Showing 66001 words to 69000 words out of 218311 words
Chapter 23 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
buɗewa a kanta, batare daya amsa maganar ƙarshe ba ya ce, “A ƙafa zamuje dan jikinmu ya warware da zaman jirgi”. Yana gama faɗa yaja hannunta kawai suka cigaba da tafiya. Harga ALLAH jitai zuciyarta ta raunana. Sam bata son ganinsa a damuwa. Hankalinta tashi yake. Musamman yanzu data fahimci irin wannan yanayin yana samosa ne daga Mamy. Dan lokacin da zasu taho ta lura da kallon gargaɗin da Mamy ke masa, wanda ta tabbatar ko rantsuwa tayi babu kaffara akanta ne game da wannan tafiyar da babu yanda zatai ta ya hana yinta da ita. Cike da son lallashinsa ta matsa jikin hannun nasa sosai ta kwantar da kanta. Cak ya tsaya yana kallonta, itama kallon nashi takeyi idanunta na ɗan tara ƙwalla. Kamar mai raɗa cikin motsa lips ɗinta a hankali ta ce, “Baka ƙyau idan kana fushi, Please kayi murmushi”.
Idanunsa dake wani kalar raunana a cikin nata ya janye slowly, sai kuma yay ɗan murmushin gefen baki a taƙaice. Murmushin itama tayi, tare da faɗin, “Thanks”. Komai bai ce mata ba suka cigaba da tafiya. Duk inda suka gitta binsu ake da kallo musamman saboda shigar jikinta da ta zamewa wasunsu baƙon abu. Kai da abu yakai ya kawo ma har tsaidasu ake dan ayi hoto. Sai dai AA yaƙi bada haɗin kai dan sai yay kicin-kicin da fuska, ko kuma ya hana a tsaya ta gefen Maanal ɗin.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣2️⃣
______________
........Sunzo dai-dai gidan wani abinci ya tsaya, kallonta yay murya a ƙurya ya furta, “Kina jin yunwa?”.
Dan kawai kar yaga ta gwalesa ta jinjina masa kai, dan bata wani jin yunwa ita kam. Ciki suka shiga, Maanal tabi wajen da kallo tana jinjina tsaruwarsa da ƙawatuwarsa. Sun kuma samu tarba ta mutuntawa da akema kowanne customer. Wajen zaman daya dace dasu aka basu, tare da takardar da tsare-tsaren abincin ke ciki. Shine ya amsa yana dubawa, dan su dai komai nasu da yarensu suke rubutawa. Hajjaju Maanal kuma ba'a iya Chaines ba. Shi kansa mamakin sanda ya iya yaren takeyi, duk da dai bata da tabbacin ko ya iya sosai-sosai ko sama-sama ne. Tana nan ta shagala a tunani har aka fara kawo abubuwa ana jera musu. Ganin yanda take bin komai da kallo sai a sannan AA yay magana. A taƙaice ya ce, “Komai dake anan Halal ne”. Ajiyar zuciya ta sauke kamar dama abinda takema waswasin kenan. Sai kuma ta ce, “Amma to musulmai ne masu wajen?”.
Kansa ya jinjina mata, dai-dai waiter ɗinsu na sanar masa an kammala. Ya jinjina mata kai cikin harshen Chaines yace, “Thanks you”. Sai da tabar wajen sannan ya maida hankalinsa ga Maanal yana ƙoƙarin tura mata abinda yasan zata iya ci a gabanta. Tare da cigaba da amsa mata maganarta. “Musulmai ne ita da mijinta dake da wajen”.
