Showing 69001 words to 72000 words out of 218311 words
Chapter 24 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
kansu kujerun bazasuyi wani daɗin kwanciya ba. Sai dai carpet ɗin dake a ƙasa. Shi kuma tana tsoron sanyi, dole dai yau ko taƙi ko taso a gado ɗaya zasu kwanta kenan. Karan farko ta ɗan kai dubanta a gadon. Ba wani babba bane can, kamar dai 6-by-6, yanda ya kwanta a gefe ta sake fahimtar ya bar mata ɗayan wajen ne ta kwanta. Batace komai ba cike da kasalar jiki data gaɓɓai ta nufi gadon, kamar mai ɗofanuwa akan wuta ta zauna kaɗan a baki-baki, sai kuma ta zubama bayansa daya juya mata ido, shima dai wando ne da riga a jikin nasa masu taushi kalar blue. Sun masa ƙyau, sai ƙamshin turarensa ke bugunta. Numfashi ta sauke ƙasa-ƙasa, sai kuma takai hannu tana jawo pillows ɗin gadon dake da yawa ta shiga jerawa a tsakkiyarsu. Ɗaya daya rage ta ajiye shi saitin ƙafafunsa sannan ta kwanta suka kasance a kwanciyar kai da ƙafa kenan. Duvet ɗin ta ɗan ɗaga ta shiga ciki, ta lulluɓe har zuwa wuyanta saɓanin shi da iya ƙafafu kawai ya rufa. A haka tai addu'ar barci, tun zuciyarta na ɗar-ɗar har barcin dai na gaske yay awan gaba da ita.
Zuwa can AA ya juya, yana kai hannunsa zai gyara duvet yaji ya tokari abu, idanun nasa ya buɗe dake cike da barci, ya ɗan zubama pillows ɗin data jera ido, sai ita kuma dake can ƙarshen gado kamar zata faɗa, dan ya tabbatar in har tai ƙwaƙwƙwaran juyi babu abinda zai hanata wantsalawa ƙasan. Kansa kawai ya ɗan girgiza, a ransa yana faɗin (yarinya idan nayi niyyar yin wani abu ba pillows ba ko block kika jera ai sai nayi) ya taɓe baki tare da maida idanunsa ya lumshe.......
_________★
GIRO
A fusace ta bankaɗe labulen ɗakinta ta fito har zanen jikinta na neman taɗeta, shi kuma ya nema kwancewa a jikin nata tai saurin yayumoshi ta soke. Cikin rawar murya data jiki ta ce, “Sailuba uban waye ya shigar min ɗakin yanzu dana fita?”.
Da farko kamar Sailuba batama jita ba, tanata tankaɗen garin tuwo da zata ɗora, sai da ta shaƙi iska dan kanta ta ce, “To Gwaggo nikam ina zan sani, nima yanzu nake dawowa sashen ina ɓangaren su Zainaba ina jiran Audu ya kawo min niƙa, wani abu akai miki a ɗakin ne?”.
A harzuƙe Gwaggo tace, “In ba wani abu akai min ba zakiga na fito ina tambaya ne. To wlhy bazan yarda ba, yanzu ƴan sauran kuɗin nan da suka rage mana ƙarshe da za'ai noma akeje aka lalube, kuma kema kin san ɗayan biyu ne, a cikin ƴaƴanki ko Haƙilah ko Sule, tunda ALLAH ya basu dogon hannu da bai iya zama waje guda sai sunyi ƴan ɗauke-ɗauke......”
“A'a Gwaggo ya zakice haka, naga ɗauke-ɗauken nan kowa ya samu dama yi yake yi, sannan yaran wasu sashen ma bazasu iya zuwa su ɗauka bane. To Haƙilah ma bata kwana a gidan nan ba tana gidanmu ne balle ace itace, shi ko Sule tun safe yace min zai tafi Suru sayen kayan sana'arsa.....”
“Siyen kayan sana'a ko sayen kayan shaye-shaye da yake koyama ƴaƴan mutane. Tunda kince basa nan sai ke ki fito da kuɗin tunda kema in kika faki ido ɗauke-ɗauken kikeyi shiyyasa gashi nan duk kin tsiyata min yaro. Lokacin da Habibu ke tare da Asiya arziƙi har zuba yake, amma ke da yake mai farar ƙafa ce bayan talauci da kika saka masa harda ciwo..”
