Showing 45001 words to 48000 words out of 218311 words
Chapter 16 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
kusan bakwai kenan abubuwa suka rikice a tsakaninsu shine kawai ta tattara ta wuce marocco sai jiya ne take dawowa, bata nan akai bikin su AA ɗin, sai bayan wucewarsu aiki ta shigo shine suketa hira da Oum ɗin dan ƙawaye ne sosai...
Baƙi da aka kira Hajiya Shuwa a waya cewar tayi ya sata tafiya gida, sai lokacin Maanal ta fito falon, tayi wanka abinta fes sai ƙamshi take. Takardar da aka basu a wajen aiki ta bama Oum ɗin, tare da zama gefenta ta ɗaura kanta a kafaɗarta. Shafa kan nata Oum tayi tana murmushi, cike da kulawa ta ce, “Ko azumin ya fara duka?”.
Shaf Maanal ta manta da ƙaryar azuminta, ta kalla Oum tana dariya. “Lah Oum ƙarya fa nayi dama babu wani azumi ɗazun ban son karyawa ne kawai”.
Idanu Oum ta zaro waje, sai kuma ta dungure kan Maanal ɗin tana dariya itama. “ALLAH ya shirya kin Baby na to da har yanzu bata canja hali ba”. Dariya itama Maanal tayi, tare da ɓoye fiskarta a jikin Oum ɗin. Itama Oum na cigaba da dariyarta ta ce, “To aiko tare zamu shiga kitchen yanzun nan idan munyi sallar zuhur”.
Haka ɗin kuwa akai, bayan Oum ta kammala duba takardun ta riƙe a hannunta akan zata nunama Abah, duk da dama ta masa bayani akan tafiyar amma bai ce mata komai ba. Salla suka je sukayi, koda suka fito kai tsaye kitchen suka nufa, sun fara aikin kenan Mamy da Hajiya Turai da Nurry suka shigo sashen. Oum ce kawai ta fita suka gaisa, basu wani jima ba Hajiya Turai tace bara ta wuce tunda taga Oum ɗin aiki suke itama zataje wani waje ne. Godiya Oum tai mata, sunzo zasu fita Maanal ta fito ta gaishesu. Tana kallon hararrata da Nurry take bata kula ba ta koma kitchen ɗin abunta. Sai da zasu fita Mamy ke faɗin, “Lafiya ƴarki ta dawo aiki da wuri haka yau?”.
“Lafiya Lau, daga office ɗin ne aka basu damar zuwa suyi shirin tafiya ne”.
Sai Mamy ta rasa ina zata kamo zancen tafiya kuma. Amma bata nema ba'asi ba dan tana son su fita su ƙarasa zancensu da suke da Hajiya Turai. Ba kuma tason ma Hajiya Turai ta fahimci bata san da zancen da Oum ɗin keyi ba dan yanzu ta gama cika mata baki akan batun dawowar Maanal a taxi. Ta nuna itace ta kafa sharaɗin sai dai Maanal ta hau taxi amma ba motocin gidan ba, shiyyasa sukaga hakan. (Mamy an iya ƙayya🤣🙏)
Tsulum Nuratu taja ta tsaya tana faɗin, “Momy bye nima zan zauna taya Oum girki, bara naje wajen sis.. Manaal ɗin”. Daga haka ta juya ciki ta nufi kitchen tabar su Oum na murmushi. Duk da dai abinda Nuratun tayi ya bama Mamy takaici, amma sai ta danne... Maanal na cikin aikinta ita da su Inte dake musu ƴan yanke-yanke a work table Nurry ɗin ta shigo. Ko kallon inda take Maanal batai ba, sai su Inte ne ke gaisheta a girmamame, itako tana amsa musu a yamutse. Sun riga sun san halinta shiyyasa basu wani damu ba. Dai-dai nan Oum ta dawo, dan haka Nuratu ta nufi wajen Maanal cike da makirci tana faɗin, “Sis.. Maanal mizan tayaki da shi?”.
