Showing 186001 words to 189000 words out of 218311 words
Chapter 63 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
ya dakata da aikin da yake yi, shiru yay cikin nazari, yasan yaron Sen... Bukar sosai, dan a yanzu sune matasan ƴan iskan yara dake tashe a birnin Abuja. Dama tunda ya baro gida yau yake jin girarsa ta haggu na rawa, sannan jikinsa na bashi akwai wani abu mai girma kamar na tunkaroshi. Wannan tamkar baiwa ce da ALLAH yay masa, yanada tsarta sosai, shiyyasa ko akan harkar kasuwancin nan bada kowa yake yarda yay huɗɗa ta manyan kuɗi ba. Ama cire duk wancan batun, Sen.. Bukar dama tun asali abokin dabi ne. Daga shi har abokansa sun jima suna masa zagon ƙasa tunda shugaban ƙasa ya bashi mukamin nan. Duk da shi yaƙi shiga sabgarsu su kowane motsinsa na akan idonsu ne. Ga lamarin Maanal daya gitta, dan tsaff sai da yay binciken kaikawon Sen... Ɗin akan Maanal hatta zuwa Giro da hidimomin daya dinga musu. Duk da yana ganin tunda yaji tayi aure zai iya haƙura amma sai bai yarda da wannan zuwan na Sen... Ba. Dole akwai dalilinsa, dole akwai manufa a wannan harƙallar. Shima kuma dole ya bincika kafin lokaci ya ƙure masa...
________★
Sosai Maanal tasha barci, dan bata farka ba sai ɗaya saura. Tafi mintuna goma shiru tana tuna abinda ya faru a daren jiya. Sai faman ɓata fuska take, ranta fal mamakin ƴan iska musamman wasu da zaka gansu ƴan yara da su ƙanana. Yanzu dan ALLAH da wannan azabar har mutum ya iya zuwa ya kai kansa. Eh dole tace azaba, dan ita dai a nata ganin banbancinsa dana farko kaɗan ne, amma Didi Amal tace mata shike nan bazata sake jin wahala ba shiyyasa ta hakura ta sallama. Haka dai taita saƙawa da kwancewarta har taji ana shirin kiran salla sannan ta yunƙura ta miƙe da ƙyar. Duk da ba ciwo taji ba, ba kuma zafi take ji kamar ranar ba kasa zama tai da ƙyau, dan harga ALLAH tana jin babu daɗi a jikinta, ga gaɓɓanta na mata ciwo sosai duk da taimakon daya bata. Wayarta ta ɗauka ta danna screen ɗin ya kawo haske. Miss calls da yawa. Na Oum, na Didi Shahidah, sai na AA da sukafi na kowa yawa. Shi harda ma message.
Saƙon ta buɗe, tai shiru tana karantawa fuskarta na canja yanayi zuwa murmushi. _“Barka da tashi My Ever-Bloom. Samun ki a rayuwata yana faranta mini zuciya kullum. Na gode kalma ce ta fatar baki, sannan kuma gama gari a cikin al'umma. Amma nauyinta da kimarta mai daraja ne a garemu Musulmai. Domin idan UBANGIJI ya mana rahama kafin komai godiya muke fara masa, ya kuma horemu da mu godema juna a yayin ƙyautatawa. Nagode Maanal, irin godiyar da bata da adadin kintace, kin canja ni, kin maidani babban mutum a zahiri da baɗinin rayuwa. ALLAH yay miki albarka, ya dawwamar da farin ciki a zuciyarki na har abada. Koda duniya tayi nauyi kasancewar ki a cikin ƙirjina nasa nutsuwata ta tabbata❤️.”_
Wayar ta kife a hankali, sai kuma takai hannu ta share guntun hawayen da suka cika mata idanu. Gaba ɗaya ma sai taji ciwon jikin ya ragu mata. Bata cutama kanta ba ta fita kitchen ta ɗaura magungunan sit bath da Hajiya Shuwa ta bar mata, ta kuma ce ta dinga yi a duk lokacin da haka ta faru har lokacin da komai zai zama jiki. Taji kunya sanda take faɗa matan, amma Hajiya Shuwa ta fuske abunta. Sama ta dawo tai sallar azhar sannan ta koma ta juyi maganin. Sosai tai sit bath sannan tai wanka ta fito ta gyara jikinta da gidan gaba ɗaya tasa ƙamshi ko'ina. Fes da ita sai dai idanun da suka sha kuka na nan da ɗan fushi. Kwalli ta saka sai ya taimaka ya ɓoye kaso mafi yawa. Yau jitai bata jin zuwa gaida Mamy, sai kawai ta wuce sashen Oum. A falon ƙasa ta sameta ita da Nuratu, Oum na duba wani littafin addini Nuratu na kallo. Ko kallon inda Nuratun take batai ba, taje jikin Oum ta kwanta, tare da faɗin, “Oumna ina kwana”.
