Showing 171001 words to 174000 words out of 218311 words

Chapter 58 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

wanda Maanal ɗin tai ƙyau dan sai yau ne itama take kallon bikin, duk yanda ake zuzuta abin a media ta kasa kalla saboda takaici, a fili ta furta, “AA Darma humm? Wai wanan shegiyar yarinyar taya take kame zukatan maza ne haka?”. Sosai taji hassadar Maanal na sake ƙarfin tasiri a zuciyarta, dan sam ba haka taso ba, da akai haka kuma na nufin ta cita wasan kenan. Idan har zataci nasarar amshe Yaya Yazeed a hannunta ta kuma samu AA Darma lallai anyi ba'ayi ba kenan. Sosai ta cije lips ɗinta tana jin tamkar ta fasa ihu dan takaici da ƙarin tsanar Maanal babu gaira babu sabar.........✍️


_Haka fa wasu suke a rayuwa. Koda baku da alaƙa ta zahirin rayuwa, ko wani ɓangare ya alaƙantaku da alaƙar marar ƙarfi, koda sun ci nasara a kanka a bisa dalilin ƙaddararka, idan ka samu cigaba daga abinda suke ganin sun amsa a hannunka maimakon su haƙura da bibiyar rayuwarka sai su cigaba da girmama hassadarka a ransu, dan su a nasu hauka tunda suka ƙwata a farko, burinsu ka ƙasƙanta a bisa wanda zaka samu a gaba domin su sami damar cigaba da maka dariya. Ya arrahaman duk wanda sharrine a rayuwarmu ka nisantamu da shi, idan mun sanshi ka rabamu, idan bamu san da zamansa ba ka hanamu saninsa na har abada🙏._













