Showing 135001 words to 138000 words out of 218311 words

Chapter 46 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

bazata.
Abinka da manya na waje ba'a wani daɗe ba aka tashi, dan shaɗaya da rabi da yawan mutane ma sun kama hanyar gidajensu. Su Oum ne ƙarshen baro wajen, yanzu kam Fawzan ne ya ja motar da suke ciki, dan haka Najma ta kasance a kusa da shi dan Nibras tuni ta koma gida wai kanta ke ciwo, su Mamy ma ba'a tashi da su ba. Ita Hajiya Majdiya ma sai al'amarin yaso fara bata dariya. Dan zuwa yau ta sake yarda lallai akwai abinda ya kamata su sani game da Mamy. Shin wannan aurerrakin take ma ƙiyayyar, ko kuwa bayan shi akwai wani abu a ƙasa daya kamata ace sun sani?.
Najma ce ta taimaka ma Maanal suka shige, dan kan Maanal ɗin ciwo yake mata sosai jikinta kansa ya ɗauki zafi, dauriya kawai take yi koshi AA ɗin taƙi yarda ya fahimta. Dan tunda ta samu ya sakar mata hannu bata sake yarda sun haɗa jiki ba har aka tashi. Shima fahimtar a takure take ya sashi bata space ɗin da take buƙata, a gefe kuma akwai nauyi da kunyar su Oum dake a wajen. Ko yanzu Fawzan nata masa shaƙiyancin wai ko ƴar rungumar sai da safe baima Lillyn ba amma yaƙi kulashi. Dan shi bama wannan ba, gargaɗin da Mamy ke masa da idanu da mugun kallon da yaga sunama Oum ita da yayarta ne ya tsaya masa a zuciya. Dan tuni hankalinsa yabar kan dinner ɗin ma ya koma ga Oum kaco kan da da su Mamyn. Dan shi fa ya yarda komi Mamyn zatai tayi masa amma karta taɓa masa Oum ɗinsa, sam bashi da jarumta ko ƙarfin zuciya akan a cutar Oum ko Manaal, shi mai rauni ne akan soyayyarsu.....


★Gajiya sosai ta saka kowa neman makwanci domin hutawa. Alhamdullah Mannal tayi farin cikin ganin ƴan uwanta na tare da ita anan zasu kwana dan Oum ta hana kowa komawa gidan Shahidah, tace tunda amarya tazo gida anan ake biki anan zasu zauna har a kammala kodan a ɗebema Maanal ɗin kewa, ta kuma ji a ranta itama amaryace da aka kawo yau gidan miji ce kamar kowace amarya. Anan ɗakin da aka ajiyeta take tare da su Amaal dan suna so suyi magana da ita, duk da Nene ta shigo tace su maidata sama ɗakin mijinta itako ta sanya mata kuka da roƙon ita dai a barta anan dan ALLAH, dariya su Shahidah suka dinga mata, yayinda Nene ta saki baki tana kallonta.
“Amma fisabillahi Maanal kada yaron nan yaga rashin hankalinmu, tunda aka kawo ki ance kina sashen Hajiya Fateema Alhaji yay masa ƙarfa-karfa ya riƙeki kin zaune a sashenta, yau kuma ace an kawoki inda yake mu mun riƙeki bayan yayi kawaici iya kawaici”.
Baki sosai Maanal ta sake turawa gaba tana hawaye. Sai Shahidah da tausayin Maanal ɗin ya cikama zuciya ta ce, “Nene ayi haƙurin, shima ai yasan kamawa tayi tunda Oum ta maida bikin sabo fil. Ba yau bane kawai sai gobe. Shina kuma bana ma zaton yana a gidan nan dan ban gansa ba tunda muka dawo. Maybe ma bazai kwana a gidan ba tunda yasan da baƙi”.
“To ai shike nan tunda kun zama yayun banza kuma”. Nene ta faɗa tana miƙama Maanal abu a kofi, koda ta tsaya kallon kofin sai Nene tai mata daƙuwa, dole ta amsa ta shanye abinda ke cikin. Amsar kofin Nene tai ta fice ta barsu suka cigaba da hirarsu. Ita dai Maanal ma kwanciya tayi abinta dan itafa komai yimata yake kamar a mafarki musamman yanzu da aka maidota wannan sashen wai da sunan sashenta da zata rayu matsayin matar aure, auren ma na Ajwaad Bestyn ta...
