Showing 192001 words to 195000 words out of 218311 words

Chapter 65 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

murmushi tayi, shima aikin gyaran kitchen ɗin ya fara tayata, suka gama suka dawo falo har can sama da bedroom ɗin da suka kwana duk da ba wani datti bane sai da suka gyara komai tsaff suka saka turaren wuta da air freshener sannan suka shiga wanka a tare. Sun jima a bayin dan sai da ya ɗan mommore sannan suka fito. A tare suka taimakawa juna wajen shiri abin sha'awa. Tsaf suka fito abinsu suna uban ƙamshi. Ƙananun kaya ne a cikinsa da sukai masa ƙyau sosai. Ita kuma sai ta saka Abaya da itama tai mata ƙyan. Fita sukai a sashen gaba ɗaya zuwa sashen Abah. Acan suka samu Oum da babban Yaya, Yaya F dai tasan yana can yana barci yau weekend.
Abah ya kasa ɗauke idanunsa a kansu, hakama fuskarta a washe take da murmushi. Cike da girmamawa suka zauna a ƙasa, Manaal kusa da Abah AA kusa da Oum. Babban Yaya da shima ke kallonsu da murmushi ya ce, “Aunta na Auta”.
Hannu Maanal tasa ta ɓoye fuskarta. Aba dake ƴar dariya ya ce, “Auta kam na auta.”
Shima dai AA murmushin yake yi. Cikin haɗa baki shi da Maanal ɗin suka shiga gaida Abah. Ya amsa musu da kulawa yana sanya ma Maanal albarka da hidima. Hakama Oum ta sanya mata albarka. Shima Babban Yaya albarkar ya saka mata. AA ya ce, “Abah tare fa mukayi, naga sai ita jaɗai ake sakama albarkar”.
Cikin waro ido Maanal ta ce, “ALLAH Besty kaji tsoron ALLAH. Kana zaune kana surutu dai nayi”.
“Oh rinto ma zaki min kenan?”.
“Kai ne dai zaka min rinto”.
Dariya sosai Abah da Babban Yaya da Oum ke musu. Babban Yaya yace, “Ni dai na yarda Lilly na kawai tayi, Aunta gaskiya bama son runto”.
Maanal ta ce, “Yauwa Yaya ai dama kasan halinsa dai”.
Abah ya ce, “Nima ina bayanki Auta. Shi dama girkin ba wani ya iya bane”.
Oum dake dariya ta ce, “Ato bara dai na shigarma Auta nima. Idan ta gaskiya za'ai shi fa ma ya koya mata girkin nan”.
“To Oum tuna musu dai idan sun manta. Amma ba komai yau an min 1-0 next”....


