Showing 72001 words to 75000 words out of 218311 words

Chapter 25 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

tana hayewa a gadon. Tsabar yanda jikinta ke rawa bama tasan ta kamo kansa ta ɗaura a cinyarta ba, ta riƙe fuskar da tafukan hannayenta biyu tana girgiza shi da kiran sunansa.
“AA! Besty! AA! Ajwaad! Ajwaad!! Na shiga uku ni Maanal Ajwaad please ka tashi, miya faru? Ajwaad dan ALLAH ka taimakeni ka tashi”.
Ina, AA baima san tanayi ba. Wani irin kuka ta saki ta kife kanta tanayi akan tashi fuskar.........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣5️⃣




______________




.........Hawayenta da damshin ruwan jikinta na wanka suka shiga sauka masa akan fuska. A hankali cikin ikon ALLAH ya shiga motsawa, sai kuma numfashinsa ya fisga alamar farfaɗowa. A yanda ya fisgi nunfashin ne ya sakata ɗagowa da sauri. Ga hawaye na cigaba da tarara akan fuskarta. Idanunsa ya ɗaga da ƙyar ya kalleta, ya zuba mata su kamar mai son ganeta, sai dai kuma kukan nata ne ke wani kalar tsinka masa zuciya, tausayinta yake ji matuƙa.
“Dan ALLAH kayi haƙuri”.
Ta faɗa hawaye na sake ɓalle mata. Duk da azabar da yake ji a nashi jikin dan kawai ta kwantar da hankalinta sai ya saki mata wani sassanyan murmushi yana ɗan lumshe idanunsa da sake buɗewa a lokaci guda. Cike da dauriya da jarumta ya motsa lips ɗinsa a hakali. “Taimaka min na tashi”.
Kanta ta shiga jinjina masa tana share hawayen dake cigaba da gangaro mata. Duk da ya mata matuƙar nauyi da ƙyar ta iya kamashin ya haɗa da nasa ƙarfin halin ya tashi zaune. Yasan bazai iya zama a wannan halin ba, sannan kuma bazai iya cigaba da kwanciya baiyi salla ba, dan tabbas AA mutum ne mai kiyaye ibadarsa, duk runtsu bai yarda yin wasa da lokacin salla ba. Sannan ita kanta baya son cigaba da ɗaga mata hankali. Wannan wani irin yanayi ne daya ɗauka tsahon shekaru a cikinsa, haka kuma zakaga ya gama jigatarsa batare da kowa ya sani ba har ALLAH yasa ya samu sauƙi ya miƙe. Har gara ma sau biyu Fawzan ya taɓa riskarsa a halin, yayta masa faɗa tare da bashi taimako, daga nan ya sake kasancewa a takatsantsan ɗin kiyayewar hana kowa sanin a halin da yake ciki, kawai yayi imanin komai yana da lokacinsa, kowa kuma da irin jarabawarsa..


