Showing 102001 words to 105000 words out of 218311 words
Chapter 35 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
da'alama wayar bata a kusa da ita.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣0️⃣
______________
........Numfashi mai ƙarfi taja, kafin cike da makirci ta ce, “Haba Aunty wannan har wani abin tada hankali ne har kina saka kanki kuka. Yo ALLAH na tuba cikin mi! Cikin ma da ƙila bai wuce kwanaki ba, kinga ko ba buƙatar zubarwa ake ba lalatashi kawai zamuyi cikin sauƙi”.
“Nana ta yaya? Yarinyar da bata taɓa cin abincin sashena ba tunda tazo. Ke ni zan ma iya rantse miki ban taɓa zaman minti goma da ita ba”.
“Wannan duk ba damuwa bane, ai azumi akeyi, kuma a irin lokacin nan abinci nasan duk a tare kuke yinsa, wannan aikin Saheeba ce zatayi mana shi, bama yanzu ba sai bayan salla. Sannan ya kamata Aunty kima Ajwaad tsiya gaskiya. Munafiki yana sum-sum da kai kamar bazaka saka masa yatsa a baki ya ciza ba amma yasan yay ma mace ciki. Idan wancan na farko yace kuskurene wannan kuma fa? To wlhy sai kin fito masa a mutum sannan, idan ba haka ba ko mun lalata cikin ma a banza tunda ba kunyace da shi ba zai iya sake mata wani a gidan kuna nan sake da baki, wama ya sani ko tun kafin su tafi Chaina ɗin yay wannan ɗin tunda shi dama taƙadari gagararren yaro n.....”
“Uhmmm Nana! Please a dinga sassauta irin tsauraran kalaman nan akan yara basu da amfani, duk da Ajwaad nada taurin kai a kaf yaran nan babu wanda nake iya lankwasawa cikin sauƙi irinsa. Su da suka sha daga jikin nawa ma ya fisu min biyayya..”
Sosai kalaman Mamy suka daki zuciyar Maman Saheeba, sai ta fahimci lallai dole ta dinga gyara kalamanta tunda har ƴar uwar tata ta fara nuna ranta ya sosu akan zagin Ajwaad da tayi. Cikin ɗan gyaran murya a fili ta ce, “Hakane aunty kuma kiyi haƙuri raina ne ya ɓaci wlhy. Kin san yaran nan da son fusata mutum. Ni dai yanzu abinda kawai nake gani kenan. Mu lallata cikin sannan ki ja masa kunne tunda wancan bai shigesa ba. Shima Fawzan kin masa maganar Amani ɗin kuwa? Wlhy yarinyar nada hankali Aunty, sannan tafi Nibras komai, ƙyan jiki, ilimi, harma da tarbiya. Itama dai uwarta ba wasa ba wajen kuɗi. So nake wlhy mu rikita zuciyar matar nan ai auren rana ɗaya dana Ajwaad da Nuratu..”
Fuskar Mamy da murmushi ta ce, “Karki damu zan masa magana shima yau ɗin nan. Dama na bari ne ya nutsu naga kwana biyu yanata kai-kawo na kwangilar nan daya samu. Ki tura min hoton yarinyar ma kada na manta”.
Cike da farin ciki Maman Saheeba ta ce, “In sha ALLAHU yanzu kuwa aunty. Harma da no ɗinta”.
Daga haka sukai sallama Mamy na sauke ajiyar zuciya. Sai taji ɓacin ran nata ya ragu sosai. Shiyyasa take ƙaunar Nana sosai......