__________★


Abin duniya ya ishi Mamy ƙwarai da gaske, tana son zuwa wajen Abah tana jin tsoro. Bata son kuma taje taga Oum tare da shi. Gashi ta ƙagu da jiran kiran Hajiya Turai amma shiru kake ji. Maman Saheeba na son wucewa itama tana tsoron ko Hajiya Turai bata gida ne. Amma dai haka ta shirya dan bata kuma ƙaunar su haɗu da Abah. Ta nema Saheeba ta kaita ita ko ta murje ido tace aa wlhy ba inda zata Babban Yaya yace ko nan da gate taje zai bata mamaki. Wannan abu ya matuƙar bama Nana mamaki kuma ya ƙona mata zuciya. Haka ta tattara ta fito, kasa zuwa yima Oum sallama tayi, Nuratu dai ta rakata bakin gate itama ta dawo, dan hakankalinta a tashe yake ita duk yau bata ga AA ba a gidan.
Maman Saheeba ta fito daga gidan Darma idanunta suka sauka akan Babban Yaya da Ameerah a mota zasu shiga gidan Hajiya Shuwa da alama daga wani wajen suke. Sai AA da Maanal su kuma zasu fita amma sun tsaya suna magana da su Babban Yayan. Maanal ce ke driving ɗin. Mamaki ne ya kamata, tai tsaye tana kallon ikon ALLAH har Babban Yaya ya gama shigewa da motar. Manaal na ƙoƙarin wucewa itama ta hango Maman Saheeba ɗin. Sai ta ɗan yo reverse kaɗan. AA ya ɗago zai yi magana yaga ta tsaya saitin Maman su Nuratu. Cikin girmamawa Maanal tace, “Aunty zaki fita ne?”.
Kamar Maman Saheeba bazata amsa ba sai kuma tace eh.
“Bismillah ki shigo sai mu saukeki”.
Sosai abin ya bama AA haushi, amma yay banza bai tanka musu ba har Maman Saheeba ɗin ta shiga suka wuce. Sai da suka bar street ɗin sannan Maanal ta tambayeta ina zasu kaita. Cike da isa ta gaya mata. Takaici ya ƙara kama AA, dan sam tafiyar tasu ba ɗaya bace ba. Maanal kuwa ko'a jikinta duk da taga ya canja fuska. Haka ta nufi gidan su Nuratu duk da tana tunanin ba lallai ta gane ba. Amma cikin ikon ALLAH sai gashi ta gane. Abin tsautsayi Maanal na gama tsayawa a gate ɗin dan batai niyyar shiga ba sai ga Sille ta fito a gidan da waya a kunnensa, saƙo wani yaronsa ya kawo masa yake son amsa ya koma. Tsaiii AA yay yana binsa da kallo, hakama Maanal. Itama kanta Mamman Saheeba kallon nasa take tana mamakin ina kuma Hajiya Turai ɗin ta samo wannan da kallo ɗaya zaka fahimci taƙadari ne. Shi ko Sille baiga su AA ba, sakamako bai san motar ba dan ƙaramar motar Maanal ce ta cikin lefe, gata tinted glass, sune kawai suke iya ganinsa. Hankalinsa kwance yay wucewarsa da tunanin tarkacen Nuratu ne tunda ya santa da masifar jaye-jaye. Bai lura da Maman Saheeba ba harta shige, dan bata side ɗin da take yake ba. Motar Maanal tama key ta bar ƙofar gidan, suka sake wuce Sille dake tsaye tare da yaronsa suna magana. Sai AA cayay “Niko kamar nasan fuskar nan fa Besty”.
Kallonsa Maanal ta ɗanyi, sai kuma ta maida hankali a titi. “Kai Besty a ina kuma? Kana ganin mutum da zubin ƴan jagaliya. Ni wlhy tsoro ma ya bani jibeshi kamar irin baƙaƙen ƴan iskan amerikawan nan. Jiki duk tatu.”
“Oh kallonsa ma kika tsaya yi kenan?”.
Yanda yay maganar a tunzure ya saka Maanal yin murmushi. Cikin kwantar da murya ta ce, “Rufa min asiri mizan kalla a wannan ƙazamin, nida nake da namijin gaske gashi kuma a gefena. Kawai dai suffarsa batai kama da mutanen kirki ba, sai nake ta tunanin mima ya kaisa gidan ma”.
Baki AA ya ɗan taɓe kamar bazai tanka ba, sai zuwa can yace, “Ai ƴar kasuwa ce matar, duk kuma wani tarkace ƙya sameshi a wajen sayen kayanta tunda tana tare da ƴan siyasa.”
“To ALLAH ya ƙyauta. Mu dawo batun su Babban Yaya. Besty anya babu wani abu tsakanin Babban Yaya da Ameerah”.
Yanzu kam kallonta AA yay sosai, sai kuma ya murmusa da faɗin, “Da nayi farin ciki ƙwarai da gaske ALLAH Besty.”
“To ALLAH ya tabbatar mana da alkairi, dan gaskiya nima zanyi farin ciki. Shike nan kaga gida ya zama kowa da mata biyu”. Dai-dai sun iso inda zasu tana ƙoƙarin parking tai maganar. Murmushi AA yay tare da kwantowa jikin kafaɗarta, sai kuma a hankali ya kamo hannunta cikin nashi. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Ni dai na auri Autar mata.”
“Uhm daɗin bakin maza”.
“Oh mu maza har daɗin baki ne damu?”.
“Sosai ma, musamman a wajen ƙara aure baku da gaskiya”.
Dariya ta bashi, amma baiyi ba ya murmusa kawai. Daga haka suka fito fuskar Sille na masa kai-kawo cikin idanunsa har yanzu. So yake ya tuna shi amma har yanzu ya kasa haskowa. Abinda kawai ya sani ba'a Abujan nan ya sanshi ba, sanin kuma ba yanzu ne yay masa ba shekarun baya ne..........✍️