Fuskar Oum da murmushi taja hancinta kaɗan ta ce, “Ina yini dai Baby. Ko duk daɗin barcin ne”.
Dariya Maanal tai tana ɓoye kanta a jikin Oum ɗin, dai-dai nan RK ke sallama shi da Nuwaira. Zaune Maanal ta tashi tana musu sannu da zuwa, Nuwaira tazo ta ɗan bata runguma sannan ta zauna suna gaisawa da Oum dake tsokanarta. Maanal kuma RK take gaidawa. Shi ko dake dariya a da gulmar AA a zuciyarsa ya amsa mata da kulawa. A ransa ko faɗi yake, (Wato fitinannen yaron nan bazai bar yarinyar nan ta huta ba) dan kallo ɗaya yayma Maanal ya fahimci taji a jikinta dan idonta ma bai ɓoye kukan data sha ba. Dan ma ta saka kwalli. Da ƙyar Nuratu ta gaishesu, shi kaɗai ya amsa a ransa yana mamakin uwar mi take anan ɗin, Nuwaira kam bama ta nuna tasan da Nuratun ba. Hirarsu suke da Maanal da Oum.
Daga baya Maanal da Nuwaira suka tashi suka shiga kitchen, RK Kuma ya fice akan zaije damai kwancema Mamy ɗori ya iso. Binsa Oum tai suka fita tare, aka bar Nuratu ita kaɗai a falon. Aiko sai taji wani irin takaici. Itafa shiyyasa tun farko bata so zaman nan sashen Oum ba, amma mamanta tace dole ta zauna dan su samu damar aiwatar da aikinsu da malam ya basu akan Oum da Maanal har ma da AA da shi kansa Aban. Dole su kame zukatan kowa su samu auren nan nata ayi-ayi sauran rikicin ya biyo baya. Ita ma kuma wani fannin nata son taita ganin AA duk da yanzu yana zarya a sashen Mamyn ma saboda dubata..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣2️⃣
______________
.......AA daya kasa haƙuri Maanal bata kirashi ba, kuma taƙi ɗaga masa kiransa ƙarfe huɗu ya dawo gidan. Lokacin sun kammala komai suna ƙoƙarin zubawa a kuloli. Nuratu na kwance har yanzu tana kallo. Kawai a bazata AA ɗin ya shigo, sai taji duk ta rikice, ALLAH da tasan zai dawo gida yanzu wanka zataje tayi taci kwalliya abinta. Shi ko kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Jin muryar Maanal a kitchen ya sashi sakin murmushi, yana jin daɗin yanda ta ɗaukema Oum kai-kawon girkin nan da take kullum dama abin na damunsa, yayi-yayi kuma ta daina taƙi, sai tace basa son abincin masu aiki, itama bata so ya za'ai ta zauna, dole ta shiga ta girka ai da kanta. Sauran ƴan uwansaa yasha ji suna nuna damuwa akan aikin nan na Oum.
