Showing 177001 words to 180000 words out of 218311 words

Chapter 60 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

inaga gobe zaki dawo aiki”.
Cike da shagwaɓa ta ce, “Amma kaifa kace sai Monday”.
“Na fasa, idan ba hakaba nima zan zauna gidan sai Monday ɗin mu dawo tare. Dama yanzu ne ya kamata fa na fara nawa angwancin tunda kwanakin duk sun tafi a jiyya”.
Ƙasa-ƙasa cikin raɗa Maanal ta ce, “Yanzun ma jiyyar zaka cigaba da yi dan ban warke ba”.
“Haba Besty kiji tausayina mana, kullum sai dai aita zuwa min cikin barci ana sani wankan dole haba mar'atussaliha”.
Murmushi Maanal tayi, muryarta na fita a maƙoshi ta ce, “To alƙawari banda jin ciwo”.
“Nayi da gudu ma kuwa zan bi a hankali My Everbloom”.
“To ka dawo da wuri”.
Ta faɗa cikin raɗa sosai. Tana gama faɗar kuma ƙitt ta yanke kiran, tama kashe wayar gaba ɗaya tana murmushi. Dan inba haka tai masa ba bazai yi aikin ba. Haka jiya kaɗan-kaɗan ya kirata har Oum ta ganosu ta ce, “Anya yau Auta zai yi aikin arziƙi a office ɗin nan kuwa”. Aiko tunda ta tashi ta gudu bata dake dawowa sashen Oum ɗin ba sai yanzu....

_________★


KADUNA


A KD kam dukan labarin shagalin biki yaje kunnen Hajiya Yaya tas. Da yake bata koma ba tun zuwan datai gidan randa Yaya Yazeed ya daki su Nusaiba. Daddy yayi niyyar sake fatattakata Ammie ta dinga roƙonsa harda kukanta. Dole ya ƙyaleta amma fa ko sau ɗaya bai nuna yasan tana gidan ba. Ita kuma girman kai ya hanata zuwa inda yake acewarta ma su zuba. Sai dai maimakon su zuba da Daddyn sai suka zuba da ɗanta Yazeed. Dan kuwa dai da gaske kan Yaya Yazeed ɗin ya juye gaba ɗaya. Babu wanda yake ji da gani sai Nazeerah da iyayenta. Kai tunda ma Hajiya Yaya ta dawo gidan bai leƙa sashen nata ba. Sai dai ta hangesa ya fito zai shiga mota ko ya dawo zai shiga sashensu. Ta aika a kira mata shi Nazeerar ta kore ƴar aiken. Hajiya Yayan taje sashen da kanta bugawar duniya Nazeefa taƙi ta buɗe mata kuma Yazeed ɗin na zaune a falo yana jinsu, aiko ranar harda kukanta, shine taje ta kai ma Babanta ƙara. Babban ya kira Yazeed amma sai cayay masa shi yamayi tafiya baya gari. Hajiya Yaya tace ƙarya yake. Baba yace to shi mizai yi kuma tunda yace baya nan. Haka dole ta dawo gida tana kukan zuci mamakin Sabuwa na girgizata. Dan yanzu kota kirata bata ɗaga mata waya itama, taje gidan ance basa nan ita da mijin. Shima kuma Yazeed ɗin ana saura kwana biyar salla yara sukazo suna sanar mata gashi can shi da Nazeefa sun shiga mota sun bar gidan harda akwati alamar tafiya zasuyi. Daga wannan fita ce har yanzu babu Yazeed ɗin babu matar tasa ga shi har sati uku kenan dayin salla. Ta gwada kiran shi a waya bata shiga alamar ma ƙasar suka bari.
Hakan kuwa akai Yazeed da Nazeefa basa Nigeria, sun fita hutawa shida surukansa, hakan kuma duk a cikin shirin mijin Sabuwa ne zai fara aiki akan Daddy. Zancen biki ma Sabuwa ce ta sanarma Nazeefa, sai kuma ranar taga Yazeed ɗin na kallo a waya shine ta kunnashi da cewar tana son ya bata no ɗin Maanal shi kuma ya tashi ya bar mata wajen gaba ɗaya...

