Showing 138001 words to 141000 words out of 218311 words

Chapter 47 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

na wuta ko aljanna. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un ya RABBI badan halinmu ba ka gafarta mana mu da iyayenmu😭🙏, dan ALLAH duk wanda na taɓa munanawa koda da magana ne, koda a rashin sani ne ya gafarceni, sai dai in kaima ka munana min ne na maida maka murtani, dan mutuwa kullum ƙawace ga mai rai, kamar yau ne zakuji ance babu Bilkisu, na tafi kamar ma ba'a taɓa yina ko yayina ba, na tafi daga ni sai ayyukana, ƙyale-ƙyalen duniyar da ake alfahari da faɗi tashi da wahalhalu duk anan zamu barshi kamar bamu wahala a nemansa ba. Ya rabba, ya arrahaman rabbi mun tuba. Mun tuba ya rabbi.🙏😭. Dan ALLAH mu bar tsorata yaranmu da ƙannenmu da abinda bamu da ilimin sanin gaibu a kansa, rayuwar aure rahama ce mai zaman kanta, ni'ima ce. ALLAH ka bama kowa zaman lafiya da mijinsa da zuri'arsa baki ɗaya. Ina muku fatan alkairi a duk inda kuke tare da fatan ALLAH ya karɓi ibadunmu yasa bamuyi kyakkyawan ƙarshe. ALLAH yasa muna a cikin ƴantattun bayi. Ya rabbi kasa abinda ya rage mana na rayuwa ya kasance mai amfani a garemu duniya da lahira.😭🙏........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣8️⃣




______________






.......Alhamdullah walima ta kasance cikin aminci, amarya Maanal tasha kuka jikinta yayi sanyi sosai, dan idan ta haɗa da lectures na nasihar iyaye da gargaɗi da wannan ya sake tabbatar mata da aure ba wasan yara bane. Dan duk abinda akace IBADA ne to lallai dole ne ka shirya da shiri na musamman. Dole ne ka yarda da dariya a cikinsa da kuma kuka a wasu lokutan, ita aljanna bata samuwa a kwance, kamar yanda kasan baka samun kuɗi a cikin mafarkinka sai ka motsa ka nema. Idan har duniya da take ba komai ba bata samuwa a garemu cikin sauƙi, taya zamu yi tunanin aljanna samunta zai kasance mana mai sauƙi. Mata ALLAH mu farka mu ajiye wani ka-ce-na-ce na hallayar maza mu nema aljanna kawai sune a ruwa. Dan aljanna duniyace malam, komai fa akwai a ciki, wohoho Bilyn ku a aljanna ai ba'a magana zamu tsula tsiyarmu in sha ALLAHU. (ALLAH kasa mu ɗin ƴan aljanna ne😭. ALLAH ka sani mun guji iskancin nan a duniya da gudun hakkin mutane duk da yanda suke da daɗi ALLAH kai mana sakamako da aljanna domin rahamarka😭🙏, mun tuba ka yafe mana kurakuranmu ka yafema iyayenmu ya rabbi ya arrahaman, ya arrahim, ya almalik, ya malikil mulki ziljalalu wal'iram😭🙏).
Ba lectures ce kawai ta gudana a wajen ba, anci ansha tare da raba souvenirs masu ƙyau da ɗaukar idanu. Abinda zai baka dariya da birgeka hoton AA da Maanal suna yara ne a jiki. Sai mutane da yawa basu ma fahimci ango da amaryar bane ba a jiki, ita kanta Manaal abin ya bata dariya da birgeta, har sai da ƙwalla ta cika mata idanu dan kuwa hoton dake jikin ita kanta bazata iya tuna sanda aka yisa ba, tana ƙarama sosai, sai su Amaal ne keta ƙoƙarin ma tunowa suma suna dariya. Bayan kammala walima amarya Maanal ta koma ciki, yayinda su Nene suke shirin wucewa. Amma Oum tace ina ai saifa gobe da safe in sha ALLAHU kowa zai tafi, dan haka suma dole hakan zasuyi, anjima da dare ma akwai event na ƴammata da yaran Darma Family suka haɗama amarya. Rasama abin faɗa Nene tayi, wai su mutanen nan basa tausayin kuɗaɗensu ne...
Dan shima dai acan ango wani ɗan biki-biki matasan Darma Family suka shirya iya su maza, shiyasa ma abokansa suma dai duk sai gobe zasu tafi. Shi dai dauriya kawai yake dan harga ALLAH a takure yake. Hajiya Shuwa ta haɗa masa bomb da turaren da take zazzagama Maanal a jiki, shiyasa ma yaketa kauce-kaucen haɗuwarsu a yau gaba ɗaya. Sosai abokan nasa suka saka shi a gaba musamman abokan karatunsu na primary da Secondary da suka san wacece Maanal a wajensa, tunda mafi yawansu sun sha duka da rashin arziƙinsa akan taɓa ta, ga rashin kunya itama ba raga musu tayi ba duk da sun girmeta. Haka suma dai wanda sukai karatu a tare na jami'a duk da bai taɓa zama ya bama wani labarin a cikinsu ba kai tsaye, sun dai tsinta wasu a cikin abubuwan da suka shafetan a wajensa sai kuma jiya sukaji komai da ganin hotuna a wajen dinner. Duk iskanci da shaƙiyancin da suke masan bai yarda ya kula ko wannensu ba, to kuma dama dai sun san halinsa na rashin son yawan magana. Yakan ɗan murmusa dai dan shi kam duk sun addabesa, badan Oum datace yau ya kwana anan ba dan su Nene sun kasa sakewa saboda jiya ya kwana a gidan da tuni ya fece gida abinsa.....


