Showing 159001 words to 162000 words out of 218311 words
Chapter 54 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
shiga duba Manaal amma ta ɓoye fuska a barko taƙi yarda ta kalla Oum, shine ta fito ta barsu ta dawo wajen Umma. Sai kuma ga RK shima ya fito daga ɗakin AA. Duk kallon Mariya dake gaishe da Umma sukai. Batare da damuwa ba RK daya gaisheta fisha shima ya kalla Doctor ya ce, “Ya ake ciki Aunty?”.
Kai Doctor ta jinjina, sai kuma ta kalla Mariya. RK ya fahimta, dan haka ya ce, “Karki damu kiyi bayani nan duk ƴan gida ne kuma iyaye”.
Kanta ta jinjina masa. Ta cigaba da faɗin, “Dole za'ai mata ɗinki gaskiya dan taji ciwo sosai. Gashi har yanzu a firgice take.”
Caraf Mariya ta ce,.........✍️
Na kula Mariyar nan ƴar ɓare-ɓare ce fa😂
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣8️⃣
______________
........“Ciwo kuma, yarinyar daba budurwa ba miyya haɗata da ciwo? Ko ɗinkin nan na zamani taje akai mata?”.
Babu wanda maganarta bata zafeshi ba a cikin su Oum, amma sai babu wanda ya tanka sai doctor da tai murmushi da faɗin, “Wlhy ko ɗaya Hajiya babu wani ɗinki. Hasalima yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce yau aka fara taɓata.”
“Budurwa? Kai likita sake dubawa dai da ƙyau. Ko ana rasa budurci ne ya kuma sake dawowa a karo na biyu? Yarinyar nan fa shekara takwas data wuce an mata fyaɗe”.
Kallonta Oum tai zatai magana rai a ɓace yanzu kam Umma ta riƙe mata hannu ta girgiza mata kai alamar kar tace komai.
Doctor ta ce, “Tabbas Hajiya budurci sau ɗaya yake ga kowacce mace, kuma baya maimaita kansa, duk ma wadda tace zata iya dawo da shi da wani magani ko ɗinki ƙarya take, sai dai tayi abinda za'a mace amma ba dawo da budurci ba. Dan sau ɗaya tak ake yaye wannan tantanin. Dan haka zan sake jaddadawa yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce yau ne karo na farko data fara sanin namiji. Idan kuna kokwanto kuma za'a iya sake kaita asibiti ma ko a kira wasu doctors ɗin su dubata banda haufi akan hakan. Fyaɗen da kuke tunanin kuma an mata gaskiya ku ƙara bincike akwai abinda ya kamata Ku sani”. Daga haka ta juya tana kallon RK. “Doctor zanje na dawo yanzun nan. Amma zaka iya samo ma su Hajiya wasu likitocin su duba yarinyar nan kafin na dawo dan su sami nutsuwa.”
Murmushi RK yay da faɗin, “Karki damu Aunty ni dai na gamsu, iyayena ma nasan sun gamsu in sha ALLAHU. Wanda bai yarda ba sai ya kawo nashi likitan. Amma ko shi ma Ajwaad ɗin a yanayin da yake ciki yau ne karonsa na farko da hakan ta kasance. Sannan da bakinsa ya sanar min Maanal budurwa ce babu abinda ya faru a waccan ranar”.
Wasu irin hawayen farin ciki ne suka silalo a idanun Oum. Ta shiga tuno kalaman AA a randa ta turkeshi akan batun fyaɗen. (Oum dan ALLAH ki bar zancen kawai. Amma ki yafe min. Ki kumayi haƙuri komai daren daɗewa UBANGIJI zai warware komai cikin sauƙi da rahamarsa. Amma a yanzu babu wani bayani da zan yi a fahimta ko a yarda. Abinda kawai na sani shi ALLAH baya barci. Ki tayani da addu'a kawai ALLAH yasa na gano inda su Maanal suke. Wannan shi nafi buƙata a yanzu) Hawaye suka sake ziraro mata. Ita kanta Umma tuna ranar da suka tirke Ajwaad ɗin take. Marukan daya sha wajen Abah da Uncle Mahmoud har sai da fuskar yaron nan ta kumbura da shatin yatsunsu. Amma akai juyin duniya yaƙi cewa komai. Daga ƙarshe ma ya yanke jiki ya faɗi, faɗuwar data zame masa sanadin ciwo na shekara kusan biyu da rabi. To mike faruwa? Ko tace ma miya faru a waccan ranar? Ranar da ranar farin ciki ce da suka taru domin yin shagalin bikin yaran su shida reras. Amma komai ya hargitse ya lalace a sanadin wannan maganar fyaɗe. Mi hakan ke nufi? Miya kamata su sani? Miyasa Ajwaad ya zaɓa yin shiru akan faɗin gaskiya?...