Kamar an faɗama Maanal ɗin sai gata ta fito daga kitchen ɗin tana ƴar dariyar maganar Aunty Nuwaira hannunta ɗauke da jug zata kai dining. Turus ta ɗan tsaya tana kallon AA ɗin, kamar yanda shima yake kallonta da sassanyan kallo. Janyewa tai ta kalla agogo, sannan ta sake juyowa ta kallesa tare da faɗin, “Hu'um tseren office ka fara Besty! Ƙarfe huɗu fa”.
Shi dariya ma ta bashi wlhy, wai tsere kamar wani ɗan yaro ya gudo daga makaranta. A mamakin Nuratu data kume a wajen sai taga AA ɗin ya saki murmushi mai ƙayatarwa yana nufar Maanal. Babu ko tunawa da tana a wajen, ko wani zai iya ganinsu kawai ya rungumeta ta baya, tare da sauke fuskarsa a kafaɗarta ya sumbaci wuyanta. Ya kai bakinsa kan kunnenta ya gwargwaɗa mata maganar da ita bata ji. Dariya taga sunyi a tare, mamakin ALLAH ya cika mata zuciya, wai AA ne ke dariya haka har haƙoransa a waje. Shin wai mi tsinanniyar yarinyar nan tai masa ne haka, su sunata wahala kullum da zubema malamai kuɗi amma babu wani ci gaba. Jiba abinda suka saka a sashenta daren ranar amma a banza babu abinda aka fasa, sai taji ma hawaye ya cika mata ido.
Manaal da idanunta suka hango mata yanda Nuratu ta zuba musu ido cike da gayya bayan sun ajiye Jug ɗin tare da AA ta juyo suna fuskantar juna. Ɗan ɗiɗɗishe tai ta sumbaci haɓarsa, sai kuma ta kashe masa ido ɗaya ta sumbaci lips ɗinsa. Tana ƙoƙarin juyawa da sauri ya riƙota. Ciki-ciki ya ce, “Kinma isa kimin ɗan kaɗan ki gudu”.
Dariya Maanal ta sanya tana ƙoƙarin ƙwacewa shiko ya mannata da table ɗin dining ɗin yana ƙoƙarin kai lips ɗinsa kan nata, itako tasa hannu tana karewa tana cigaba da yin dariyar ƙular da Nuratu....
Gyaran murya RK da basu san da shigowarsa ba yayi. Dakatawa AA yay yana wani yin luuu da idanunsa irin na (ɗan yawar nan ya katse min jin daɗi) sai kuma ya ɓata fuska kamar ba shi ba ya juyo yana kallon RK ɗin da harara. Ita dai Maanal samu tai ta zille ta gudu. Shima RK ɗin kallon AA yake cikin ɗage gira da shaƙiyanci.
Cikin ƙara balla masa harara AA ya ce, “Kai dai wlhy anyi kawun banza”.
“Oh koba Kawun banza ba. Idan ni Kawun banza ne kai miye naka sunan. Ɗan iskan yaro kazo ka matse yarinya a sashen mamanta ko kunya baka ji jarababbe kawai”.
Cokali AA ya zara dake dining ɗin ya wulla masa. RK ya kauce yana dariya. Murmusawa shima AA ɗin yay, batare da ya sake cemasa komai ba ya nufi ƙofa. Binsa RK yay suka fice tare...
Wani irin takaici, baƙin cikin da ƙunar zuciya Nuratu take ji, a ranta ko ayyanawa take bazata iya cigaba da zaman sashen nan ba. In ba hakaba wataran sai ta bubburmawa Maanal wuƙa wlhy, sai dai itama a kasheta.....