*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
AJIYA A DUHU


84


.......Saƙo ya isa ga Mamy dai-dai da shigar Saheeba sashen tana kuka. Bata kula su Mamanta dake a falo zaune ba ta danna kai cikin bedroom ɗin Mamy, a lokacin ɗayar mai aikinta tana bata ledar da maigadi ya kawo tace saƙone mai delivery ya kawo. Da ɗan mamaki a fuskar Mamy dake kumbure har yanzu ta amsa ledan, dan tasan ita dai bata da wani order a waje gaskiya. Sannan batai da kowa zai aika mata saƙo ba. Ita duk yau ma bazatace tabi takan waya ba. Zata buɗe ledan kenan Saheeba ta faɗo, su Mamanta da suka biyota biye da ita.
Cikin tsawa Aunty ta ce, “K lafiya zaki shigowa mutane kina kuka?”.
“Daddyn Naufal ne ya rufe ƙofa wai bazan shiga ba na dawo nan sai ya nemeni”.
“To saboda mi?”.
Maman Saheeba ta faɗa a harzuƙe. Mamy kam kallon Saheeba kawai take kamar ta samu tv da idonta ɗaya da rabi. Ga ciwon kai da zazzaɓi dan ƙafar nan zugi take mata bana wasa ba, ga inda ta ƙone shima yana damunta. Bata son hayaniyar da suke mata a kai, dan haka ta buɗe baki da ƙyar ta ce, “Kira min shi a waya”.
Wayar Mamyn Maman Saheeba ta ɗauka, ta lalubo number Babban Yaya ta kira. Amma mi a kashe ma gaba ɗaya. Wayar ta ajiye ta ce, “Ya kashe wayarsa. Bara na aika a kirashi”.
Aunty da abubuwan nasu suka fara daina birgeta kallon Saheeba kawai take. Ita fa gaskiya yau badan kar ace sunbar Mamy cikin wani hali ba da yau zata koma Kano. Wannan abun kunyar ya fara isarta. Ta gode ALLAH da bata da ɗiya mace ƴaƴanta biyu duk maza ne. Kasancewar Mamy ta rigasu aure har AA ma ya girma babban ɗanta sosai. Shiyyasa duk cakwakiyar nan ba sanin ainahinta tai ba..... Dawowar Maman Saheeba a fusace ya katse tunanin Aunty. Cikin hargagi Maman Saheeba ta ce, “To yama bar gidan, ance ya zuba yara a mota sun fice.....”
Zata cigaba da magana Aunty ta dakatar da ita. “Nana tunda dai dole zai dawo gidan ba sai ayi haƙuri a jirashi ba. Kunga dai ita ba lafiya ne da ita ba wannan hayaniyar ma ba so take ba muje falo.”
Badan Maman Saheeba taso ba suka fice. Mamy ta sauke ajiyar zuciya a hankali. Sai dai taji sun rufe mata ɗakin sannan ta buɗe, wayarta ta ɗauka da hannunta mai lafiya ta gwada kiran Babban Yayan itama. Amma a kashe, sai kawai ta ajiye. Saukar hannunta akan ledar nan ya sata kallon ledar, ita har tama manta da ita. Da hannu ɗayan ta buɗe, ganin an nannaɗe abu kamar box da leda ne yasa ta ajiye ledar ta fara ƙoƙarin warware box ɗin. Kwaline kuwa, koda ta buɗe cikinsa waya ce kawai ƙarama, sai takarda fara. Wayar ta ɗauka ta danna sai taga ta kawo haske. Kamar jira ake ta danna ɗin kira ya shigo. Kasa ɗauka tai har wayar ta tsinke, aka sake kira. Anan dai sai ta daure ta ɗaga, cike da ƙarfin hali tace, “Wanene?”.
“Hajjaju! Hajjaju! Kina tsoron ko kidnapper ne shiyyasa kika kasa ɗauka. To kwantar da hankalinki Mrs Aliyu Darma”.
Da mamaki Mamy ta ƙara cewa “Waye kai?”.
“Ni ba ɓoyayye bane, musamman a gareki, BABBAN ƊANKI ne da kika manta tsohon shekaru. Amma yau ya dawo ya tuna miki da kansa, da hakkinsa na ɗa dake a kanki. Maimakon na baki wahalar tunani ɗan fara duba ɗayan saƙon”.
Ajiye wayar Mamy tayi, zuciyarta na ɗan tsinkewa, ta ɗauka takardar da aka naɗe abu a ciki ta shiga kiciniyar buɗewa abinka da mai hannu ɗaya. Da taga zata sha wahala sai ta yage ta kawai da baki. Hotuna ne suka faɗo har guda biyar. Na farko ta ɗauka kamar mai jin tsoro. Hoton Maanal ne, bata wuce 14-years ba a jiki. Gefenta da ɗan sauran jikin mutum kaɗan an yage sa da alama ba ita kaɗai ce a hoton ba. Kai tsaye kuma Mamy ta gane Ajwaad ne a wajan. Ajiyewa tai batare data fahimci komai ba da farko, sai kuma kamar wadda aka haskoma wani abu a brain tai saurin sake ɗaukar hoton ta juya bayansa. Ai wani irin waro idannunta tayi, sai kuma cikin rawar jiki ta ajiye ta ɗauka na biyu, hoton Jariri ne sabuwar haihuwa a cikin zanin atamfa batik ta da, babu kaya a jikin yaron, daga gani kasan sabuwar haihuwa ne da ko awanni bai yi da haihuwa ba aka ɗauki hoto. Yanzu kam zuciyar Mamy ce ta motsa sosai a cikin ƙirjinta. Ta ƙurama zanin ido zuciyarta na tsitstsinkewa, sai kuma ta kai dubanta ga date ɗin da aka ɗaɗara a jikin hoton tamkar da gayya. A wannan gaɓar jitai tamkar zuciyar tata ma ce ta zubo cikin bakinta, jikinta kam rawa yake sosai, wayar ta ɗauka ta danna kiran Number, bugu ɗaya kuwa a ka ɗaga mata. “Wanene kai?”. Ta faɗa cikin hakki da sarƙewar numfashi.
Wata shegiyar dariya Sille yayi daga can, cike da iskanci ya ce, “Ya da ruɗewa haka Mrs Darma, ko har kin gama kallon hotunan ne duka? Idan baki gama ba ƙarasa tukunna”. Ƙit ya yanke kiran.
Idan Mamy tace bata jin kamar zuciyarta zata fashe a yanzu ƙarya take, cikin rawar hannu dana zuciya ta ɗauki hoto na uku, yaro ɗan shekara bakwai da babban mutum a gefensa da suke matsannciyar kama. A yanzu kam jikin Mamy tari ne ya sarƙe Mamy mai ƙarfi, ta kalla ƙofa da sauri tana danne bakinta domin hana tarin kanta na wani irin bubbugawa kamar ana dukan ƙarfe da ƙarfe. Lips ɗinta na rawa-rawa ga hawaye na gudu ta furta. “Ju..j... Junaid”. Hoton ya suɓuce a hannunta ya faɗi, tamkar mai tsoron taɓa wuta ta ɗauka na ƙarshe. Matashin saurayi ɗan shekaru kusan ashirin da biyar ne a jikin hoton, tabbas ta taɓa sanin fuskar, amma ta manta a ina ne, kuma yaushe ne??...
Dai-dai nan kira ya shigo wayar. Jitai tana tsoron ɗaga ma kiran a yanzu harya tsinke aka sake kira na biyu. Zuciyarta dake bata shawarar ta ɗaga taji wanene shi? A ina ya samo wannan hotunan taci ƙarfinta. Ɗaukar tayi sai dai ta kasa magana. Daga can Sille dake jiyo fitar numfashin Mamy a sarƙe cike da shaƙiyanci ya ce, “Nasan kin gama kallon hotunan nan duka zuwa yanzu Mrs Darma? Nasan kuma kin gane wasu a ciki, musamman Surukarki, Tsohon zumanki, da Jaririn nan”.
Sosai jikin Mamy ke ƙara ƙarfin rawa, har tana buge ƙafarta mai ciwo, azabar data ratsata ta sata sakin ƴar ƙara saboda ƙafarta. Daga can Sille dake iya jiyota ya ce, “Relax Mrs Darma, karki ruɗar da kanki. Dan ban baki hotunan dan ki ruɗe ɗin ba. Na tabbatar dukansu suna tare da alamar da zaki tunasu. Idan kuma baki tuna ɗin ba zan baki lokaci ki tuna su daga nan har zuwa 1 week sannan ki banbanta su da tunanin miya alaƙantasu a waje guda, bayan kowanne kinyi AJIYA A DUHU ne a mabanbanta GURBI. Na barki lafiya Mrs Darma”. Ƙittt wayar ta yanke. Ba ƙaramar zabura Mamy tai ba domin son dakatar da shi, amma ina ya kashe, hannunta na rawa tai ƙoƙarin sake kiransa wayar amma switch off. Yunƙurawa tai zata tashi ruɗani ya mantar da ita halin da take a ciki azaba ta ratsata. Ai tuni ta saki wayar tana sakin wata azababbiyar ƙara. Wuff Haule ta shigo ɗakin kamar wadda take jiranta dama. Koda yake jiran nata take a ƙofa kam.
Itace ta riƙeta dan ƙoƙarin faɗowa a gado take. Cikin dabara kuma tana tattare hotunan nan ta kwashe da hannu ɗaya, sai da ta kwantar da Mamyn sannan ta duƙa ta ɗauka wayar dake a ƙasa dan idon Mamy a rufe suke sai zufa take. Wayar da hotunan Haule ta tura ƙasan gadon Mamy bada nisa ba sannan ta miƙe tana faɗin, “Hajiya bari a kira su Aunty”. Kafin ma Mamy tai magana Haule ta fice da sauri.....