Cikin matuƙar ɓacin rai Sailuba ta miƙe tana nuna Gwaggo. “K! Tsohuwar banza ya isheki, kodan kinga kwana biyu na ɗaga miki ƙafa ne a gidan nan shiyyasa kike tunanin dawo da tujarar taki. To bari kiji Sailu na nan da kika sani ban canja ba. Kuɗinki ɗin banza da zanje na ɗauka, kuɗin ma da wani ne ya bayar ba guminki ba, sai dai idan ɗan naki ne ya ɗauka ko shi Baban tunda shima ɗan hauma-haumar ne ai”.
Kafin kace mi rigima ta kacame tsakanin Gwaggo da surukarta Sailu. Hakan ba sabon abu bane a gidan, dan sau karo biyu Sailu na lakaɗawa Gwaggo duka. Ƴaƴanta kuwa idan kaji zagin ƙare dangi da sukema Gwaggo bazaka taɓa yarda kakarsu data haifi ubansu bace ba.
Sosai sashen ya cika da matan gidan, maƙota ma na leƙe ta katanga. Abin zai baka mamaki yanda kowa Sailu kawai yake bawa haƙuri, duk da kuwa zagin da take surfama Gwaggo a gaban kowa. Kuka Gwaggon ta sanya yuuu-yuuu tana rantsuwar yau sai Habibu ya saki Sailu a gidan, idan ba haka ba sai ta tsine masa.
Sailu dake ɗura mata zagi ta ce, “A hayye nanaye koba saki ba. To maza sakashi ya sake nin kiga idan zai iya. Ko an gaya miki ni Asiya ce kukarki mai daɗin hawa. Iyayenta sun muku bauta sun gina ɗanki kunci amanar zuminci, to wlhy Talle ni nafi ƙarfinki, ke wanda ma ya fiki nafi ƙarfinsa. Tsohuwar banza da bata iya komai ba sai sa ido, ɗanki na kwanciyar aure dani kina leƙenmu ta taga saboda ke kwartuwa ce....”
Ai gaba ɗaya gida ya ɗauki salati da sallalami, yayinda Gwaggo ta fashe da kuka tana rantsuwa sharri Sailu take mata. Amma ina kowa yaƙi saurarenta sai aibantata akeyi akan wannan al'amari, saboda kowa dai ya tabbatar Gwaggo zatayi abinda yafi hakan. Ana cikin hakan wani matashi ya shigo, agaba ɗaya shekarunsa basu wuce goma sha ba. Amma abin tausayi da mamaki a kallo ɗaya zaka gane shaye-shaye ya gama kassara rayuwarsa. Ga raunuka a jikinsa na tabbacin wuƙace da sauransu. Sule kenan, da ake kira da AUTAN MASHAYA a garin na giro. Wasu kuma suke ƘARAMINSU BABBANSU. Dan kuwa Sule hatsabibin yaro ne na gaske, baya ji ƙwarai da gaske, ga sata ko ɓera albarka, dan duk iya tattalinka da kayanka idan Autan mashaya ya ƙyalla ido a kansu sun zama ba naka ba. Baya tsoron kowa a garin baya shakkar kowa. Idan ma ka cika takura masa koda da kallo ne kaɗan daga aikinsa ya maka zanen yarbawa a fuska koya tsiyayar maka da idanun. A ƙarancin shekarun nan nasa ƙaramin dila ne na kayan shaye-shaye anan cikin ƙauyen har ma da ƙauyukan kusa da su, babban tashin hankalin da ƴan garin suke ciki yanzu yanda yake koyama yaransu ƙanana masu tasowa shaye-shaye, a yanzu haka bawai ya gama kaiwa cikakkun shekarun balaga bane, amma yasan yanda zai tarfa mata a lungu ya mammatse koda kuwa matan aure ne, kai koda tsoffi ne. Dan ita kanta Gwaggon ya taɓa matseta a cikin ɗaki wataran taita ihu tana neman taimako, kafin wani ya shigo ya ware ta taga, daya faɗa uwarsa ta ƙaryata.