Kai Maanal ta jinjina, sai kuma ta saki murmushin daya sashi tsayawa yana kallonta. Tana ɗagowa suka haɗa ido tai masa alamar (miye) da ido tana ɗaure fuskar. Kansa kawai ya ɗauke ya fara cin abincin a nutse. Itama fara ci tayi, ba laifi da daɗi, sai dai test ɗin akwai banbanci mai nisa tsakaninsa da namu na gida. Haka dai ta daure taci batare da yin ƙorafi ba. Shi ko jira yake tai ƙorafin dan yasan zatayi, da batayin ba kuma yayi mamaki amma bai ce komai ba. Sun ɗan jima a gidan abincin kafin su fito, yanzun ma a ƙafa suka cigaba da tafiya, sai dai tafiyan bai nisa ba suka isa wani ƙaton Mall mai ƙyawu sosai. Dan bayan wajen shopping akwai wajen wasan yara, da ɓangaren games na manya, akwai wajen hutawa na masoya, kai da abubuwa daban-daban. Sudai wajen kasuwar suka nufa, ɓangaren tufafi ma. Anan ɗin ma sun sha kallo, dan Maanal har sai da taji kallon ya fara mata yawa ita kam. Dan haka ta ƙara maƙurewa jikin AA. Shi da kansa ya shiga zaɓa musu kayan daya kamata, na fita da na shan iska da sai dai a saka a cikin ɗaki. Sai jackets musamman ita duk da yasan ba garin sanyi bane sosai sai irin yamma haka da safiya, a yanzu haka ma yayi mamaki da batai ƙorafi ba, koda yake ƴammar bata gama yi ba rana ce da ɗan sauran zafi kaɗan. Hannunta yaja ɓangaren underwear. Maanal tai tsuru-tsuru kunya duk ta baibayeta. Cike da neman magana ya ce, “Anan aikinki ne ke zaki zaɓa mana Besty”.
Cikin ɗan waro idanun ta ce, “Mi ɗin?”.
Da ido yay mata nuni da underwear ɗin. Ai ba shiri ta juya baya tana faɗin, “Ni ALLAH ka daina min irin haka baida ƙyau”.
Ɗan murmushi ya samu kansa da yi, sai kuma ya ɗan leƙa fuskarta. Da sauri taja mayafinta ta rufe fuskar. Abinm ma sai ya bashi dariya. Amma dai bai dara ɗin ba ya barta yaje yana zaɓa musu. Nashi ya fara zaɓa a ɓangaren maza. Sai kuma ya koma na matan. Dan tsabar son ƙureta parckeg na b&p ya ɗakko yazo gabanta, kamar ba daga bakinsa maganar ta fito ba ya ce, “Besty wane size?”.
Ya subahannallah, mutum nan dai so yake ya kasheta kafin su bar ƙasar mutane, ai da gudu-gudu ta nema barin wajen amma ya riƙoto, hannun daya riƙetan ta kama ta ɗan ciza. Babu shiri ya saketa yana faɗin, “Ouch! Ke dai muguwa ce”.
Gwalo ta masa tabar wajen. Cikin ɗan ɗaga murya kaɗan yace, “Zamu koma masauki ai zaki biya diyya yarinya”.
Cak ta tsaya, shi kuma ya juya abinsa yana murmushi ya zaɓa mata wanda ya tabbatar zasu mata duk da dai ƙiyasi yayi da zuciya......
_________★
Yau RK ya kamo hanyar Abuja domin dawowa kan aikinsa. Kasancewar yana son ɗaukar Najma a Zaria ta mota ya biyo. Aiko bai ɓata lokaci a Zaria ɗin ba dan itama Najma ɗin a shirye take tsaf shi kawai take jira. Alhamdullah ƙarfe biyar a ƙofar gidan su AA tai musu. Lokacin da motar RK ke shigowa babban harabar gidan Saheeba da Nuratu da Mamy na zaune suna shan iska. Sai su Naufal dake yawo a motocinsu ƙanana shi da Anum. Oum bata nan tana maƙota gidan Hajiya Shuwa. Dan tunda ta dawo bata shiga ba sai yau. Nibras da babban yaya da Fawzan kam basu dawo aiki ba. RK na kallon irin kallon ƙurullar da suke bin motar tashi da shi, dan basu santa ba sabuwa ce dal daya ɓare saboda angwanci. Tinted glass ne shiyyasa basa iya ganin kowaye. Najma ce ta fara buɗewa ta fita, cike da ɗoki ta ƙwala kiran sunan Naufal da Anum. Atare yaran suka juyo motocin nasu kowa na rige-rigen isowa saboda ganin Aunty Najman Zaria. Suna isowa kowa ya fito suka rungumeta. RK na fitowa sukai arba da shi suka saketa sukai kansa, gaba ɗayansu ya ɗaga a tare yana dariya. Dai-dai nan motar Fawzan ta shigo gidan, kamar haɗin baki babban Yaya biye da shi. Sai a lokacin Saheeba da Nuratu suka taso suna faman taɓe baki dan Mamy ce tace suje kar ace basu tarbesu ba.
