saluɓewa kuzari ya shiga takawa a slowly, yana zuwa dai-dai gabanta ya tsaya, dai-dai ta ɗan sake duƙewa ta ɗago cikin nasara ta zare kunneta ɗaya daya riƙe, motsawar da zatai kawai tai karo da mutum. Cak ta tsaya zuciyarta na mata gudu a ƙirji, sai taji hawaye ma sun cika mata ido. Dan tasan ya ma riga ya gama kalleta daga ita sai b&p tunda tayi sama da rigar ne gaba ɗaya. A bazata kuwa, matuƙar bazata taji saukar lallausan hannunsa a saman ƙugunta, kafin a hankali ya shiga matsar da shi har zuwa gadon bayanta ya zagayosa ta ɗayan gefen cikinta. Matsota yay ta manne da jikinsa. Ji tai ta ƙara daburcewa, shi kansa zuciyarsa tsitstsinkewa take, dan wannan shine na farko da yake ganinta a haka. Koma yace yake ganin mace a haka a gabansa. Tuni idanun ƴan maza sun juye cikin ƙanƙanin lokaci, sai faman taunar lips yake tamkar zai hudasu da haƙora. Hannunta da take ƙoƙarin turesa ya riƙe, sai ya maida shi baya ya riƙe a hannunsa dake gadon bayanta. Ɗayan kuma ya shiga zare mata rigar jinin jikinsa na narkewa. Rigar na gama fita Maanal tai ƙoƙarin duƙewa, cak ya kamota gaba ɗaya ya tsayar akan ƙafafunta, kafin ya fara tafiya da ita sannu-sannu suka dangane da bango. Bata daina ƙoƙarin turesa ba, ga jikinta na rawa hawaye na gangarowa, sai dai ta kasa magana. Jin ya manneta da bango sai kawai ta kife a jikinsa dan bata da wani zaɓin daya wuce yin hakan. Hawayenta yaji suna sauka a ƙirjinsa duk da akwai riga a tare da shi.
Sake rikicewa gangar jikinsa tayi, sai ya dinga jin kamar bazai iya riƙe kansa ba yau. Kamar bazai iya haƙuri da juriyar daya ɗauka ɗammara ba. Kamar bazai iya riƙe alƙawarin Abah ba. Tabbas bazai iya ba, dan kuwa cikin yamutsewar tunani ya kai fuskarsa cikin wuyanta ya fara bata sumba masu zafi da shinshinar wajen yana busa mata numfashinsa. Ƙoƙarin ɗagowa datai a rikice zatai magana ya bashi damar riƙe lips ɗinta cikin nashi.
Harga ALLAH Maanal bata taɓa tsorata da shi irin yau ba, dan kuwa a karo na farko hannunsa ya sauka a inda wani mahaluki bai taɓa kaiwa ba koda Ammie ko ƴan uwanta, dan ita ko kaya kunyar sakawa take a gaban Ammie, kai tunda tai hankali wlhy b ɗinta idan ta wanke bata yarda ta shanya inda wani zai ganin mata. Dama su Didi ke siya mata, suma sun san yanda take jin kunya sai su saka mata a cikin kaya bawai su bata hannu da hannu ba, ita kanta kunyar kanta take ji ta yanda koda wasa bata taɓa tsayawa gaban mirror ta kalla jikinta ba. Sosai taji mahaukaciyar gigita mai tarwatsa brain, ga azabar yanda yake mata na ratsata. Cikin sa'a ta ƙwace bakinta saboda yanayin da yake a ciki ƙarfinsa ya fara sanyi, amma inba hakan ba wane ita, ko a fuska ka kalla AA kasan a wajen mazan ma bazai daku ba balle ita ƴar tamatsitsi. Roƙonsa ta shiga yi cikin kuka har tana roƙonsa dan girman ALLAH yayi jaƙuri. Jin yaƙi sakinta ta koma tabbatar masa wlhy in bai bartaba bazata taɓa ta yafe masa ba....
“Kinji nace ki yafe min ne daman?”. Ya faɗa murya a shaƙe yana ɗagata cak zuwa gadon. Ina Maanal fa ta fahimci yau sai ta ALLAH wlhy, aifa jikinta ya shiga rawa ganin yana zame tufafinsa, gashi ya riƙeta da hannu ɗaya kawai amma ta kasa motsi. Sai ta shiga magiya da roƙo da ban haƙuri tana haɗashi da girman ALLAH. Abun yazo mata a bazata ne shiyyasa ta gigice. Gefe kuma zuciyarta na tuna mata wata rana data shuɗe, ranar da bazata taɓa goguwa a brain ɗinta da tarihin rayuwar su ba har abada. Dan ta zame musu tamkar tabo ne mai barin tambari a fuska na har abada. Wani gefe kuma nasihar likita da yace mata ta daina tsorata, tarayya da namiji ba mutuwa bace ba...
Cikin shiɗewar kuka da sallamawa idannunta a rumtse ganin ya gama zare kayansa gaba ɗaya bakinta na rawa ga hawaye wasu na bin wasu ta ce, “Shike nan Ajwaad! Shike nan kayi duk yanda kaso, ai dama basan kana ɗaukata ne kamar wata dabba mara daraja, tunda ma ka iya keta min haddi a shekarun da ban wuce sha biyar ba taya zaka jini a yanzu, ta yaya! Ta yaya zaka jini. Wlhy tsoro nake ji! Tsoro nake ji Yaya Ajwaad ka taimaka min na tuba! Na tuba dan ALLAH kada ka aikata min komai!!”.
Ai cak AA ya tsaya daga yunƙurin sake haɗe lips ɗinsu da yake yi, dan maiba wani ji kalamanta na farko ba balle su masa tasiri, amma kalmar _(Wlhy tsoro nake ji! Tsoro nake ji Yaya Ajwaad ka taimaka min na tuba! Na tuba dan ALLAH kada ka aikata min komai)_ har cikin tsakkiyar kansa suka dinga zirarawa kamar ana buga ƙusa a cikin bango, zuciyarsa ta wani shiga rartabewa gida daban-daban saboda wani tausayinta daya ratsashi, dan jikinta rawa yake sosai. Gaba ɗaya abinda yake ji a jikinsa komai ya tsaya kamar an daka musu tsawa. Jikinsa da ya ɗauka wani kalar ɗumin zazzaɓi lokaci guda ya janye daga nata, sauka yay a gadon gaba ɗaya, gaba ɗaya ji yake ɗakinma na juya masa, kalamanta na sake maimaita kansu a kunnensa cikin amsa kuwwa. Da ƙyar ya iya kai kansa bayi, baima san a yaya ya rufe ƙofar ba kawai ya tsinta kansa ne a ƙarƙashin shower..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣5️⃣
______________
.......Maanal kam tunda ya raba jikinsa da nata taja duvet cikin rawar jiki ta duƙunƙune kanta waje guda, sosai jikin nata ke rawa. Ga hannunsa da take ji har yanzu a jikinta, ga wajen na mata