Wajen ƙarfe ɗaya gidan ya ƙara zama shiru mafi yawa anyi barci dan an gaji. Hakan ya bama AA damar shigowa ya haye sama ya kwanta shima. Nene data gansa dan ta fito zata ɗauki abu data ajiye anan falo tai saurin komawa da baya. Sai da ya gama hayewa ta fito tai abinda zatai. Maimakon ta koma ɗakin da zata kwana sai ta nufi na Maanal, ganin har sun kwanta bai hanata ƙoƙarin tada Maanal ɗin ba ta hanyar kiran sunanta. Maimakon ita ta farka sai Amaal ce ta farka, barci cike da idonta ta ce, “Nene Lafiya dai ko?”.
“Lafiya Lau koma barcin ki. Maanal nake son ta tashi ta wuce ga mijinta can dai a gida zai kwana, ɗazu nayi magana kum kakkare cewar ba'a gida zai kwana ba tunda yasan nan zamu kwana. Ni na taɓa ganin irin wannan ƙarfa-karfa yaro a hanashi matarsa tsawon wata biyu kamar aure fulani”.
Amaal da abin yaso bata dariya ta danne da ƙyar tana tashi zaune. “Kai Nene wai kamar auren fulani. Nene a barta dan ALLAH, ba yau bane kawai dai, gobe iyanzu in sha ALLAHU mun bar musu gidan ai. Shima nasan bazai ce anyi ba daidai ba. Kuma bama tada lafiya sai da tasha magani ta kwanta taɓa jikinta kiji”.
Rasa abin cewa Nene tayi ita kam. Dan ta kula wannan yayun na Maanal sai a hankali, sam basa ganewa. A taƙaice ta ce, “Shike nan sai da dafe” ta juya ta fice. Cikin raɗa Aunty Sakina data farka itama ta ce, “Da alama dai Nene ta ƙagara ango ya angwance, irin wannan damuwa haka”. Dariya Amaal tayi kaɗan, tare da faɗin, “Bata san tana sake firgita ɗiyar tata bane, dan gaba ɗaya auta a tsorace take tun ɗazun wlhy.”
Murya a sanyaye Shahidah ta ce, “Nima tausayi take bani ALLAH. Ita da ba wani jikin azo a gani ba tana tafiya kamar zata ɓalle, sauƙin ma Ajwaad ɗin azumi ya ɗan sakashi raguwa, amma ya mata yawa ni dai nake ga mutum a murɗe haba jama'a”. Ta ƙare maganar a sanyaye kamar zatai kuka. Dariya sosai Aunty Sakina keyi, ta ce, “Yayun ƙarshen zamani kenan, dama namiji nama mace yawa ne? Kuna nan zata baku kunya nan da wata tara mu dawo suna. Balle ma Maanal mace ce, koda take da rashin ƙiba ai tana da jikin cikakkun mata. Ga gaba ga baya ko'ina Alhamdullah. Amma fin wata biyu an hana bawan ALLAH matarsa kai jama'a a tausaya masa mana ga uban gyara tasha”.