Duk da bawani iya riƙesan da ƙyau Maanal tai ba saboda ya mata nauyi haka ta lallaɓa sukaje har zuwa bayi ko miƙewa da ƙyau bai iyayi. Suna isa ƙofa ya dafe bango yace taje tai sallarta zai iya. Hawaye ta sake sharewa, ta juya kanta a ƙasa. Binta yay da kallo, sai kuma ƙasa-ƙasa ya furta, “Kina da alwala ko?”.
Tsayawa tai cak, sai kuma ta jinjina masa kanta batare da ta juyo ba. Dan hawaye ne ke ta gudu sosai a fiskarta, saboda sarai ta fahimci minene matsalarsa. Ita kuma harga ALLAH tana jin tsoro, matuƙar tsoro ta yanda bata san ya zata iya miƙa wuya domin taimaka masa ba. Dan tasan hakan ne kawai samun lafiyarsa yanda ya kamata. Har ta kimtsa tai sallar asuba bai fito ba, tashi tai taje ƙofar bayin, tai shiru tana tunanin yanda zatayi, sai kuma ta kai hannu da niyyar ƙwanƙwasawa dai-dai nan ƙofar ta zuge ya bayyana. Baya ta ɗan ja kaɗan, ta sauke kanta ƙasa ganin daga shi sai towel, sai wani ƙarami dake a hannunsa. Sosai ya zuba mata idanunsa, sai kuma ya janye a hankali ya ƙarasa fitowa a ɗan duƙe dan bai iya miƙewa da ƙyau. Da ƙyar ya iya kaiwa cikin sofa yana cigaba da naɗe ruwan kansa batare daya sake kallonta ba ya ce, “Bani dogon riga”.
Da sauri ta nufi akwatinsu, dan anan taga jallabiyu har biyu daya sanyo, ta ɗakko ta saman kawai ta iso inda yake. Amsa yay ya sanya kafin ya kunce towel ɗin a zaunen sannan ya miƙe. Kamar dai a yanda ya zauna a haka ya lallaɓa kan sallayar datai salla yayi shima. Tana zaune a bakin gado tana kallonsa cike da damuwa, hawaye kam har yanzu lokaci-lokaci sharesu takeyi. Yana idarwa baima iya yayi ko azkar ba ya lallaɓa ya dawo saman gadon ya kwanta, a waje guda ya dunƙule kamar ɗazun, kafin a hankali ya kalla Maanal dake kallonsa. Murya a shaƙe ya ce, “Zoki kwanta mana”.
Kanta ta girgiza masa. Sai ya lumshe idanu ya sake buɗewa. Muryarsa na sake komawa can ciki ya ce, “Miyasa?”.
Tata muryar na rawa ta ce, “Ban jin barci”.
“Zoki tayani to”.
Yay maganar da ƙyar yanzu kam. Kallonsa tayi, ganin haka ya sashi basarwa. Itama sai a hankalin takai kwance nesa da shi, sai dai suna facing juna sannan yanzu ba kai da ƙafa ta kwanta ba. Idanu kuwa suka zubama juna, tsahon lokaci kafin sannu a hankali nasa su lumshe, itama tun tana kallonsa har barcin ta kwasheta. Batayi wani barcin kirki ba ta farka, dan mafarki tai AA ɗin a cikin mummunan yanayi. A zabure kuwa ta tashi, sai idannunta suka sauka a kansa. Yanda ya sake dunƙule jikinsa waje guda ya sake tabbatar mata da mafarkinta. Jikinta har rawa yake ta matsa kusa da shi, tana kai hannu kansa taji wani irin masifaffen zafin da har sai da ta rumtse idannunta da ƙarfi.. gaba ɗaya sai taji tama rikice, ita ko ina zata kama a ƙasar mutane, gashi bata san inda sauran abokan tafiyarsu suke ba. Dabarar