“Wai lafiya naga an tarar mana a part ɗinmu ne?, kufa wannan zuri'ar na fahimci kun fara zama ƴan tsugudidi”.
Sule ne ke maganar cikin yanayinsa na ƴan daba........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣4️⃣
______________
.......Cikin ƙanƙanin lokaci taron ya fara watsewa, dan tsoronsa kowa keji kamar mutuwa, tsabar makirci sai lokacin Sailu ta ɗaura hannu aka ta ƙwallara kuka. Cikin wani irin zaro idanu Sule ya ce, “Kai! Ikon wahabu, k! Tsohuwa ince dai lafiya kike irin wannan tsuwwar haka. Shin ko dai Baba ya wulla ne na fara shirya bikin fatin cin gado?”.
Kukan Sailu ta sake fashewa da shi, sai kuma ta nuna Gwaggo da tun shigowar Sule tai lakur na tsoro. “Ba kakarku bace tace wai ka shiga ɗakinta ka saci kuɗi, shine ta tara mutanen gida tanata zagina, harda cewa sai ka shiga wuta kai da Haƙila da ni, wai mun zame mata jaraba babanku ya talauce sanda Asiya na tare da shi kuɗi har zuba suke a ƙasa..”
“Kan uban can kai.. ke tsohuwar nan ko, to wai ma tsaya Babanmu, da take faɗar haka ita ma ai wutar zataje, bakiga fuskarta ba tafi kama data ƴan wuta. K! Wlhy Talle idan baki daina sanya mana ido a gidan nan ba sai na miki sabuwar kaciya da gatarina, shegiya mai suffar kwaɗi. Kuɗi kuma na ɗauka zan ƙara jari ne, idan kin isa ki ƙara magana ALLAH kinji na rantse ko sai na juya fuskarki daga gaba ta koma baya. Dalla shige daga ciki zanyi lissafi....”
Ai da gudu Gwaggo ta afka ɗaki ta danno ƙofa, jikinta sai rawa yake kar-kar harda ɗan fitsarinta a cikin zani. A waje ko tuni sule yaja tabarma ya baje kayansa dake cikin jakar daya ratayo. Ba komai bane sai ƙwayoyi da ganyen tabar wiwi. Ko'a jikin Sailu ta koma ta zauna ta cigaba da tankaɗenta tana kallonsa. Idan ma taga wata tabar tafi wata da yake ƙullawa sai ta ce, “Waccan kamar tafi sauran yawa ɗan baba. Kodai wani ɗan ludayina ƙarami zan baka yanda zaka dinga gane gwajin?”.
“Eh to kema kinzo da shawara kawo, idan naga kuɗin ya fita ribar da ɗan auki zan baki ƙulli ɗaya ki busa”.
Dariya Sailu tai tana miƙewa. “A'a ɗan baba rabani da busawar nan. Wannan ai sai ku ƴan zamani, mukam tafi ƙarfin mu”.
Dariya ya ƙyalƙyale da ita da faɗin, “Babanmu kefa dama tuni na fahimci kanki ƙarami ne, tun randa na baki zoɓon nan nawa da zaƙami a ciki kika baje kikaita barci har kwana uku nace tabb Babanmu fa ta bazu da yawa”.
Nan ma dariyar takeyi daga ɗaki. A haka ta fiddo masa da ɗan ludayi na cikin madarar jarirai ta miƙa masa. Ya ce, “Yauwa uwa maba da mama, kinga ko gashi ɗan kif-kif abinsa. Zako kici burodi anjima da shayi da ƙwan wajen kalla”.
Daɗi sosai Sailu taji, ta shiga sanya masa albarka. Duk abin nan da akeyi fa Babu na gidan, a kwance yake baida isasshen lafiya, dan ranar ma daga gona sai ɗakkosa akayi. Hawaye ne suka shiga gangaro masa, rayuwarsa da Ammie da ƴan ƴaƴansu uku ta faɗo masa a rai.......