Wani shegen murmushi kawai Maanal ta saki tana kallon Nurry ɗin a tsakkiyar ido, a zuciyarta faɗi take, (Yarinya ai indai makirci ne baki yar a ƙasa ba, idan kuma kikace ni dake ta haka zamu buga wasan ƙasa zaki sha kuwa a hannuna). A fili kam maimakon bata amsa fruits da za'a gyara ta nuna mata da hannu fiskarta da murmushin har yanzu. Oum data ƙaraso inda Maanal ɗin take ta ce, “Yauwa gyara su kam Nuratu, sai a gama da wuri dan yau nasan Auta a jigace zai dawo gidan nan ba'a aika abincin rana ba hira da Hajiya Shuwa ta ɗauke min hankali”.........✍️
_Hhhhh gaskiya Maanal baki ƙyauta ba, ya zaki bama Nurry ɗinmu gyaran fruits 🤣🤣_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣2️⃣
______________
........Matuƙar tiƙe Nuratu takaici yayi, amma bata da damar cewa bazatai ba tunda itace ta kawo kanta. Sannan duk iskancin nan nata mugun shakkar Oum take ji, sosai matar na mata bala'in kwarjini, ga son da kowa yasan AA na mata tana son tai kamun ƙafa da ita. Kai bama ita ba, ko iyayen nata kan faɗi irin cika musu idon da Oum ɗin keyi, dan duk yanda suka shirya tunkararta da rashin mutunci suna yin arba da ita komai ke ƙwace musu. Cike da son ƙular da Nurry Maanal ta shiga yima Oum hira suna dariya. Aiki sosai Nuratu ta shaƙa, dan ji ta dingayi kamar ta juya ta caka ma Maanal wuƙar hannun nata.
Sunata aikinsu da hira, dan Maanal ma dai ke girkin Oum hira kawai take tayata, Nurry kuma anata aikin gyara fruits da take yi cikin takaici shiyyasa bata wani sauri, koda yake ba aikin ta iya ba dan bayi take ba sam. A gida komai masu aiki ne ke mata shi, idan iskancinta na ka ma hatta underwears ɗinta basu take su wanke sai tace matching baya wankewa da ƙyau. Su Inte dai sun gama sun gyara wajen sun fita suna gyaran falo da saka ƙamshi. Dai-dai nan AA ya shigo da sallama. Da sauri Nurry ta juya har tana neman yankewa da wuƙa, sai Oum da itama ta juya tana masa murmushi. Maanal kam tamkar batana san mike faruwa ba aikinta kawai take yi.
“Lallai yau Auta ne da tashi a office ko five baiyi ba ma?”. Oum ta faɗa tana miƙa masa ruwan data tsiyaya masa a cup. Amsar ruwan yayi, tare da jan kujerar work table ɗaya ya zauna. A kasalance ya janye idanunsa dake akan ƙullin da Maanal tai ta bayanta na rigar girki dake jikinta. Kamar wanda baya so ya ce, “Oum na gaji ne ALLAH shiyyasa na gudo”.
Murmushi kawai Oum ɗin tayi, dan tasan ba hakan bane ba, ta tabbata dan Maanal ta dawo ne. Cike da ɗan rawar murya Nuratu data tsaresa da kallo ta shiga gaisheshi. Ikon ALLAH, to shifa sai yanzu ma yasan akwai wani a kitchen ɗin bayan Oum ɗinsa da Maanal. Waiwayowa yay ya kalleta, sai kuma ya ɗauke idanun a taƙaice ya amsa, cikin kuma halin ko'in kular nan nasa kai kace baima gane Nuratun ba. Oum da bataji daɗin yanda yayma Nuratun ba tace, “Nuratu ce fa baka ganeta ba ne Auta?”.
“Na ganeta mana Oum! Nifa yunwa nake ji”.