__________★
GIRO
Zaune Gwaggo take ta zabga tagumi abin duniya ya isheta, yau ko abinda zasu ci basu da shi. Tunda Sule ya tattare ƴan sauran kuɗaɗen wajen Sen... Suka koma ƙarƙaf, ga Babu bashi da lafiya sosai. Haka kawai sai ya yanke jiki ya faɗi. Sun ɗan kira mai camix ɗin garin ya dubashi yace ulser ce ke damunsa, sai kuma hawan jini. Nan dai ya ɗan bashi magunguna yay masa ƙarin ruwa. Daga nan ne ma yake ɗan samu ya fita zuwa ƙofar gida. Amma daga ba nan ɗin ba baya iya doguwar tafiya, dan ko azumi ma baya iya yi. Kai zata iya cewa ma itace kawai mai yin azumin a wajen, dama ba'a maganar Haƙila da Sule, Sailu ko ta murje idanunta tace itama ulser gareta mai zafa bazata iya azumi ba. Dan haka da rana sai su dafa abinda ransu keso ita da yaranta suci, ko Babu sai sun gadama ma suke bashi. Itako in aka sha ruwa sai wanda yaga ALLAH yaga Annabi ya sammata kunu a gidan. Shi dama Baba ba magarsa ake ba, sauran matan nashi ma suke cida kansu. Sauran ƴaƴanta kuwa na ma'auri suma taimakon suke nema, tunda dama dai Babu ɗinne taƙamarsu a baya, tunda komai ya suɓuce kuma suma suka shiga halin shiga ukun.
Haƙila ce ta shigo wajen tana taunar cingam tana waƙe-waƙe, kanta ɗauke da botikin cin-cin da take yi na sayarwa. Duk da azumi ne haka take fita da shi talla, idan akai magana tace yara take saidawa ai. Ko suma yaran azumin suke. Rashin mutuncin Sule dama ita Haƙilar kanta da uwarsu kesa babu wanda ya iya cigaba da magana. Dan suma mazan gidan yanzu tsoronsu suke ji. Muƙut Gwaggo ta haɗiye yawu tana bin botikin cin-cin ɗin Haƙila da kallo duk da azumin da take. Haƙila ko ko kallonta batai ba ta shige ɗakinsu ta ajiye botikin, babu jimawa ta fito da ɗaurin ƙirji alamar yin wanka, sai ƙunƙuni take a ranta wai Temo... ya bata wahala, shege gashi ba wani kuɗin kirki yake bata ba. Duk yanda zai gurjeta baya iya wuce dubu biyar yace ta bishi bashi. Kullum kuma aikin kenan, ita kuma tana zuwa ta bashi kanta ne kawai saboda yana mata yanda take so. Temo... Dai inyamuri ne irin masu shiga ƙauyukan nan su buɗe shago, sunansa Temoty ne. Mutanen Giro ke kiransa Temo.... Temo shine ya fara keta budurcin Haƙila saboda shegen kwaɗayinta, tun tana shan wahala harta goge, dan gaba ɗaya har zuwa yanzu shekarun haƙila basu wuce goma sha ba. Kai ko ƙirjin ma yanzu ne yake bayyana a jikinta sosai, ƙwailayen ma bata gama cika cif-cif ba amma idonta ya buɗe. Dan yanzu har cikin Suru samarine da ita kala-kala. Abin tausayi ga rayuwar yarinyar nan indai ta fita a gida to yini take daga ɗakin wancan saurayi zuwa wancan kango ko gajiya batayi, ba kuma komai ya sata zama karyar maza ba sai shan magunguna kamar ba yarinya ba. Sarai Sailu ta jima da sanin Haƙila nabin maza, amma kuɗaɗen da take kawo mata da ɗan shayi da burodin baba kalla da indomie da tsire yasa ta kasa yin magana. Kai bama ita ba matan gidan kansu sun sani, tsoron Sailu ya hana su cewa uffan...
Gwaggo na ganin Haƙila ta shige bayi ta miƙe da sauri ta afka ɗakin. Cin-cin ɗin ta ɗebo a cikin zani ta fito, jikinta na ɓari ta afka ɗakinta ta ɓoye. Ta goge hannunta da man cin-cin ɗin ya ɓata ta dawo ƙofar ɗakin ta sake zama kamar batai komai ba.