*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣5️⃣




______________




.........Haushi sosai Hajiya Turai taji da ganin Maman Saheeba, amma sai ta dake suka gaisa, koda Maman Saheeba ke sanar mata ai sunata kiranta a waya tun ɗazun sai tace ta fita ne yanzu take dawowa. Akwai kayan ta da suka ɓace a airport shine sukaje ake nema ga mai kayan ma har yazo amsa yanzu. Dan tasha jinin jikinta tabbas sunga Sille. Aiko sai cewa Maman Saheeba tai, “Ko shine ma mukaga yana fita yanzu”.
“A eh kwarai shine! Shine!”.
“Kai wanan kasuwanci naku kuna ƙoƙarin, ai ni wannan mutumin sai ya firgitani”.
Cikin murmushin yaƙe Hajiya Turai tace, “To mu da muka kasa a siya ina ruwanmu da s....” maganar ta maƙale saboda shigowar Sille..
Daburcewa Hajiya Turai tayi, haka shima sai ya tsaya turus yana kallon Maman Saheeba, dan ya santa, kai kaf dangin Mamy ma ya sani saboda a biye yake da komai nata tsahon shekaru, sune dai basu sanshi ba sai ita Hajiya Turan. Cikin in ina Hajiya Turai ta ce, “Yauwa ka dawo? Dama nace ko na ɗakko maka wanda ke hannuna kafin wancan su fito?”.
Shiru Sille yay bai tanka ba, sai ma zaune da ya kai a cikin kujerar. Hajiya Turai data fahimci mi yake nufi saita kalla Maman Saheeba. “Nana muje ciki, idan na ƙarasa da shi zan shigo”.
Miƙewa kuwa tayi zaram dan dama harga ALLAH a tsorace take ita kam. Yo kallon idanun Sille kawai abin firgitarwa ne. Tana shigewa Hajiya Turai ta tabbatar ta shige ɗin ta dawo kusa da shi cike da tashin hankali da lallashi ta ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri Baby, wlhy ban san zata zo ba, nima ganinta kawai nai yanzu”.
Batare da ko kallon Hajiya Turai ɗin yayi ba a daƙile ya ce, “Ki sallameta yanzu nan ta koma inda ta fito kota kama gabanta, dan ban gama abinda nake ba bazan tafi saboda wata banza ba matsalarku ce”. Ya miƙe abinsa ya wuce bedroom ɗinta yana wani tafiyar rangajin iskanci. Ji Hajiya Turai tai kamar ta sanya kuka, amma tasan dole ne ta sallami Nana kamar yanda ya faɗa dan bazai bar gidan ba kuwa.
Mamman Saheeba na a ɗakin da take sauka idan tazo Hajiya Turai ta sameta. Fuskarta ta ƙawata da murmushi tana kallonta. Sai kuma ta ce, “Kinga ko kinzo a dai-dai, dama akwai ticket dana saya yau zan je Kano sai batun kayan nan ya shigo, dole zan canja na tafi Lagos anjima dan wai kayan nacan. Ga mutumin nan bai da kirki ya bani daga yau ne zuwa gobe kayansa kawai ko kuɗinsa. Ni kuma na cinye kuɗin, tare ma zamuje lagos ɗin da shi”.
Cikin rashin damuwa Maman Saheeba tace, “Ai kije Lagos ɗinki kawai ki dawo zan zauna abina. Saina kira Nuratu ta tayani zama”.
Hajiya Turai ta danne takaicinta ta ce, “Ai bazai yiwu ba Nana, mutumin nan yaje yay bi baya ko yasa azo a cutar daku, shiyyasa ma naji daɗin da Nuratu bata gidan. Baya ji fa cikin Abujan nan kaf tsoransa ake ji, nima tsautsayi wani ministar ne ya taɓa aikosa amsar kaya a wajena shine sanadin da ya fara sayen kayan shima ga shi nan ya zame min alaƙaƙai. Dan haka faka-faka shirya mu wuce airport nima daga can zan wuce.”