Fitar Haule dai-dai da shigowar AA da Fawzan sashen. Dan kiran da Oum tai masa ya sashi dole ya baro sashensu. Su Shahidah na shigowa sashen shi kuma yana sakkowa daga upstairs. Cike da gulma suka zuba masa ido, sai da yay gab da gama sakkowar suka fuske kowanne na mamaki a zuciyarsa, dan kaga AA a fuska zaka rantse bazai iya kallon mace ba saboda jin kai. Amma munafukin yama ƴar ƙanwarsu walmakalifatu yanzu ya fito yana wani basarwa.
Aunty Sakina kawai ya gaisar, itama dai Amaal dake gimtse dariya ta gaishesa. Ciki-ciki ya amsa zai wuce dan ya fahimci munafuncin dake a fuskokin su musamman Shahidah da Amaal Shahidah ta ce, “Oh ni bazaka gaisheni ba”. Harara ya zuba mata, cike da baƙar magana ya ce, “Sai kin ƙara girma”.
Dariya Aunty Sakina ke musu, hakama Amaal ƙasa-ƙasa take tata. Shahidah tai ƙwafa ta ce, “Haka kace ko, zako kasan na girma yau kuwa, dan da Auta zan wuce har sai kazo ka durƙusa ka gaisheni”.
Kallonta yay kamar zai yi magana sai kuma yay shiru, a duniya babu wanda ya saka shi gaba kamar mutane uku, Yaya Fawzan, Shahidah, Rafeeq. Ficewa yay batare da yace mata komai ba, sai kuma ya saki murmushi yana cizar lips dan bai ƙyaleta ba, saboda Aunty Sakina da yake jin nauyi kawai ya zaɓi yin shirun yanzu, amma taci bashi. Sashen Oum ya nufa gaisheta ya samu ƴan kano basu tafi ba suma ya zauna suka gaisa shine Oum ke sanar masa Mamy babu lafiya. Ya fito da nufin zuwa duba Mamyn suka haɗu da Yaya Fawzan. Zai fara aikin tsokanarsa shima yaja hannunsa yana faɗin, “Fara rakani na duba Mamy mu dawo zan iya da kai kaima”.
Dariya Fauzan yayi, bai musa ba suka nufi sashen Mamyn. Shine suna shigowa suka samu Haule na sanar ma su Aunty halin da Mamyn ke ciki. Ba ƙaramin tashi hankalin AA ya shiga ba da ganin halin da Mamy ke ciki ba. Nan fa ya shiga tambayar Fawzan accident sukai. Babu wani alamar ruɗewa irin ta AA ɗin a tare da Fawzan ya ce, “Aa sunce ta faɗo ne daga stairscase jiya da dare......” nan dai yay masa bayanin komai.........✍️
AJIYA A DUHU