Mariya kam tuni ta fice a sashen jikinta na rawar mazari na gulma. Tamkar wadda aka jeho haka ta faɗo ma su Mamy dan ɗakinta duk suke a yanzu ana dubata. Fuskarta ta kumbura suntum idanun sun shige ciki, hakama ƙafarta ta dama da hannun haggu sun kumbura da alama dai taji ciwo koma karaya kamar yanda doctor ta faɗa, har ma tama wani abokin aikinta daya san harkar ƙashi magana zai zo ya duba Mamyn yanzu. Shayin da likita tace a kawo Mamyn ta sha Haule ta haɗo mata da zafinsa. An bata kenan zata fara sha da hannunta mai lafiya Mariya ta afko, duk kallonta suka juya sunayi harda Haule dake duƙe tana haɗama Mamy ƙwai a cikin bread wai ko zata iya ci dan bakin ma a kumbure yake saboda raunin haɓarta. Hakama goshinta yay wani irin tulluwa. Kai fuskar dai babu ƙyan gani kamar wadda tai haɗarin mota.
Cikin matuƙar fargaba da ƙaulani da su Maman Saheeba ke ciki na jiran sakamako dama ta ce, “Mariya lafiya kuwa?”.
“Uhhhmm!! Lafiya Lau, wani abin mamaki ne ko al'ajabi zan kira shi oho. Wai yarinyar nan matar Ajwaad budurwa ce, babu wani fyaɗe da aka taɓa mata yanzu likita ke faɗa, wannan yaron kuma ƙanin Hajiya Fateema shima yace Ajwaad yace masa babu abinda ya faru a waccan ranar wai.”
“What!!”.
Maman Saheeba, Hajiya Turai, da Saheeba suka faɗa a lokaci guda suna miƙewa tsaye zambar. Yayinda kofin shayin hannun Mamy ya suɓuce shayin ya ƙyalaye mata a jiki gaba ɗaya kuma akwai azabar zafi. Aiko babu shiri ta fasa ƙarar da ta sakaku juyawa kanta gaba ɗaya. Cikin sauri Doctor ta ɗauka gorar ruwan sanyi data gani kusa da Mamy ɗin ta juye mata a jiki. Sai dai ina azabar ta riga ta gama ratsata har wajen fitsarinta saboda a yanda take zaune ƙafa a bubbuɗe...
Haule ma jikinta har rawa yake ta fice. Gaba ɗaya tabar sashen ta nufi can wajen garden ta kira sille a waya.
Harta tsinke bai ɗaga ba, ta sake kira. Tana gab da tsinkewa ya ɗaga yanzu. A fusace ya ce, “Bana faɗa miki zan dawo yau ba. K nifa bana son jaraba dan nasan abinda ya dame ki kenan kiketa son damuna”.
Cikin raunin murya ta ce, “Wlhy ba haka bane Dear, Update ne da ɗumi-ɗuminsa. Wai matar Ajwaad budurwa ce ba'a taɓa mata fyaɗe ba. Yanzu wata ƴar uwarsu ta shigo tana faɗa da'alama daga sashen Ajwaad ɗin take”.
Wata irin mahaukaciyar dariya Sille ya kwashe da ita daga can irin ta ƙeta. Kafin ya ce, “Ajwaad! Ajwaad!! Shegen yaro. Tabbas na yarda ya cini wannan wasan, amma kuma ya jira sabon wasa dan yanzu ne za'a fara tsakanin ni da su. Ƙarfe biyar na yamma kizo gida ki saman zan bada saƙo a isar min da shi cikin gidan..” daga haka ya yanke wayarsa. Kasare Haule tai tana kallon wayar dan babu abinda ta fahimta a zancen nasa. Hasali ma ita har yanzu bata san ainahin abinda ya haɗa AA ɗin da Sillen ba. Kawai dai ya sata ta dinga ɗauka masa rahoton kowa na gidan da motsinsa. Amma har ga ALLAH tana son sanin minene tushe sanadin wannan BASHIN GABAR.....
________★
A ɓanagaren su RK ma tuni Oum ta fito ta nufi sashen Abah duk da tasan akwai su Uncle Mahmud dan anan suke kwana kasancewar akwai ɗakuna wadatattu. A falo ta samesu zaune zasu sha coffee. A yanda Oum ɗin ta shigo duk suka bita da kallo, ita ko babu wani damuwar ganin ƙannen nata a tare da Abah ɗin taje ta rungume Abah ta sakar masa kuka. Sosai hankalin Abah ya tashi, suma su Uncle Mahmud duk suka miƙe nasu hankalin a tashe. Cikin ƙarfin hali Abah daya rungumeta shima ya ce, “Lafiya kuwa Fateema? Ko wani ne ya rasu?”.