Hummmm, kowa ya tuba dan wuya ba lada😮💨😮💨🥱
____________★
Alarm ɗin daya saita musu domin tashi sallar asuba ne ya farkar da su. Cikin kasala irin na mai barci ya buɗe idanunsa da sukai masa nauyi sosai. Fin minti biyu kafin ya yinƙura ya tashi zaune bakinsa na ambaton sunan ALLAH. Hannu ya kai ya kunna lamp dake a bed side drawer. Hasken ya bashi damar sauke idanunsa akan fuskar Maanal dake facing inda yake. Samun kansa yay da zuba mata idanun, fin mintuna biyu kafin ya matsa sosai, kishingiɗa yay akan hannunsa daya tokare kansa da shi yana facing ɗinta sosai fuskokinsu dab-da-dab dan sai da ya janye filon wajen. Yatsarsa ya kai saman tsukakkun lips ɗinta ya shiga zagayawa, yaja fin minti ɗaya yanayi kafin ta fara motsawa kaɗan-kaɗan, sai kuma idannunta suka fara rawa, da ƙyar ta shiga ɗagasu sama a hankali tana buɗewa. Da farko shaaa take iya ganinsa, sai kuma sannu a hankali idon ya washe ta ganshi da ƙyau. Cike da wani irin kasala da shauƙi ta zuba masa idanun nata da suka sake shanyewa saboda sanyi, shima dai kallon nata yake da nasa dake a raunane kamar wanda yasha kafso yay marisa. Wani irin kallo sukema juna mai kassara garkuwar jiki dana ɓargo, mai saukar da kasala da tsitstsinka jini. Illahirin gaɓoɓin jikinsu na sakewa a lokaci guda.
Cikin wani irin motsa lips kaɗan ya furta, “Amarya mai rowa”.
Sosai taji ƙirjinta ya buga sakamakon yin maganar tasa, babu shiri ta waro idanun gaba ɗaya domin tabbatarwa bafa a wancan yanayin bane, domin kuwa mafarkinsa take yi a like yanda yake a kusa da itan nan sai kuma gashi ɗin reality. Yanda ta waro idanun shima sai ya ɗage mata gira ɗaya sama yana mata irin kallon (Miye kike kallona ba haka bane?) ɗin nan. Hakan da yay ya sake tabbatar mata reality ɗin ne fa ba a mafarkin ba, ai da sauri tai yunƙurin juyawa zuciyarta na dumm-dumm.
Hannunsa ya ɗaura akan jikinta ya taro fuskar tata ya hanata juyawa, jitai gaba ɗaya tama gama daburcewa, ga wani yanayi na saukar mata a cikin jiki. Wannan yanayin ta jima tana fuskartarsa a tare da ita musamman lokacin gabatowar asubahi har zuwa safiya. Wani lokacin takanji kamar tayi kuka saboda yanda take shiga matsuwa da son kasancewa kusa da abokin halittarta. Tsaf AA yake wani binta da kallo daki-daki, dan ya fahimci halin da take a ciki itama sarai a idanunta. Samun kansa yay da ɗan murmusawa kaɗan, sai kuma ya sake matsar da fuskar tasa gab da tata suna busama juna numfashi. Rawa jikin Maanal ya nema farawa, hakan ya bashi damar janye filon dake ta wajen cikinsu ya matsota jikinsa kawai ya rungumeta, bai wani jira maida ba'asi ba ko bata dama ya manne lips ɗinsu waje guda. Da wani kalar sanyi jiki da na yanayin asuba yake sumbatarta, yanyinda itama yanayin da take a ciki ya sata shagaltuwa ta fara ƙoƙarin miƙa masa wuya. Sai kawai yaji ya ƙara rikicewa...
Tafiya tayi tafiya ya fara ƙoƙarin kai hari wani sashin daban, a lokacin ne ta nema dawowa a hanyyacinta, sai dai duk yanda taso janye jikinta hakan ya gagara. Kanta ta shiga girgiza masa tana ƙoƙarin ture masa hannu, sai ga hawaye sharrr-sharrr na sauka har a fuskarsa. Jikinta kuwa rawa yake na tsoro, dan brain ɗinta ƙoƙarin dawo mata da wani abu daya shuɗe a shekarun baya take yi. Sosai yanzu ta fara kicin-kici, a wannan yanayin ta buge masa ƙasan ciki da gwiwar ƙafarta batare da ta fargaba itama, dan da gaske AA tunaninsa yayi nisa da duniyar da take ciki.