kiran wayar hotel ɗin ce tazo mata, duk da bata jin yarensu sai tai tunanin yin turanci. Haka kuwa akayi, ta sanar musu tana buƙatar wani a ɗakin da suke ta faɗi number ɗakin, bata jira amsa ba ta yanke wayar saboda yanda taga AA na yamutsa fuska da sake dunƙule jikinsa. ALLAH ko ya taimaketa sai gashi anzo anyi knocking ƙofar, babu shiri ta miƙe tana gyara veil ɗinta taje ta buɗe. Ma'aikacinsu ne namiji, bayan sun gaisa ta sanar masa mijinta ne baida lafiya ko suna da doctor dazai duba shi?. Da sauri ya ƙarasa shigowa ɗakin ganin yanda take magana a ruɗe, yana ganin a yanayin da AA ɗin yake ciki bai wani sake tambayarta ba'asi ba ya zaro waya a jikinsa yay kira. A mamakinta ko minti biyar ba'a cika ba wasu suka shigo sanye da kayan asibiti da ɗan abun ɗaukar mara lafiya. Gaba ɗaya suka ɗaga AA zuwa kan abun, shi kuma ma'aikacin yace ta ɗakko jacket ta taho dan akwai sanyi yauvkaɗan gashi safiya ce. Tashi ta jiya kawai ta yayuma ta biyo su, a tare suka shiga elevator, minti ɗaya da sakanni ta kawosu ƙasa harabar hotel ɗin, amamakinta ambulance ma na jiransu. Ciki aka saka AA itama akace ta shiga, sai ma'aikatan asibitin. Shi kuma ma'aikacin hotel ɗin da driver na gaba. Cikin sharara gudu na masifa suka iso wani ƙaton gini, da yarensu akai rubutu dan haka Maanal bata fahimci komai ba, amma dai ta tabbatar asibiti ne dan ga ambulance nan da yawa tako ina. Bata da lokacin tunani dan fitowa sukai aka shiga da AA ciki. Sai faman share hawaye take, ma'aikacin hotel ɗin nan na lallashinta da turancinsa mai fita da harshen Chaines.
Sunyi zama yakai na mintuna talatin kafin cikin ma'aikatan asibitin wani ya fito. Da Chaines yayma ma'aikacin hotel ɗin magana, sai shi kuma ya juya yana kallon Maanal da turanci yace ga matarsa nan. Kallon Maanal ma'aikacin yayi, shima da turancin ya bata takardar hannunsa yace tai signing. Bata san mi aka rubuta ba tunda Chaines ne a jiki, dan haka tai tambayar ta miye? Dan bata iya yaren ba. Su duka biyun sun fahimci tasan abinda take yi, dan haka ma'aikacin hotel ɗin ya amsa ya ciro wayarsa yayma takardar hoto, miƙa mata wayar yayi ya nuna mata inda zatai translate ya koma mata da duk yaren da take so. Godiya tai masa tayi duk yanda ya nuna mata, sai ko gashi ya koma mata da turanci. Sai da ta kammala karantawa ta fahimci komai sannan ta amsa pen tai signing ɗin ma'aikacin ya koma ciki. Bayan kamar mintina ashirin ya sake fitowa yace zata iya shiga wajensa.
Wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tare da masa godiya. Ma'aikacin hotel ɗin yace mata zai koma bakin aikinsa shima. Idan suna buƙatarsa tai magana ga ma'aikatan asibitin zasu kira hotel ɗinsu zai zo. Godiya tai masa sosai shima sannan ta nufi ciki shi kuma ya juya ya tafi.....