Kai ta girgiza masa.
Ya ce, “Rashin lafiya ne?”. Dan yayi zaton zuwa yanzu tasan halin da Mamy ke a ciki. Amma a nan ma sai ta girgiza kanta.
“Gobara ce?”.
Cikin kuka Oum ta ce, “Ajwaad bai yi ma Maanal fyaɗe ba Gadanga, babu abinda ya faru a waccan ranar ashe. Shiyyasa ya ƙi magana akan dukkan tuhumar da kukai masa”.
Shi kansa Abah sai da yaji abu ya tsarga masa. Su Uncle Hussain ma suka shiga kallon kallo. Cikin ƴar rawar Murya Abah yace, “Ban gane komai ba Fateema. Yimin bayani, Please yimin bayani yanda zan fahimta. Taya akai kika gane Ajwaad bai aikata ba?”.
Ɗagowa Oum tai tana share hawayen da ke cigaba da ziraro mata. Babu wani ɓoye-ɓoye ta shiga yi musu bayanin komai daya faru a sashen AA. Aiko Abah sai da yaji shima hawaye sun cika masa nasa idon. Ya tuna yanda ya ringa zubama fuskar AA maruka a waccan ranar masu gigitarwa. Da yanda ya fara jifansa da munanan kalamai sai da Baba Sardauna ya kwaɓesa, ya tuna yanda AA yaƙi magana, ya ƙi musu bayanin komai. Ya tuna wahalar ciwo daya sha na tsawon shekaru har biyu. Ya tuna yanda ya daina shiga sabgar yaron gaba ɗaya duk da yana cikin halin rashin lafiya. Har depression ɗin daya shiga a lokacin da akace a dinga zama da shi shi yace babu mai zaunawa yama haukace sun sallama shi. Haka zaije asibiti ya duba Oum amma ko kallon gadon AA bayayi duk da matsanancin halin da yaron ke a ciki.
Jagwab ya kai zaune abubuwa masu yawa na dawo masa ta yanda ya hora Ajwaad babu tausayawa babu rangwame dan harga ALLAH yaji zafin abin nan ne matuƙa. Ya ji zafin yanda Ajwaad ya lallata Maanal ƴar su ta amana. Su kansu su Uncle Mahmud komai ji sukai ya tsaya musu cak, dan suma dai gwargwadon iko sun taka rawar gani a hora Ajwaad.....
________★
A lokacin da ɓangaririn biyu ke a wancan yanayin anan sashen su AA doctor ce ta dawo tare da wata Nurse. Sun sami Umma nata lallaɓa Maanal tasha tea da RK ya haɗo ya kawo. Sai dai yanda bakinta babu daɗi ta kasa sha. Ga zazzaɓi sai uban rawar sanyi take yi. Ga azaba dan ko zama ta kasa yi sai da aka saka mata fillo ta karkace a kishingiɗe tunda ba damar tasha tea ɗin a kwance. Da ƙyar tasha rabin kofi Umma ta fita doctor ta fara aikinta. Bayan tama Maanal allurar kashe zafi. Ji Maanal take a ranta yau mai rabata da AA sai ALLAH a gidan nan, dole ma ayi walle-walle kowa ya kama tsaginsa dan sashen Oum zata koma. Ita zai ma wannan baƙin muguntar ya gudu ya barta ko sannu baizo ya mata ba...
Tuni ta saki wannan saƙe-saƙen nata saboda azabar zafin ɗinkin duk da anyi allurar kashe zafi. Tako sha kuka sosai da jerama AA ALLAH ya isa a zuciya tafi cikin kwando. Doctor data bama tausayi tana gamawa ta rungumeta tana lallashi da share mata hawaye. Ta ɗora da mata nasiha mai ratsa jiki, da yanda zata kula da kanta dan wajen ya warke da wuri. Kafin ta sake mata allura ta shiga ɗaura mata drip kuma. A haka Oum ta shigo ta samesu. Kan Maanal data fara lullumshe ido ta shafa cike da so da ƙauna da tausayawa. Fuskarta ko murmushi ya kasa ɓacewa. Yanzu ta shiga ta dake shiga sukaga Ajwaad ita da Umma shima dake barci mai nauyi saboda alluran da RK ya masa ga ruwa da ya sanya masa. Shima yasha albarka da tarin addu'oi a wajen Umma dan yau ji take kamar ta ɗaukesa shi da Manaal ɗin ta goye tai ta zagaya Abuja da su.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣9️⃣
______________
.........Har sashen su Abah suka shiga suka duba AA da Maanal, duk da dai basu shiga ɗakin da Maanal ɗin take ba. Sai dai na AA kuma yanata barcinsa. Hakama matan sun cika sashen anata taya juna murna. Suma sun shiga sun duba Maanal. Su Baba Sardauna kansu da ke Kano tuni labari yake kunnuwansu, haka ma sauran ƴaƴa da suka wuce dan dama a maza Uncle mahmud, Hussain, Hassan ne kawai suka rage sai yau suma zasu wuce da matan dan su gaba ɗayansu suna nan Abuja ƴaƴa da iyaye. Kowa dake ta ɓangaren Darma yau ka kalla fuskarsa kasan yana acikin farin ciki sosai, dan abinda ya faru a tsakanin Maanal da AA na shekarun baya zasu iya cewa shine tarihi mafi muni da girma dake jingine da wani ɗansu na cikin zuri'ar. Dan haka yau jin wannan mummunan tarihin ya goge babu shi yay matuƙar motsa musu zukata. Su Abah kansu sun ƙagara AA ya farka suji ta bakinsa.