Babu shiri kuwa ya saketa, saboda wata azaba data ratsa masa jiki har zuwa tsakkiyar ƙwaƙwalwa. Jikinsa ya dunƙule a waje ɗaya ya riƙe cikin da duka hannaye biyu ya rumtse ido da matuƙar karfi. Dan tabbas badan ya kasance jarumin gaske ba babu abinda zai hana ya fasa ihu. Amma ina jikinsa ne kawai ke ɗanyi kamar yana rawa... Maanal kam data samu ta kuɓuta tsoro ne ya sakata direwa a gadon, cikin sauri ta wuce bayi. Tana maida ƙofar ta rufe ta jingina a jiki jikinta na karkarwar tsoro hawaye na bin fuskarta. Ji take kamar zai biyota, dan bata taɓa ganin AA a irin wannan mugun yanayin ba, tru-tru fa ya fita a yaccinsa ƙoƙarin isa inda zuciyarsa ke raya masa kawai yake yi. Ina bata shirya hakan ba, wlhy bata shirya ba, da gaske tsoro take ji, matuƙar tsoro. Duk yanda jikinta ke nuna mata buƙatuwa da irin wannan yanayin ko'a film in tana kallo taga kiss ya fara wuce na hankali sai kaga jikinta ya fara rawa tsoro ya kamata, dan wancan abun daya faru a waccan ranar ne yake dinga dawo mata, wani lokacin sai take jin ma kamar zata suma dan tsoro. Shiyyasa bata iya sakin jiki ta kalla film ɗin turawa musamman na soyayya. Gara na faɗa yafi bata kwanciyar hankali. Kai ko'a karance-larance novels ɗinta bata taɓa karanta irin wannan wajejen. Idan kuma ta fahimci book yayi shaiɗanci da yawa gara ta haƙura dan English novels ba komai zaka samu ana ɓoye ba...
Ita kanta bata san adadin lokacin data ɗauka a wajen ba, dan ƙafafunta har sun fara sagewa. Sauran guntun hawayenta ta share, kafin cikin ƙarfin hali ta ƙarasa shigewa bayin. Dole cikin gilashin da ake wanka ta shiga, ta sakarma kanta ruwa kawai batare data iya cire kayan barcin ba. Ratsatan da ruwan keyi yasa ta fara sakin ajiyar zuciya a jajjere, wani irin tausayin duk yarinyar da akama fyaɗe na sake raunana mata zuciya, dan wanda ya fuskanci ƙalubalen kawai yasan mi ake ji koda gwada yimasa akai ba'ayi ba kuwa. Ta jima ruwan na dukanta, sai da taji nutsuwa matuƙa sannan tai wanka sosai ta kuma tsarkake jikinta dan dole tai hakan, bathrobe ta ɗauka ta sanya, ta ɗaure igiyar da ƙyau, taji daɗin yanda ya saukar mata ƙasa sosai. Sai kuma taja towel ta naɗe kanta sannan ta fito a ɗakin cikin ɗari-ɗarin zuciya.
Sai da ta ɗan kalla cikin ɗakin taga babu alamar shi sannan ta fito gaba ɗaya, tayi ta wajen gado kaɗan dan ɗaukar kaya ta koma bayin ta sanya a mamakinta sai ta gansa duƙunƙune a yanda ya barsa, gashi babu alamar ma yana motsi. Gabata ne ya faɗi, cikin tsoro-tsoro ta shiga matsawa da sanɗa, har tazo jikin gadon bai motsa ba, ta ɗan duƙo ta leƙa fuskarsa, idanunsa a kulle suke, kuma sai taga kamar baya numfashi da gaske. Kamar mai tsoron taɓa wani mugun abu haka takai yatsarta saitin hancinsa a slowly. Tai ɗan jimm tana saurare, sai taji da gaske fa baya numfashi sam.
“Na shiga uku ni Maanal”. Ta faɗa a gigice