_________★
Alhamdullahi Mamy dai an kwance karaya, dan haka Aunty Babba ta wuce. Maman Saheeba kuwa tace sai nan da kwana biyu. Amma a washe gari itama zata bar gidan gidan Hajiya Turai zatai kwana biyun. Auntyn tace ita ta sani kuma wannan ita dai tai wucewarta dan AA da kansa ya saya mata ticket, ya kuma yimata tsaraba mai yawa batare da sanin ko Mamyn ba. Itama sai da aka kaita airport ɗin ne driver ya bata yace inji AA, ya kuma bata wata leda yace inji Maanal. Jitai gaba ɗaya kunya ta ƙara kamata, dama gashi Oum ta cikata da nata abin arziƙin, ta kuma saka Fawzan da Babban Yaya sukai mata. Itako wadda tai wahalar jiyyar ma da faɗa suka rabu wato Mamy, saboda ta sake mata nasiha akan al'amarin Oum dana Maanal Mamyn ta birkice mata, sai kawai ta ƙyaleta ta bita da addu'ar ALLAH ya ganar da ita gaskiya kafin lokaci ya ƙure mata.....
A ranar Maman Saheeba bata wuce gidan Hajiya Turai ba sai washe gari. Sai dai kafin ta wuce ɗinne saƙon Sille ya sake iske Mamy a karo na biyu tunda farar safiya. Saƙo ne daya ƙara birkitata fiye ma da wancan karon. Dan ya ce mata yana son su haɗu, sannan kuma yana son kuɗi miliyan goma, idan zata taho address ɗin daya rubuta mata tazo masa da su. Idan ba hakaba kuma shi zaizo gidan Darman da kansa ya amsa, kuma sai ya naƙasta rayuwar AA ta wani ɓangare dan ta tabbatar bada wasa yazo ba.
Zufa sosai Mamy keyi a zaune jikinta na rawa. A cikin wannan yanayin Maman Saheeba da taje suka gama ƙulle-ƙullensu da ƴaƴanta dan har Saheeba an bar mata abinda zata dinga sakama babban Yaya a abinci, dan haka itama zata maida hankalinta a sashen Oum tunda taga yanzu a can yake cin abincin ta shigo ta samu Mamy. Sosai ta tsaya tana mata kallon mamaki. Sai kuma ta ce, “Aunty wai lafiyarki kuwa? Sai zufa kike fa ga jikinki na rawa”.
Miƙewa Mamy tai, da ƙyar ta iya faɗin, “Ba komai” ta wuce bedroom ɗinta fuuuuu. Maman Saheeba da mamaki ya cikata tai sagade tana kallon ƙofar, sai kuma ta taɓe baki ta gyara zama ta hau cin naman da Mamyn ta saka akan gasa mata zataci. Itafa wlhy irin wannan cin daɗin yasa idan tazo gidan nan bata son tafiya...
Kai-kawo Mamy ta shiga yi a cikin bedroom, karo na farko ta bama brain nata damar yin nazari akan wannan mai turo saƙon. Dan ya kamata tasan ma wanene shi? Saboda idan zata auna da hankalinta abinda ya turo matan, ko yake mata barazana da shi ta AJIYE SHI NE A CIKIN DUHUN da babu wani mahaluki a duniya daya taɓa sanin koda labarinsa. Hatta kuwa da kakarta da babanta da suke kwana suke tashi a gida ɗaya lokacin. Kai hatta da Junaid kansa. Sai dai me, kalaman Junaid ɗin ne suka shiga maimaita mata kansu a ƙwaƙwalwa tamkar yanzu ne yake faɗa mata su.
_(Lallai kinyi kuskure Kamila, babban kuskure ma kuwa na cin amanata. Amma ki sani kuma ki shirya ɓadda Junaid a wannan duniyar tamkar kin KASHE MACIJI NE BAKI SARE KANSA BA. Domin akwai AJIYA A DUHUn ki a hannuna dake a karan kanki bazaki taɓa iya hasaso minene ba har sai a lokacin dake zaki koma cikin duhun. Maza jeki, jeki da iya gudun da zaki iya ki taka irin taki rawar yanda kike so, ni kuma ZAN DAWO a gaɓar da ƙafafunki da gangar jikinki har ma da zuciyarki da ƙwaƙwalwa suka gaji. Dan kinfi kowa sanin JUNAID baya barin BASHIN GABA)_.