Wani sassanyan kallo Najma da Fawzan sukama juna, duk da kuwa tare yake da Nibras a motar. Koda suka fito cikin ƴar basarwa ya ɗaga Anum dake masa oyoyo yana kallon Najma ƙasa-ƙasa yace, “Ba gaisuwa love?”.
Da sauri ta kalla gefensu tana fatan kada wani yaji, sai taga hankalin kowa nakan Uncle Rafeeq. Maimakon ta fara gaida Fawzan sai ta fara gaishe da babban yaya. Cike da kulawa da ƙauna irin na ƴan uwantaka da aka san duk wani jinin Darma da ita yake amsa mata yana tambayar Mamanta da sauran ƙannenta. Ta ce, “Duk kowa lafiya yake suna gaishe ku yaya”.
“Muna amsawa. Amma nan za'a mana azumi ba?”.
Kanta ta jinjina masa tana murmushi. Shima murmushin yayi da sanya mata albarka, sannan ya maida hankalinsa ga RK da suke gaisawa da Fawzan. Itama sai lokacin Najma ɗin ta gaida Fawzan ɗin. Amsa mata yay normal kamar yanda ya saba a baya. Ta juya ta gaida Saheeba. Tasan Nuratu, sai dai basa shiri, dan Nuratu fa ita bata cika zaman lafiya da mutane ba musamman idan ta fahimci ka fita to in sha ALLAHU kai ka zama abokin gabarta. Ƙin gaida Nuratun tayi ta juya ga gaida Nibras. A daƙile ta amsa mata, wannan ita kuma halinta ne, dan haka Najma bata kawo komai a ranta ba.
Inda Mamy ke zaune suka nufa, fuskar RK da murmushi yake gaisheta, yayinda Najma taje ta rungumeta tana faɗin, “Oyoyo Hajiya Mamyn mu”.
Da ƙyar Mamy ta haɗiye abinda ta tokare mata zuciya, dan ranta a ɓace yake tun tafiyar su AA ta jiya. Gashi har yanzu basu kirasu ba balle ta tusa masa gargaɗin dake a ranta. Sun gaisa cike da mutunta juna ita da RK, kafin ta maida hankali akan Najma. A kuma lokacin ne Oum ke shigowa gidan. Wayyo tuni Najma ta saki Mamy ta sheƙa da gudu ita da su Naufal wajen Oum ɗin. Suma su Babban Yaya da Fawzan da RK ɗin duk wajen Oum ɗin sukayi. Haka suke mata ko yaya ta fita data dawo duk su zagayeta kamar wasu yara. Da mamaki Oum dake shafa kan Najma tana rungume dasu Naufal tace, “Lallai yau ango ne a Abuja? Ai mun zata kayi ƙaura ka koma Kano”.
Dariya RK yayi da faɗin, “Dafa za'ace nai hakan ai da kun min gata Aunty”.
Dariya Babban Yaya da Fawzan suka sanya, yayinda Oum ta riƙe baki. Babban Yaya yace, “Uncle ai babu damuwa barinka zamuyi ka koma abinka”.
RK yace, “Yauwa Son kuyi taimako, ni dama za'a saya min ticket zuwa bayan isha'i ina Kanon dabo abina ai da yafi”.