Sarai Oum ta fahimci zancen Nuratun yake so a kawar, dan haka ta girgiza kai kawai da juyawa ta kalla Maanal dake ta aikinta. Juyowa tai ta kalla AA kuma, sai taga ya zubama Maanal ɗin ido ne a kaikaice. A take Oum ta fahimci akwai abinda ke faruwa a tsakaninsu, dan da wuri take gane idan sunyi faɗan nasu. Nan ma kanta ta ɗan girgiza, batare da tace komai ba ta buɗe ƙaton freight ɗin kitchen ɗin ta fiddo kwalin fresh milk, a gabansa ta ajiye tana faɗin, “Fara da wannan ga Baby nan na mana girki an kusa kamallawa”.
Idanu ya waro waje, “Kai Oum ana dai mana jagwalgwalo, miyasa baki mana da kanki ba?”.
Dariya Oum tayi, ta nufi hanyar fita tana ƙoƙarin ɗaga wayarta dake ring, ta ce, “Oh jagwalgwalo ko? Babyn ce ke jagwalgwalo! ALLAH yasa ta hanaka abincin nan mu gani”. Ta fice batare data jira mizai ce ba. Shima bai ce komai ba, sai ma ajiye kofin fresh milk ɗin daya ɗauka zai fara sha yay ya miƙe. Nuratu da gaba ɗaya jikinta ke wani irin tsuma, tana jin kamar ta daka tsalle ta rungumesa take ji ta bisa da kallo, duk da tun kwalliyar safe ce a jikinsa yama cire jacket ɗin samna suit ɗin sai fara tas ɗin long sleeve shirt dinsa dake clean harda karin gugarta kamar yanzu ya sakata wani irin ƙyau yay mata, ga ƙamshinsa mai saka kasala na tashi kamar a yanzu ne ya saka turaren.
AA kam ko kallon inda take baiyi ba, hankalinsa kwance, kansa kuma tsaye ya ƙarasa inda Maanal take ya tsaya dab da ita. Ita ko da yake ta juya masa baya bama tasan da zuwansa wajen ba, tadai ji yawaitar ƙamshin turarensa sosai. Hannayensa duka biyu ya zagaya a saman cikinta ya rungumota, tare da ɗora kansa a wuyanta duk a lokaci guda. Harga ALLAH tsorata tayi, dan haka tai wata ƴar zabura tana ƙoƙarin juyowa. Amma sai ya sake riƙeta da ƙyau ta yanda hakan ya gaggareta.
“Ni kika wulaƙanta kika tawo a taxi ko? Ki saurari hukuncina dan sai na saɓa miki”. Ya faɗa a cikin kunnenta cike da isa babu alamar wasa a furucinsa. Amma irinsu Nuratu dake a gefe sai su ɗauka wata maganar soyayya yay mata a kunnen, dan daya gama faɗa harda su manna mata ƙaramar sumba a kan wuya ya ƙara faɗin, “Ai dama kinfi kama da Kukun”.
Haushi ya saka Maanal ɗaga ludayin hannunta kamar zata ƙwala masa saboda yace tafi kama da kuku. Sakinta yay yaja baya yana murmushin ƙeta na cin nasarar ƙular da ita, dai-dai ta juyo gaba ɗaya yay mata gwalo kuwa, zaburowa tai kansa da ludayin. Aiko da ɗan gudu ya ɗauka fresh milk ɗinsa ya fice a kitchen ɗin yana dariyar data saka Nurry yin sumar tsaye dan mamakinsa da al'ajabi da yanda dariyar tasa tai bala'i bala'in tafiya da imaninta. Dan zata iya rantsewa bata taɓa ganin yana dariya kamar haka ba a rayuwar sanin datai masa kaf. Bawai yana ƙyaƙyalƙyalawa bane sosai a yanzun ma, amma illahirin haƙwaransa sun bayyana a waje. Oum dake shigowa itama tana dariyar yanda AA ɗin ya fito a kitchen ɗin da ɗan gudu ce ta riƙe ludayin Maanal, tana dariya ta ce, “Amasa haƙuri babyna bazai ƙara ba”.