Babu jimawa kuwa Haƙila ta fito ta sake wuce Gwaggo. Tana ko shiga ɗakin su sai gata ta fito kamar an jehota. Zaram Gwaggo ta miƙe abinka da mara gaskiya, gashi data ɗauka cin-cin ta manta ta rufe botikin. Wani irin cin kwallar Gwaggo Haƙila tayi cikin ƙaraji kamar sa'arta tace, “To tsohuwar banza bani kuɗina, munafuka ɓarauniya”.
Muryar Gwaggo har rawa take, “Kudinki kuma haƙila, ni na ɗauka miki kuɗi ne?”.
“Wlhy zan iya sharara miki mari anan gurin kema kin sani, idan baki ɗauka min kuɗi ba ai kin ɗauka min kayan kuɗi ƙaramar ɓarauniya dako satar baki iyaba ma. Ban kuɗin cin-cin ɗina inba haka ba wlhy na saki zanen nan anan nai tsirara mu daku.....”
“Haƙila! Haƙila! Uwar tawa kika shaƙema wuya haka kina jifanta da sunan ɓarauniya?”.
Babu ne dake shigowa yay maganar. Baki sosai Haƙila ta gatsina, cike da tsiwa da rashin girmama iyaye tace, “Yo Babanmu ita taja, daga fa shigata wanka ta afka ɗakin Innarmu ta ɗiba min cin-cin, itama ba haka take kiranmu ɓarayi ba, bayan kuma a wajenta muka gaji satar tsohuwar alakwankwan kawai”.
Wani irin runtse idanu Babu yayi ƙirjinsa na masa zafi. Cikin rawar murya ya ce, “To kiyi haƙuri ki saketa. Gwaggo miyasa kika taɓa mata kaya?”.
Kuka Gwaggo ta fashe da shi itama. Dan harga ALLAH taji shaƙar nan ta Haƙila. “Yanzu Habibu ka yarda da maganar ƴarka kenan na ɗauka mata cin-cin ɗin?”.
“To Gwaggo ni mizance. Kinga fa ranar sai da nai miki nasiha akan al'amarin Sule da Haƙila a gidan nan, na nuna miki ki daina shiga sabgarsu su ba kamar su Shahidah bane da kike iya tankwarawa. Uwarsu kuma ba kamar Asiya bace da zatai miki kawaici ta kauda ido. Kika min alƙawarin dainawa gashi tun ba'aje ko'ina ba kunayi.”
“To wai dama kai baba kana tunanin wannan kilakakkiyar tsohuwar zata kama kanta ne a cikinmu. Mu dan ALLAH ma ka daina mata wata nasiha ka barmu da ita mu gurji ruɓaɓɓen bakinta da baya iya shiru jarababbiya kawai. Kuma wlhy sai kin biyan kuɗin cin-cin ɗina ko kuma yanzu na kira Hure dilalliya tasai tsohon gadon ɗakinki a kuɗina”...
“Ai bama sai kin kira Hure ba ni kaina muyi ciniki ƙanwata dama na gaji da kwana ƙasa cinnaku namin walmakalifatu.”
“To shike nan ma Yaya Sule”. Haƙila ta faɗa tana sakin wuyar rigar Gwaggo. Ƙarasowa Sule yay ciki batare da ko kallon Babu yayi ba, dan shi bama ya magana da Babu saboda ya masa faɗa gaba yake da shi. Gwaggo da Babu na tsaye kamar gumaka su Sule suka shiga ɗakin Gwaggo. Gadon ƙarfenta ƙarami suka ɓallo, bayan sun zazzage mata katifar rimi dake kai da ƴan tsummokaranta. A gabanta, a gaban Babu sukai cinikin gado Sule ya bama Haƙila kuɗi yace ta tayasa su kafa gadon a ɗakinsa dake tsakanin na Gwaggo da na uwarsu.