___________★


Siyayya ce sosai yayo ta azumi, sai dai samun gidan shiru ya fahimtar da shi matar gidan barci take yi. Bai tasheta ba dan yasan wahalar data sha a hannunsa daren jiya. Sai kawai ya shigar da komai kitchen ya juya ya fita, dan yana son zuwa ya amso nama da kifi na gidansu da ya sayama iyayensa na azumi kamar yanda yay musu siyayya da kuma nasu na nan gidan. Kusan awa ɗaya da rabi ya sake ɗauka sannan ya dawo. Mamaki ya kamashi ganin har yanzu bata tashin ba kuwa. Ledojin hannunsa ya kai kitchen, sai kuma ya nufi ɗakin barcinsu. Barcin kuwa take a ƙasan tils, yay ɗin jim yana kallonta, kafin ya matsa ya ɗan taɓata yana kiran sunanta.
“Huznah! K Huznah!!”.
Motsawa tai, tare da buɗe ido sai kuma tai miƙa tana kallonsa. Zaram ta miƙe kamar wadda ta tsorata da ganinsa, sarai ya fahimceta amma sai ya fuske. Cike da kulawa yace, “Wannan wane irin barci ne? Da alama ma ko girki baki yi ba ko?”.
Fuska ta ɗan yamutsa sai kuma ta jinjina kai alamar eh.
“Okay, ki tashi kiyi salla ga nama can na kawo da kayayyaki ki adana su. Ni naje massallaci zan taho mana da abinda zamuci”.
Bai jira amsarta ba ya fice. Da kallo ta bisa, sai kuma hawaye sharrr suka shiga rige-rigen sakko mata. Wlhy bata son mutumin nan, ko kallon fuskarsa bata sanyi. Tasan in har AA na wannan duniyar bazata taɓa son kowa ba. Ita kaɗai tasan a irin ƙuncin zuciyar da take kwana, ga Sageer ya maidata kamar jaka. Sam baya raga mata, safe da dare wani lokacin har da rana idan ya dawo gidan sai ya nemeta. In ma ta masa gardama ya murɗeta yay abinda zai yi ya ƙara gaba. Ya kwace mata waya ta rasa ta ina zataji Umminta, ta ina zataji labarin AA a bakin Sille. Ji take kamar ta kashe Sageer ta hutama ranta. Sanin halinsa na tasan inya dawo baiga ta yi abinda yace ba yasa ta miƙe. Sam bata jin daɗi, kwanciyar ƙasan tils ɗin nan ce kawai ke mata daɗi, kuma babu inda ke mata ciwo a jikinta. Wanka ta farayi tai salla. Sannan ta nufi kitchen ɗin, ta jima tana kallon kayan daya jibge mata kafin ta fara ɗaukewa cikin ɓacin rai zuwa store ɗinsu. Sannan tazo ta buɗe ledar naman. Rasama yaya zatai da shi tayi, dan aikin nan dai ba sabawa tai da yi ba a gida sai masu aiki, a yanzu ma sakata gaban da Sageer ɗin yayi ne aka ɗan samu canji. Ledan kifin itama ta buɗe, ai kamar jira ƙarnin na bugar hancinta ta wani rikice, a guje ta buɗe ƙofar baya ta fita ta fara sharara amai a ciki filawoyin wajen. Sageer dake shigowa ciki kakarin aman nata ya sashi nufo bayan cike da mamaki. Shi sai ma ya tsaya kawai yana kallonta. Sai da ta gama tai lagab a ƙasa sannan ya ƙaraso wajen, da yake akwai rijiya ata bayan ruwa ya jawo ya zuba a boket dake ajiye ya kawo mata yana mata sannu. Kanta ta jinjina masa ta ɗauka ruwan ta wanke bakinta da fiskarta, ta zuba akan filawoyin data ɓata sannan ta miƙe da ƙyar. Taimaka mata yay suka shiga, suna shiga kitchen ɗin tasa hannu ta toshe hancinta. Kitchen ɗin yabi da kallo, sai kuma baice komai ba ya shige da ita cikin falo. A kujera ta zaunar da ita, sai dai bata iya zama ba ta zamo ƙasa ta kwanta. Muryarta har rawa yake tace, “Bana son ƙarnin kifin can, dan ALLAH ka fita da shi”.
Sosai yake kallonta da mamaki, dan shi dai yasan a zuwanta gidan nan yasha sayo kifi ya kawo suci har ɗanye suyi abinci balle yace bata ci tun fil azal. “Yau kuma kifin ne zaki ce baƙya so Huznah?”.
Hawaye ya cika mata ido ta ce, “Wlhy bana so, dan ALLAH ka taimakeni ka fita da shi. In ba haka ba zan sake yin amai”.
Shike nan ba damuwa zan fita da shi tashi kici abinci”. Yay maganar yana ajiye mata ledar takeaway daya yi musu. Shi kuma ya nufi kitchen ɗin ya shiga gyara kifin da naman dan a tunaninsa sabon iskanci ne dan kar ta gyara, tunda sarai yasan halinta dan ma baya mata da wasa ne. Tsaf ya gyara komai ya zuba su a freezer ɗinsu sannan ya koma falon shima.......✍️


Hajiya Huznaty😂🤣🤣bara dai nayi shiru.