Da wannan dariya suka shige sashen Oum. Bayan su Mamy sun mata sannu da dawowa. Sai dai su basu bisu ba, sai ma takaici ne daya saka Mamyn wucewa sashenta tabar Nuratu da Saheeba anan suna gulma. Nibras kuwa tayi sashensu dan yanzu ba zuwa sashen Oum ɗin take ba tunda su AA suka bar ƙasar.....
Najma na baza idon son ganin Maanal Oum ta sanar mata ai basa ƙasar, jiya suka wuce Chaina amma kwana goma zasuyi zuwa sati biyu su dawo. Sam Najma bata so hakan ba. Amma ta musu addu'ar dawowa lafiya.
Shi ko RK dariya yay da faɗin, “Ɗanki ya samu lafiya dai, harda tafiya honeymoon”.
Itama dariyar tayi, ta ce, “Aiki fa sukaje Rafeeq. Honeymoon ɗin nan ko za'aje shi sai dai bayan salla in sha ALLAHU. Ni nazata da Nuwaira zaku taho nan ɗin”.
“Wlhy naso hakan Mah-mah ce ta hana, wai na bar mata yarinyarta sai bayan salla tunda bata jin daɗi”.
Oum tace ALLAH ya bata lafiya. Fawzan cike da tsokana yace, “ALLAH ya raba lafiya Uncle”.
Filo RK ya ɗauka ya jefa ma Fawzan, ya miƙe ya fice yana dariya. Shima RK da Babban Yaya miƙewa sukai suna dariyar suka fita dan lokacin sallah yayi. Oum dai nata murmushi, dan ita kanta da RK ɗin yace Nuwaira bata jin daɗin abinda zuciyarta ta kawo mata kenan har an samu ciki. Addu'a tai musu tare da miƙewa ita da Najma sukai ciki domin yin sallar magrib tana addu'ar ALLAH ya kaita randa zataga na AA da Fawzan haka..
Bayan sallar isha'i sukai zaman cin abinci, anata hira cike da farin ciki dan harda Abah duk da a sashen Mamy yake yau. Amma ganin ɗan uwansa yace anan zaici abinci shima. Saheeba da Nuratu dai suna sashen Saheeba ɗin sun ƙulle suna tsogume-tsogume, dan tunda AA ya wuce ko sashen Mamyn ma Nuratu ba son zama take ba, koda yaushe tana nane da ƴar uwarta ne. Itako Nibras tana sashenta, abin duniya ya isheta. Tun juya take dakon jiran jin AA ya kira waya amma shiru kake ji. Har gwada number sa da yake amfani da shi in yaje Chaina ɗin tayi amma bata shiga ba. Dama ta sata ne a wayar Fawzan, ta adana da wata ɓoyayyar number ɗinta data tanada dan AA amma tunda ta sai layin ta kasa kiransa balle masa ko text ne saboda tsoro. Ana cikin hirar Fawzan da Najma suka saci jiki kitchen kamar masu tattare kaya, anan sukai ɗan sabuwar gaisuwa da hira sama-sama. Gudun kada a gane su suka dawo. Shi dai RK ma dariya suke bashi, dan yanzu kam ya sake tabbatar da abinda yake hasashen..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣3️⃣
______________
......Sai da AA ya tabbatar ya tura dukkan siyayyar tasu masaukinsu sannan. Maimakon wucewa gida wani garden ya kaita. Wajen ya matuƙar birge Maanal. Anan sukai salloli suka huta har zuwa duhun dare kafin suka fito. Ganin yanda take naɗe hannaye a gyale saboda sanyi ya sashi cire jacket ɗinsa. Gabanta ya dawo ya tsaya, hakan yasata ɗago idanunta ta kallesa. Shima kallon nata yake. Cikin sanyin murya idanunsa a cikin nata ya ce, “Sanyi?”.