__________★


Kuce dani ina hajjaju Mamy ne? Tana can a sashenta abin duniya ya matuƙar isarta, dole kuma ta danne ta haɗiye saboda wasu a cikin ƴan Kano a sashenta suke zaune. Badan ALLAH ba dole ta taushe tafashen azabar baƙin cikin dake zafafa zuciyarta tanata yaƙen dole ga ciwo na cinta a tsaitsaye jiya ma sai dare akabi aka saka mata drip da allurar barci a ciki sannan ta samu ta rutsa, amma abinda ya faru a wajen dinner ɗin nan ya matuƙar tsaya mata a rai. Kowa Oum yake tayawa murna matsayin uwa, komai za'ai ta ɓangaren uwa Oum Mc ke ambata. Babu mai kallonta, babu kai tunawa ita ta ɗauka cikin Ajwaad wata har goma sai a cikin na sha ɗaya ta haifesa. Tsabar ma an maida wulaƙantaciya ita aka dinga nunawa matsayin step Mom ɗinsa wai. Ya rabba wannan abu ya Zafafa mata zuciya. Har sai da taji idonta na gani bishi-bishi alamar jini ya haura mata sama sosai. Shiyyasa suka baro hall ɗin kafin ma a tashi. Koda suka shigo gida saita sakar ma Babban yayarsu dake riƙe da ita kuka dan can suka baro maman Saheeba tace sai taga komai. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga ƙirjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al'amarin na Oum fa na neman zame musu ɗan zane. Ga tsagwaron rainin hankali a ciki, yo inba rainin hankali ba taya zata shirya wannan abubuwa haka batare da ita Mamyn an nuna wani matsayinta ba matsayinta na mahaifiyar Ajwaad balle su danginta, sannan ga auren Fawzan da shima akai matuƙar raina musu wayo a gefe, wanda da ƙyar suka taushi Mamy ɗin akan kar tace komai har a gama wannan taron kowa ya watse sannan su zauna da Abah. Dan basu so kowa ya tafi dasu a baki akan hakan.
Yau ranar walima yanda Mamy ta nema ɗaga hankalinta yasa suka taru a kanta harda dangin mahaifiyarsu da sukazo wajen biki suka dinga tausarta. Wasu suna gaya mata gaskiya da tuna mata itafa ta ɗauka yaran ta bama kishiyar tata. Miyasa kuma zataji zafi dan yanzu an danganta yaran da ita. Wasu ko goyon bayanta suke da tayata kishi. Haka dai sukaita cece kunesu batare da su Oum sun ma sani ba. Koda lokacin walima yayi tace bazata fita ba ƙyaleta kowa yayi. Tabbas Oum ta lura bataga Mamy ta fito ba, sai kuma hayaniyar mutane da maƙwafta masu shigowa da abokan arziƙinsu nan cikin abujar ya ɗauke mata hankali. Ana gama walima kuma sallar magrib kawai akai aka shiga shirin faty na yaran family ɗin da suka shiryawa amarya. Anan cikin gidan shima akayi a garden, yanzu ma amarya Maanal tasha ƙyau harta gaji cikin doguwar rigar atamfa data mata ƙyau sosai. An gudanar da komai cikin aji da halin girma. Amarya Maanal tasha kyaututtuka daga ƙannen ango dan mafi yawan yaran family ɗin mata su AA sun girmesu, sai dai kamar iyaye irinsu Majdiya, ko su Nuwaira matar su RK matsayin iyayen su AA ɗin suke ai. Ƙarfe goma an tashi kowa ya nema makwanci. Yau ma cike da murna Maanal ta kwanta ƴan uwanta zagaye da ita.