Dariyar shaƙiyanci suka sanya, duk da da gaske har cikin ƙasan rai tausayin Autar tasu suke ji. Duk abinda suke faɗa Maanal na jinsu, dan itama tun shigowar Nene ta farka. Gaba ɗaya sai taji tsoron na ƙara tasiri a ranta. Dan da gaske gaba ɗaya a firgicen take, yau har addu'a tayi ALLAH yasa jininta yazo, amma bawan ALLAHn nan shiru kake ji. Sai kawai taji hawaye na ciko mata idanu, musamman data tuna abinda ya dinga faruwa a tsakaninsu a watanni biyun nan, musamman a Chaina daya kusa samunta har karo biyu ALLAH dai ya ƙwaceta da ƙyar. Gashi idonta ya rufe da soyayya har tana wani ɗaukar masa alƙawuran randa aka kawota zatai miye-miye ko ubanwa ya aiketa..........✍️




🤣🤣😂😆Kya dai gayama ƴan Giro Manaaluwa😛








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣7️⃣




______________




........WASHE GARI kamar waɗanda ke akan ƙaya Nene ta azalzalesu suka fara shirin gyara gidan. Duk abubuwan dake a kwalaye aka ciresu, tun daga bedrooms na sama banda ɗakin AA saboda girmamawa, sunce in ma akwai abinda yake buƙata idan sun tafi ita da shi sa sanya a ciki. Amma bedrooms biyu nata da wanda ke matsayin na yara duk an gyara su, an shirya mata kayanta a closet, falon sama ɗin ma komai an saka har labuloli, aka goge ko ina aka saka ƙamshi. Ƙasa ma sun sake gyarawa, akama canja zaman kujerun gaba ɗaya sannan suka shiga kitchen, kayan da bazata buƙata a kusa ba aka danƙare su a store, sannan aka sake shara tsaf anan ma aka baza ƙamshi. Koda aka kawo musu break fast ma sun gama gyaran ko'ina. Suna gama ci aka shigo da kayan lefen Maanal da AA ya haɗa mata, mamaki ya kama kowa, ganin anfa kai lefe a wancan karon, amma sai Hajiya Majdiya ta tabbatar musu ango yace wannan nasa ne. Haukacewa ƴaƴan su Hajiya Yaya suka sake yi dan mamaki da ruɗani. Musamman da aka fara buɗe akwatina ana fiddo fitinannun kaya naban mamaki designers na manyan matan masu kuɗi ƴan gata. Ya subahannallah kowa sai ya rasa baki magana. A take Shahidah ta bada tukuyci ita da Amal, wannan tukuyci ya sake girgiza su Nasiba.
Maanal ɗin kanta sai da lefen ya girgizata, dan tabbas ya ɗan tambayeta wasu abubuwa a Chaina, musamman colours haka da sauransu, amma bata ma kawo ma ranta mi zaiyi da shi ba. Haka aka gama murna da kallon kaya aka sanya albarka aka kumayi videos Dan nunama Ammie da Daddy. Maanal dai tun jiya bata sake saka ango a idonta ba har zuwa yanzu da za'a fara shirin walima, bata damu da rashin ganin nasa ba, ba kuma ta tambayi kowa ba. Ita gaba ɗaya ma kasancewar ƴan uwanta a tare da ita ya sakamata farin ciki da mantar da ita komai. A haka lokacin walima yayi, Hajiya Shuwa da mai kwalliya suka shigo, duk da dai yau ma Hajiya Shuwa tace bamai yawa za'ai mata ba. Amma kafin ayin ma tasha turare harda na tsiya, kai Hajiya Shuwa tasan sirrin ƙamshi na kata'i, tsaf aka kwalliyeta aka sakata ta shirya cikin Abaya mai ƙyau fara tas da adon golden. Matuƙar ƙyau Maanal tayi kam kamar ka saceta ka gudu. Ga wani ƙamshi mai azabar daɗi tana bulalawa. Anan harabar gidan aka shirya walimar, dan tabbas gidan su AA babbane matuƙa ta yanda basa jin ko ɗar idan sabga ta tashi. Idan ba irin su dinner ba da wahala kaga sun kama hall ɗa sunan yin wani event a yayin sabgar su. Sosai walima ta ƙayatar dan iya mata ne kawai, sai malamai da aka gayyata suka zuba lectures masu ratsa jiki da saka nutsuwa musamman akan ma'aurata da shi kansa ma zaman auren da daɗin dake cikinsa da ƙalubale.