Itama dai Hajiya Yaya labarin biki kaf yaje kunneta a bakin ƴaƴanta. Duk da cike da hassada yaran ke bata labari basu rage mata komai ba. Aiko ta girgiza, abin kuma ya tsaya mata a zuciya sosai har ya nema gagararta barci. Washe gari ta tashi da wannan ɓacin ran sai kuma ga Hajiya Basariyya an dawo da ita. Kawu Manu da kansa ya maidota, ta rame sosai tayi baƙi kamar ba Hajiya Basariyya ƴar gaye ba. Su kansu yaran tambayarta suka dinga yi tayi rashin lafiya ne. Tunda ta dawo yanda bata kula kowa ba itama Hajiya Yayan bata kulata ba. Ammie kam bata nan ita da su Waleed Daddy ya kwashesu sun ma bar ƙasar kwannansu biyar kenan.
Itama dai Hajiya Basariyya ko hutawa bata gama yi ba yaranta suka shiga bata labarin bikin Maanal. Wani irin ƙuna ta dinga ji a zuciyarta, daga ƙarshe ta daka musu tsawa alamar su barta bata buƙatar ji. Dole sukai shiru kuwa. Ranta a ɓace ta korosu daga bedroom ɗin nata dan dama duk suna zagaye da ita ne acan. Wayarta ta cire daga caji data sanya ta shiga kiran layin Huznah. Amma switch off. Shiru kawai tai abin duniya ya isheta. Sai kuma ta tashi ta hau gyaran jikinta dan ita kanta ƙyanƙyamin kanta take balle wani. Sauƙinta ma Daddyn baya gida balle ya ganta ta koma kamar bola, duk da dai taji zafin jin wai basa ƙasar shi da Ammie da ƴaƴanta. Gefe ga yaran sun ƙara mata wani ɓacin ran da labarin bikin Maanal. Aiko sai haɗiyar zuciya take tana fesarwa cikin ƙunar rai.....


_________★


KANO


A ɓangaren Huznah tunda taga shagalin bikin AA da Maanal a wayar Khadijah jikinta ya sake rikicewa. Da farko bata san abinda ke faruwa ba tunda ba wayace da ita ba. Tsautsayi a washe garin dinner ɗin su AA Sageer ya kaita gidansu dan ta yini, saboda da salla bai barta taje ko ina ba. Ganin kwana biyu laulayin ya ɗaga mata sai ta bashi tausayi da zaman kaɗaicin yace ta shirya ya kaita can ta yini. Ashe rabon ta ganoma kanta abinda zai dameta. Aiko ta tarar Khadijah na kallon shagalin biki a TikTok. Ita Khadijah batare data san akwai wata alaƙa tsakanin Huznah da AA ba ta shiga bata labari. Huznah sai taji kawai tana son ganin bikin tace ta bata ga gani, Khadijah tace ai datan ta ya ƙare. Dubu ɗaya Huznah ta bata tace taje ta sanyo, aiko cike da murna ta amsa taje ta sako ta bama Huznah waya.
Ai tunda taci karo da fuskar AA da Maanal shike nan. Bata ƙarasa ma kallon video ɗin ba ta yarda wayar, bayin gidan ta shiga taci kukanta ta fito. Sai tai kamar amai tayo. Haka dai tai wannan yini babu daɗi, ƙagara ma tayi dare yayi yazo su tafi gida. Tun ranar laulayinta ya dawo sabo fil, ƙarshe dai sai da aka kwantar da ita asibiti. Yau kwana biyu kenan da sallamota.....