Washe gari kam da wuri Nene tasa suka gyara ko'ina na sashen Maanal. Dai-dai nan mota ta iso daga Kaduna ta kayan gara daga Daddy sai kuma kayan rabo da zasuyi na buɗar kai. Dan zuwa ƙarfe ɗaya na rana an gama shirya Manaal cikin wani arnen lafaya da yay mata ƙyau. Ana idar da sallar azhar sama-sama sukaci abincin da aka kawo musu na lunch, sannan sukai zaman sake yima amarya Maanal daketa hawaye nasiha. Bayan sun kammala sashen Oum suka nufa da Maanal dan acan za'ai buɗar kai. Dole suma dangin Mamy nan suka zo aka haɗu gaba ɗaya. Anyi buɗar kai, tare da damƙama su Oum kayan rabo na al'ada daya bada mamaki, dan su Shahidah sunyi matuƙar ƙoƙarin nuna bajintarsu suma. Saboda tunda akace za'aima Maanal biki kafin tarewa suma suka shiga yin wannan tanadi su da Ammie babu wanda yaji ko ya gani sai Nene. Sai yau da ake fiddo kayan arziƙi ƴaƴan su Hajiya Yaya da na Hajiya Basariyya sukai tsuru-tsuru jikinsu na ƙarasa yin sanyi. Dan da gasken gaske an goge musu kaf haddarsu a wannan biki. Hatta su dangin Mamyn abin ya basu mamaki, dan su dai Mamy ta gama sanar musu Maanal ƴar matsiyata ce. Sai gashi a wajen baye hatta su Naufal dake matsayin ƴaƴa sai da aka basu rabo. Haka kaf manyan family na Darma kowa da nashi har su RK dake ƙananun uncle's kuma ta ɓangaren mace ma. Ga kayan gara mota guda, kaf kuma a sashen Oum aka ajiyesu ba'a ajiyewa Maanal komai a cikinsu ba dan sun ɗan saka mata wasu abubuwan a store da su Shahidah sukai dabarar saya suma ta ɓangaren kayan abincin.
Bayan gama rabo aka zagaya da Maanal gaban iyaye. Anan fa suma Darma Family suka sake zuba tasu bajintar. Dan sun sakama amarya kuɗin al'ada sosai, saboda ba kunya Oum ta bada babban basket na kaba tace sotake ta gansa cike da kuɗi iyayen ango da ƙannensa da auntys. Cikin dai raha akai wasa akai dariya. Tuni dangin Mamy suka tsure, dan da alama dai zasu sha kunya a wajen. Saboda su wai a gadarance suka taho da kuɗi mai dubu ɗari mai hamsin Maman Saheeba ma ɗari biyu wai za'a nunama Oum ita ba komai bace koda basa son amarya sai sun bada mamaki sai suka ga yara ƙanana na ajiye 1m da 500k kamar kuɗin banza. (To banda abin talaka ana faɗa da mai kuɗi ko gasa ne akan kuɗi😆😜🥱). Tuni su Mamman Saheeba suka fara ɓoye ƴan dubu ɗari biyu dana hamsin ɗin su, daga baya dai Saheeba data fahimci kunya fa dangin nasu zasu sha tace su haɗe kuɗin waje guda su bata. Haka sukayi, ita kuma ta fita ta ƙundumo 1m a cikin kuɗin sana'arta ta haɗa ta ajiye matsayin na dangin Mamy gaba ɗaya. Tsabar muguntar Hajiya Majdiya sai tace to matan yayyan ango Saheeba da Nibras kenan dole suma su sanya, hatta kuma Najma bata ɗagama ƙafa ba.
Wannan abu ya girgiza Saheeba. Nibras da duk ta fige ta rame a kwanakin bikin nan uwarta tazo ta ajiye 1m dan itama bata son harkar zubda girma🤣. Ganin haka fa Saheeba aka sake zuwa aka ɗakko 1m aka ajiye itama. Aunty Rufaidah na ganin haka tazo ta ajiye 3m matsayin na Najma tace ta fanshi ɗiyarta itama. Zokaga ihu da ihu na shaƙiyancin yaran family ɗin darma. (NIKO NACE SHEGIYA NERA, ALLAH KA BAMU NERA MAI ALBARKA😆🙏). Wanna abu ya tsayama Saheeba da uwar Nibras a ƙahon zuciya, dan ita Nibras ma hankalinta ba awajen yake ba. Uwarta kuwa tayata kishi take da ƴan uwanta akan Najma. Dan ko bikin nan sun halarci shi ne kawai dan kar ace gashi-gashi. Amma Maman Nibras ta gama shirya bala'in da zasuyi da Mamy jira take kawai biki ya watse taji dalilin yima ƴarta kishiya batare da an sanar dasu ba..........✍️






*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣9️⃣




______________


https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Shin kuna Neman in da zamu samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?kayan yara masu kyau unique na yan gayu ? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi tanayi🥳🥳