“An gama babban yaya, amma tsaya abama Baba la'adar ganin ido mana”. Haƙila ta faɗa tana matsawa kusa da Baba ta saka masa ɗari biyu a aljihu, tako zo kim-kim suka kama gado zuwa ɗakin Sule suka haƙa. Katifarsa da taima gadon yawa dan ta 6by6 ce daya sato a wani gida haka suka ɗorata a gadon. Ya haye ya wani baje yana sauke numfashi. Itama Haƙila hawa tayi tana faɗin, “Yaya bara na ɗana nima”.
Dariya ya sanya da faɗin, “Ƴar son banza, ai ni wannan satar cin-cin tamun rana. Wai ina babarmu?”.
Baki haƙila ta taɓe, “Kaima ka sani tana can biye-biyen ƙauyuka wajen malamanta neman asiri”.
“Ko kuma masu danneta ba”.
Dariya Haƙila ta sanya, cike da shaƙiyanci tace, “To kaga laifinta ne, Baba ya riga ya ruɓe dole taje inda zata samu ƙarfi. Nidai tsorona kawai karta kwaso mana ciki wani susu can. Amma bari nasan maganinta, maganin hana ɗaukar ciki zan dinga jefa mata a ruwa bata sani ba”.
Dariya sosai Sule ke kwasa. Kai bakace hirar uwarsu mahaifiya suke yi ba..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣1️⃣
______________
.........A waje kam jiri ne ya nema kwasar Gwaggo, sai da Babu dake hawaye ya kamata ya zaunar sannan. Zama yay shima kansa a ƙasa yana kuka yace, “Gwaggo kinga sakamakon ko? Ni nasan hakkin Asiya bazai barmu mu zauna lafiya ba, hakkin ƴaƴana bazai barmu mu zauna lafiya ba. Baba Umar ya min komai na gatan rayuwa shi da Mama Lubabatu. Amma suka tafi suka barni da ƴarsu ɗaya jal na gagara riƙe amanarta, na cinye dukiyarta, na wulaƙantata, na ƙuntata rayuwarta, haka nake hanata hakkinta saboda karuwaina, nazo a ƙarshe ma nace ƴaƴan da muka haifa ta hanyar sunna ba nawa bane ba. Gwaggo duk kece kika ɗorani akan hakan, kika takura sai na auri Sailuba wai dan tayi maganin Asiya. Yau gashi ba maganin Asiya Saulu keyi ba maganinki da ni take yi ita da ƴayanta. Jiba yanda na koma, kamar ban taɓa sanin a daga ilimi ba, kamar ban taɓa rayuwa a birni ba, kamar ban taɓa yin aiki ba wai aikin ma na ƴan sanda harda matsayin dpo. Gwaggo hakkin Asiya bazai barmu ba. Jiba inda muka samu Asiya, jiba ƙyaƙyawar rayuwar da take ciki, ƙaton gida, tana auren babban mutum, ta ƙara komawa yarinya kamar ba ita ta haifi su Shahidah ba, ƴaƴa mazan da kike mata gori taje ta haifesu acan. Ni ga nawa nan ya zame min ƙadangaren bakin tulu. Nayi nadama Gwaggo, nayi ALLAH wadai da halina”..
Kuka ya sarƙeshi, itama Gwaggon kuka take sosai kamar numfashinta zai bar gangar jikinta......
__________★
AA na sashen Oum har sai da ruwan ya ƙare ya cire mata. A hakan ma bashi da niyyar tafiya sai da Abah ya kaɗa kansa. Badan yaso ba ya tafi. Alhamdullah itama Maanal ɗin da asuba sai ta tashi jikin bawani zazzaɓi. Sai ƴar ramar da tayi a fuska. Babu yanda Oum batai da ita karta ɗau azumi ba amma ta marairaice akan zata iya, dole ta ƙyaleta ta ɗauka....