Sam ba haka Maman Saheeba taso ba, gashi bata son komawa gidan Darma tana kunyar haɗuwa da Abah. Ga al'amarin nan na babban Yaya da ƴar Hajiya Shuwa ya tsaya mata a rai. Ƙin gaisheta da AA yayi, har ma ta shiga motar ta fita bai nuna ya santa ba nan ma ya zafeta. Haka dai ta shirya badan taso ba Hajiya Turai ta ɗauketa suka tafi airport. Suna isowa sai ga kiran Mamy ya sake shigowa Hajiya Turai, kaɗan ya rage taja tsaki ALLAH dai ya kiyaye. Koda ta ɗaga cike da wayancewa taba Mamy haƙuri da tsarata kamar yanda ta tsara Maman Saheeba. Mamy tace “Ba komai, dama wani hoto na tura miki ta WhatsApp dan ALLAH idan ban takuraki ba ɗan duba ki gani yanzu”.
Babu musu Hajiya Turai ta shiga WhatsApp ɗin kuwa tana faɗin, “Haba ba komai ai” dai-dai tana buɗe hoton dan bata yanke kiran ba. Ta ce, “Wannan ai Ra'iz ne. Badai zancen first night ɗin yaran nan bane ke neman tada ƙura?”.
Mamy da abin ya daketa cikin dauriya ta ce, “Shine kuwa Hajiya Turai, ina son nasan gaskiya kafin Aban su Ajwaad yace zai yi bincike. Kinga dai ƴan uwansa duk suna a gidan nan maganar nan ta fito, wannan shirun nasu kuma na tabbatar akwai wata a ƙasa. Ina Ra'iz yanzu? Ina son naji shin da gaske baima yarinyar nan komai ba a wacan ranar amma ya amsa mana yayi.”
“Tab babbar magana. A yanzu Ban san ina Ra'iz yake ba gaskiya. Dan tun bayan aikin nan wata alaƙa bata sake haɗamu ba”.
Ji Mamy tai kamar ta zandara ihu. Amma ta danne da ƙyau zuciyarta sai bugawa take. Cike da damuwa ta ce, “Lallai akwai matsala Momyn Nuratu”.
“Amma ni sai nake ganin abun duk mai sauƙi ne. Ki zauna da shi Ajwaad ɗin mana. Nima kuma zan bincika inda Ra'iz ɗin yake”
“Zama da Ajwaad ba shine mafita ba shiyyasa ma ban masa ko zancen ba har yanzu. Kin san wannan matsiyacin yaron Rafeeq ne ya baza musu zancen yarinyar virgin ce. Ina da tabbacin koshi Ajwaad ɗin babu wanda yay maganar da shi akan hakan har yanzu, alamun akwai abinda suke shiryawa. Nasan su wanene wannan family ɗin Turai, wlhy akwai damuwa. Gashi na saka a bincika min Dr Tofa ɗin ma har yanzu babu wani bayani. Idan nace kuma zanje Kanon da kaina a yanzu akwai damuwa”.
“In dai dan wannan ne ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe zansa a bincika mana Dr Tofa ɗin shima”.
Mamy ta ɗan ji sanyi a ranta, amma zuciyarta a birkice take fiye da farko. Tana ajiye wayar zufa na keto mata. Gadai Hajiya Turai ta tabbatar mata yaron da suka saka aiki ne akan Maanal. To miya haɗashi da Junaid kuma? Sannan Junaid bai san da zaman jaririn can ba taya za'ai hotunan su su kasance tare a wajen mutum ɗaya? Yau ta shiga uku mike shirin faruwa da ita? Ga batun Abah na ɗaga mata hankali. Kada dai ace abubuwa ne zasu rikice mata a gaɓar da take ganin nasararta zata fara, ƴaƴanta da komai nasu zai dawo tafin hannunta. Mijinta da take ganin ta gama nasarar wawashe zuciyarsa gaba ɗaya zuwa yanzu amma zai suɓuce mata. Wai wanene wannan mai tura mata saƙon? Wanene shi? Miyyasa zai shigo duniyar ta a gaɓar samun nasararta da ribantuwa da wahalhalunta da haƙuri da juriya da tai na shekaru aru-aru. Mafita ɗaya gareta a yanzu ta sanin wanene shi? T kuma yarda su gana kamar yanda ya buƙata, to amma idan ta amince lokaci guda zai ɗauketa shashasha. Bari ta ɗan latsashi na wani lokaci kamar bata damu ba. Kuɗi kuma bai isa ya ci su ba....