Kanta ta jinjina masa tana ɗan lumshe nata idanun dan bazata iya jurar kallon nan nasa ba. Shima nasan ya lumshe ya kuma buɗe a hankali. Sai kuma ya dafa kafaɗarta ya matsota jikinsa sosai. Harta gama sallamawa rungumeta zai yi sai taji saɓanin hakan. Jacket ɗin tashi ya rufo mata ta baya, sannan ya ɗan matsa ya gyara mata ita a kafaɗinta sai ta rufeta ruf. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, sai kuma ta ɗan kallesa ta kauda idanun ta ce, “Kaifa? Riganka fa baida wani kauri”.
“Karki damu bana jin sanyi”.
Ya faɗa ƙasa-ƙasa yana kama hannunta suka cigaba da tafiya. Yanzun ma a ƙafa suka nufi hanyar gida, yasan ta gaji, amma gara suyi hakan dan in sun kwanta su samu damar yin barci da ƙyau. Sosai birnin Shanghai ya ƙara burge Maanal. Tana mamaki da jinjina fasahar mutanen nan wajen iya tsara gine-gine dogayen gaske. Ga wutar lantarki da ba'a maganar ɗaukewarta ma. Akan titi fa suke amma haske tako ina abin zabbirgewa. Suna isowa hotel ɗinsu taji zuciyarta ta fara rawa. Amma sai ta dake tana mai roƙon UBANGIJI hana tabbatuwar abinda take ma tsoron. Sosai tayi mamakin ganin dukkan shopping ɗinsu a ƙofar ɗakinsu. Card ɗin ƙofar yasa ya buɗe, kafin yakai duƙe ya ɗiba kayan duka ya shiga da su, ita kuma tabi bayansa. A hankali ta zare rigar tasa daga jikinta kamar bata so, dan wani irin nutsuwa da sanyin zuciya ƙamshinsa ke sakata. Zama tayi akan kujera, shi kuma ya shiga ƙoƙarin rage kayan jikinsa. Sai kawai ta duƙar da kai ƙasa. Yana lure da ita, sai dai baice komai ba ya gama ya wuce bayi. Ya ɗan jima kafin ya fito, nan ma bata kallesa ba. Tadai fahimci wanka yayo kodan mayataccen ƙamshin shower gel daya cika ɗakin. Shi ko hankalinsa kwance yay shirin barcinsa da ɗaya daga cikin kayan da sukai shopping dan harda na barci. Cike da godiyar UBANGIJI yakai zaune a bakin gadon yana ɓalle murfin robar ruwa yakai bakinsa. Sai da yasha kusan rabi sannan ya dubi Maanal dake zaune kamar wata marainiya. Kansa ya ɗan girgiza, kafin ya ajiye ruwan babu wasa a muryarsa ya ce, “A zaune zaki kwana kenan?”.
Kanta ta girgiza, sai kuma ta mike batare data kalla inda yake ba. Wajen kayan shopping ɗin nasu ta nufa, tunda a gabanta ya ɗauka kayan barcin, a kayansu kuma ɗazun taga bai ɗakko mata nataba dan iya kaya kawai ya zubo mata kala shida. Sai b&p ɗinta ƙwara ɗaɗɗaya datai amfani da su ɗin nan da zasu fita. Cike da nuƙu-nuƙu ta ɗauka duk abinda take buƙata, ta wuce bayin sum-sum kamar za'ace ar ta fece. Shi dai ta ƙasan ido kawai yake kallonta, a ransa ko dariya yake da mamakin mutuwar bakin tsiwa. Ta jima a bayin dan shi har ma barci ya ɗaukesa sannan ta fito, dama kuma tayi zamanta ne dan har yay barcin. Daɗi kuwa taji sosai maganin yayi ɗin, kayan data cire ɗin ta ajiye, sannan ta zare ribbon ɗin kanta ta tifke gashin, veil ɗinta na abaya ta ɗauka ta ɗaura a kan, sannan ta juya tana kallon ɗakin. Bayan gadon babu wani abu da zata iya kwantawa akai, dan su