Dummm kanta ya yi, zuciyarta na rawa da bugawa. Dan a wancan lokacin sam bata ɗauki kalamansa da wani muhimmanci ba face cika baki da kirarin banza irin na wanda akaci wasa. Amma sai gashi a yau fa kamar kalamansa na neman kama hanyar tabbata ne. Kai ina hakan bazai yiwu ba. Bama zai taɓa yiwuwar ba sai dai idan a cikin yaran Junaid ɗin ne wani ke son mata barazana da son tatsarta kuɗi tunda gashi ya ambata a yanzu. To aiko zata nunama ko wanene ita ɗin ba ƙaramar ƴar wasa bace. To amma kuma minene ya alaƙanta yarinyar nan Maanal da wancan AJIYA A DUHUN nata na tsawon shekaru da babu mahalukin daya sani. Hoton nan dai na Maanal tabbas itace ta bada shi da Maman Saheeba da Hajiya Turai a lokacin da suke son ai musu aiki. Kuma idan bata manta ba a lokacin Hajiya Turai ce ta haɗasu da yaron da zai yi aikin, dan lokacin suna zaune ne a Lagos, sun zo ganin gida ita da mijinta da Nuratu da zata girmi Maanal kaɗan, kasancewar basu san wazasu samu ya musu yanda suke so ba saboda gudun mizai je ya dawo sai Nana tace ta bari ta shawarci Hajiya Turai ɗin dan tasanta itama ƴar ƙunar baƙin wake ce. To bayan sun tattauna da Hajiya Turai ɗin shine tazo wajen bikin da saurayin da zaiyi kusan sa'a da AA a lokacin tace ɗan ƙanin mijinta ne, tace ya zauna wajen su Fawzan har a gama biki dan sun san AA bazai shiga harkar shi ba dan shi babu ruwansa da kowa sai Maanal. Fuskar yaron ce ke son dawo mata, amma ta kasa tunashi da ƙyau. Sai tai tunanin duba hotunan ranar. Closet ɗinta ta nufa, ta buɗe wani box dan tun suna asibiti tai kiran Haule tace ta kulle mata ɗakinta saboda hotunan, Haule najin haka ta gane, sai ta kwaso hotunan daga inda ta ɓoye ta ajiye mata su saman gado sannan ta kulle ɗakin. Koda aka sallamosu suka dawo gidan bata yarda an buɗe ɗakin ba shiyyasa ma ta zaɓi yin jiyyar a nan ƙasa sai jiya ta shigo da kanta da za'ai shata ya kwaso su taɓoye sannan. Shine yanzu ɗin ta ɗakkosu a inda ta ɓoye. Hoton matashin yaron nan ta ciro, ta maida sauran ta ajiye. Bakin gado ta dawo ta zauna ta zuba masa ido, tsahon lokaci zuciyarta na tabbatar mata shine wani sashe na cewa a'a. Da taga dai tana neman rikicewa sai tai kiran Maman Saheeba a waya tace ta shigo ta sameta..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣3️⃣
______________
.........Babu jimawa Maman Saheeba kuwa ya shigo, kusa da Mamyn ta zauna, ita tama yi zaton wani sirrin zasuyi, amma sai taga Mamyn ta miƙa mata hoto. Amsar hoton tayi tana kallo, tsahon mintuna ta ɗago tana kallon Mamyn. “Aunty waye shi?”.
Numfashi Mamy ta fusrzar, sannan ta amshi hoton ta ce, “Zaki iya tuna fuskar yaron nan da Hajiya Turai ta kawo yay mana aiki a shekarun baya?”.
Jimmm Maman Saheeba tayi, sai kuma ta ce, “Kai ai