(Please muɗan yi magana anan mana. Akwai wani abu dake cin raina a duk sanda naci karo da shi a social media. Idan budurwa na nuna ɗokinta da farin ciki a ranar aurenta ko lokacin shagalin biki sai kaga ana faman zaginta ko tsoratar da ita akan al'amarin maza ko auren ma gaba ɗaya a comment section. Hummm jama'a mu fuskanci wani abu fa, ita rayuwa akwai jarabawa da ƙalubale a cikinta, sannan ba lallai abinda kai aka jarabceka da shi a jarabci wani ba. Ba lallai dan ke baƙya jin daɗin rayuwar aurenki kice kowa ma haka take ba ko haka zata faru ga wasu ba. Zata iya yiwuwa ita jarabawarta ba'a rayuwar mijin bane ko halayyar mijinta. Wallahil azim yanda muka san mata da yawa nashan wahalar rayuwar aure da rashin ƴanci a gidan aure to akwai mata da yawa kuma dake jin daɗin aure da farin ciki a cikinsa. Akwai matan da dayawa suke samun soyayya da kulawa ga mazajensu fiye da rayuwar novels. Dan ALLAH mubar karya zukatan yaranmu da ƙannenmu masu tasowa akan abinda UBANGIJI ne kawai mai ilimin saninsa. Mu dinga ƙarfafasu da hakan, koda bata samu yanda take hangeba zuciyarta zata wadatu da abinda taje ta samu, dan shi dama ɗan adam ai ba komai yake samu hundred percent a rayuwarsa ba. Dole idan aka baka farin ciki anan a jarabceka anan kuma. Yanda muka san akwai maza marasa adalci ga mata haka ma akwai adalai masu tausayi da nuna kulawa ga iyalansu da yawa a cikinmu. Akwai kuma hatsabiban matan da suke wahalar da mazan su kuma amma mazajen nasu na haƙuri da su. Dan haka yake ƴar uwa, kada ki wani bari zuciyarki ta raunana kota karaya da tunanin ko hangen gidan miji KURKUKUN AZABA ce, dage kiyi addu'a ki miƙama UBANGIJI lamarinki da zaɓinki ki tsarkake zuciyarki, ki yarda ALLAH mai rahama ne mai jin ƙai, kiyi addu'ar samuwar miji na gari mai addini, mai kamala, mai neman na kansa, wanda ya iya ƙyaƙyƙyawar mu'amula da mutane, mai tausayin iyayensa da ƴan uwansa wlhy in sha ALLAHU, ALLAH zai baki fiye ma da wanda kika roƙa ɗin in har kema kin kasance tsarkakkakiya, kin wadata zuciyarki da tsoron ALLAH, baki kusanci ZINA ba, kin nisanci MAƊIGO, kin nisanci shaye-shaye, kin nisanci ƙawayen banza da samarin banza ƴan aci duniya a titi. Kin ƙyautatama iyayenki kullum kina zagaye da addu'arsu, kin ƙyautata mu'amularki da kowa, kin cirema kanki hassada da gulma da aibanta wasu ko rayuwar wasu da danne hakkin mutane komai ƙanƙantarsa. Ajiye batun ƙyale-ƙyalen matan media duk buge ne wlhy, mafi yawansu hodace da zanen jagira dana jambaki sai filter da ƙaryar an tara amma komai fanko ne da haɗa-haɗe, mafi yawansu ƴan koda rigima da zubda mutunci ne sai na ɗinka na saka na saya na saka dan na burge mabiyana a media. Wata idan kika ganta a zahirinta da asalin rayuwarta da sanin wacece ita wlhy har gaban abada bazaki sake marmarin zama irinta ba in har kina jin tsoron ALLAH. Dan haka ki rufama kanki asiri, ki gargaɗi zuciyarki daga barin wannan ƙyale-ƙyalen banza da wofin dan ita MEDIA GIDAN KASHE AHU CE, sannan ALALAN GERO CE. Ki dinga tunawa ba farkon ba ƙarshen, da yawa sunyi tashen a mediar da fariyya da alfahari da ƙaryar amma tarihinsu ya shafe ko labarinsu baka sake ji, kuma suna a cikin duniyar ba mutuwa sukai ba, kawai dai an ƙyanƙyaso waɗan da suka fisu iyawa ne dan kowa fanɗarewar wani babban wani ne, wani ma sai dai a kira shi kakan wasu. To kwantar da