__________★


Gaba ɗaya Yazeed baya gane komai a yanzu sai umarnin mahaifin matarsa. Ji yake ko wuta yace ya faɗa zai faɗa domin faranta masa. Nazeefa kuwa wata irin soyayya yake nuna mata kamar ya cinyeta. Balle da maganar cikin jikinta ta bayyana. Ita kanta sai abinda tace yayi yake yi. Dan haka take mugun tatsarsa kuɗaɗe, tana daga kwance shike mata tausa shine fita sayo mata abinci, shine mata wanki kai komai daya kamata tama kanta, tai masa matsayin matar gida yanzu shine keyi. Ga itama Sabuwa na zuba nata capacity ɗin a gefe. Sai da suka tabbatar sun gama samunsa a yanda suke so, sannan suka dawo gida Nigeria. Dawowar tasu kuma ta kasance rana ɗaya da dawowar su Ammie da Daddy suma.
Sosai Daddy ya zubama Yazeed ido, yaron ya rame yayi duhu daka ganshi kasan baya a cikin hayyacinsa. Ji Ammie tai ƙwalla sun cika mata ido, dan a wannan dambarwar dai shi Yazeed shi aka cuta wlhy, tana ƙaunar Yazeed tana tausayinsa, dan yaron ya taka rawar gani a rayuwarsu suma, kuma in sha ALLAHU ta ɗauki aniyar taimaka masa a wannan gaɓar, bazata so cigaba da ganinsa a wannan yanayin ba. Daddy kam bazaka taɓa fuskantar komai a fuskarsa ba. Amma shima al'amarin Yazeed ɗin na matuƙar damunsa a zuciya. Sai dai ya zuba ido ne dan Hajiya Yaya taji a jikinta. Sai dai tabbas bazai yafe mata ba, dan ta cutar masa da yaro. Ɗansa babba abin sonsa, mai hankali da nutsuwa ga jin ƙan iyaye ta zama sanadin da aka maida masa shi ƙarƙashin ikon mace..

Yaya Yazeed kam sai yaji kunyar ganin Daddy da Ammie, dan ko wancan dawowar har suka sake barin ƙasar bai bari sun haɗu ba duk da gida ɗaya suke kwana suke tashi. A mamakin Nazeefa sai taga yaje yana gaida Daddyn da Ammie. Wannan abu ya mata zafi, fuuu ta wuce sashensu batare data gaida Daddyn ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login