85


........Zama AA yay kusa da Mamyn ya share mata hawayen da yaga suna silalo mata, ga jikinta na rawa. A mamakin kowa sai ta buɗe idanunta tana kallonsa, sai kuma ta sake runtse idanun dan abinda ta jiyo jiya ne ke rige-rigen dawo mata a cikin kunne saboda kallon fuskarsa da tayi. Cikin rawar lips muryar na fita da ƙyar zuciyarta na ƙuna ta ce, “Ajwaad ku kaini asibiti ƙirjina”.
ALLAH sarki rayuwa, ɗa mai jinƙai daban yake komai wahalar da kake bashi a rayuwa. Mamy bata gama rufe baki ba AA harya miƙe, layin RK ya fara ƙoƙarin nema. Babu jimawa kuwa ya ɗaga, zai fara tsokanarsa shima AA ɗin ya katsesa da faɗin, “Rafeeq kana ina ne?”.
Ɗan jim RK yay daga can, sai kuma ya nisa ya ce, “Ina asibiti. Miya faru?”.
“Ambulance! Ka turo Ambulance yanzu ta ɗauki Mamy.”
Murmushi RK yay mai sanyi, a ransa yay hamdala dan dama abinda yake jira kenan tun ɗazun, daurewa kawai yake yi amma hankalinsa gaba ɗaya nakan halin da Mamy ɗin ke ciki. Sai dai yasan bazai samu abinda yake fata ba sai AA yaje yaga halin da take a ciki saboda wasu dalilansa. Cikin abinda baifi mintinan ashirin ba Ambulance ɗin ta iso, zuwa lokacin harsu Oum na'a sashen dan abun kamar wani magic jikin Mamy ɗin ya rikice alamar jininta ya haura sama ko gani idannunta basa yi. Su Abah sun fita tun ɗazun, hakama Babban Yaya bai dawo ba. AA da Yaya Fawzan da kansu suka sakko da Mamy ƙasa, sannan aka sakata a abin ɗaukar mara lafiya aka fita da ita. ALLAH sarki Oum baiwar ALLAH, itace ta shiga kusa da Mamy ɗin. Su kuma su AA suka shiga motar Fawzan. Saheeba ma ta ɗauka su Mamansu suka bisu....