Misalin takwas duk suka tashi, kamar yanda suka saba su matan suka fara shirin fita tafsir. Suna fitowa AA da RK na shigowa gidan a motar RK. AA ne ke driving ɗin, samun waje yay yayi parking hankalinsa duk akan Maanal da Oum ke gyarama hijjab wai ya natse mata wuya da yawa. A tare suka fito, RK ya tsaya yana amsa gaisuwar su Najma, AA kam hannu kawai ya ɗaga musu ya ƙarasa inda Oum da Maanal ke tsaye. Cikin muryar nan tasa mara fitar da sauti mai ƙarfi ya furta, “Oum ina zakuje haka da safe?”.
Kallonsa Oum tayi tana murmushi, yayinda shi kuma suka haɗa ido da Maanal, sai kuma duk suka janye a tare cike da basar da juna. Dai-dai nan Oum ke bashi amsa da, “Tafsir mana Auta, koka manta ne? Kuma za'a tambaya ai daga ina haka da safe”.
“Oh na manta Oum, munje nan baya ne ganin wani fili, wajen kuma ma dai sai a hankali bai wani min ba, amma Uncle R ya dage a saya sai a gyara”.
Kai Oum ta jinjina alamar gamsuwa, Maanal kam dariya take a zuciyarta, ALLAH bata taɓa jin AA ya kira RK da Uncle ba sai yau. Shima RK daya iso wajen sai da yace, “Tab Aunty hakan ɗanki ya fara tsorona ne, wai ni yake kira Uncle yau imagen”.
Dariya Oum tayi, haka itama Maanal sai da ta murmusa. Sai kuma a hankali tace ina kwananku?”.
RK ne kawai ya amsa, tare da tambayarta yaya jiki. Shiko AA kallonta kawai yake. Haka kawai murmushin da tayi ɗin ya bashi haushi, a ganinsa miyasa zatai murmushi a gaban RK. Yi Maanal tai kamar bataga yanda ya canja fuska ba suka wuce abinsu, tunda dama tasan ai haushinta yake ji, jiyan ma dan kawai ya ganta a halin ciwo ne yasa ya sakko...
Sai a lokacin itama Mamy ta fito da tata tawagar. Babu wani damuwa a fuskar RK ya gaida Mamy, sai ya ɗan matsa gefe kamar zai amsa waya. Risinawa AA yay yana gaisheta. Bata amsa masa ba, sai alama da taima su Nuratu da ido su wuce. Haushi Nuratu taji, gashi sun gaida AA ɗin daga ita har Saheeba babu wanda ya amsawa, dama kuma da baƙin ciki da tashin hankalin maganar cikin Maanal ta kwana ta tashi. Dan da catai ma zata koma gida harta haɗa kaya sai da uwarsu ta kiranta ta kwaɓeta, tare da tabbatar mata in dai ciki ne na banza dan sai sun ɓarar da shi. Wannan ne ya ɗan sanyaya mata zuciya harta fito domin binsu tafsir ɗin.
Cike da isa da gadara Mamy dake kallon AA tace, “Saboda ban isa ba zuwa yanzu kasan daɗin mace shiyyasa bakaje har inda nake ka gaisheni ba sai anan?”.
Wani kalar kunya ce ta ratsa AA saboda furicin Mamy, wai saboda yasan daɗin mace ya rabba. Kansa dake ƙasa ya girgiza mata, sai kuma a hankali ya furta, “Ba haka bane Mamy. Tun sallar asuba bamu dawo gidan ba ni da Rafeeq sai yanzu. Amma kiyi haƙuri”.
“Kai ka sani dai, zamuje tafsir, idan mun dawo ina nemanka. Idan kuma kaƙi kazo zanzo har sashen uwar taka da kake ganin ta fini daraja na sameka ni....”
Wani irin rumtse idanu AA yayi, zuciyarsa na wani kalar rarrabewa. Sai kuma kamar wanda aka tunatar yay saurin buɗe idanunsa da har sun canja launi yana kallon compound ɗin. Ajiyar zuciya ya sauke ganin babu RK a wajen. Wlhy baya fatan wani a kaf ɗin ahalinsu