Farin ciki yay farin ciki babu wanda ya lura da rashin ahalin Mamy ko ɗaya a masu shiga sashen AA ɗin sai Abah, amma uffan bai ce ba. Sai daga baya ne Hajiya Majdiya da itama take lure da komai tai magana.
“Wai nikam halan su Aunty Kamila basu san halin da muke ciki ba yau a gidan nan? Naga banga kowa ba daga sashen. Haka ma Fawzan shi da matarsa ban gansu ba”.
Rashin sanin halin Mamy yasa da yawansu sukace, gaskiya maybe basu sani bane. Aiko sai Hajiya Majdiya ta fice zuwa sashen Mamy tana faɗin, “Aiko nice zan kai albishir ɗin nan”.
Aunty Rufaidah ta miƙe itama ta ce, “Aiko Aunty harda ni. Sai itama matar Uncle Hassan tace itama da ita”.
Murmushi RK yayi, shima ya zaro waya yana neman Fawzan. Dan ya kira shi ɗazun ba'a ɗauka ba. Shiyasa ya ƙyalesa, yasan shi da barcin tsiya. Balle su duka suna hutu yau sunce bazasu koma aiki ba sai sun huce gajiyar biki...
A lokacin da kiran RK ke shiga wayar Yaya Fawzan yana barci ne sun gama tafka bala'i ne da Nibras, dan tun daren jiya suke yinsa, bayan ta gama haukar kukanta koma ace tana tsaka da yi shi kuma yazo mata da buƙata tace bai isa ba kamar yanda take masa. Shima ko yace bata isa ba ya biya sadaki bamai hanashi biyan buƙatarsa. Kamar yanda ya saba ya saka mata ƙarfi. Tunda fa ya samu natsuwa bata barsu sun huta ba take ta gaya masa maganganu masu zafi ta kuma dage akan sai ya saketa. Shi ko ya banza da ita, haka ta kwana tana azabarta, sai da safen abin nata ya fara hawa masa kai ya shashsheƙama fuskarta maruka. Aiki shine wutar ta ƙara tashi a tsakaninsu. Ta rantse yau sai ta bar gidan kuma da saki. Ta kira mamanta kuma tana kuka ta faɗa mata ƙauli da ba'adi shine tace ta jirata gata nan zuwa gidan.
Shi ko Fawzan yana jinsu sarai, sai ma ya buɗe wani ɗakin ya shiga ya kwanta abinsa dan jiya ta hanasu barci. Vibration ɗin wayarsa na kiran da RK ke masa ne ya farkar da shi. Da ƙyar ya iya ɗaga wayar cikin muryar barci ya ce, “Assalamu alaikum”.
RK ya kwashe da dariya kuwa, cike da tsokana ya ce, “Sai da kai kasa uwar barci. Ana nan anata hayya-hayya kana can kai barci ma kake abunka. To maza ka fito mutuminka baiji gargaɗinka ba yama ƙanwarka biji-biji gata can rai a hannun ALLAH”.
Tsabar gulma tarwai Yaya Fawzan ya buɗe idanu, sai kuma ya tashi zaune wani kalar shegen murmushi na mamaye fuskarsa. Ya ce, “Uncle karka ce min Auta?”.
“Yo inba shi ba sai wa. Yaro yaji wuta ya tona ma kansa asiri yau ƙanwarka dai fil take a leda babu abinda ya faru a waccan ranar”.
“What! Are you serious dan ALLAH?. Kai ni wlhy kama rikitani, ina dai zuwa”.
Ya faɗa yana yanke wayar ya afka bayi, brush yayi sharp-sharp ya fito. A dai-dai lokacin motar Momyn Nibras ke shigowa gidan. Ko kallonta baiyi ba ya wuce sashen AA da aketa shigi da fici.......
_________★
A bangaren su Mamy kuwa abu kamar wasa ta samu ƙuna sosai. Tsabar azabar dake ratsata tama kasa hawaye sai idannunta