hankalinki ki ɗaurama dokin rayuwarki sirdi da linzamin banbance abinda ya dace da ruɗanin duniya mara amfani ki rungumi mijinki ki godema UBANGIJI ki ɗaya baki shi, ki wadatu da ni'imar da ALLAH yay miki ta kasancewa a ƙarƙashin bautarsa dan aure dai ibada ce, sai ki zauna lafiya kiyi barci mai daɗin gaske, ana hayya-hayya, ke kina salama-salama saboda UBANGIJI ya tsaya miki. Mu dinga yawaita addu'ar samun zaman lafiya da soyayyar mazajenmu da rage zafin kishi, mu kama sana'a, mu rage buri, mu rage zalunci, wlhy zamu kasance masu nasarori bama nasara ɗaya ba. Karki sake wata banza ta canja miki tarbiyyar uwa da uba akan abinda maybe ita sai da ta saɓama ALLAH ta samu. Ɗaukesu ƴan a kalla ai dariya da mamaki a wuce kawai ba ƴan a ɗauki darasi ba ko yin koyi dan ke dasu tamkar nisan samaniya da ƙasa ne a daraja wlhy. Kina da ƴaƴa, in baki haifa ba ma zasu zo da ikon ALLAH, idan auren ne bakiyi ba zakiyi mijin aurenki duk nisanku sai ya isko ki kada kiyi tunanin sai kin ɗau waccan hanyar zaki sameshi shi mutunci madara ne idan ya zube ƙasa baya kwasuwa. ALLAH ya baku mazaje na ƙwarai, ya haɗamu baki ɗaya ya bamu farin ciki a gidajen aurenmu. Masu fuskantar jarabawa UBANGIJI ya sassauta ya samar da farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwar aurenku da mu baki ɗaya. Mu dage da addu'a ƴan uwa, mu cirema zukatanmu son mallakar maza ta kowane hali, mu tashi mu nema sana'a, mu tsarkake zukatanmu mu yawaita istigafari, mu gyara ibadarmu da mu'amularmu da mutane. Dan wlhy a wasu lokutan sharrin da kake aikatawa ga mutanen dake a zagaye da kai ta fuskar rayuwa ko rayuwar social media ɗin nan da muka raina sai kaga ya dawo cikin rayuwarka ka gagara gane komai, harshenka ya kasance mai kaifi a wajen mutane, kai kuma sai mijinka ya zama mai kaifafa maka a cikin gida ko dangin miji. Mu kiyayi bakinmu da hannayenmu musamman a wajen comments ɗin nan na social media da muke rainawa, dan wlhy babu makawa sai an tambayemu, saboda ko (a) kika rubuta sai Mala'iku sun rubuta suma a littafinki. Abin tashin hankalin wani ma ko wata har abada bazaku taɓa haɗuwa ba a zahirin rayuwa balle ka roƙa gafarar sa, kai wasu ma ba karanta comments ɗin suke ba balle susan dake kin kuma ɗaurama kanki nauyi a banza a wofi dole kuma ki biya bashinsa da ayyukanki ko ke a baki nasu na sharr. Idan kuma ya karanta ɗin kin ƙuntata mata da comments ɗinki ko kin ƙuntata masa har ya kamu da wani ciwo ta sanadinki tofa aiki ya sameki dan sai kin amshi wannan sakamakon koda su ba mutanen kirki bane, balle bamu san tsakanin UBANGIJI da bawansa ba. Wlhy ƴan uwa idan Bamu kula ba muna cikin masifa, dan wayoyin nan dake a hannunmu hummm. Mudai sani bazamu iya biyan bashin zagi, ko aibantawa, ko cin hakkin mutane a ranar gobe kiyama ba, dan yanda muke tunanin lahira ta wuce da sanin mu, UBANGIJI ba abokin wasanmu bane. Hakkin mutane a kanka koda na kallon banza ne ba ƙaramin tashin hankali bane da nauyi mai girma da bazaka iya biyansa a ranar lahira ba. Tsaiwar mala'ikan mutuwa a kanka kawai ya isheka tashin hankali mai girma balle aje ga zare ran😭🙏, amsa tambayoyin kabari😭, kwanciyar kabarin kansa 😭, tsaiwar hisabi, ƙishirwa, zafin rana, karɓar sakamako daga littafinka, haye siraɗi, makomar gaba ɗaya data kasance zaɓi guda biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login