Cike da shagwaɓa Maanal ta ce, “Oum gwalo fa ya min, yace nafi dacewa da kuku, kinga yana sake yimin gwalon ko”. Tai maganar tana nuna bayan Oum da AA yake tsaye daga can waje. Juyowa Oum tai ta kallesa itama, sai ya haɗe fuskar kamar bashi ke yin tsokanar ba. Oum data tabbatar yayi ɗin ta ce, “Okay na bari ta kwale ka ko”.
“Tadai fasan kai Oum, kuma dan ALLAH kinga na kulata tunda na shigo?”.
“To ya zan sani tunda fita nayi, sai dai a tambayi Nuratu.” Oum ta faɗa. Maanal ce ta amshe da faɗin, “ALLAH Oum yayi, kuma a tambayi Nuratun ma ai tana ganinsa”.
Ai kafin ma Nuratu da takaici ya kume tsigar jikinta har wani tashi take yi tayi magana ya sake ma Maanal gwalo yabar wajen. Karaf kuwa a idon Oum. Salati Oum ta ɗauka da faɗin, “ALLAH ya shiryaka Auta ka daina tsokalar min yarinya kaikuwa. Sai kuma ta kama hannun Maanal, kinga manta da shi zaki rama ne, badai zai dawo cin abinci ba taron dangi zamu masa harda Fawzan in ya dawo”. Daga haka suka koma Oum ta tayata suka ƙarasa girkin aka bar Nuratu da takaici. Gashi babu damar barin kitchen ɗin kuma. Dole ta haƙura suka kammala ikin duka suka shirya a dining sannan suka tafi salla. Sanin AA nan zai dawo yasa ta maƙale abinta, acewarta sai ta sake ɗaura ɗammara na maganin Maanal ɗin, hakan kuma bazai faru ba sai ta nutsu ta fahimceta....
________★
Shagali sosai aka sha a gidan Sen.. Bukar, sai dai shi gaba ɗaya hankalinsa nakan Rabilu ne dan ya fahimci akwai magana a bakinsa. Duk kuma yanda yaso su kebe da Rabilun hakan ya gagara, dan uwargida yau tayi masa kane-kane. Kuma tsaf ta fahimci inda hankalin nasa yake dan haka taita dariya a ranta. Zuwa yanzu babu abinda bata sani ba game da Maanal. Tun sanda mijin nata ya kawo mata batun ƙara auren nasa ta shiga bincike da bibiyarsa har sai da ta gano akan wadda yake rawar ƙafar. Da farko ta shirya tsaf domin nakasa rayuwar Maanal ɗin, dan ta ɗaukama kanta alwashi wata bazata sake shigo mata gidan miji ba, wanda suke a cikin ma tana shirin ficewarsu ne. Sai kuma UBANGIJI mai hikima ya nuna mata ikonsa rana tsaka ta samu labarin auren Maanal ɗin da AA Darma, yaron data taɓa ji a bakin mijin nata yana aibantawa da ɗaukar alwashin wulakanta rayuwarsa saboda yafi su kusanci da shugaba ƙasan. Dariya sosai sukaci ita da ƙawayenta masu ɗaurata a hanya, dan ita babu abinda ya dame ta da wata matsalar mijinta da AA Darma, ita AA Darma ma ya biyata a yanzu tunda ya ɗauke Maanal. Farin cikin wannan aure yasa ta shirya wannan liyafar ta Anaversary ɗinsu, abinda bata taɓa yi ba kuwa. Shi kansa Sen yayi mamaki, amma sai shanye a ransa yana faɗin (Hakan dai bazai hana ƴar shilata Maanal shigowa ba).