________★


Kamar jiya yau ma Maanal ta hana Oum yin komai, ita tayi girki tsaf su Inte suka shirya a table. Dan yanzu shima Babban Yaya ya dawo nan cin abinci. Suma su Naufal anan suke gun Oum ɗin. Maanal ɗin ce ma taje ta ɗakkosu a school jiya. Yau ma tana ganin biyar tayi ta ɗauka key ɗin motar Oum dan nata sai an kaisu service. Tare da Inte da tace zata rakata suka tafi. Babu jimawa sai gasu sun dawo. Kusan dai-dai lokacin shima AA ya shigo gidan, amma ya rigasu dan Maanal na shigowa da mota ciki shi kuma yana fitowa.
Ganin motar Oum ya sashi dakatawa da mamakin ina Oum ɗin taje haka da yamma. Fitowar Anum da gudu ya sashi gane Maanal ce, kai tsaye wajensa yarinyar tayi cike da farin ciki. Shima sai ya ɗauketa ya ɗaga sama yana murmushi da faɗin, “Oh oh Oumna ta dawo school”.
Shima Naufal AA ɗin ya nufa ya rungume, dai-dai nan Maanal ta fito itama idonta a kansu. Gira ya ɗan ɗage mata ita kuma tai murmushi. Koda ta iso inda suke tana masa sannu da zuwa sai yay mata nuni da ido tazo. Bata musa ba ta matsa, ya wani matsota ya haɗa ita da yaran ya rungume. Cikin kunneta ya raɗa mata, “In sha ALLAHU nan da 5years haka zan dinga haɗaku ke da yara ina rungumewa”.
Murmushi tayi tare da ɗan mintsininsa zata fita a jikinsa ya hana hakan, sai da ya bata wani ɗan sumba a kan wuya yanda yaran bazasu lura ba, da mata raɗa ya ce, “Ina taya kaina murna yau a angona nake”. Harararsa Maanal ta ɗanyi da matsawa yanzu kam dan karma wani ya fito ya gansu. Sai dai bama ta sani ba komai da suke a idon Nibras ne, hakama ma Saheeba dake dakon jiran dawowar Babban Yaya tana a barandar sashen Mamy ita da Nuratu da itama taga komai. Yana ɗauke da Anum ya riƙo hannunta cikin nashi suka nufi sashen Oum. Naufal kuma na ɗauke da ledan tsarabar da AA ɗin yay musu dan kayan sunma Inte yawa ta kwashi school bags nasu da lunch box.
Yanda yake murza mata hannu yasa ta kallesa, shima kallon nata yayi cikin lumshe idanu da buɗewa. A saman lips ya furta, “Hannunki yana da sanyi mai nutsar da raina. Ina jin kariya da salama idan kina kusa da ni. Zan so naita riƙe hannunki a haka har abada Besty”. Abinda ta gani kwance cikin idanun nasa yasa ta kauda kanta kawai tana murmushi. Shi ko ya ɗan cije lips da sake lumshe idanu da buɗewa. Suna shigowa main falo ta hanga Oum ta cire hannunta a cikin nasa, bai hanata ba dan duk rashin ta idonsa baiyi a gaban Oum. Barsu dai suyi ɗan faɗansu da tsokanar juna shi da Maanal ɗin shike nan.
Oum kam sarai ta gansu amma ta basar, tama maida hankalinta ama su Naufal oyoyo. Suko sun zagayeta, yaran na matuƙar ƙaunar Oum, ana hanasu zuwa inda take ne kawai dan basu da yanda zasuyi. Dan sam ba ƙaunar zama sashen Mamy suke ba. Amma uwarsu ta kafa musu sharaɗin sai can kawai. Shiyyasa yanzu da suka dawo sashen Oum ɗin wani kalar daɗi suke ji ko neman uwar kuwa basayi ma sam...........✍️


Wa yaga tufƙa da warwara Mamy. Kina ƙoƙarin janye wasu, wasu na karuwa, shifa kyakkyawan hali zanen dutse🥰🥰🥰❤️