___________


..........To su dai su Shahidah sunyi godiya sannan aka kai Maanal sashen Mamy, Mamy na bedroom, su Shahidah suka zauna a falo. Kasancewar tare suke da Aunty Suhaima, da Aunty Zainab, sai Aunty Kursiyya matan Uncle Hassan da Hussaini da Uncle Mahmoud kenan suka shiga har cikin suka mata magana kasancewarsu matan ƙannen miji. Dole Mamy ta danne ta fito sanye da hijjab, dan kwance take ciwon kai ya addaba mata. Ganinsu warr a falon suka cika mata ido, dole ta aro murmushin yaƙe ta yafama fuskarta. A gabanta aka zaunar da Maanal dake lulluɓe. Da ƙyar ta iya daurewa tace ALLAH ya sanya albarka kawai. Wai ai tasan duk wanda ya isa ya mata nasiha ita basai tace komai ba.
Shahidah da a yanzu Maanal ta gama nuna mata wani abu kaɗan daga Mamyn sai tai murmushi kawai, tare da fassara zancen nata da ƙyau a zuciya. Ita kanta Nene yau dai kam tasha jinin jikinta akan Mamyn, amma batace komai ba suka fito da Maaanal. Sashenta suka maidata, aka ƙara mata nasiha sukai sallar la'asar suka firfito dan tafiya. Kuka sosai Maanal keyi abin tausayi, dan ma Amaal na nan tare da ita sai Aunty Sakina. Sai zuwa magrib su zasu koma gidan Shahidah su sake kwana gobe su wuce kd.
Sashen Oum suka koma yimata sallama. Sosai Oum tai mamaki ganin wannan tafiya tasu ta yamma haka. Ta shiga lallashinsu akan su bari sai gobe da safe Nene tace ina ai in sha ALLAHU yau a Kaduna zasu kwana, abin ai sai ya koma rashin kangado kuma. Anyi komai an gama ai suma sai a barsu su huta haka nan abi yara da addu'ar zama lafiya.. Badan Oum taso ba ta haƙura, nan fa aka shiga shirya musu kayan biki da aka tanada domin su, dan hatta Ammie sai da Oum ta haɗa mata nata. Sashen Maanal ɗin suka sake dawowa tare da ita, acewarta ya kamata suyi sallama da AA dan ta kaisu sunyi da Abah yanata musu godiya, a can kuma suka sami Mamy itama. Kiran wayar AA datai a kashe kuma Fawzan ya tabbatar mata yana gidan sanda suke buɗar kai ya shigo ya sata biyosu.
Rungume Maanal dake zaune a bakin gado ta takure waje guda tana sharar hawaye har yanzu tayi, cike da tausasawa ta shiga lallashinta. Kafin ta bata umarnin hawa sama ta kira musu AA ɗin. Mayafin lafayarta ta gyara da ƙyau, tayi ƙyau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan ƙamshinta daban ne, ga ƙunshinta raɗam yanata ɗaukar ido daga baƙin har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autan ta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai ɗorewa kuma. Tare da Oum suka baro bedroom ɗin nata suka haura sama. Zuciyar Maanal bata ƙarasa fashewa ba sai da ta hawo upstairs ɗin, ya subahannallah komai yaji, ga wani mayataccen ƙamshi mai ratsa zuciya. Zama Oum tayi a ɗaya daga kujerun, Maanal ɗin zata zauna itama ta katseta tana nuna mata kofar bedroom ɗin AA. Jikinta cike da sanyi ta nufa ƙofar, tana gab da isa sai gashi an buɗe. Cak ta tsaya tana kallonsa. Kamar yanda shima yake kallonta irin na mamakin nan dan ko motsinsu bai jiba. Yama fito ne zai fita dan dama wanka ya shigo yayi rabonsa da wanka tunna safe manyan kayan jikinsa sun takurasa shiyyasa yazo yay wankan ya canja da ƙananu. Juyawa kawai Maanal tai tabar wajen, shima sai bai ce komai ba ya biyota saboda hango Oum zane a falon.
Bata zauna ba, sai tai kamar ana kiranta a waya ta gudu ta barsu dan ta basu damarsu. Murmushi kawai Oum tayi danta fahimci wayo Maanal tayi ya gudu babu wani kiranta da akayi. Bedroom ɗinta ta wuce inda su Nene suke. Bata wani jima ba Oum ta shigo da sallama itama. Ta sanarma Nene ga AA zai shigo suyi sallama. Gyagygyarawa suka shiga yi kafin ya shigo bakinsa da sallama. Duk suka amsa banda Maanal datake kallon hotunansu a wayar Aunty Sakina. Cike da girmamawa ya rissina ya gaida Nene, hakama Aunty Sakina duk da ba girmarsa tayi ba, amma tunda akace matsayin ƙanwa take a wajen Ammie yake girmamata. Shahidah ta ce, “Oh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login