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣6️⃣




______________




.......A zaton Maanal kwantar da shi sukai a ɗaki kamar dai a Nigeria, amma a mamakinta sai taga wajene da yake duk kujeru ne da zasu iya kai goma kamar wajen masu jiran ganin likita dai haka, babu kowa a wajen sai shi kaɗai, zaune yake a ɗaya daga kujerun bayansa jingine da kansa. Idanunsa a lumse, sai hannunsa ɗaya da kanula ana masa ƙarin wani ɗan mitsitsin drip da aka rataye. Gani tai kamar ya rame mata ma, dan fuskansa yay fayau sai glowing take. Gashin kumatunsa kwance luff-luff kamar ya gyara shi. Yanda lips ɗinsa suka ɗan tattare waje guda zai tabbatar maka yau fa maza sun jigata.
Motsin zamanta a kujerar kusa da shi daf ya sashi buɗe lumsassun idanunsa datai tunanin barci yake. A hankali ya saukesu a kanta. Sosai zuciyarta ta jijjiga da ganin yanda suka kaɗe jazur har wani firi-firi suke kamar an watsa jan a cikinsu. Sai kawai hawaye suka gangaro mata, fuskarsa ya ɗan kawar gefe, alamar baya son ganin hawayen nata. Fin minti guda sannan ya ɗan sake waiwayo wa. Kan Maanal na duƙe tana wasa da yatsunta cikin juna dan ta kasa tsaida hawayen sam. Ita kanta kuma bata san miyasa take kukan haka ba, kawai dai tana jin tausayinsa.
Cike da kasala irin ta mai ciwo AA ya sauke ɗayan hannunsa da babu komai a kan haɓarta ya ɗago fuskarta, babban yatsarsa yasa ya share mata hawayen sannan ya maida hannun nasa kan hannayenta da take cuɗawa cikin juna. Dai-dai hawayen da suka sake gangaro mata na zubowa sai suka sauka akan hannun nasa. Ƙasa-ƙasa ya zubama hawayen nauyayyun idanunsa, sai kuma a hankali ya ɗan rumtse hannayen nata cikin nashi ba wani da ƙarfi ba dan baida isasshen ƙarfi sam a yanzu.
“Kin san fa bana son kuka Besty?”.
Ya faɗa a can cikin maƙoshi da ita kanta ma da ƙyar ta iya jiyosa. Hannunta ɗaya ta janye a hankali ta shiga share hawayen da bakin veil ɗinta. Sai da ta goge tas duk da wasu sun sake cika idanun sannan ta ɗago ta kallesa. Shima dai ita ɗin yake kallo ta ƙasan ido. Sam bata son kallon jajayen idanun nasa, dan haka ta sake maida nata ta risinar, muryarta na rawa ta ce, “Yaya jikin?”.
Maimakon amsawa da baki hannunta ya ɗan matsa alamar amsawar kenan. Dai-dai nan wata Nurse ta ƙaraso, sannu tama AA da Chaines, batare daya kalleta ba ya jinjina kansa, ta ɗan kalla Maanal ta ce, “Hello”. Kai Maanal ɗin ta jinjina mata tare da daga mata hannu, ita ma sai ta ɗaga mata hannun tana murmushi ta cigaba da aikinta, dan ita kam yau a karo na farko taji baƙaƙen fata sun birgeta dan gasu nan ƙyawawa da su. Ƙaramin roban ruwan ta janye ta saka wani ɗan babba amma bai kai babba na Nigeria girma ba, sannan tai allurai har uku a cikin ruwan, duƙowa tai ta kama hannun AA ɗin tana saita shigar ruwan fiye da yanda yake da. A ɗan daƙile Maanal ta janye idanunta daga kallonsu gefe. Sannan fuskarta ta ɗan canja. Dan murmushin cikin ƙirji AA yayi yana kallon Maanal ɗin data juya baya. Sai kuma ya lumshe idanunsa kawai. Ita dai Nurse ta gama tabar wajen batare data san laifinta ba. Fin minti biyu da tafiyar tata Maanal taƙi juyowa inda yake, kaɗan ya ɗan Matsa hannunta da har yanzu ke cikin nashi, shiru bata juyo ba. Ya sake matsawa, nan ma shiru. Sai kawai yay ɗan mitsitsin murmushin gefen baki da inba ma kallon ƙurulla

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login