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖8️⃣8️⃣




______________


.........Kusa da Oum AA ya zauna, ya saka kansa a kafarta yana faɗin, “Haba Oum ki ƙyale jikokin nan naki kiyi ta ɗanki”.
Cike da tsokana Maanal dake wucewa kitchen ɗauka masa ruwa ta ce, “Jealousy”. Harrarta yay yana ɗaukar pillow kamar zai wulla mata ta masa gwalo ta shige kitchen da sauri”.
Pillow ɗin ya ajiye yana cije lips alamar zan kamaki, Oum dake murmushi ta shafa kansa. Hannun data shafa masa kan ya kama ya sumbata. Sai kuma cikin ɗan damuwa ya ce, “Oum wai yaushe Abah zai dawo ne? Nifa idan ina gida nafi son naita ganin duk kowa na nan”.
Oum da itama take cikin damuwar tafiyar Aban dan cikin fushi suka rabu akan ƙin zuwa duba Mamy asibiti da yay, tambayar duniya kuma yaƙi gaya mata mike faruwa. Amma bata bar su AA ɗin sun san hakan ba, cike da kulawa ta ce, “Maybe cikin satin nan dai, baƙwa waya ne?”.
“Munayi, kawai dai na tambaya ne. Dan dana tambayesa jiya cayay min yana da uziri sosai”.
Murmushi Oum tayi, kafin tace wani abu Maanal ta ƙaraso da ruwa a tray, a gaban AA ta ajiye, dan haka ya tashi daga kwantar da kansan da yay a kafaɗar Oum ya zauna sosai. Ruwan data zuba masan ya amsa yasha ya miƙa mata kofin yana wani binta da kallon ƙasan ido. Maanal dake basarwa saboda idon Oum ta ce, “Abinci fa?”.
Mikewa yay yana faɗin, “No zan fara wanka, sai ma anyi magrib cin abincin gaba ɗaya yafi daɗi. Oum bari naje sai na dawo”.
“To Auta a dawo lafiya”.
Sai da ya fita da fin mintuna biyar sannan Maanal ta tashi itama. Ruwan da ya sha ta ɗauke ta maida kitchen, ta can tabi ta ƙofar baya ta gudu. Dama jiya haka tayi, aiko mi Oum zatai ba dariya ba. Dan ma ta tabbatar Inte ta kira, koda ta fito cemata tai, “Ina Baby?”.
Inte dake ƴar dariya ta ce, “Oum ta fita ta back door”. Itama Oum dariyar tayi, tace “Ja'ira”. Inte dai ta koma ciki tana cigaba da dariyarta. Yanda Maanal ɗin keyi daɗi yakema Oum, dan ta fahimci Autanta zai samu irin kulawar da magidanci ya kamata ya samu ga iyalansa ba irin matan su Fawzan ba. Wannan shine babban dalilinta na ɗora Hajiya Shuwa akan gyara Maanal ɗin dama. Dan bata son Babynta tai rayuwa irin tasu Saheeba sam.....