_________★


Su Maanal basu san mike faruwa ba. Tana can da ƴan uwanta dan ba ƙaramin farin ciki tayi da ganin yayun nata ba, duk da yanda suke tsokanarta musamman Amaal ita dai tanata ɓoye fuska, har suka gaji suka barta, sun baje mata kayan daɗin da suka kawo mata kowa na wani tattalinta. Sai Ammie da suka kira ta video call suka sha hira. Maanal na kuka Ammie nayi saboda farin cikin yanda abubuwa suka canja, baiwar ALLAH ji take kamar tai tsuntsuwa tazo Abujan ma. Albarka da addu'a babu irin wadda bata jerama AA ba yau harma da Maanal. Sunyi hirarsu cike da farin ciki da shaƙuwa. Maanal nata zubama Ammie shagwaɓa wai tana son ta tazo Kaduna idan ta warke sai ta dawo.
Ammie dake murmushi ta ce, “A'a Auta kiyi zamanki a ɗakinki kinji, ko sashen Aunty ban yarda ki koma ba balle Kaduna. Kefa yanzu kin girma, kiyi zamanki gidan aurenki kima mijinki hidima. ALLAH yay muku albarka ya baku zuri'a mai albarka kinji. In sha ALLAHU zanzo bikin Fawzan ai nan da sati uku”.
Murmushi Manaal tai mai sanyi, cike da shagwaɓa ta ce, “Amma Ammie a wajena zaki kwana ko?”.
Dan kawai Ammie ta kwantar mata da hankali sai tace eh. Aiko hakan yama Maanal ɗin daɗi sosai. Bayan sunyi sallama da Ammie suka koma hira a tsakaninsu, hirar da gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne akan batun fyaɗen nan, Amaal ta sanya Maanal gaba da sabuwar tsokana. Tun tana ƙyaleta harta fara ramawa, suka fara tsiyar tasu ta sako-da-sako.
Daga ƙarshe suka yanke shawarar zuwa Giro da babbar salla. Dan Maanal ta rantse sai taje ta maidama Gwaggo da kaf mutanen gidansu murtani babu fashi. Yanda tayi ɗin ya tabbatar ma su Amaal ƙanwarsu ta dawo ainahin Maanal ta shekarun baya data mutu. Aiko ɗari bisa ɗari suka bata goyon baya akan wannan ƙudirin nata, sun kuma roƙi Aunty Sakina kada ta gayama Ammie dan sai sun dawo zasu sanar mata karma ta hana su. Ta tabbatar musu bazata faɗa ba, kuma tana goyon bayan zuwan nasu itama....
Sai da sukai Magrib sukai ƙoƙarin tafiya, a lokacin ne Hajiya Shuwa ta shigo yima Maanal gashi take sanar musu ai an tafi da Mamy asibiti jikinta ya rikice. Mamaki ya kama Maanal dan sai lokacin ma ita take sanin Mamyn bata da lafiya gaba ɗaya...


★Matuƙar sanyi jikin Auntyn su Mamy yayi da ganin yanda RK ke tsaye akan al'amarin Mamyn tunda suka iso asibitin, dan cikin ƙanƙanin lokaci likitocin da zasu dubata sun rufu a kanta. Sai taita kallon Maman Saheeba da tace bata yarda a kira Rafeeq ya duba Nuratu ba tun a jiyan. Itama kuma Mamyn da akace a kira Rafeeq ya dubata da safe catai bata yarda ba. Ta maida kallonta kan Oum datai shiru damuwa kwance a fuskarta, AA da Fawzan sun sakata a tsakkiya suna lallashi. Sai Auntyn taji kamar ta fara jin kunyar kanta. Anya kuwa babu gyara akan al'amarin su na ƙin baiwar ALLAHn nan Hajiya Fateema. Koba komai fa itace sanadin shigiwar ƴar uwar tasu a wannan daular. To wai miyema aibunta da suke zaginta? Ƴar uwarsu fa ce da kanta ta ɗauka yaran ta bata..... Wannan tunani shine danƙare a zuciyarta har RK ya fito yana sanar musu karaya ce fa a ƙafar Mamy, sannan akwai ƙonewa a jikinta...
A tare Oum da Ya Fawzan sukace,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login