Bayan an gama shagali yanda ta kanainaye shi dole ya haƙura, dan ya ma nema Rabilu ya rasa. Bai san ita ta kora Rabilun ba dan dama ta mugun tsanarsa saboda tasan shine mai nema masa matan auren kuma kawalinsa na matan banza. Ta jima da son rabasu sai dai hakan ya gagara....
“Sen... Namu”. (ALLAH sarki Uncle ɗina KA BARI YA HUCE MAI RABON YA ƊAUKE🤣)
__________★
Daga sashen Oum AA sashen Mamy ya nufa domin gaisheta, dan ƙa'idarsa ce yin haka daga shi har ƴan uwansa. Da safe zasu shiga su gaisheta, hakama idan sun dawo aiki, sai dai da wahala kaga sunyi zaman mintina ashirin a wajen nata. Saboda tun farko bata jasu a jikinta ba, ita a dole tanama Oum kawaici. Wanda sai daga baya AA ɗin ya fahimci ba hakan bane ba...
Zaune ya sameta a falo Haule na gyara mata ƙumba suna kallo, glass bowl ne a gabanta tana shan fruits da aka yanka ƙanana a ciki. Cike take taf da haushin zaman Nuratu a sashen Oum. Da sauri Haule ta shiga gaisheshi. Batare daya kalleta ba ya amsa ciki-ciki yana kaiwa zaune a kujerar kusa da Mamyn, ganin yanda taketa faman ɓata fuska ya sashi yin murmushi a zuciyarsa. Shi wlhy wani lokacin yanda ta saka kanta a ƙunci babu gaira babu sabar tausayi take bashi. Da ace zata ajiye makanamta dai zata kasance cikin farin ciki ne da nishaɗi ta kuma samesu fiye da yanda take so su da take faɗan a kansu. A hankali ya matsar da jikinsa kusa da ita gab, batare da yayi magana ba ta zare spoon ɗin dake hannun nata ya ɗauka yanka ɗaya na apple ya kai mata baki. Ƙuri tai tana kallonsa kamar wadda ta suma. Domin abune da bai taɓa kwatanta yimata ba sai dai taga yanama Oum. Shi kuma ya ɗauka aniyane a ransa na canja salon mu'amularsu ko hakan zai sassauta zuciyarta ta ajiye makaman yaƙinta akan Oum, dan baya fatan wani a gidan ya fahimci halayyar nan ta Mamy. Ganin yanda take kallon nasa tamkar hawaye na son taruwa mata a ido ya sashi jinjina mata nasa kan tare da sakar mata murmushi mai sanyi, sai kuma ya ɗan buɗe bakinsa alamar (haa). Kamar sakarai a hankali ta buɗe lips ɗinta kuwa ya saka mata yankam apple ɗin, ta shiga taunawa tana kallon nashi. Sai ta samu kanta itama da amsar spoon ɗin ta ɗauka kankana ta bashi. Babu musu ya amsa yana mata murmushi, kafin ƙasa-ƙasa ya furta,.....✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣3️⃣
______________
.........“Jazakhallahu khairan Amaryar Abah, aminiyar Oum, Maman Fadeel da Fawzan da Auta Ajwaad”.
Yanda ya jero kalaman nasa masu kama da kirari ya sata sakin murmushi a bazata, sai kuma a hankali takai hannunta ta shafa kwantaccen gashin fuska tana sakin murmushi mai haɗe da ƴar dariya. Samun kansa yay shima da yin dariya, ya kama hannun nata ya sumbata. Ji Mamy tai tamkar zuciyarta na ɓaɓɓarewa gida biyu, cike da shauƙi mai girma ta sake kai hannun nata saman sumar kansa ta barbaza. Nan ma dariyar yay mata. Tare da faɗin, “Thanks you Mamy. Dan ALLAH ki daina damuwa akan komai, nafi son kullum nazo naga fuskarki cikin farin ciki. Na tabbata kuma idan kika ajiye komai zaki