★Tuni Maanal ta shiga sashensu dan tasan AA na sashen Mamy dubata. Bedroom ta wuce dan haɗa masa ruwan wanka. Ta shagala a haɗa masa turarurrukan ƙamshi a ruwan ya shigo batare da taji motsi ba ma. Sai da ta fito ta ganshi tsaye a closet yana zare jacket ɗin suit ɗinsa. Kallonsa tai ta ɗauke kanta, zata wucesa ya riƙo mata hannu. A slowly ya maidota baya ya jingina da glass ɗin closet ɗin. Shima ya matsa jikinta sosai ya dafa glass ɗin da hannunsa ɗaya.
Fuskarsa ya sauke a hankali a gefen wuyanta, yanda yake busa mata numfashi da manna ma wuyan tagwayen kisses ya saka tsigar jikinta tashi, cikin wata irin kasalliyar murya a cikin raɗa ya ce, “I miss you my heart”.
Motsawa tai ta shige jikinsa, tare da zagaye duka hannayenta a bayansa kanta na kwance a ƙirjinsa. Shima sai kawai ya rungumetan yana sauke ajiyar zuciya. “Rungumarki tafi laushin katifa, laushin jikinki ni'ima ce mai sauke gajiya da nauyin jikina. Hakan tamkar kwantar da tarnaƙin dake zagaye da ni ne, dan kin saka jikina na min magana fiye da kalmomina. Zan so kiyita kasancewa a cikinsa na har abada, hakan a gare ni gata ne da riritawa”.
Itama cikin raɗa ta ce, “I miss You you too My Root-Soul! Nima idan har nayi ko awa ɗaya batare da kai ba duniyata bata da tushe ko kwanciyar hankali. Dauriya kawai nake yi saboda Ina ganinka a kowanne murmushi na, domin kaine ka shuka shi.”
A hankali ya wani busa mata iska cikin kunne, tare da raɗa mata, “Zan cigaba da ajiye wannan murmushin kuwa na har abada in sha ALLAHU akan ƙyaƙyawar fuskar nan taki”.
Ƙanƙamesa ta sakeyi sosai tana jin kamar ta tsagashi biyu ta shige cikin jikinsa kawai. Shima dai hakan yake ji a ransa. Sun fi minti uku a haka kafin ya cirota daga jikin nasa ya riƙe fuskarta a cikin tafukan hannunsa suna kallon juna. Sosai take karantar ruɗaɗɗen al'amarin dake a cikin ƙwayoyin idanunsa, kamar yanda shi kuma yake karanto tsoro da fargaba mai haɗe da sallamawa a garesa. Lallausan murmushin kwantar da hankali ya sakar mata. Muryarsa na sake komawa cikin maƙoshi ya ce, “Mizan samu?”.
Akan lips ta bashi amsa da, “Komai ma”.
Ya ɗage gira sama tare da taɓe baki a yanayin murmushi yana jinjina mata kai irin na (kin tabbatar?). Ido ɗaya ta kashe masa alamar (Yes) sai kuma tai ɗiɗɗishe da ƙafafunta kasancewar ya fita tsaho sosai ta zare gilashin idanunsa, hannayenta gaba ɗaya ta zagayo akan wuyansa ta matsar da fuskarta gab da tashi har suna zuƙar numfashin juna. Sai kuma ta lumshe idanunta cike da jin nauyi da kunya. Shi dai kallonta kawai yake kamar ya samu television. Idanun nata a lumshe ta ɗaura lips ɗinta akan nashi ta sumbata. Tana ƙoƙarin janyewa ya hana hakan ta hanyar riƙo kanta kawai ya kamo lips ɗin nata da ƙyau ya tura cikin bakinsa. Da jikin closet ɗin ya mannata, sai kuma ya kamata ya ɗaga cak a jikinsa, tako harɗe ƙafafunta a bayansa kamar yanda ta harɗe hannayenta...
A haka ya dinga tafiya da ita har cikin bayin, bai kuma tsaya ba har sai da ya tsaya dasu ƙasan shower, kawai ya sakar musu ruwa mai ɗumi a jiki. A tare suka sauke ajiyar zuciya, ya kuma cigaba da yin yanda yaso da lips ɗinta. Kafin ya saki da ƙyar ya shiga rabasu da kayansu. Daga haka ya sake ɗaukarta ya fito a wajen wankan suka shige jacuzzi. Anan ne fa ya fara tabbatar mata ta tsokalo ƴan samari, dan sai da idannunta suka fara raina fata ganin zai ɗauki wani sabon layin. Ta fara roƙo da magiya da son kuɓutar da kanta. Shi ko ya nuna mata a wannan fannin bai san wasa ba, bai san ɗanɗani haukaci ba. ALLAH dai ya taimaketa akai kiran sallar magrib, amma data gayawa mutanen Giro kam. A gurguje suka ƙarasa wankan suka fito, ta taimaka masa da shafa mai da saka kaya kamar yanda ya buƙata, da ɗan hanzari ya sumbaci goshinta ya fice dan sallar ake ƙoƙarin tayarwa.
Yana gama fita ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma tai murmushi, dan ita da kanta bama kanta dariya take. Itafa komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login